Showing 396001 words to 399000 words out of 467220 words

Chapter 133 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12167

se su dawo. Yanda take lan?wasa murya tana masa magana seka Wauka wata budurwa ce yar shekaru ashirin da saurayinta da suke kan ganiyar soyayya. Me mata gyaran jikin data kasance ?awarta tun ta yarinta se kallonta takeyi abin na bata mamaki da kuma sha'awa se murmushi take kawai tana kallonta harta gama wayar ta kalleta tace
"Hajiya Uwa ya akayi ne se kallona kike kamar kinga ba?uwar halitta. Matar tayi dariya tace
"Ai dole na kalleki Hajiya abun naku ne ya burgeni ya kuma bani sha'awa. Ina ma ace nima zamu farfaWo da tsohuwar soyayya irin haka da Babansu Hamza? Nifa yanzu idan kikaga munyi waya da shi to la budda zakka aka aiko da ita gida baya nan ya kira yayi kashedin kar a kuskura a taSa". Hajiya Zubaida ta ringa dariya kafin tace mata
"Hajiya Uwa kenan, ai ita soyayya bata tsufa sedai masuyin ta su tsufa kuma sau da yawa mu mata mu muke mayar da kanmu baya har suma mazan mu cire musu mararin abin a ransu. Da yawan mata da zarar an fara tara yara shikenan se mace ta tattare duk wata kulawar miji ta watsar ta mayar da hankalinta kacokan kan yara, masu Wan taSukawa sune suke ja da nisa har se an fara aurar da yara daga nan su dauki girma su Worawa kansu komai suce na yara ne yanzu idan kuma shi miji ma bu?atar kulawa ya nemo wadda zata bashi se ace yayi butulci seda matarsa ta manyanta sannan ze mata kishiya bayan ita ta tsofar da kanta komai ta denayi tace na yara ne shi kuma yana da bu?ata ya ake so mutum yayi?"

"To ai Hajiya dole ce take sakawa, ban da ku da rayuwa take tafi muku kamar ku kuka tsarawa kanku shiyasa har kun doshi tsufada shau?in soyayya a ranku mu kuwa kullum kana cikin tunanin ya zaka rufawa kanka asiri ina kaga ta wani soyayya da miji" Hajiya Uwa ta sake faWa. Zubaida tayi murmushi tace
"Haka dai kikace amma ita soyayya babu ruwanta da wadata ko talauci kaine zaka koyi yanda zaka tafiyarda ita daidai ta matsayin da kake ciki. Yanzu saboda Allah dubi fatarki wai sunan kina aikin gyaran jiki amma dubeki a bushe fatarki har tsagewa takeyi, ?amshin nan da kika sakawa mutane ya kama jikinsu ya kamata ace da ke ya zama jikinki ma amma ko aikin zaki fito kalli fa a yanda kike fitowa kamar wadda aka koro kuma idan mijinki ya hango wata da jikinta yake luwai luwai kice zakiyi jidali bayan laifinki ne baki gyara kanki ta yanda zaki cigaba da Wauke hankalinsa daga kallon matan waje ba, ya kamata da....." Maganganun ta suka katse dalilin faWowar da Hajiya Binta tayi Wakin tamkar jifa ta tsaya a kansu tana muzurai.
A tsorace Hajiya Uwa me dilka tayi baya tana cewa
"Subhallahi, a'uzubillahi minashshaidanirraj baiwar Allah daga ina?"

"Kallon sama zuwa ?asa Hajiya Zubaida tayiwa Hajiya Binta dake tsaye tana haki idanunta na yawo a Wakin kamar son tantance meye ?????!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!"da meye a ciki kafin ta mi?e ta doshi banWaki tana wata tafiya ta ta?ama wadda kana gani kasan da gayya akayinta domin a tunzura wani ko daga yanda take juya mazaunanta da suke nan har sannan da sauran mutunchinsu musamman da ba ?iba ce da ita can ba kuma bata wani haihu da yawa ba hakan ya taimakawa jikinta zama in shape, tana dab da shiga banWakin Hajiya Binta ta farga cikin Waga murya ta dakatar ta ita tana cewa
"Ina zakije tsohuwar kilaki? Ko in ce magajiya domin naga alamar kin samu ?arin matsayi a barikin". Me dilka taja gefe tana ganin ikon Allah, Hajiya Zubaida kuwa juyowa tayi fuskar ta washe da murmushi tana gyara Waurin towel Win da yake jikinta ta kalleta tace
"Duk wanda kika kira bakiyi kuskure ba Binta, gaskiyar ki ina dab da samun promotion daga kilaki zuwa magajiya me daraja ta Waya a gidan sweetyna Alhaji Abdulwahab" ta ?arasa tana kashea Hajiya Binta ido Waya abinda ya matu?ar harzu?a ta ?irjinta har sama da kasa yake tsabar yanda bala'i yake cin ranta ta nunata tana cewa
"Ke ?aramar yanyan, bana bu?atar maimaita miki karatun baya kin sanni kin kuma san me zan iya yi dan haka gargaWi nazo nayi miki da kaina ba aike ba tun wuri sahunki a likafa ki san inda dare ya miki domin baki da guri a gidana idan kuma tsautsayin tozarcin daya fi na baya kike nema se in ce Allah ya baki sa'a".

"Oh Allah sarki ai kam dai bama bu?atar tunasar da juna baya kin sanni na sanki, da naji kince gidanki kuma wannan ne bani da labarin yaushe sweet ya mallaka miki gidan? Koda yake wannan ba matsala ta bace domin bani da haWi da gidan domin ni bazan iya zaman cikin yawa hayaniya ta hanani more amarci da angona ba kin san muna da carry overs. Banda ma fitina irin taki Binta wane kishi kuma zaki tsaya kinayi yanzu ke kina fama da kanki idan adalci zakiyi ai da kanki ya kamata ki ajiye kwananki ki nemo masa wadda zata maye masa gurbi domin dai a yanda kike baki da wata sauran mamora dubeki dan Allah idan kuka jera da Alhajin ma yanzu ai se ace babban Wanki ne" Zubaida ta faWa cikin tsantsar sha?iyanci, a mugun fusace Hajiya Binta tayi kanta tana cewa
"Abu ta kazan uba ni zaki kalla Zubaida kice na haifi Audu ni zakiyiwa wannan cin fuskar?".
Gaba Waya ta tafi da niyyar fizgo Hajiya Zubaidan tayi mata casar gero kamar yanda zuciyarta take ingizata a lokacin, tsautsayi, kafarta ta tunkuWe wani kofi da Zubaidan ta ji?a kuSewa da ruwan Wumi tana jira ta ji?u tasha se gashi Hajiyar ta tan?waSar ba tareda ta sani ba kuma ta taka ji kake tim santsi ya kwasheta ya watsar a ?asa, ?un?uminta ya amsa ta dafe baya lokaci Waya ta ?wala ?ara ta shiga malelekuwa a gurin azaba na ratsa.
Hajiya Zubaida ta kaWa kanta ta shiga banWaki ba tareda ta bi ta kanta ba se me dilkarce ta tsaya akanta tana cewa
"Wai, Allah sa baki targaWe lafiyayyar ?afar ba, mata kina zaman lafiyarki kin fito neman jidali ashe tsautsayi ne ya kirawoki".

Hajiya Binta dai kuka take a zaune dan ba ?aramin buguwa tayi ba ta kuma kasa tashi data dafa hannunta se ya zame bata ma fahimci ruwan meye haka me sulSi daya kayar da ita ba. Halima ta shigo Wakin kawowa surukarta kazar da ta Wumamo mata ta tarar da Hajiya Bintan na kuka ta ringa salati ta fita da sauri ta kira Dr Hassan da yake gida yana shirin fita suka haWu da me gadi suka kwashi Binta aka sakata a mota tana ta wash wash bema tsaya tambayar meya faru ba suka tafi. Da Zubaidan ta fito ta tarar Uwa me dilka tana gyara gurin kaya kawai ta fitar ta saka a jikinta ba taredata tambayi ina Hajiyar ba duk kuma yanda Uwar taso taji ?arshen gulma tunda dai ta gane Hajiya Binta kishiyar Zubaidan ce tayi shiru bata ce mata komai ba dole ta tattara ta tafi dan sun gama aikin ranar se kuma gobe.
****************************************
Jafar ya sauke Hajiya Ummu tareda Anty Munirah a gaban kantin da zasuyi siyayya ya wuce yana nazarin maganganunsu a zuciyarsa. Baya fatan auran Hajiyarsa ya mutu a dalilinsa ko Afeeyah sannan kuma besan ta yanda ze kaucewa fushin Alhaji ba tareda yaga laifinsa ba. Duk da ace Alhajin beyi gaggawa ba yana da ya?inin ze iya shawo kan Hajiya ta yarda da muradinsa a hankali amma wannan abin sake dagula komai yayi gashi duk waWanda yake zaton zasu masa maganin matsalar ta hanyar rarrashin Alhajin sun zame, daga me goyon bayan abinda Alhajin yayi Baba Al?ali kenan se wanda ya nuna shi son Afeeyar ma yakeyi. A fili ya furta "babban kawai, ko me zatayi dashi da wani ?aton cikinsa oho" yayi tsaki.
Seda ya tsaya yayi sallar la'asar a hanya domin bai mantawa da takararda Ahmad yake yawan yi masa a kullum ta tsayar da salla akan lokaci. Yakan gaya masa gwargwadon wasa da sallarka gwargwadon yanda rayuwa zatayi maka ?unci domin sallah tana daidaita al'amuran mutum" ya kuma gamsu da hakan yana kuma iyakar ?o?arin sa domin ko wasa zasu buga muddin yaci karo da lokacin sallah yakan ro?i alfarmar kar a sakashi a farko har se yayi tukunna idan kuma suna ciki ta riske shi se ya nemi duk yanda yayi aka cireshi ya gabatar da sallarsa.
Be tashi daga masallacin ba ya kira wayar Afeeyah, duk da ya so se bayan magriba zeje amma yanzun yaji baze iya jurewa ba kewar ta yakeyi sosai. Seda ya kira sau uku kafin aka Waga, shigen muryarta amma baya kai tata sanyi da tasirin da take dashi a kunnuwansa ba.
"Tana sallah ne, idan ta idar zata kira" Anty Sauda data Waga wayar ta faWa kafin ta kashe. Sake kira yayi ta amsa tana sake maimaita masa abinda ta faWa da farko yace
"Am, daman zanzo gurinta ne idan ta idar kawai ki gaya mata ina hanya"
"Tana nan Jambulo ai kasan gidan ko?" Anty Sauda ta bashi amsa. Ya Wan shafa kansa yace
"Ina wuni" saboda ya gane wacece, daga ta amsa kafin tace
"Gata ma ta idar" ta mi?awa Afeeyah dake kallonta wayar, ta karSa ba tareda tace komai ba ta katse kiran. Rufeta tayi da faWa akan me zatayi haka?
"To ni nace ki amsa mun waya ne balle har ki gaya masa inda nake? Saboda da fa yace zeje can gidan yasa nazo nan kuma kawai kin kama kin gaya masa" Afeeyan ta faWa tana zumSurar baki. Anty Sauda tayi tsaki ta wuce tana ce mata
"Ai se ki tashi ki canza she?a munafuncin banza kawai ana so ana kaiwa kasuwa to sedai kiwa wanda be san halinki ba kuma badai ni ba" ta wuce ta barta tana ku ?un?uni.

Jafar kuwa tashi yayi ya kama hanya, seda ya tsaya a Rufaida na kabuga ya siyawa au Amal tarkacen ciye ciye dukda bashi da tabbacin tare ta tafi dasu sannan ya isa gidan yayi mamakin yanda akayi ya iya gane hanya dan rabonsa da gidan tun ranar cocktail Win auranta da Ahmad. Me gadi da Anty Sauda ta sanar masa da zuwan Jafar Win yana ganin mota ta alfarma ba ko tambaya ya wangale get, ya shiga yayi parking, ya ringa kallon compound Win anyi sauye sauye amma be manta zuwansa na farko ba ranar da suka fara haWuwa da Afeeyah dan zuwansa na biyu cocktail ta baya ne gurin da akayi bata cikin main house Win ma ake shiga ba get daban ne amma yaga kamar an shigo da filin ciki dan compound Win ya ?ara girma sosai.
Hibban babban Wan Anty Saudan ya fito sanye da Jersey me Wauke da number AJAY, ya rungume Jafar tamkar ya wani sanshi sannan ya fitar da wayarsa yayi musu selfie shidai Jafar se murmushi yakeyi ya tuna zuwansa na farko lokacin yana Wan yaro haka ya fito da gudu ya rungumeshi sannan ya taro masa yaran layin wai suzo suga Jay a gidansu amma gashi yanzu ya zama saurayi a ?alla ya kusa shekaru ashirin.
Tare suka shiga cikin gidan ya kaishi har falon Abbansu yana ta murmushi yace
"Bari na kirawo Anty Afeeyan"
"Saura kuma yau ma kayo mun gayyan abokanan ka irin na wancan lokacin. Hibban ya ri?e baki yana dariya yace
"Mutum uku kawai, Aa huWu" ya nuna da yatsunsa, Jafar ya girgiza kai alamar Aa sannan yace
"Bana cikin yanayi me daWi ka bari wani lokacin ba yau ba". Badan Hibban yaso ba ya juya ya kira masa Afeeyah wadda seda Anty Sauda ta auna mata ashar kafin ta tashi taje.
"Kasa zama kikayi saboda zirgilli zuwansa gidan nan na farko amma yanzu saboda munafunci ko, Allah ya yafe miki Afeeyah" Anty Sauda ta faWa tana yin ?wafa.

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 38*

"Se dai ka kira Zakariyyah ko Yakubu dan ni ka ganni yanzu na wuce Zariya Abuja zanje" Naziru ya faWawa Dr Hassan daya kirashi ya sanar dashi Hajiya na Asibitin sa. Se bayan da aka dubata ya tabbatar babu wata babbar matsala buguwa ce kawai kuma an mata allurar rage raWaWi har tayi bacci bayan data gama musu iface iface kamar wadda ake zarewa rai shine ya kira Nazirun dan su sani. Cike da mamaki ya kashe wayar, babu wani jimami ko damuwa tattare da Nazirun daya shaida masa mahaifiyarsa ta faWi har gata a Asibiti sema uzuri ya bashi akan ya kira wani cikin yayanta. Ya shiga lalubo number Yakubu dan Alhaji Zakariyyah yanzu ai ya zama uzuri shima maridi ne me bu?atar a kula dashi. Har ya danna layin Yakubun ya maza ya katse daya tuna duk cikin yayan Wakin nata ma babu ta?adiri wanda be damu da shirginta ba irinsa.
Zuciyarsa ta raya masa ya kira Jafar dan shi kaWai ne ko ke yakeyi ze baro ya taho amma kuma wata zuciyar da tausayin Jafar ya cikata ta hanashi. Yaron yana cikin yanayi be kamata ya ?ara masa wata damuwar ba gara koma menene daga baya ya sani dan haka se kawai ya shiga group Win da Ahmad ya buWe musu ya nemo number Nazira ya kirata ya shaida mata, ba'a jima sosai ba kuwa tazo tareda Sarah sannan ya fita dan ba Asibitin yayi niyyar zuwa ba tsautsayin da Hajiyar ta samu ne ya kawo shi. Se bayan magriba kafin Hajiyar ta farka lokacin Hajiya Ummu da Munirah sunje bayan da Nazira ta lallashe su da?yar, tana farkawa kuwa ta niyyata Worawa daga inda ta tsaya a tijararta tana zage zage da cin alwashin rama abinda Zubaida tayi mata. Hajiya Ummu ta dubi Nurse Win data shigo duba Hajiyar duk ta?i tsayawa tana ta rashin hankali tace mata
"Kina ji yar nan, a Asibitin nan nasan ba zaku rasa irin allurar nan da akeyiwa masu tare hanya ba ko?"

Binta tayi shiru tana kallonta dan bata fahimci abinda take nufi ba, Nurse Win kuwa murmushi tayi dan take ta gane allurar guba take nufi da akewa yan fashi wadda take cin jiki a hankali harta kashe mutum. Tace mata "Ba'a aje irin kayayyakin nan a Asibiti nan Mama". Ummu tayi tsaki ta sake cewa
"?ila dai baki sani ba, bari hassan yazo ayi mata akwai a taimaketa a gajarta mata zango, jahadi babba zamuyi wannan masifa har ina? Ranki ke kaWai Binta kin addabi duniya ai wlh gara ki ?ara gama mu samu nutsuwa kafin mu biyo ki" ai ko ta fashe da kuka musamman da Su Nazira duk halin da suke ciki suka fashe da dariyar maganar Hajiya Ummu. Shikenan suka samu salama tayi shiru bayan data gama cewa kowa ya tsaneta, ace Ummu ce zata ce a mata allurar guba ta mutu me ta tsare musu a duniya? Ita dai Nurse da gayya ta ?ara mata allurar da zata daWe tana bacci ko sa samu salama. Se goma su Nazira suka tafi Ummu tace ba zata kwana da ita ba ?arshe se Munirah ce ta zauna har sannan kuma babu wanda ya biyosu daga can gida abinci ma se order Sarah tayo musu to waya ma san abinda ya faru? Munirah kuma tayi waya yarinyar da take zaune tareda ita ta kawo mata yan kayyakin da zata bu?ata na kwana.

JAFAR
Seda yayi jiran mintuna biyar kafin ta fito. Ya ringa kallonta yanda ta Waure fuska kamar wadda taga dodonta baki a tunzure ta samu kujera can gefe ta zauna ba tareda tace masa komi ba. Yayi murmushi dukda yanda ta shigo masa ba sallama ta kuma wuce ta zauna ya sosa masa rai. Baya son wula?anci musamman daga gurin na ?asa dashi tunda dai ko babu komai tsakaninsu ai ya girmeta, koda yake damar sa ta gani, ze kuma saita mata layi. Bisa umarnin zuciyarsa ya tashi daga inda yake zaune ya koma kujerar dake fuskantar ta ya zauna ba tareda yace mata komi ba ya zuba mata ido kawai yana kallonta.
So yake ya fahimci abinda ke tattare da ita daya saka zuciyarsa ta mutu akanta, ya kamata ace abubuwan da suka faru sun saka ta fice daga ransa amma babu abinda ya canza sema sake samun guri da tayi ta hana rayuwarsa yin armashi ba tareda ita ba.
Irin kallon ?urillar da yake mata shi kansa yasan ya zarce na shari'a, yana ganin yanda ta zama restless, se mutsu mutsu take ta kasa kuma haWa ido dashi tana motsa baki da labudda yasan zaginsa takeyi ko makamancin haka. Sama da mintina biyar suna haka kafin tayi jarumtar mi?ewa saboda tsakani da Allah kaifin idanunsa da ya zuba mata sun fara huda tsokar jikinta bama iya kafin fata ba, wata girgiza zuciyarta takeyi ?arfi da yaji da lura so yakeyi seya tayar da abinda ke bacci cikin ?irjinta. Da sauri ta runtse ido saboda jin ya ri?e hijabinta daidai tazo giftashi. Taja numfashi me ?arfi ta fesar huntunta daya bushe saboda bata wani yi numfashi me kyau ba da take zaunen. Kamar wata igiya haka yaja hijabinta ?iiii ya maidota baya, da kanta ta nemi guri ta zauna saboda yanda ?afafunta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login