Showing 306001 words to 309000 words out of 467220 words

Chapter 103 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12392

Abokiyar kukanta ita ko yanzu ba'a sakata a lissafi dan tana can gidan masu rangwamen hankali abin dai ba'a cewa komai. Daman hausawa sukace komai nisan dare gari ze waye to ita dai Turai har nata garin ya waye da wurwuri kuwa, a lokacin da take tsaka da cin duniyarta da tsinke ta sakankancw se gashi Allah ya kamata

Irin mugun asirin mallakar data ringa dirkawa Mijinta daman bokan nata yasha gaya mata idan fa Alin ya mutu akwai ayyukan da zasu iya juyawa kanta, a izgilanci irin nata lokacin tace ba komai kafin ya mutun se a warware sedai ba'ayiwa Allah wayo balle dabara, lokaci ya ara mata ta zuba sharafinta se gashi babu zato babu tsammani ya Wauke Alin ya kuma juyar mata da duk wani mugun abu data Wauki lokaci tana aikatawa akanta.

Duk kuma da wannan abu daya samu Turai be zamewa Binta ishara ba, gani ma takeyi tamkar sakacin Turai ne yaja mata, kamar yanda tace dangin Mijin Turai ne suka jefeta saboda su cinye mata gado, kuma itama tasan duk abinda yake faruwa su Aisha da Rabi dan haka a yanzu menan mafita take kota halin ?a?a.

Yan uwanta tun asali bata Wauke su a bakin komai ba balle ta kai musu kokenta, koma ace tana shawara dasu Win wannan matsalar da take ciki ba wadda zasu sani bace domin Allah ya ?ara zasu mata su kuma haWa mata da tofin ala tsine tun ba Hajiya Ummu da Munirah wadda har yau kuka take tana nadamar biyewa mugun halin Binta, shekarunta Hamsin da bakwai a duniya ta rigada ma ta cire ran yin aure a rayuwarta shiyasa ta siyi gida ta Webo yayan dangi suke tayata ta zama tana kasuwancinta da Allah ya sanya mata albarka ciki take komai takewa Yaran da suke hannunta, a Kano take zaune amma seta shafa watanni bata ma le?a Bintan ba saboda sun dena shan inuaa Waya balle kuma sauran da suke Kaduna indai ba wata hidima ba babu abinda yake kawo su gidan Bintan itan ma kuma hakan ne hidimar ma ba kowacce ba se ta Wanda ya isa take zuwa dan haka babu yanda za'ayi ta tafi neman mafita gurinsu a yanzu.

Yayan da take zaton zasu zame mata rufin asiri abun ya gagara. Dama dama Alhaji Zakariyya yakanzo su tattauna ko yanzun shi yace ze kaita gurin wani malaminsa asan abinda za'ayi akan Alhajin dan shi kansa daman yana da bu?atar zuwa saboda wasu abubuwa da be gane musu ba da suke faruwa a kamfani.

Naziru ko tuni ya zama Wan kansa, se ya kwashe watanni shida be shigo Najeriyar bama gaba Waya balle yaje gidan sedai suyi magana a waya abinda yasa bata damu sosai ba saboda yanzu kuWaWen ta na gurinsa ana ta juyasu kuma mahaukaciyar riba take samu ba kaWan ba.

Shi kuwa Yakubu tace ta sallamawa duniya shi muggan kalamai babu Wanda batayi masa ba shida Faisal dalilin tunda suka cicciSashi ya zama AG na Bechi group ya tare duk wasu hanyoyin da take kwamuso kuWaWe shi kaWai yake morar abin se Faisal da ya shiga shima yanzu sun haWe kai suna azurta kansu ita dai ta kafasu yanzu kowa ya watse ya barta a gurin Jafar kaWai take jin sau?i shi take kira tayiwa kuka ya rarrasheta sannan ya tura mata da ko nawa ta bu?ata.

A yanzu ita da kanta take so ya bar ?wallon ya dawo gida tunda ta fahimci shi kaWai ne abin yarda cikin yayan data haifa, shi kaWai ne baze mata mugunta ba dan haka ya dawo gida zata shiga ta fita duk inda ya kamata ta sake maido da martabarta da ikonta a gidan, ba zata Sata shekaru aru aru tana gini se sanda tazo gangara kuma ace komai ya lalace mata baze yuwu ba, shi kansa Jafar Win se tayi aiki sosai akansa ta rabashi da tsinannen yaron nan daya zame mata ciwon ido sannan ta sake mallakeshi yanda ko wuta tace ya faWa ze shiga ba tareda musu ba kafin nan komai ya koma hannunsa.

Kamar kuwa yanda Alhaji Zakariyya ya mata al?awari bayan ya samo musu appointment a gurin Malaminsa suka shirya tafiyar, kusan Bodar Najeriya da Nijar ta Jigawa mutumin yake, tafiya sukasha kamar zasu Sata, tun guraren la'asar suka shiga ?auyen da Ma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?laminyake amma basu kai inda gidansa yake ba se ana kiran sallar Magriba harta fara tunanin kodai siyar da ita Zakariyya zeyi tunda yanzu duniyar babu Allah cikinta komai ma me iya faruwa ne seda suka isa kafin hankalinta ya kwanta.

Aka basu masauki, daga waje gidan kamar tsohuwar firzin amma, katon gini me bene seda suka shiga idontaya buWe ganin guri ?al?al ga Wakuna rututu kamar hotel. Seda ta bubbuga sallolin da basuyi ba ba kafin ta kishingiWa ?afafunta duk sunyi tsami dan ma basa tare da yunwa dake Zakariyyan yasan inda zasuje shi guzuri sosai yayi musu tun tanawa abincin cin daWi kuwa har ta ture ta koma zare ido. Har bacci ya kwasheta bugun ?ofa ya farkar da ita a gigice, ?arfe daya harda rabi na dare Zakariyyan yace ta fito layinsu yazo. Haka suka tafi tin?is tin?is Wakin da Malamin yake ganin ba?i, Zakariyyan ne ya fara shiga dan yace kowa nada sirrinsa su shiga daban daban befi minti sha biyar a ciki ba ya fito lokacin har baccin gajiya ya sake kwasarta a inda take zaune.

Tana shiga ta fashewa Malamin da ke nan kamar mahaukacin Aljani da kuka, seda tayi me isarta kafinta fara zayyano masa matsalolinta da burikan da take so ya cika mata shidai jinta kawai yake yana zare ido harta gama kusan awa guda tana aurutu kamar lalatacciyar radiyo kafin tayi shiru tana goge ido.

"Ke kuwa kamar kinfi kowa matsala a duniyar nan Hajiya, sannan bukatunki ai sun zarce hankali Allah ne kaWai ze iya miki wadannan abubuwan da kika lissafo a lokaci guda. Banda ma dai zuciyarki ta rigada tayi hannun riga sa Imani a shekarunki yanzu Hajiya ai kamata yayi ki kama carbi kiyita Istigfari ba wai kici gaba da neman duniya ba dan ko ni na kai shekarunki watsar da duk wani tsubbu zanyi na koma ga Allah amma tunda kinzo zamu miki abinda zamu iya, kije wanda kuka zo tare yasan yanda akeyi ze kaiki inda zaki biya Aljanu sadakin aikinsu" Malamin ya faWa mata yana zare idanu, tayi mici mici da ido zata cigaba da rattaba zance ya Waga mata hannu yana cewa

"Tashi kije tun kafin Dan inna ya shanye miki ?afa dan ya ?osa da maganganunki da basu da ?arshe" kafin ma ya dire tuni ta kai ?ofa, a shanye mata ?afafu ta koma gida tacewa Audu me? Ita da tayi masa ?aryar Kaduna zataje Mijin Salima Bashida lafiya ta koma da sili silin ?afafu ana gani za'a san aikin Jinnu ne ta sake shiga uku ta lalace.

Seda ta Wora hannu akai sanda aka karanto mata miliyoyin kuWaWen da zata bayar wai a sunan kafin Al?alami idan aiki ya kammala zata cika sauran, dubi Wari biyar ta sako a jaka shima saboda yanda Zakariyyan ya ringa nanata mata zata kashe kuWi amma zata samu biyan bu?ata se gashi tashi Waya ana neman miliyan goma deposit, kamar tace ta fasa amma data tuna halin da take ciki da nasarar da zata samu idan aikin ya kammala haka ta daure aka cire ta account ta bayar dan yace baze ranta mata suzo gida tace bata san zance ba, haka suka sake yo asubanci suka juyo Kano seda sukazo Gadar Lado harta fara hamdala saboda fara jiyo ?amshin gida a garin shan rawun wata babbar mota tayi tafiyar yaji dasu se ga motarsu tsamo tsamo cikin lambatu.

*Mg's skincare*


Sister's duk wacce bata anfani da products na mg's skincare hakika anbarku abaya acan karshen bayama kuwa domin duk Mai tantama akan kayan gyaranjiki yacire products na mg's domin kayansu dayane tamkar dubu>???shin pimples ne matsalan,tabo,sunburn,acne,eczema,knuckle,black head,wrinkles kokuma kinshafa maine yabatamaki jiki yar'uwa kinrasa yanda zakiyi kijaraba products na mg's bi iznillahi zakisha mamakin yanda skin dinki zaikoma Koda iya soap dinsu kadai kika dana saikinsan gidan abun kikazo=?L?Ina Wanda sukeso su haskaka fatarsu tagoge kidinga glowing kizama kalar Madara qirar models =?
?yazama duk inda kikashiga Sai anjuya>?p?
Kayansu =د? natural ne sannan organic zaigyaramaku jikine fiye da tunaninku yafiddo muku da ainihin natural beauty dinku
Sunada sabulai kala kala dakuma set na mayuka dasu scrubs da sauran kayan gyara=??
Akwai kit hawa hawa na gyaranjiki daidai da aljihunku=??
Ina Wadanda basasan anfani da cream mg's skincare sunada special soap da zaitafi daidai da skin dinku Wanda ko baki shafa Mai ba zallan sabulun zaiyi fitting skin dinki ya baki duk result din da kike nema=??
Suna da hadin amare na musamman Wanda duk Wanda yayi anfani dashi bakya bukatar zuwa wani gurin gyaranjiki=?
?domin yanda fatarki Zata koma ke kanki sekinsan kinhadu fad'?
Price list na kayan mg's
-Herbal whitening black soap 4k
-Special soap 10k
-student package 10k
-beauty kit 14k-18k
-flawless skin beauty kit 22k
-bridal kit 25-30k
Mesan kayan mg's should chat 08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391

Note:iya wadannan numbers din kawai zaku samu products na mg's skincare kawai duk wata number da ba wadannan ba bata mg's skincare bane=?O?

Adade anayi Sai gaskiya siyan nagari maida kudi gida>??


*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 17*

Jama'a suka Wauki salati, da taimakon Allah aka samu aka janyo motar aka fito dasu daga Hajiyar har Zakariyya babu wanda yake cikin hayyacinsa shi kansa ya fashe ma saboda glass daya daka yana zubar da jini babu Sata lokaci aka shige dasu Asibitin Malam kafin wanda suka kaisu suka fara laluben Ahalinsu. Wayar Hajiya da take a buWe aka samu number Jafar da basu daWe da gama magana dashi ba abin ya afku, shiya kira Yakubu ya sanar dashi abinda ya faru Yakubu kuma ya kira Alhaji .

Dashi da Momy tareda Faisal se Sarah suka tafi Asibitin a hanya ya kira Baba Al?ali shima ya gaya masa halin da ake ciki yace gashi nan zuwa can Asibitin suka haWe gaba Waya sun samu likitan daya dubasu ya masa bayani akan ita Hajiyar ta samu karaya guda biyu Waya a cinya daya a tsintiyar hannunta na dama se buguwa da yan ciwuka a inda ba'a rasa ba da safe za'ayi mata Wori Zakariyyan dai abin yafi muni dan buguwar da yayi akamsa ba ?arama bace a yanzu ma ba zasu iya cewa ga matsayin da yake ciki ba har se bayan ya farka an masa gwaje gwaje tukunna.

Sun Wan jima suna tattaunawa kafin suka wuce gida aka bar Sarah da matar Zakariyya uwar gidan se Faisal zasu zauna dasu.

Se washe gari da safe sannan Hajiya ta farka cikin azabar ciwon jiki ga karaya data fara tsami, ta ringa kuka kamar yarinya likitoci na bata ha?uri suna gaya mata jininta saman ya hau idan taci gaba da kuka abin baze mata da kyau ba tama godewa Allah babu wani mummunan abu daya sameta ga Wanta nan shi har sannan be farka bama balle asan halin da yake ciki. Da akazo batun za'a Worata fafur tace ba za'a mata na Asibiti ?afarta da hannunta su?i warkewa su ruSe a cuceta, aka kaWa aka raya tace bata yarda ba.

Aka kaWa aka raya tace ita ba ta yarda ba, Yakubu yayi zuciya yayi tafiyarsa se Faisal ne ya kira Alhaji ya gaya masa yace su barta jikinta ne tayi yanda take so haka ko suka tattara suka wuce gida aka shiga neman me Wori abu kamar sa hannu aka rasa. Har gidan sarkin Wori Alhajin ya aika akace duk masu Worin sun fita amma idan sun dawo zasuje, safiya ta wuce rana yamma har duhun dare yayi ba labari ga Hajiya ?afa nata suntumewa tana sakeyin tsami, daka ?arshe dai haka ta sake kwana ba tareda an Worata ba ba zancen bacci kwana tayi tana walagigi tana wayyo, da safe da Alhajin ya shiga yaga yanda take ciki ne yace a Wauke ta a kaita Asibitin kota ?arfi ne amma ta tirje, ransa ya Saci, suna tsaka da mahawarar akazo akace ga me Worin an samo wani dattijo da yar jakarsa ta aiki se mataimaka guda biyu suka gaisa da Alhajin kafin ya fita ya basu guri.

Kafin a gama seda ta suma sau uku, kashi da fitsari kuwa masu Worin seda sukayi guzurinsa a jikinsu kafin kace me zazzabi me zafi ya rufeta da ciwon kai da jiri ko ba'a faWa ba jininta ne ya hau tsabar wuya jikinta har wani gafgaf yake ta zabge lokaci guda ta fita a hayyacinta haka dai masu aiki suka gyarata suka gyara guri Dr Charles yazo ya dubata yana ta surutun ya za'ayi ayi mata Worin gida Alhaji yace babu ruwansa yayi abinda ya kirashi kawai ya tafi.

Haka Hajiya ta shiga jinyar ?afa da hannu cikin tsananin Azaba kullum kuka bata samun sau?i se tasha magungunan da aka bata na rage raWaWi a cikinsu akwai me saka bacci ga karaya duka biyu kullum ?ara suntumewa sukeyi hannu da cinya se kyalli suke amma matar nan kamar me ta kafe ba za'a kaita Asibiti ba wanda yayi mata Worin dai kwana bibbiyu yake zuwa yana dubawa ya kawo mata ji?e ji?en da zata shafa yana ce mata ai kumburin alamar warkewa ne ta daure,seda aka ci sati yaso dubata yace wai Wori beyi ba se an sake karya gurin sannan a sake sabon aiki.

Mutan gida kowa na Wakin sa ihu da kururuwar Hajiya ya fito dasu akazo aka tarar da ita a sume yaran me Wori sun daddanneta shi kuma yana hada karare za'a sake sabon aiki aiko take Alhajin yasa security sukayi ram dasu ita kuma aka kwakwasheta se Asibiti.

Bayanin da likitoci suka farayi akan karayar tata ya saka Alhaji sakawa a nema mata visa tareda Zakariyya da za'a fitar Germany saboda shi tunda ya farka bincike dai ya nuna komai nasa lafiya lau amma a zahiri ba haka bane ba dan baya magana baya motsa jikinsa da kansa se an taimaka masa sannan babu tabbacin ma yana jin maganar idan anyi masa, haka aka tattara su suka tafi jinyar se fatan Allah yasa a dace dan dai ?afar Hajiya da alamu ko zata warke tofa zata nakasa ba zata mi?e taci gaba da tafiya yanda take a da ba har gara hannun shi da sau?i sau?i.

Jinyar su Hajiyar da yanda kowa ya rasa kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan dalilin iface ifacenta ko bacci me daWi basa iyayi shi ya Wauke hankalin jama'ar gidan daga abubuwa da yawa. Tunda abin ya faru sau Waya Ahmad sukaje tareda Fatima suka dubata suka kuma je Asibiti suka duba Alhaji Zakariyya kwana biyu tsakani Fatima ta tafi Umarah shi kuma ya tafi Lagos dan yaran ma nan gidan aka kawo su gurin Momyn to kururuwar Hajiya da basu saba da ita ba duk ta firgitasu suka ringa kuka su gida zasu tafi shine aka kai su gidan Sarki dan yana kusa da makarantarsu suka zauna acan, se bayan su Hajiyar sun tafi ne kafin hankalin Alhaji ya koma ka Ahmad da ya kwashe kusan wata Waya a Lagos Win gashi ko a waya se anyi da gaske ake samunsu idan ma ya sameshi basa doguwar mahanayse yace yana uzuri ze kira kiran kuma da ba ze yi ba kenan.

Momy kanta Alhajin take tambaya ko suna magana da Ahmad se yace mata Aa, ya tambayi Baba Al?ali shima yace baya samunsa har gara a WhatsApp suna chat amma idan ya kirashi voice call baya amsawa, hankalinsu be sake dugunzuma ba seda Fatiman ta dawo tace ai itama tunda ta tafi sau biyu sukayi magana yace mata ze shuga Cotonou akwai kayan da ze duba tun ranar bata sake samunsa a waya ba kuma be kirata wannan Al'amari ya dugunzumawa kowa hankali Alhaji ya shiga bige bigen wataida kansa ya ke nemo lambobin abokanan harkar Ahmad Win Mr Olamide ubangidansa nacan Lagos Win bama ya ?asar yacewa Alhajin bema san Ahmad ya shiga Lagos ba kuma duk yaransa da suke kasuwanci tare babu wanda ya ganshi ko yasan ya shiga garin.

Wannan abu ya tayar musu da hankali matu?a dalilin Ahmad Win be saba haka ba, duk inda zeje seya sanarwa Momy da yayi aure kuma motsinsa komai ze gayawa matarsa, kwanaki biyu ana cikin jimami da tashin hankali tareda binciken inda za'a laluboshi har sun fara tunanin ko dai kidnapping nasa akayi? Amma idan haka ne tsayin wata gida yaci ace wanda suka Wauke shin sun magantu amma shiru babu wani labari.

Alhaji Audu, Baba Al?ali tareda Alhaji Abdullahi suka shirya tafiya Lagos neman Ahmad, jirgin Yamma zasu bi, ?arfe uku na rana suna zaune a falon Alhaji Audun tareda Momy da Fatima da duk ta fita hayyacinta a lokacin ma kuka takeyi, rarrashinta Baba Al?ali yakeyi yana cewa

"In sha Allah za'a same shi, jikina yana bani lafiya lau yake domin da da wani abu mara kyau addu'ar da ake tayi ina da ya?inin da yanzu mun sani, ku kwantar da hankalinku ki kuma dena damuwa kinji in sha Allah lafiya lau mijinki ze dawo" haka yake ta lallabata yanamata kalamai masu kwantar da hankali, Momy ma dai hawaye take sharewa da gefen Hijabinta, Al'amarin da rikitarwa tareda ban tsoro ace an nemi mutum an rasa an kuma kasa gano takamaimai inda yake.

Wayar Fatiman ce tayi ?ara, jikinta ya shiga rawa har tana suSucewa saboda ganin lambar Ahmad akan screen Win ta Waga duk suka zuba mata ido saboda rikicewar da suka ga tayi.

"Babe nazo gida bakya nan, kina gidan Umma ne ko wani gurin kika tafi?" Ya faWa cikin Sanyi bayan data amsa wayar. A maimakon ta bashi amsa se kawai tasaka kuka. Momy ta zare wayar daga hannunta zuciyarta na bugawa Baba Al?ali yace ta saka a speaker,
"Kuka kuma, meya faru?" Muryar Ahmad ta karaWe kunnuwansu.

"Ahmad kana ina? Ina ka tafi la barmu cikin zullumi da tashin hankali?" Momyn ta faWa muryarta tana rawa alamar itama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login