Showing 117001 words to 120000 words out of 467220 words

Chapter 40 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12504

da Milo da Sukari kadan kafinta tsiyaya Ruwan zafinta motsa, ta zubanata a kofi ta zubawa Abdullahi se ta qara ruwan sanyi akan sauran ta dan qara musu Madara da Milo sannan ta zubawa sauran Yaran.

Yanda suka rarumi Kofunan duk sunbata tausayi musamman Zakariyya da yake qaraminsu a ranta tace
"Wato muguntar harda dan cikinta takeyiwa" tana kallo ya kafa kai yana kurbar shayin a yunwace Babannan yace
"Umma Burodi da kwai"
"Yanzu zan baka ai uban gajen haquri" ta fada tana tura masa farantin data saka masa Burodinsa da kwan akai sauran ma duk ta miqa musu nasu. Abdullahi yakai kofi bakinsa ya kurbi shayi ba zato Bara'atu taji ya fesoshi da qarfi harya batata, a zafafe ta buga masa tsawa tana cewa

"Wane irin wulaqanci ne haka ai kasan shayin da zafi zaka kurba ya qonaka ji yanda ka batani duk ka tsalla mana yawu acikin abinci"
Abdullahim dake karkada harshe yawu na dilala dakyar yace mata
"Umma ba zafi bane, gishirine a ciki kamar ze tsinke mun harshe"

"Gishiri?" Ta fada cikin mamaki, Babangida daya matse fuska yace
"Nima da akwai a cikin nawa Umma".
Robar da sukari yake ciki ta janyo dan ta tantance ko kuskure tayi gurin daukowa sedau sukari ne a ciki, se kuma ta saka cokali ta dibi shayin gabanta dan kadan ta kai baki ai da sauri itama ta fesoshi jin wani azababben gishiri tamkar an jiqe kwano gida ciki ruwan fulas din to meya kawo gishiri ciki?

Kofunan hannun Babannan da Zakariyya wanda qiris ya rage ya shanye nasa ta kwace da alama shi be gane banbancin dandanon gishirin bama. Ta hade su a Jug kafinta miqe a sanyaye ta shige kitchen dinta na cikin daki. A Butar tafasa ruwa ta saka nan da nan yayi zafi bata ko Jira ya tafasa ba ta juyo ta sake hada musu wani zuciyarta ta aminta da cewar da gangan Binta ta zuba musu gishiri a ruwan shayi wai me wannan matar take nema da ita fisabillahi.

Bayan sun gama ta tattaro kwanuka ta fito dasu danta wanke sedata hado ma cikin kitchen ta zauna ta fara wanke wanke, Shayin dayaqi shayuwa ta tsiyayar a rariya Ta bude Fulas din zata zubar da sauran na ciki kenan ta ji muryar Binta a kanta tana cewa
"Aa, Maman Baba meya faru naga kin sheqar da shayi a rariya?"

"Shayi kuma?" Audu sa suka fito tareya tambaya yana kallon rariyar da shayin be gama wucewa ba,
"Gashi nan kuwa ka gani hadin kauri kuwa wlh, qila sun hada ya musu yawa ne maimakon ki barshi an jima ki dumamawa yara susha kuma se ki zubar ai Almubazzaranci ne wannan" Bintan ta sake fada. Bara'atu bata iya dagowa ba balle tace wani abu dan wannan Bom din kam tilas ya tashi da ita dan tafi kowa sanin Audu baya son wulaqanta abinci tun zamanin tana ita kadai a Bechi kafin su dawo Kano ko abu ya siyo ze gaya mata idanba zata iya amfani dashi duka ba ta fitar ta bayar kar abarshi ya lalace balle yanzu akan Idonsa ta zubar da shayi a rariya tasan ko Binta bata saka baki ba se yayi fada.

"Yanzu saboda wulaqanci abinci zaki wulaqanta haka? Da yayi muku yawa me yasa bazaki bawa Abdullahi ya fita ya bawa Almajiri ba?" Audun ya fada cikin fushi. Murya a sanyaye tace
"Kayi haquri ba yawa ya mana ba, kuskure aka samu gishiri ne a cikin ruwan da aka dafa se bayan dana hada mana sannan muka ankare kaga baze shawu ba shiyasa ma zubar"

"Gishiri a cikin shayin?" Ya tambayeta cikin sigar rainin wayo irin be kama abinda ta fada ba. Fulas din gabanta ta tura masa tana cewa
"Dama ba zaka yarda ba amma ga sauran ruwannan ka dandana kaji"

"Ikon Allah a garin yaya gishiri ya shiga ruwan shayi? bari muji" Binta ta fada tana dauke fulas din cikin mugunta datayi kama da kuskure ta sakeshi daga tsayen da take ji kake tush ya tarwashe a qasa ruwan ya watse duk ya tsallar musu a qafa harda Audun.

"Innalillahi na qone" Bintan daya fi zubar mata ta fada tana daqe qafafu, Audu ya zabga tsaki yana cewa
"Wane irin sakarci ne zaki yada fulas se kace bakya gani? Se ki dakko tsintsiya ki tattare gurin ai kafin yara su fito wani ya taka kwalba" yana fadar haka ya baza Babbar rigar da ta zame masa Kayan sawa yanzu ya fice daga gidan.
"Ke kin dauka zaki kwanta ki miqe qafa in daga miki abinci? To ba Gishiri ba idan bakiyi sannu ba wata ran shinkafar bera zan zuba miki" ta wuce ciki tana tsaki.

Sanadin zam????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
an Bara'atu boyi boyi kenan a gidan, da ranar girkinta da ba nata ba muddin tana so yaranta suci abinci kan lokaci sedai ta tashi tayi, an koma makaranta Abdullahi ya koma makarantar kwana dan haka ita zatayi shara ta hada abin kari ta shirya yan makaranta su tafi sannan tayi wanke wanke ta hado wankin kayan Yaranta dana Bintan da wani sa'ilin harda nata kayan take tulo mata kuma bata isa taqiyi ko tayi magana ba ranar Audu ya ringa surfa mata bala'i akan ta fiya fitina bata qaunar a zauna lafiya.

Nana da nan kyan da tayi da cikar jiki suka zagwance Rama ta maye gurbinsu kulawar da take samu gurin Audun ta rasa domin ko sun shirya na dan lokaci Binta zata sake kunna wata wutar da zata wargaza su, a haka Watan Azumi ya kama aiki ya ninkar mata dan bayan abincin gida harda na sadaka sukeyi wanda A baya Mairo da Lantana ke aikin yanzu da babu su itace komai haka zata wuni tsaye kan qafafunta idan dare yayi lokacin da kowa yake Tsaye yana ibada ita kuma gabbanta sun gajiya sedai ta kwanta tayi ta muqususun ciwon jiki ga babu godiya balle kyautatawa daga Megidan a kullum gazawarta yake gani yan uwanta kuma sun gagara gane halin da take ciki idan ka cire Hadiza wadda tasan kan zaman da takeyi.

Sallah saura kwanaki Biyar su Yakubu suka zo Kano, a gidansu suka sauka da yake jirgi suka biyo se dab da shan ruwa suka tafi gidan Audu kamar yanda suka tsara da Yakubun sanda ya dakkosu daga Iyafot. Kasa magana Balaraba tayi sanda taga Bara'atu, Yakubu kansa kallo daya yayi mata sannan ya kalli Audu wani abu ya tokare masa maqoshi, farin cikin daya taho dashi ya dishashe nan take yanayinta ya nuna cewar an koma yar gidan jiya kenan Audu tuban muzuru yayi ba dagaske ya gane kuskurensa ba.

Shan ruwan haka sukayi shi babu karsashi Binta kadai ke subadadi ita kadai kamar kanta ya qone dan shi kansa Audun tunda yaga canjin fuskar Yayan nasa yasha jinin jikinsa domin yasan baze wuce dalilin ganin Bara'atu ba amma ta yaya zeyiwa Yakubu bayanin halin Bara'atu ya fahimat? Ita din Majicin sari ka noqe ce babu me fahimtar ainihin halinta se wanda ya zauna da ita. Suna gama tsakurar Abincin Yakubu yace ze tafi Balaraba ma ta miqe wannan ya qara tabbatarwa da Audu tabbas Yakubun ya fusata dashi ne.

A qofar gida Bara'atu data bi bayansu ta fashe da kuka, tuni Balaraba ta shige mota dan tace ba zata iya magana da Bara'atu ba zuciya tana iya dibanta ta watsa mata mari ko ta daddana mata Ashar haba wannan mutuwar zuciya har ina ta zauna Kishiya da Miji su nemi kasheta da ranta.

"Dan girman Allah Yaya Yakubu ka taimakeni kai kadai nake saka ran zaka fahimceni a yanzu, bazan iya yi maka bayanin halin da nake ciki ba amma ina roqonka da kayiwa Allah ka shiga lamarina ka nema mun yanci a gurin Dan uwanka wlh na gaji, ban zata cewar wahalar data fi ta bayace take kirana zuwa gidan nan ba, ban dauka ya maidoni bane saboda ya qara biyamun karatun da be kammala a baya ba, ni dai na haqura ina fatan wahalar dana sha ta zame mun kaffara a rayuwata" ta fada cikin matsanancin kuka daidai nan Audu ya qaraso Soron ya kalleta ya kalli Yakubun daya daga kai sama yana kokawa da bacin ran dake taso masa.

"Me kikeyi a nan gurin Dallah wuce ciki" Audu ya fada yana zare mata ido ta juya cikin gidan bayan data sake kallon Yakubu irin kallon ka taimaka mun.
"Na zata anan zakuyi sallar Isha in aka idar da Tarawi se na maida ku gidan" Audu ya fada cikin inda inda, Yakubu ya juya ze fita yana cewa

"Babu damuwa zamu koma gida kasan muna tare da gajiyar hanya, idan ka samu lokaci kazo ina son magana dakai" daga nan ya sa kai ya fice daga gidan.

Masifa da Bala'i Audu ya ringa zazzaga mata bayan daya koma cikin gidan akan seta gaya masa abinda ta fadawa Yakubu dayace yana neman sa amma tayi shiru banda kuka babu abinda takeyi daya gaji ya fita gaba daya ya rikice dan be san me Bara'atun ta fadawa Yakubu ba, maganarta ta qarshe kadai yaji da tace wahalar datasha ta zame mata Kaffara wace wahala? Amma dai ba a gidansa take nufi ba? Ya ringa tambayar kansa. Sallar ranar dai yayita ne kawai ana idarwa kuma ya tafi gidan Yakubu.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*

Audu ya ringa Jijjiga kai yana buga qafafu haka nan zufa take keto masa kamar wanda yake zaune kan Kunama, bakinsa har kumfa yake saboda masifa Yakubu ya zuba masa ido yana kallonsa kawai, shi yanzu tantama yake anya Audu bashida wata matsala akansa kuwa kodai shaye shaye yakeyi be sani ba. Tambayarsa yayi akan me yake faruwa tsakaninsa da Bara'atu ya ringa zana masa maganganu marasa lissafi bare kan gado, a duk abinda ya fada masa babu guri daya dayaji laifin illa tsantsar Zalunci da Azabtarwa da ita suke mata, ya mayar da ita tamkar Baiwar daya siyo da kudi a cikin gidansa shin wai me Bara'atu tayiwa Audu ne a rayuwa dayake daukar fansa akanta yanzu?

"To Audu kasan dai Aure anayinsa ne bisa yarjejeniyar Mutum biyu Mace da Namiji, haka nan idan har ya zama da cutarwa kowanne bangare yana iya neman sauqi ta hanyar rabuwa idan har babu wata hanyar samun daidaito bayan wannan din, ni Ina ganin tunda dai zaman ku ya zamana da cutarwa ku rabu hakan ze fi Alkhairi akan kuci gaba da zama daya yana daukar Alhakin daya" cewar Yakubu.

Audu ya dago a fusace yace
"Wato ce maka tayi kasa na saketa kenan dazun?"
"Haka tace, ta gaya mun ta gaji da cutar da ita da kakeyi kaida matarka dan haka tana neman sauqi ka sawwaqe mata auranka taje tayi rayuwarta ta samu wani can ta Aura wanda ze sota tsakani da Allah ya san darajarta kaje kaci gaba da zama da matarka da kake ganin tafi maka kowa" Yakubun shima ya mayar masa cikin daga murya. Se Audu ya miqe yana cewa

"Bazan saketan ba, ka gaya mata idan tana da qarfi tazo ta kwaci sakin ko kuma ta saki kanta"

"Ai kuwa idan baka saketa ta Arziqi ba zaka saketa ta tsiya dan wallahi maka ka zanyi a kotu qaryar taurin kai kakeyi Audu zan nuna maka jini daya ne yake gudana a jikinmu yanda kake jin ka gado Taurin kai seda na fara gada kafin ka samu ragowa, karka kawo mun takardar sakinta kafin nan da gobe kaga yanda zamu kwashe dakai" daga haka ya shige ciki ya bar Audu a tsaye yana tsuma, Bara'atu tace ya saketa? Ita da kanta ko kuwa wannan matar Yakubun ce ta zugata?

Kwanaki uku aka kwashe cikin wani yanayi mara dadi, kwana biyu da Audu yaje gidan Yakubu bayan ya dawo ya samu Bara'atu yayi mata cin mutunchi da tijara ya kuma jaddada mata sedai ta mutu amma baze taba sakinta ba washe gari da safe yana kamfani se ga magatakarda daga Kotun Musulinci an aiko masa da sammaci, ya karba ya duba kiransa akeyi daga kotu matarsa ta shigar dashi qara ya wuto gida Afujajan sedai be tarar da Bara'atu ba tun safe yana fita itama ta fice ta tafi gidan Yakubu tare dashi sukaje Kotun da kanta ta shigar da qarar bayan Yakubu ya sake tambayarta ko zata yi haquri ta bada lokaci su sasanta ta rantse masa akan wallahi ta gama zama da Audu muddin baso suke wata rana a wayi gari zuciyarta ta buga ta mutu ba su qyaleta jin haka yasa yace su tafi Kotun take kuma aka rubuta takadda aka kaiwa Audu.

Ranar Jajiberin sallah Bara'atu ta karbi takardar sakin igiya daya data rage tsakaninta da Audu, a ranar ya kamata suyi zaman kotu, tun Asuba daya dawo ya kulle kansa a daki yaqi fitowa, besan yanayin da yake ciki ba wani irin qunci da zafi zuciyarsa takeyi masa. Binta da duk abinda akeyi a kunnenta da idonta amma tayi biris tamkar bata san wainar da suke toyawa ba tana tsakar gida tana aikace aikacenta tana waqoqi Musbahu yazo, bayan sun gaisa yake ce mata gurin Baba yazo ta masa magana qarfe Goma ne zaman kotun nan gashi Tara da rabi tayi, dataje ta gaya masa beko waiwayo ba ya miqa mata farar takarda, duk yanda taso ta daure bayan ta karanta abinda yake ciki ta kasa seda ta rangada guda kamar wadda take saka Amarya a lalle. Tana bawa Musbahu takardar ta hau taka rawa a gabansa se ya rasa abinda zeyi kawai ya tsaya yana kallonta kafin jiki a sanyaye ya juya ya fice daga gidan ya kaiwa Yakubu saqon Audu.

Sanda takardar ta shiga hannun Bara'atu ji tayi kamar an mata bushara da gidan Aljanna, da Ajami ya rubuta dan haka ta gane komai abu daya daya dameta a ciki shine cewar da yayi karta tafi masa da Da ko daya, ta yaya zata barwa Binta yaranta? Matar data tsaneta kuma zata iyayin komai akanta da yaranta.
"Karki sakawa ranki damuwa akan yara babu abinda ze same su sannan kina nan a matsayinki na mahaifiyarsu babu abinda ze goge hakan komai daren dadewa kuma zasu nemeki. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, ki tashi kinemi ilimi ki tsaya da qafafunki in sha Allahu ubangiji zeyi miki sakayya a gaba da Mafi Alkhairi kinji" Yakubu ya tausheta.

A ranar suka tafi Bechi gaba daya dan dama can zasuyi sallah. Shiya kaita har gidansu ya kuma yiwa Inna Hajara bayanin komai, bayan tafiyarsa kuwa wuta ce kadai Inna Hajara bata hura ta jefa Bara'atu a ciki ba, ta kasa hango rayuwar da yarta take ciki da ta sa ta haqura da daular da ita hange, damuwarta kadai mutane zasuyi mata dariya, zasu rasa tallafin da suke samu a gurin Audun tunda ya kwace Yayansa, ita da take saka ran idan Bara'atun ta sauke farali Bana badi kuma a sakata a lissafi shine tayi mata baqin ciki shin Bara'atu wace irin yarinya ce ne? An gaya mata da akwai Auran da ake jin dadi dari bisa dari ne a ciki? Wace Macece zata samu Miji kamar Audu daula iya daula tayi wasa da damarta ai se sakarya irin Bara'atun gashi yanzu Auran ya mutu murus babu damar gyarawa.

An cinye watan Shawwal Mahajjata suka fara shirye shiryen tafiya qasa me tsarki, Audu ya rigada ya biyawa Bara'atu, Bilki da Aminu se Balaraba matar Yakubu, a hannun Aminun ya damqa duk wani abu daya kamata na Bara'atun, babu wanda beyi mamaki ba dukda sun san da ita cikin jerin matafiyan amma abinda ya faru yasa suka dauka za'a fasa tafiyar da ita sedai Audun ya basu mamaki. Lokacin tafiya yayi suka shirya sunyi bankwana da yan uwa da Abokanan Arziqi, dalilin su Bilki da Aminu ya saka Audu yi musu rakiya Iyafot dukda qasan ransa badansu yaje ba, haka nan zuciyarsa ta kasa nutsuwa a kwanakin, kullum ya kwanta se yayi mafarkin Bara'atun haka da rana wuni yake da tunaninta a ransa yana jin kamar ta cancanci ya nemi afuwarta koda har yanzun be yarda da cewar ya cutarda ita ba kamar yanda mutane suke fada amma kuma haka nan zuciyarsa take ingizashi ga neman afuwar da besan ta mecece yake da buqata ba.

A iyafot Mahajjata sun hau layin karban tikitin shiga jirgi, yana daga tsaye can gefe dan ya sake zama baqo a cikin danginsa tun da ya rabu da Bara'atu ya sake rasa karsashin sakewa musamman a gaban Yakubu yanzun ma ganinsa tsaye suna sallama da matarsa yasa duk ya kasa sakewa gashi yana so yayi magana da Bara'atu amma shegiyar zuciyarsa me masa hudubar tsiya tana gaya masa girmansa ze zube idan aka ga ya mata magana a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login