Showing 27001 words to 30000 words out of 467220 words

Chapter 10 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12163

Karan datayi girkin dashi ya cika mata qirji shikenan numfashi ya fara sama sama washe gari kuwa da sassafe Audu ya kwasheta duk yanda take tirjewa seda sukaje Asibiti. An mata Allura an kuma rubuta mata magunguna ya siya bayan dokoki da sharuddan da likita ya kafa mata akan ta kiyaye duk wani abu daze hadata da qura ko hayaqi suka dawo gida. Wunin ranar zur a dakinta yayi shi haka qannensu da matansu duk suna nan suna hidima da Dadan da gaba daya tayi wani laushi dukda tace taji dadin Allura da maganin data sha abinda take ji a qirjinta ya yaye amma jikinta babu qarfi dama kuma likitan ya gaya musu magungunan akwai me kashe jiki yasa bacci dan haka Audu yace ta kwanta ta huta.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*

*FREE PAGE 8*

Goggo Fadi ta ringa sakin maganganu a tsakar gida wai Lamarin Dada dai ta rasa ma abinda zatace akai wannan rashin kunya har ina ta ringa hawa mashin Yara na goyata sannan danbata da lafiya kamar wata jinjira ta langwabe duk se wani zuruftu yara suke akanta, lokacin da take maganar Dada ta fito Aisha ta rakata kewaye ta fito tana daura Alwala. Seda ta idar ta kalli Goggo Fadin da murmushi tace
"Yaya kenan, indai nice kin kusa ki dena ganina ballantana nayi abinda ze sakaki surutu".

Goggo Fadi ta ce
"Eh ba shakka Hafsatu wato daman naji ance zakuyi qaura Birni yo ni ai haka nake so ku tattara ku tafi ku barmin gidana yanda kuka zo kuka sameni, bari ma wannan yaron yazo kuyiwa gurin naku kudi kawai ya fiddaku shikenan wanda ya hada ya raba"
Har Dadata zura qafarta a daki ta sake waiwayawa tana murmushin da seda gaban Goggo Fadi ya yanke ya fadi haka kawai tace
"Toh ai Malam ba sauri yayi ba Fadi, zan bishi kema kuma komai dadewa zaki biyo bayanmu" daga nan ta shige dakinta tabar Goggo Fadin na sababi ita kadai.

Da dare Audu ya kawo mata Kaza gasashshiya da Madara sabuwar tatsa dan gama tafasata kenan ya karbo ko hucewa batayi ba. Dada na cin naman Baballiya na gefenta yana so yaci Audu ya hanashi Abdullahi daman tuni ya gudu gurin Bara'atu tunda yaga Audun ya shigo da ledoji kuma har Goggo Fadi seda ya miqawa. Dada taci ta qoshi ta turawa Baballiya tana cewa
"Ci ubana kaji haka kawai yabi ya takuramun kai"
"Wlh Dada ke kike dada sangarta yaron nan ya girma amma baze dena sakarci ba a haka kake cewa zakaje aikin Sojan" Audu ya fada, Dada ta kishingide tana sakace tace

"Ze dena ne, aikin Soja kuma nasan indai kana raye seka cika masa burinsa kamar yanda ka dakko hanyar cika na dan uwanka. Ina Alfahari dakai Abdulwahabu ina kuma roqon Allah yaci gaba da hada kanku ya baka ikon ji gaba da jajaircewa akan zumunchinku, ina fatan har yaya da jikoki kuci gaba da hada kanku karku yarda qata baraka ta shiga tsakanin ku, Banida haufi domin kunyo dacen mata na kwarai saboda rayuwar Namiji komai nagartarsa idan yayi kuskuren dace da macen aure anan yake samun tawaya dan haka ina horar ku cewar ko gaba koda ace kunyi sha'awar qara aure kuyi qoqari gurin zabo matar da zata tayaku kuci gaba da hada kan gidanku ba wadda zata tarwatsa muku farin cikin da kuka ginu akai ba. Sannan yan uwanku kuci gaba da haquri dasu kuna jan su a jiki da sannu wata rana zaku koma tamkar baya sanda Malam yana raye".

Haka ta ringa masu nasiha me shige da wasiyya, Baballiya na gama cin kazarsa ya sheme a gurin ita da Audu sukaci gaba da yar hira har ta fara gyangyadi kafin ta hau gadonta yaja mata abin rufa bayan ya shafa mata man zafi a tafin qafarta ta saka safa. Seda ya zubo toka me zafi a babban kaskon da ake ajiyewa a dakin yayi masa mazauni me kyau saboda gudun tsautsayi kafin ya tashi Baballiya ya gyara kwanciyarsa yaja musu qofar ya fita jikinsa a sanyaye saboda maganganun da Dada ta fada masa, yanda take nanata masa hadin kan Iyalinsa kamar wadda take hango wani abu a gaba haka ya shiga dakinsu Bara'atu har tayi bacci ya raba gefenta ya kwanta sedai be jima da kwanciya ba bugun qofar gida ya farkar dashi.

Da mamakin wayake musu bugu cikin dare ya dauki fitila ya fita, seda ya tambayi waye, muryar Yakubu dayaji ta sakashi bude qofar da sauri ya rabe ya shigo ganin yanda yake rawar Dari dan rigar jikinsa bata da nauyi haka nan kansa babu hula ga dare ya tsala dan haka gari yayi sanyi qarara. Yakubun na goye da Jakarsa medan girma kana kallonsa ko baa fada maka ba zaka san yasha wuyar tafiyar da yayiwo ya wuce ciki Audu yabi bayansa zuciyarsa na bugawa abinda ya fara zuwar masa Yakubun ya samu matsala da karatunsa ne. Yana so ya tambayeshi daga ina haka cikin dare ba kuma ya so hayaniyarsu ta tayar da Dada ko Goggo Fadi ta samu abin sharri dan haka yabi Yakubun daya doshi dakin Dada kai tsaya ya tura qofar ya shiga Audu yabi bayansa.

Tana kwance tana bacci hankalinta kwance ya kai hannu ze tayar da ita Audu ya riqeshi yana cewa
"Haba dai ya zaka tayar da ita tana bacci"
"Na kasa nutsuwa saboda ita na baro Ikko babu shiri me ya samu Dada kullum cikin tunaninta nak abin kuma har ya zarce misali?" Yakubun ya fada yana duban Audu, Audu yayi waje yana cewa
"Babu abinda ya sameta kaje ka kwanta kaga dare yayi da safe se muyi magana" suka wuce, seda yayita kwankwasa qofar barinsu kafin Balaraba ta taso a dan rikice da alama tana baccin itama bugun ya riske ta, ganin Yakubu ne kuma se fuskarta ta washe da murna suka shiga suka maido qofa se sannan Audu ya shiga dakinsu zuciyarsa fal da wasi wasin abinda ya taso Yakubun haka koda yake ya sani shidin me qulafucin uwa ne ta yuwu rashin lafiyar Dadan ce ta taba shi har ya kasa zama ya taho ya ganta haka ya ringa juyi a gado sedai sam bacci ya qauracewa idonsa dan haka ya tashi ya dauro Alwala ya shiga Nafila Bara'atu dai tayi daidai abinta a gado dan cikin nata irin me baccin nan ne da se a iya sace mutum sedai ya farka ya ganshi a wata Nahiyar.

Asubar Fari kururuwar Baballiya ce ta saka Audu sallame sallar da yakeyi babu shiri ya fita daga daki da gudu, a bakin qofa sukayi kicibus da Yakubu da shima ya fito a rikice dan da gani ma daga wanka ya fito ya saka dogon wando ga rigarsa nan a hannu ko sanyin da ake busawa ma bayaji suka shiga turereniyar shiga dakin Dada inda Baballiyar yake qarawa Ihunsa qaimi matan kuma da duk suka fito suma harda Goggo Fadi sun tsaya daga waje kowanne abinda zuciyarsa ta bashi wuta ce tunda lokacin sanyi ana yawan samun wannan matsalar saboda Rushi da ake kaiwa daki dan aji dumi idan yazo da tsautsayi abinda ze iya kama wuta ya shiga ciki se kaga gobara ta tashi amma kuma basu hango jan wuta a cikin dakin ba ko kuma hayaqi to ko wani mugun kwaron ne ya cije shi?

Yakubu ne akan gaba, burki yaci yana kallon Dada dake kwance idanuwanta a bude tana kallon rufin dakin hannunta daya na dafe da qirjinta dayan kuma ya saki ya sakko qasa, dukda cewar gawa daya ya taba gani ido muraran wato ta Malam amma baya buqatar a gaya masa cewar Dadan ta rasu. Lokaci daya wani kuka me cike da rauni ya kufce masa, ya durqushe gaban gadon Audu ya tsallake shi ya qarasa shigewa dakin dan be fahimci dalilin tsayuwar Yakubun ba ga Baballiya dabe fasa ihu yana kiran ya shiga uku ba.

Hannun Dadan dake qasa ya daga ya maida kan gadon, sanyi qalau yaji shi, ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta tareda kiran sunanta ganin ta zubawa guri daya ido Yakubu dake kuka kamar qaramin yaro, ashe Alhinin rasa mahaifiya ne ya hanashi sakat har seda ya kamo hanya ya dawo sedai an saba haduwar, bashida rabon zasu sake zantawa da ita rai yayi halinsa. Kama hannun Audu dake jijjiga Dadan yayi cikin kuka yace masa
"Bari jijjigata ta rigamu gidan gaskiya"
Ze iya cewa be fahimci abinda Yakubu yake nufi ba dan kwakwalwarsa gaza fassara hausar tayi dan haka ya shiga qoqarin dagata yana cewa Yakubun ya tayashi su fita da ita ya kaita Asibiti Yakubu ya miqe yana janye shi cikin daga sauti yace masa

"Ka dena wahalar da ita Audu na gaya maka ta rasu" kalaman da suka fi duk wasu kalamai daya tabaji a rayuwarsa Muni, Dada ta rasu? Dadar da suka gama hira dazu daman duk wasiyya take masa?
Kalaman Yakubu suka janyo hankalin su Goggo Fadi dake qofar daki take suka fasa kuka kafin kace me maqota sun jiyo aka fara shigowa rayuwa kenan tabbas dan Adam abin tausayi ne yanzun kaine qiftawar ido ana iya cewa babu kai. Duk wanda yaji rasuwar Dadan se yace jiya fa da La'asar sakaliya ya ganta a Mashin Audu ya dauke ta har sun gaisa, a masallaci ana idar da sallah aka bada sanarwar Jana'izar, kafin ko gari ya gama wayewa tangararau har an shiryata tsakanin Yayanta baka iya fidda wanda mutuwar tafi duka. Bilki suma tayi sanda saqon ya risketa Aisha tafita dauriya kuka ta ringayi Audu kansa duk taurin rai irin nasa ya koka hada kai sukayi da Yakubu suka ringa kuka gwanin tausayi.

Bayan an kaita an dawo aka zauna zaman karbar gaisuwa, Goggo Fadi tayi wata zugewa lokaci daya, mutuwar Dadan ta daketa matuwa ta kuma yi nasarar maidata cikin hayyacinta.
"Malam beyi sauri ba, nima zan bishi kuma kema kina tafe komai daren dadewa" kalaman Hafsatun na jiya suka ringa mata yawo a kwakwalwa ashe mutuwa Hafsatu zatayi? Da tasan haka da bata takaleta ba, data nemi yafiyarta akan abubuwan da ita da yayanta suka ringayi mata. Hashimu kansa yaji mutuwar amma da yake Dan Adam ne ana kwana daya ya ci gaba da sabgoginsa be ko sake zama gurin karbar gaisuwar ba ya bar su Audu dasu Aminu da idan ka ganshi zaka dauka mahaifiyarsa ce ta rasu. Su Audu kuwa ba'a magana duk sun sukurkuce bayasu ba baya matansu ba amma ya zasuyi haka aka share zama bayan anyi bakwai Abokanan Audu na Kano sunyi masa kara mota guda suka yi sukaje masa gaisuwa bayan da suka samu labarin rasuwar a bakin masu daukar kaya yan garinsu.

Wannan karon tsakanin Audu da Yakubu rasa wanda ze lallashi wani ya koma bakin nemansa akayi. Seda Dada tayi sati biyar da rasuwa, Yaya Baba ya kirasu cike da Alhini bayan ya sakeyi musu gaisuwar rashin da sukayi kafin yace musu
"Naga dukkanku baku da alamar komawa bakin neman ku musamman kai Yakubu da kuke tsaka da Karatu ka taho ya kamata kuyi haquri ku dauki dangana zamanku bashi ze maido da Goggo ba A yanzu Addu'a kadai take da buqata daga gareku sannan kuci gaba da jajircewa akan abinda take da burin ganin kun cimmasa".

Maganar Yaya Baba tasa suka fara shiri jiki a sabule babu wani karsashi sun kasa sabawa da Rashin Dada, tunanin yanda rayuwarsu zata cigaba ba tareda ita ba sukeyi yanzu dawa zasu ringa barin matansu? Tunanin Audu kenan. Da dare ya samu Yakubu a bangarensu yana zaune shiru Balaraba na gefensa itama shiru duk ta fice hayyacinta tamkar Bara'atun sa ga tsohon ciki haihuwa ko wanne lokaci na iya zuwa shigowar Audun yasa ta cicciba ta basu guri.

"Wata shawara nake da ita Yakubu" Audu ya fada bayan daya gyara zamansa. Yakubu ya kalle shi Audu yaci gaba da cewa
"Daman akan Iyalanmu ne, kaga yanzu Babu Dada gaskiya hankalina baze taba kwanciya ace mu barsu a nan ba kaga dai halin da gidan nan yake ciki lokacin da ranta ma yaya balle yanzu da babu idonta"

Yakubu ya jijjiga kai yace
"Hakane, ni kaina ina wannan tunanin ga yanayin da suke ciki gaba daya kowacce na da buqatar kulawa ta musamman, amma kai menene shawararka me kake gani za'ayi?"

"Dama dai tun zuwansu Ma'aruf na gaya mishi ya dauki kudi cikin cinikin da akayi a qarasa ayyukan da suka rage na gidan nan mu koma can kawai gaba daya da zama kaga hankalina zefi kwanciya na kuma tsaya a guri guda amma kai me kake gani?" Audu ya fada. Yakubu ya muskuta yana cewa
"To wannan shawara ce amma kana nufin kenan zamu bar Bechi da zama gaba daya?"

"To me muke dashi a nan da ze sa muci gaba da zama? Karka manta mun rasa uwa da uba dangi kadai suka rage mana kuma zamu ringa kawo musu ziyara lokaci lokaci musamman kaga Bara'atu iyayenta suna nan baze dauki lokaci me tsayi ba zamu ringa leqowa muna ganin dangin mu" Audu ya sake fada.

"To gida kuma fa haka zamu barshi ya lalace?" Yakubun ya sake fadaz cike da qosawa Audu yace
"Nidai na rigada na yanke shawara bazan iya cigaba da zama a gidan nan ba idan na kalli dakin Dada gani nake kamar zata fito daga ciki zuciyata bazata iya ci gaba da dauka ba" yayi maganar a raunane sukayi shiru baki daya kafin can Yakubun ya sake cewa

"Ina ganin zan kama daki a Ikko da zamu iya zama da Balaraba zuwa na qarasa karatuna kafin muga abinda Allah zeyi"

"Wannan shawara ce me kyau, amma kuma a halin da take ciki baze yuwu ka dauketa ba dole sedai a jira har seta haihu kuma kaga lokaci yana qara tafiya kamata yayi ka fara yin gaba kaje ka shirya duk abinda ya kamata idan ta sauka ta yada wanka se kazo ka dauke ta ku tafi ko ba haka ba?" Shawarar Audu.

Yakubu yayi na'am da maganar tasa dan haka suka shiga shiri, sun sanar da matayensu abinda ake ciki haka yan uwansu da suke uba daya, Goggo Fadi ta fasa musu kuka sanda suka gaya mata shirin nasu tana cewa wai me yasa zasu ce zasu bar gidan kenan ita basu dauketa uwa ba ba zata iya kula musu da matansu ba? Daga Yakubun har Audu babu wanda ya kula maganganunta dan gani sukeyi ihu ne kawai bayan hari basu yarda wai har zuciya Goggo Fadin tayi tuba na gaske ba. A satin suka shirya tafi, sun tsara da gida ya kammala Audu ze kwashi Bara'atu da Balaraba duk su koma Kano da zarar Balaraban ta haihu kuma zata koma Wailari tayi wanka inda daga can zata bi Audu, da akwai Yayanta da yake zama a Ikkon shima Shanu yake kaiwa daga baya kuma yayi zamansa can matansa biyu ya kai daya can sunzo ganin gida zasu jima dan haka suka bari akana idan Yaya Iron ya tashi komawa zata bisu su tafi tare.

Ana i gobe zasu tafi da maraice Balaraba ta haihu ta samu ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? mace wannan karon Ubangiji ya bata da sauqi dan da tasowar ciwon gaske da haihuwar beyi awa daya ba, Audu ya fita qaraso musu siyayyar dan abinda zasu buqata kafin su koma Kano se dawowa yayi ya tarar da yar Baby me kama da Dadarsu sak haka ya kwasheta seda sukaje Asibiti aka tabbatar ita da yarta duk lafiyarsu qalau, farin ciki ba'a magana, Yakubu yayi mata hudu ba da Hafsatu zasu ringa kiranta Dada dan duk wanda ya gabta se ace Dada ta tafi Dada ta dawo. Haihuwar tasa suka qara kwana biyu, yan Uwan Balaraba suka dauketa zuwa gida wanka Audu ya wuce Kano tareda Yakubu daze koma Ikko. Wata daya bayan haka Audu da Bara'atu tareda Baballiya sukayi qaura Kano, qarshen zamansu a Bechi kenan.

Ranar da zasu tafi mota guda ya dakko aka kwashi yan rakiya dan an kwashe kayansu daman tuni. Yan uwan Bara'atun uku Yayarta daya se Matar wanta da qanwar Babarta sauran sukace a hankali zasuje suga inda suka koma se murna suke tasu ta koma Birni suma sun samu gurin zuwa haka Inna Hajara har wani qafafa take tana yadawa wanda suka ringa Adawa da Auran Bara'atun da Audu magana ciki harda Babanta. Yan gidansu Audu ma kafataninsu su Bilki dasu Amina harda Matar Yaya Baba data Aminu da Amaryar Hashimu wadda se bayan sun tafi ya samu labari ya ringa tijara yana rashin mutunchi Goggo Fadi da tabi hanyar Allah tuni tun bayan rasuwar Dada batace masa qala ba, ita kanta taso zuwa amma ciwon qafa daya sakata gaba kwana biyu ya hana amma Audu ya mata Alqawarin da kansa ze dawo ya dauketa taje ta kwanar musu biyu kuma tafiyarsu ba tana nufin sunmanta dasu bane, basu da wasu dangi a duniya bayan su, su goman nan da Mahaifinsu ya haifa sune dangin Kansu.

Yan Bechi suka ringa santin gida, kwanan su daya suka juyo Audu ya hado su da sha tara ta Arziqi qememe Abdullahi yaqi bin Babarsa Audu yace a barshi daman ai Abdullahi Dansa ne, uwar bata so ba dan daman ita ba wai son zaman da yake a gurin Bara'atun take ba kawai dai dan Aminun tsayayyae ne yasa ta kasa magana yanzun da Audu yace a barshi tace
"Amma Babansa be sani ba zeyi fada idan aka koma babu shi"

"Idan kin koma ki gaya masa ni Audu na riqe Abdullahi idan yana da jaa yazo ya dauke shi da kansa" ya fada mata zata sake magana Amina ta harareta tana cewa
"Sedai kece zaki cr bakya son zamansa a nan dan dai Yaya Aminu ya dade da fadawa kowa ya barwa Audu Dan nan kuma wannan baqin ciki kikewa Danki ze zauna a Birni yayi Karatu me kyau ya tashi a waye"

"Meye haka Yaya Amina?" Audu ya katseta, ta sake cewa
"Gara na fada mata ai idan kuma ta ce se a bata danta gashi nan ta tarkata su tagi dana Koma zan hadowa Muzammilu kayansa a kawo maka shi ga Yaran nan tuli a dangi har

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login