Showing 441001 words to 444000 words out of 467220 words

Chapter 148 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12115

tamkar ma da gayya suka ringa baibayeshi, ya barta a zaune ya tafi can da friends Winsa suna ta having fun dan ta kasa sakewa ganin kanta take kamar wata Alien cikin mutanen dake gurin. Da taga kamar ma ya manta tare suke kawai ta sulale ta koma Wakin su, seda dare ya raba kafin ya dawo lokacin tasha kuka harta godewa Allah ta ha?ura.

Tana kwance tayi lamo ya shiga Wakin ya ringa kiran Babe ta masa banza tana jinsa ya gama abinda zeyi ya kwanta a bayanta be wani ja lokaci ba bacci yayi awon gaba dashi alamar ya gaji, ansha kayya kayya ai dole ayi bacci bata san sanda ta fashe da kuka me sauti ba, wato tahowar da tayi baya damesa ba, be koyi tunanin yabiyo bayanta ya tabbatar ta koma Wakin lafiya ba se sannan yaga dama ya dawo tunda kuma babu abinda yake bu?atar ta masa shiyasa be tasheta ba yayi kwanciyarsa. Ta ringa kuka harda shashshe?a abinda ya farkar dashi daga bacci ya tsaya yana kallonta for some seconds as if trying to figure our the cause of kukan nata. A hankali ya jata jikinsa ta fizge ta sauka daga gadon, a maimakinta kawai taga ya juya harda jan duvet ya rufe har kansa aiko tayi zaman dirshan ta shiga rera kuka kamar me tilawa wani abu me kama da nadama auransa ya ringa shigarta.

A shekara takwas da tayi da Ahmad ba zata taSa tuna ranar daya Sata mata rai cikin saninsa ba balle har yaga tana kuka a dalilinsa kuma ya juya mata baya yayi bacci. Ta san Ahmad da Jay sun banbanta ta ko ina, babu haWi a kamewa da kuma halayyarsu amma tayi tunanin yanda yake nuna soyayyar ta tana gaba da komai nasa bazeyi mata irin haka ba. Koda yake itama son ne ya rufe mata ido harta kasa hango bawai iya kacin hajiya ce zata iya zama tasgaWo cikin zamantakewarsa ba harda nasa halayen da suke ba?i a gurinta. Ta yaya zata iya rayuwa tana kallonsa matan waje basuda birki dashi idan tayi magana kuma yace fans ne, su fans basu san boundary ba? Haka ta raba dare tana kuka, gashi bata da waya balle ta kira wani a gida taji sanyi a ranta. Tayi tunani ma yanzu wa zata kira tayiwa ?orafi halinsa ai se ta zama laughing stuff.

A inda take zaune bacci ya kwasheta bata farka ba seda rana ta fito sosai ta ringa mamakin yanda akayi ta koma kan gado harta lulluSa. TaSe baki tayi data tuna ?ila shi ya mayar da ita, abinda ya mata jiya ya goge duk wani farinsa da take gani dan gara ace ya ribga mata wula?anci daga shi se ita ya mutuntata a waje tasan ai da Fatiyyah ce bazeyi mata haka ba ?ila. Haka tayi wanka tayi sallah ta zauna zuciyarta cike da ?unci. Wato dan ba?in hali ko tashinta tayi sallah beyi ba ya fice abunsa. Tana nan zaune ta rafka tagumi tayi nisa a tunanin rayuwar da ?addara ta jefota ya shiga Wakin, seda ya tsaya gabanta kafin ta kalleshi sau Waya ta Wauke kai gefe. Babu yabo babu fallasa yace mata
"Kin tashi kenan?" Tayi shiru bata amsa ba se ?o?arin tashi daga gurin data farayi hakan ya hasalashi kuwa ya balbaleta da masifa yana cewa
"Kin san bana so ina yiwa mutum magana yayi shiru upon that kuma you want to walk out on me ni sa'anki ne Afeeyah? Yaushe na fara wasa dake?" Seta koma ta zauna ta haWe kai da katakon gado ta fasa masa kuka, ransa ya ?ara Saci yace

"Saboda jiya kinyi tafiyanki bance miki komai ba shine har kika samu daman yin fushi kinawa mutane kuka. Were you in ur right senses da zaki fito daga gurin nan ke kaWai? Kin san irin mutanen da suke a nan baki san zasu iya cutar dake ba?" Ta Waga kai fuska jage jage da hawaye ta kalleshi tace
"Idan sun cutar dani kana da matsala da hakan ne? If you truly care me yasa baka biyo baya na ba? Ka tsaya can gurin matan banza da suka fini muhimmanci a gurinka sannan kazo kana yi mun ihu akai meye damuwarka dani? Kuka ka bani wayana ni tafiya zanyi. ka raboni da kowa nawa zaka kasheni da ba?in ciki to bazan zauna ba tafiya zanyi" ta faWa tana mi?ewa tsaye, ?afa ya sa mata ta tafi Allah ya taimaketa ta faWa kan gado ko a jikinsa ya nunata yana cewa

"In dai zaki iya gamsar da zuciyarki ta yarda ban damu dake ba go ahead Afeeyah kiyi duk abinda kika ga ya miki amma koda wasa karki kuskura mu sake fita tare ki taho ki barni bana so" ya mi?a hannu ya Wagota gaba Waya zuwa jikinsa. Tana kuka tamkar ranta ze fita tace
"Ni gida zan koma, just 1 week amma kullum se ka saka nayi kuka. Har na gama rayuwata da Ahmad ban taSayin kuka a gidansa ba se dai na daWi ko rashin lafiya amma kai fa? Daga zuwana zuciyata ta fara rasa sukuni, ni wlh ba irin wannan rayuwar nayi hasashen samu a gurinka ba" yanda yake kallonta yasa tayi shiru taci gaba da kukanta a hankali ya saketa ya juya yana cewa
"Se ki koma gurin Ahmad Win ya cigaba da baki irin rayuwar da kika saba da ita" ya buga mata ?ofa har seda ta tsorata. Gaba Waya kuma se jikinta yayi sanyi, bata manta ba daren daya fara kasancewa da ita bayan sunyi sallah ya ri?e hannunta yace mata

"Ina da kishi sosai Aafeeyah and when it comes to you bazan yiwa kowa uzuri ba. Nasan kinyi wata rayuwa a baya kafin wannan, i want to ask you for a favour idan zaki iya ki manta komai. Bana so koda wasa ki kawo mun wata magana data shafi zamantakewarki ta baya, ni ba tsohon mijinki bane karki taSa tunanin daidaita ni dashi. Halayyarmu, daSi'un mu da komi sun banbanta. Bazan taSa iya baki rayuwa irin tasa ba amma nayi miki al?awari zanyi ?o?ari na baki rayuwar da ba zakiyi kukan rashin komai ba. Kiyi ha?uri dani kuma kiyi mun uzuri duk sanda ki kaga na kauce kuma ki ringayi mun addu'a in sha Allahu komi ze daidaita komai ze wuce duk da nasan rayuwa ba zata koma yanda take a baya ba amma in sha Allahu zanyi ?o?arin gurin sauke nauyi biyu da yake akaina, wanda Allah ya Wora mun da kuma amanar da Yah Ahmad ya bani akanku. Yasan rayuwa ta dake ta baya kuma yace har a lahira ya bar mun ke, ina fatan dani dake mu tarar dashi da alkhairin da zeyi alfahari da tarayyar mu bayan ransa".

A lokacin ta shiga ruWani matu?a ta yanda yace wai Ahmad ya san ala?arsu ta baya, yaushe? Waya gaya masa? Sannan tsayin wanr lokaci yake kallonta da abin?. Data tambayeshi ce mata yayi shima be sani ba, sanda yayi confessing masa kunya da nauyi suka saka ya kasa tambayar sa yanda akayi ya sani but it doesn't matter any more, ya rigada ya wuce ba kuma yasan duk abinda ze ringa dawo masa da rayuwar baya she should only fucus on there future not what has already passed. Akan haka suka gina daren cikin soyayya da al?awarurrukan kasancewa da juna komai wuya komai daWi har bakin rai se gashi sati Waya kacal table ya fara shaking.
Ta share hawayen fuskarta jiki babu ?wari ta fita falo inda ta tarar dashi a zaune kan kujera ya ri?e kansa da hannaye duk biyu,ya kalleta sau Waya ya mayar da kai, seda ta tsorata da yanda taga idanunsa sunyi jajir. Zuciyarta ta karye hawaye suka fara sakko mata. A hankali ta ?arasa kusa dashi ta zauna, hannunta na rawa ta rungumeshi ta sakar masa kuka.

Jay yayi ?aramin tsaki yana kallonta yace
"Ki tashi daga kusa dani karki ?aramun damuwa akan wadda nake ciki"
"Kayi ha?uri i didn't mean that, baki nane ya suSuce wlh" ta faWa tana sake shiga jikinsa seya janyeta ya mi?e tsaye ba tareda yace mata komai ba ya wuce Wakin ta sake binsa tana kuka. Ita kam tana jin bakin Umma ne ya kamata da tace mata kukan da ta ringayi sanda zata auri Ahmad ba kuka bane na gaske yana gaba. Wanka ya shige ya barta, kafin ya shigo ta fita falon tayi microwaving breakfast Win da aka kawo musu. Seda ta ware masa komi data san zeyi amfani dashi kafin ta kwanta a ?asa jiki da zuciya duk basa mata daWi. Ko kallonta beyi ha daya fito cikin shiri ya Wauke wayarsa da mu?ullin motar da yake amfani da ita ya fice tsabar yanda wani abu ya tsaya mata kasa tashi tayi ta bishi da ido kawai hawaye na sakko mata. Shikenan saboda ta kira sunan Ahmad se abu ya zama jidali? Ita da yayiwa wula?anci ta ha?ura se shine ze ringa wani abu a ina ake haka dan Allah?

Haka ta wuni ita kaWai cikin ?uncin zuciya, a kwanakin da sukayi tare ko sunyi faWa sedai ya?i kulata amma baze fita ya barta ita kaWai ba kuma data lallashe shi shikenan ze sakko su cigaba sharholiya amma da gani yau fushin har zuciya yake yinsa. Tasha kukanta a ta ?oshi gashi ta bincike kayansu tsaf ko zata ga inda ya Soye mata wayarta ta samu tayi connecting da WiFi ko a whatsapp ne tayi magana da yan gida taji sanyi amma ta rasa, haka ta ha?ura ta zauna har yamma kafin ya dawo har sannan kuma bashida wata walwala amma dai da sau?i akan yanda ya fita dan shi ya sameta har inda take zaune ya rungume ta ya mata peck a goshi kafin ya saketa ya wuce Waki. Yanda yayi wani sukuku se ta ringa tunanin kamar ba iya abinda ya faru tsakaninsu bane kawai kamar yana da wata damuwar ta sake tabbatar da hakan bayan data shiga Wakin ta tarar dashi a zaune yayi tagumi. Cikin sanyi ta isa kusada shi, ya jata jikinsa hannayensa biyu akan waist Win ta yana shafawa yace
"You look pale, kinci abinci kuwa?"

Kai ta girgiza masa dan ruwan shayi kaWai tasha yinin ranar, jikinta da zuciyarta duka babu daWi balle ta iya cin wani abu. Seya mi?e tsaye yana tafiya da ita suka fita Wakin bayan ya warware mata scarp Win data Waure kanta dashi. Dining sukaje, duk su biyun tsakurar abincin kawai suka ringayi daga ?arshe ma ya aje cokalinsa itama ganin haka tace ta ?oshi seya Wauka yaci gaba da bata shima yana ci kaWan har taci da yawa sannan suka koma Wakin. Guraren tara tana cikin jikinsa bayan da suka gama yamutsa junansu, wayarsa tayi ?ara ya tashi ya Wauke ta daga kan mirror ya fita. Ta zumSuri baki dan abinda yazo mata matarsa ce ta kirashi. Wato shi yana waya da mutanensa ita ce ya ?wace mata waya. Wanka ta shiga tana fitowa shima ya shiga bayan ya gama wayar yana lura da fushin da ta sake Wauka be ce mata komai ba se bayan yayi wanka ya kwanta shima sannan ta fara masa mitar ya bata wayarta tana so ta kira gida itama ai bashi kaWai yake da waWanda yake son magana dasu ba. Ta ringa mita har se da ya gaji ya ce mata

"Idan kinyi ha?uri gobe ma zamu koma gidan in sha Allah" ya faWa mata sounding disturbed" ta kalleshi da mamakin abinda ya faWa, a hankali tace
"Gobe kuma? Zamu bar nan ko kuma zamu koma gida gaba Waya?". Seda ya juyo da ita suka fuskanci juna kafin a hankali yace mata
"Nigeria, akwai matsala ne that i need to be there as soon as possible. Gobe idan Allah ya kaimu zamu tafi, but if you want to stay back or move to the UK i can arrange that, ba daWewa zanyi ba idan naje da zarar komi yayi daidai zan dawo". Bata ce masa komi ba tayi shiru kawai tana tunanin meya faru kuma? Tasan dai baze wuce matsalar hajiya bace, ?ila ma cewa tayi seya dawo da ita shine ze wani yi mata alaye. Washe gari tunda suka tashi sallar asuba bata zauna ba seda ta haWe musu kayansu tsaf dukda yace mata evening flight ne. ?arfe shida sukayi checking out by 9pm jirginsu ya lula sararin samaniya seda kuma suka fara tafiya taji kewar garin ta fara kamata. She really had a great time in Bahamas, ba zata taSa manta wannan lokacin ba, dukda hawa da saukar da suka sha da ogan but if she will say the truth farin cikin data samu ya rinjayi ba?in cikin and daga yanda ta lura itace take da bu?atar gyara wasu abubuwan daga rayuwar data saba da ita a baya.

Bata shiga taitayinta ba seda suka hau jirgin da ze kaisu Kano daga Lagos a safiyar Alhamis bayan da suka ?ara kwana Waya a Lagos Win. Tayi ?wal ?wal da ido tana kallonsa, yayi murmushi yace
"Menene kuma?"
"To ni yanzu a ina zan sauka?" Ta faWa kamar zata fashe masa da kuka. Yayi shiru yana tunani, ta gaya masa Umma tasa ta tattara kayan tsaf tace idan sun dawo ta wuce gidanta kawai za'a biyota da kaya. Beyi tunanin dawowar su nan kusa ba dan haka all his plan was sanda zasu dawo an kammala komai na ginin da yakeyi can zasu sauka se gashi kuma dawowar tazo babu shiri. Yayi shiru har suka sauka be bata amsa ba gaba Waya ta shiga ruWani, bata san da idon da zata kalli Umma ba idan taje gidan yanzu. Ganshi tunda suka tafi sau Waya ta kirasu randa sukaje ai ko bata ce karta dawo mata gida ba wannan laifin ma yaci ta shata mata layi ita yanzu ba abin taje gidan Anty Sauda ba tasan ba rufa mata asiri zatayi ba duk se taji dama da yace tq zauna Win ta yarda yaje ya dawo abinsa. Haka ta ringa wasi wasin me ya kamata tayi, abu biyu dai ba zata yarda ya kaita gidan su ko gidan matar sa ba.

Hankalinta ya tashi jin yana sanarwa driver da yaje Waukansu inda ze kaisu, can gidansu fa gidan Baffa kamar ma baya jinta duk magiyar data ringa masa akan ya kaita gidan Anty Sauda ya mata banza kawai setayi shiru itama ta zubawa hanya ido. Gori kam yau zata shashi sedai Allah ya bata ha?urin jurewa. Har cikin gidan ya shiga yana Wauke da jakarta ita kuwa a gareji ta ci burki bata shiga ba seda ta jiyo muryar Baffa yana masa maraba hakan ya bata ?warin guiwa tunda Baffa yana nan tasan Umma ba zata koreta ba, ta wuce ciki sum sum saSanin yanda tayi tunani fuska a sake Umma ta amsa sallamarta harda yi mata maraba. Ta samu gefe can ta ma?ale kamar sabuwar amarya tana sunne da mayafi. Baffa dai ya amsa gaisuwar ta da fara'a yana musu sannu da zuwa Umma ta kawowa Jay ruwa yace sauri yakeyi zuwa dare ze dawo. Yana fita Umma ta kalleta ganin bata da niyyar tashi tace
"Ba zaki taka masa ba kenan".

A gareji ta tarar dashi tsaye ya jingina da gini yayi shiru kamar me tunani, yana ganinta ya nufeta ya rungumeta yana cewa
"Zanyi kewarki, ki zauna cikin shiri idan na kasa jurewa zan dawo mu tafi". Ta rungumeshi sosai a hankali tana cewa
"Wai me yake faruwa? Ka sanar dani please yanayinka ya fallasa akwai wata damuwa sosai"
"Karki damu all shall be well da yardar Allah. Take good care of your self, i love you" ya faWa yana cireta daga jikinsa bayan da yayi pecking goshinta. A Waki ta tarar da akwatinta Umma ta shigar mata da shi, ta ringa tunanin kodai Umma jira take Baffa ya fita kamin ta rufe gida ta mata abinda zata mata? Bata tsinke da lamarin Umman ba seda taga ta kawo mata abinci tana cewa
"Gashi nan kici, idan kuma se kin fara wanka toh, bari na le?a gidan Safiya, Zaliha ta haihu shekaran jiya an dawo da ita wanka gida" ta zura hijabinta ta fita gidan ya zama se ita kaWai.

***************
Daga gidansu Afeeyah kai tsaye shadikwata inda aka kai hajiya Jay ya wuce damuwar da yayita kokawar Soyewa ta ?arasa bayyanar masa gaba Waya. Baze iya faWar yanda yaji ba sanda labarin ya isa kunnuwansa. Tunda suka tafi ya kashe wayarsa, lokaci lokaci yakan kunna ya kira Fatiyyah da hajiya, besan me yasa ba tun ranar laraba baya samun number hajiyan se yayi tunanin kashewa tayi tunda dama hi hi suke tace ma ya dena kiranta tunda ya zaSi was akanta yaje can ya ?arata. Har Faisal ya kira ranar Saturday yace ua haWashi da hajiyar amma yace masa baya gida idan ya koma ze haWasu shiru be kirashi ba shima kuma ya manta se ranar talata da safe ya kunna wayarsa ze kira Fatiyyah kenan Nazira ta kirashi kuma ita ta sanar masa da abinda yake faruwa. Ya shiga tashin hankali matu?a, ba ?aramar dauriya ya ringayi na nuna babu komai ba. Tun farko abinda ya ringa tsoro kenan zuciyarsa bata kwanta da wannan ajiyar ta Naziru ba amma kuma be taSa tunanin abin zeyi muni har haka ba.

Tunaninsa yaushe har Naziru yayi wannan lalacewar? Yaushe ya fara wannan mugun kasuwancin babu wanda ya sani? Babban abinda ya ?ara tayar masa da hankali yanda tace Alhaji yace babu ruwansa a ciki, ya sani da ace yayi magana babu yanda za'ayi su ri?e hajiya tsahon sati Waya nan. Da?yar aka barshi yaga hajiyar bayan daya isa gurin. Seda yayi hawaye daya ganta, lokaci Waya ta zabge ga kafarta tayi kumburi da?yar take takawa se an kamata, tana ganinsa ta fashe da matsanancin kuka tana cewa
"Dama na san kai kaWai be kake ?aunata kai kaWai ne gata na a duniyar nan ka taimaka ka fitar dani daga gurin nan Jafar tun kafin su kashe ni". Wata officer data fito da ita tace
"Amma dai Mama kiji tsoron Allah me mukeyi miki anan gurin Win? Meye banbancin ki da wanda yake a gidansa na tabbatar yanda ake riritaki a gurin nan ko a gidanki se haka. Ai wlh ki godewa Allah kinci arzi?in masu arzi?i banda haka ai da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login