Showing 315001 words to 318000 words out of 467220 words

Chapter 106 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12183

da sugar sa yayi masa allura tukunna ya kwanta baccin ma ba wani me daWi yayi shi ba dan mafarkai mara sa kan gado da suka aureshi a kwanakin yayi tayi harya gwammace ya ha?ura da baccin kawai ya tashi yayi nafila sannan ya zauna yayi ta lazumi, tunda ya dawo daga sallar Asuba kuma ya zauna a falon, kukunsa ya haWa masa abinci saboda zesha magani be ma iya ci ba ruwan shayi kawai ya kurSa yasha maganin yace ya kwashe abincin shi kuma yaci gaba da zama yana jan carbi zuciyarsa kuma ta lula tunanin rayuwa.

Kamar jifa haka Issan ya diro masa ya dafe kujera yana haki saboda saura kaWan ya kifawa Alhajin akai cikin fushi yace masa
"Wane shashanci ne wannan Isah zaka faWowa mutane guri babu ko sallama?"

"Kuyi ha?uri Alhaji, bakoce tazo kuma tace Alhaji ?arami yana kwance bashida lafiya" Issan ya bashi amsa yana ja da baya. Alhaji Audu ya zuba masa ido alamar yana neman Karin bayani da sauri Issan ya sake cewa
"Alhaji Amadu namu, da Hajiyansa duka babu lafiya suna Asibiti".

"Ahmad kuma?" Alhajin ya faWa cikin yanayi kamar na mamaki kafin kuma yace masa ya shigo da ba?on, yana nan zaune Issan ya sake dawowa tareda Alhaji Munzali yana rakoshi ya juya. Cikin mutuntawa suka gaisa da Alhajin,

"Yana gida ko Asibiti?" Alhajin ya tambayeshi, a ta?aice ya bashi amsa cewar yana Asibiti.
"Jikin babu daWi Alhaji a hanzarta isa gareshi domin kowacce sa'a tana iya zamtowa ta bankwana a garesa yanzu" Alhaji Munzalin ya faWa kansa a ?asa. Kamar wanda ya lafta masa guduma a tsakiyar kai haka Alhaji Audu yaji maganar tasa, ya kafe shi da idanunsa da duk ?wa?war mutum da wuya ya gane abinda yake ?unshe cikinsu, murya a rarrabe yace

"Me ya faru? Menene yake damun Ahmad?"
Seda Alhaji Munzali ya kalleshi yanayinsa ya tabbatar masa da cewar bashida wata masaniya dangane da ciwon dansa, shi kuwa ba za'aji irin wannan gingimemiyar magana a bakinsa ba, shida basu haWa jini bama ya shiga tashin hankali akan abinda yaji inaga uban daya haifeshi? A maimakon ya bashi amsar abinda ya tambayeshi seya mi?e yana cewa

"Babu lokaci Alhaji, koma menene idan kaje zaga sani dan Allah a sanar da mahaifiyarsa idan tana raye ku taho yanzu jinkiri ze iya janyo muku nadama ta har abada" yana gama faWar haka yasa kai ya fice daga falon ya bar Alhaji dake zaune Shirim kamar wanda yayi makuwa. Kusan minti uku da fitar Alhaji Munzalin kafin ?wa?walwarsa ta gama tattara bayanai, da saurin gaske ya mi?e jiri ya mayar dashi be kai ?asa ba ya dage kujera yana haki.

"Ashe kana ?asa Alhaji ai dana sani da tuntuni nazo na tayaka hira" muryar Hajiya Binta ta karaWe kunnensa ta ?arasa inda yake tana cilla ?afa shidai yana tsaye seda yaji abinda yana masa yawo tsakanin kai zuwa zuciya ya lafa lafin ya sake yun?urawa ya nufi hanyar shiga cikin gidan. Da mamaki Binta ta bishi da kallo kafin da sauri ta mi?e zata bi bayansa, da alama ta manta ?afar ?arfe ce a jikinta yanda ta tashi da sauri yasa tayi gaba babu wani makari da zata kama dan haka ta tafi gaba Waya jikake ?um ta bige kai da center table Allah ya taimaketa gurin katakon ta buga ba gilashi ba amma fa ta bugu gurin be fashe ba amma take yayi ?ululu amma haka ta cangala dafe da goshi tabi bayansa.

Alhaji Audu kuwa kaitsaye falon Momy ya nufa, tana zaune kan abin sallah tana lazumi Waya hannunta kuma wayace tana ta kiran layin Fatima wayar na ringing amma ba'a amsawa, da sauri ta saki wayar ganin Alhajin a kanta, ba ?aramin abu ne yake sakashi shiga gurinsu ba yanayin shigowar tasa kuma da yanda ya tsaya yana zare idanu ya tabbatar mata da ba lafiya ba.

"Lafiya Alhaji me ya faru?" Ta faWa tana mi?ewa tsaye, bakinsa ya masa nauyi dan haka da hannu ya yafitota alamar tazo ta nufeshi se ya juya ya fice suka sake cin kiciSus da Binta bema lura da ita ba ya angajeta ya wuce Momy tabi bayansa cikin tashin hankalin rashin sanin me yake faruwa.

Se bayan sun zauna a bayan mota direba ya kunna kafin ya tuna ai mutumin be gaya masa sunan Asibitin da Ahmad Win yake ba, ya dafa kansa da hannu Waya direba dai ya taka mota ya fita guda daga securities na ganin motar Alhajin ya rugo da gudu se direban ya tsaya, sunan Asibitin ya shaida masa a cewarsa mutumin ne ya bar musu sa?o. Alhajin ya sauke ajiyar zuciya Momy kuwa tana jin an ambaci Asibiti ta fara hawaye dan tasan tabbas Ahmad ne. Hasashenta ya tabbata sanda taji Audun yana magana a waya kuma da alama da Al?ali yake yana sanar masa yazo Asibitin an sake kwantar da Ahmad.

"Ka gaya mun idan mutuwa yayi Alhaji na shiryawa abinda zan tarar" ta faWa cikin yanayi me ban tausayi da karya zuciya, kallonta yayi kawai ya girgiza mata kai ba tareda yace komai ba ya zubawa wundo ido yana kallon titi har suka isa Asibitin bakajin komai a motar se shashshe?ar kukanta. Kasa fita yayi daga motar bayan da direba yayi fakin Momy dai tun gabanin motar ta ?arasa tsayawa dakyau ta fice Alhaji Audu kuwa be samu kuzarin taka ?afarta ba seda Baba Al?ali ya iso gurin, tare suka shiga inda Fatima ke kwance wata nurse ta kaisu suka tarar da ita da Momy sun haWa kai sunata kuka gwanin ban tausayi.

"Wai me ya samu Ahmad Win ne kuma? Yanzu Fatima ba zaki dena koke koken nan ba dubi yanda kika lalace kodai akwai wani abu da kuke Soyewa ne ke dashi bakwaso mu sani?" Baba Al?ali ya faWa yana kallonta.

Alhaji Audu kuwa zamewa yayi ya fice ganin haka Baba Al?ali ya rufa masa baya, Nurse Win da ta rakasu suka sake tambayar inda Wayan mara lafiyar yake tayi wani duru duru tana kallonsu cikin tsawa Alhaji Audu ya shiga tambayar ina likita yake ina kuma mara lafiyar da aka kawo cikin dare duk ma'aikatan dake reception Win sukayi tsilli tsilli suna kallonsa kwarjininsa duk ya cika su. Ya sake buWe baki ze balbalesu da masifa Alhaji Munzali tareda likitan suka fito daga office Winsa yana ganin su Alhaji Audu ya nufesu yana cewa likitan
"Ga mahaifansa"
"Sannunku da zuwa bismillah Alhaji ku shigo daga ciki" ya faWa a duburburce yana buWe ?ofar office Win, Alhaji Audu Bechi ya bishi Baba Al?ali seda ya tsaya suka gaisa da Alhaji Munzali yayi masa godiyar Wawainiya kafin yabi bayansu.

Tunda likitan ya fara magana sukayi shiru tamkar ruwa ya cinyesu harya kammala ya tura takaddun sakamakon gwaji da hotunan da sukayiwa Ahmad Win gabansu yana cewa
"Addu'a kawai yake bu?ata a yanzu babu wani abu da zan iya cewa bayan wannan".

"Wannan ciwon shi yayi sanadin Hashimu, Aminu, Aisha, Lawwali ga Dada tasha da?yar seda aka yanke mata mama, nayi zaton ita kaWai ce taiyo gadonsa a cikin sauran zuri'armu ashe dai yana bibiye damu, yanzu kuma Ahmad Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yah ubangiji ka bamu juriya da karfin zuciyar Waukar wannan jarabawa, ubangiji ka sassautawa Ahmad" Baba Al?ali ya faWa babu zato kuka ya ?wace masa.

Alhaji Audu dai kamar mutum mutumi haka yake zaune akan kujera yana kallon likitan da alamun ruWu ya bayyana a fuskar sa, abinda ya fahimta basu san da ciwon dansu ba, amma ta yaya ace mutum na fama da lalura me tsanani kamar ciwon daji na Sargo (bone marrow cancer) har ya kai mataki na huWu kuma na karshe ace wani nasa be sani ba abin da mamaki.

Cikin lallashi yake cewa Baba Al?ali
"Kayi ha?uri Alhaji ka dena kuka"

"In dena kuka kace? Kasan akan wa kake magana kuwa? Ahmad Wina fa kake gayamun na shirya rasa shi a kowanne lokaci daga yanzu, koda ace kuka zunubi ne ina da ya?inin ubangiji baze kamani akansa ba domin ya fini sanin irin alhinin dake tattare da rashin da kake i?irarin mu shirya zuwan sa, shine duk wani buri da fatana, shi ne abinda nake tsammanin ko bayan ran mu baze bari zuri'armu ta tagayyara ba ashe ashe..." Kuka yaci karfinsa ya kasa ?arasa abinda yayi niyyar faWa.

Kamar wanda aka tsirawa Allura Alhaji Audu ya mi?e tsaye, Baba Al?ali ya kalleshi fuska jage jage da hawaye, idan ka kalli Audun zaka iya cewa babu wani abu dake damunsa tamkarma beji abinda aka faWa ba ko kuma be shafe shi ba amma shi Baba Al?alin ya karanci abinda shi kaWai yake iya ganoshi a idanun Wan uwan nasa.

"Ka zauna Audu karkace zakayi tafiya yanzu" Al?alin ya faWa yana ri?e hannunsa. Yayi ?i?am a tsaye yana zare ido kafin ya koma jaSar ya zauna kamar an watsa shi, a hankali ya saka hannunsa na hagu yana bubbuga saitin zuciyarsa, Baba Al?ali dai yana cigaba da share hawaye Likitan kuma sun zame masa kamar Tv ya kalli wannan ya kalli wancan amma fa tausayin Baba Al?alin ya cikashi taf da alamu ba ?aramin so yakeyiwa dan nasa ba.

Waya Alhaji Audu ya zare daga Aljihunsa ya shiga kiran Hassan, ringing biyu ya amsa ba tareda ya amsa sallamar daya masa ba cikin muryar bada umarni yace masa minti goma ta kawoshi Asibitin ya kashe wayar harya ajiyeta ya Wauka ya shiga kiran Muhammad, shi yake kula da duk wani abu daya shafi harkar tafiye tafiyensa kasashen waje, shima umarnin zuwa Asibitin da suken ya bashi sannan ya ajiye wayar ya haWe hannu biyu yana furzar da iska daga bakinsa.

A kusan tare Dr Hassan da Muhammad suka isa Asibitin dan haka tare suka shiga Muhammad Win ya kira Alhaji ya faWa musu inda suke.

Idanunsa fes akan Hassan kusan minti biyar yana kallonsa kafin ya iya buWe baki yace masa
"Wane ciwo ne yake damun dan uwanka Ahmad?"

Tamkar wanda aka jonawa shocking haka jikin Hassan ya Wauki rawa daman tunda yaga Kiran Alhaji ya kuma ce yaje Asibiti ya sameshi yasan tabbas abinda ake Soyewa ne ya bayyana. In ina ya farayi jiki da bakinsa suna rawa yace
"Ban sani ba Alhaji, duka test da mukayi masa ya nuna negetive ragowan kuma kafin akai ga yinsu sample Win ya lalace nayi nayi kuma yaje a sake Wauka yace shi yaji sau?i babu komai da yake damunsa kuma..." Be kai ga dire maganar ba ta yanke saboda mari me Wauke ji da gani da Alhajin ya zabga masa yana Wauke hannunsa kuwa jini ya fara biyo hancin Hassan Win seya dur?usa ?asa yanajin komai na juya masa Muhammad da Dr Musa sukayi kansa.

A mugun fusace tamkar zeyi aman wuta yace
"Me yasa ka Soye? Mecece ribarka? Ashe kaima kamar sauran kake ban sani ba Hassan?"

Dukda azabar da yake ji akansa da fuskarsa maganar da Alhajin yayi ma daga can nesa yake jiyota amma tsoro yake yayi shiru ya sake antaya masa marin da ze ida zautar dashi shiyasa ya shiga juya kai yana cewa

"Wallahi tallahi na rasa yanda zanyi, sanda na sani nima lokaci ya ?ure kuma ya sakani nayi masa al?awarin rufewa karna bari kowa ya sani saboda ciwon ya kai matakin da babu sauran saka rai da warkewa, damuwa da zullumi haWe da fargaba sun aureni ko abinci bana iyaci sosai duk sanda na tuna Ahmad bashida lafiya kuma bani da wata hanya da zan taimakeshi ga nauyin al?awarin daya saka na Wauka wlh ji nakeyi na tsani duniya da abinda yake cikinta. Kayi mun uzuri bada niyya nayi haka ba, na yarda na goya masa baya ne kawai saboda itace alfarma ta farko daya taSa nema a guri na na kuma kasa bijirewa hakan domin ina tsoron ya zama abu na ?arshe daze gifta a tsakaninmu" ya ?arasa yana fashewa da kuka kamar mace.

Shiru Wakin yayi kafin Alhajin yaja tsaki me ?arfi ya nufi ?ofa yana cewa

"Ka karSi sallamarsa ka wuce dashi Asibitin ka, kai kuma duk yanda zakayi karka kuskura a haura awa arba'in da takwas ba'a fita dashi ba, ze rayu, Anayin dashen Sargo ku kaishi ko inane cikin duniyar nan bana so naji wani abu in har ba zancen Ahmad ya samu lafiya ba" yana gama faWa ya fice saurin da yakeyi yasa Babbar rigarsa ta harWeshi ya dafe ?ofa"

"Ka zauna Audu karka kuskura ka bari ka kai ?asa komai ze iya faruwa ka dawo ka zauna muyi magana hargagi baze kawo mana mafita ba a yanzu dole mu haWa kai mu ceci Ahmad. Kai Hassan da kaida wannan likitan kuzo ku zauna ku tattauna, abinda akeyi a wajen shi akeyi anan, ku tuna karatun da aka koya muku tun daga firamare ta yuwu kun manta wani abun, za'a iya samun wata hanya da za'a magance abinda yake damunsa kuyi maza ku tunano dan Allah kar Wanda ya sake cewa baze rayu ba ai babu wata cuta da ubangiji ya saukar a doron ?asa ba tareda ya saukar da maganinta ba" Baba Al?ali yayi maganar tamkar wanda ya rikice ya shiga tattaro takaddun hotunan X-ray da akayiwa Ahmad Win yana Worawa Hassan su akan cinyarsa yana cewa

"Duba ka gani yace ?asusuwansa sun huje, ?odarsa ta taSu kuma wai tunani da damuwa sun raunana zuciyarsa nasanka da ?o?ari Hassan zaka iya samo dabarar da za'a gyara duk wani abu daya lalace maza ka duba ayi komai a gama mu kashe maganar a tsakaninmu base Aisha da matarsa sun sani ba"

"Kayi shiru Baba" Muhammad ya faWa yana kama hannun Baba Al?ali ganin jikinsa na rawa babu alamar ma ya San me yake cewa.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 20*

Kusan awa guda Alhaji Ausu ya bawa Momy yana sauraron kukanta dake tafe da kalaman neman agajin ubangiji akan wannan al'amari me girma daya sameta, tun tana kukan da ?arfin ta har ya zamana muryar ta dashe se hawayen da suma suka tasarma ?afewa data gaji da zaman ta sulale a ?asa tana cigaba da nanata Innalillahi wa'inna ilahi raji'un, tausayinta mai tsanani ya dabaibaye shi, ubangiji ne kaWai yasan halin da shi kansa yake ciki a lokacin amma yanayin Aishar ya sake raunatashi ta yanda duk dakiyarsa da iya bagarar da abu seda ya gaza ya tashidaga kan kujerarda yake zaune ya bita kasan sannan ya tallafota jikinsa yana cewa

"Kiyi ha?uri kukan ya isa haka in sha Allahu ze samu lafiya"
"Me yasa ya Soye mun?" Ta faWa muryarta can ciki.

Cikin sanyin da babu wanda zeyi zaton yana dashi yace mata
"Nasan yana gudun sakaki a damuwa da tashin hankali ne, kinga fa yanayin da kika shiga yanzu daga samun labarin abinda yake damunsa, idan da ya sanar miki da tsayin shekarun da suka gabata bakiyi su cikin walwala da farin ciki ba ?ila da yanzu ciwon damuwar abinda yake damunsa ke yayi Ajalin ki kafin cikar nasa wa'adin".

Kallonsa ta ringayi, ko kusa bata kalli maganganunsa a masu daWi ba kai tsaye fassara abinda yake faWa tayi da irin ita ya shafa, ciwon Ahmad Win be dame shi ba koda yake hakan nema domin yanda ya zauna yana zayyana mata halin da Ahmad Win yake ciki kamar me bata labarin wani abin farin ciki ya isa ya nuna mata rayuwa ko mutuwar Ahmad bata gabansa.

Tattara ?arfin tayi ta fizge jikinta daga nasa tana kallonsa da idanunta da suka ?an?ance saboda kuka tace
"Kai ne silar komai. Tunda kaja Ahmad jikinka komai ya canza, me yasa baka da wani buri a duniya bayaga ?untata mana? Yanzu ai se hankalinka ya kwanta, ba?in cikin da kakeyi na ina samun farin ciki a gurin Ahmad ze kau, nayi nadamar auranka Audu, dama zaman Ahmad nakeyi a gidan nan muddin na rasashi ka sani na gama auranka" tana gama faWar haka ta mi?e tana haWa hanya ta fice Waga Wakin, akan matakalar bene ya zauna taci gaba da rera kuka me ban tausayi. Daga tashin Ahmad har yayi aure be taSa yanke wani hukunci ba tareda shawararta ba, tunda Alhajin ya jashi jikinsa shikenan ya canza ya dena gaya mata komai koda ta matsa sedai yayi mata kwana kwana ko ya gaya mata abinda ba haka ba yanzu ace Ahmad Winta na tattare da ciwon cancer ace bata sani ba ta tabbatar da shirin Audu ne shiya hana ya gaya mata, ya san komai shi yasa be nuna damuwar sa akan canje canjen Ahmad din ba, se yanzu da ya rayuwarsa ta fara zuwa gangara shine ze gaya mata.

Seda taji idanunta na neman rufewa saboda azabar kuka kafin ta rarrafa ta fice daga Sangaren nasa, daga Asibitin ya Wakko ta bayan ta shiga ta duba Ahmad wanda yake bacci, yanayin data ganshi ya kiWimata rama da ba?in da ya sakeyi ya birkita mata ?wa?walwa tana fitowa ta fasa kukan se an gaya mata abinda yake damun Wanta Alhaji Audun yace suje mota ze gaya mata be sanar da itan ba seda suka isa gida ya jata can uwar Wakansa kafin ya shiga karanto mata abunda ya kusa ya janyo tsayawar numfashinta.

Ita musulma ce imaninta baze cika na har seta yarda da ?addara me kyau ko akasin haka dan haka ta karSi abinda ubangiji ya saukarwa Ahmad Allah baya kuskure ta sani yana da dalilinsa na hukunta faruwar hakan abinda ba zata iya ba kawai shine hana kanta kuka da kuma damuwar da Ahmad Win ya guji zasu shiga idan suka san lalurarsa. A falonta ta zube bayan data kira ?anwar ta Maimuna ta sanar mata da abinda ya faru, tana isar mata da sa?on ta jefar da wayar dan bata bu?atar abinda ze raunanata a yanzu, ?warin guiwa take nema da ?arfafawa akan tunkarar jarabawar data sameta.

Alhaji Audu kuwa bayan fitar Aisha tamkar wanda ruwa yaci haka yayi shiru yana bin ?ofar data fita daga kallo maganganunta nayi masa sukuwar sallah a ?wa?walwa. Me yasa Aisha zata zarge shi akan Soye ciwon Ahmad? Ashe haka take masa kallon mugun mutum har tana i?irarin rayuwa ko mutuwar Ahmad bata dameshi ba? Dagaske zaman Yayanta takeyi bawai dan har

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login