Showing 456001 words to 459000 words out of 467220 words

Chapter 153 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12242

na ha?ura ka aureta amma bazan iya zuba ido in kalli jininka da nake so in gani ya gauraya dana mayu ba in sha Allahu badai ni Binta na haWa jini da Hafizu bakanike ba".

Yanda take kuka tana maganganun ya sanyaya jikin Jafar sosai, ya zata Hajiya ta ha?ura da lamarin Afeeyah, dukda dai ko a waya ya nemi ya haWa su ta gaisheta bata taSa yarda amma yanda kwata kwata bata masa zancen Afeeyar ko wani abu daya shafeta yasa yake tunanin a hankali komai ze wuce zata karSe ta amma kuma maganganun da takeyi yanzu yasa yaji kamar abin zeyi wahala. Ya tuna sanda tace in har Afeeyah ce zata haifar masa yaya tana fatan Allah yasa ya dawwama be haihu ba, duk irin yanda Hajiya take da buri akan ya haihu ace zata zaSi karya haihun in dai har Fatima ce uwar yayan tabbas kuwa ba ?aramar ?iyayya take mata ba. Be san har se zuwa yaushe zata zubar da makamanta ta karSe ta a matsayin suruka ba wannan burin shine abinda ya rage masa dama a kullum addu'arsa guda biyu ce, Allah ya bashi Wa namiji ya saka masa sunan Yah Ahmad sannan kuma Allah ya daidaita tsakanin Afeeyah da mahaifiyarsa ta karSe ta ta dena tsanarta ko da ace ba zata sota ba. Yanzu addu'arsa Waya ta karSu Fathiyyah nada ciki yana fatan kuma ya kasance namiji ne saura tsakanin Afeeyah da Hajiya.

Wuni zir yayi yana kwantar mata da hankali har yace kodai kawai ya shirya mata komai idan ma baze yuwu su tafi tare ba tunda kwana biyar kawai zeyi daga baya ta bishi can kawai tayi zamanta ?ila tafi samun nutsuwa amma tace Aa bata so, cikin gidan nan zata zauna duk wanda baya son ganinta sedai ya mutu dan ba?in ciki babu inda zata je. Seda ya zagaya duka Wakunan ya gaida sauran matar a gurin Momy ma yaci abinci ya gaya mata Fathiyyah nada ciki. Cikin sanyin murya bayan ta gama yi masa addu'a tace
"Ita kuma fa Mamarsu Amal?" Yayi shiru dan be fahimci tambayar tata ba. Itama shirun tayi tana ?o?arin hana hawayen dake son Salle mata zuba. "Ashe rabon daya kashe Ahmad Win ma yana da nisa" ta raya a zuciyarta se tayi saurin yin istigifari, sau da yawa zuciya takan sa?a mata me yasa daga Jafar har Fatima suka rufe ala?ar su ta baya? Me yasa basu bayyana ba? Tasan da Ahmad baze aureta ba ?ila da wannan rabon da ake faWa beyi ajalinsa ba. Ta goge ?walla, tabbas Allah ne me kashewa a sanda yaso kuma ya raya wanda yaso be kyautu a ringa ala?anta samuwar wani abu da rashin wani ba, tamkar dai yanda kowa yake nanata rabon Jafar dake jikin Fatima ne ya kashe Ahmad.

Washe gari ya Wauki hajiya ya kaita sabon gida wanda an kammala komai kaya kaWai ya rage a saka a ciki. Sosai hajiyar taji daWi domin dai yayi ginin da babu me irinsa kaf gidansu. Haka nan ta ringa dogara sanda ta shiga ko ina a ?asa ta gani sama dai tafi ?arfinta ganin komai biyu iri Waya yasa ta kasa ha?uri tace
"Amma dai na Wauka can tsohon gidan zaka gyara mata ko? Ita wannan da zata fara tara yaya ai tana bu?atar guri me yalwa su sakata su wala. Kuma danaga Waki can an masa fentin yara ina dai ba agololin zata tare dasu ba?"

Shi mamaki ne ma yasa yayi mata shiru da farko, seda yaga ta hasala kafin cikin taushin murya yace
"Nafi son iyalinna su zauna a guri Waya hankalina zefi kwanciya, sannan yaran nan kuma da kike magana hajiya amanata ne, ko ban auri mahaifiyarsu ba ni zan ri?e su". Tayi masa banza, har suka bar gidan kuma bata sake cewa komai ba seda suka kusa isa gida sannan tace
"Amma dai da ita Fathiyyah zaka koma ita waccen ta dawo tunda banga amfanin zamanta ba bayan ga wadda tafi bu?atar a kula da ita" yayi murmushi yace
"Zanso hakan nima toh amma a yanayin da Fathiyyah take ciki ba ze yuwu tayi tafiya ba har se cikin yayi ?wari tukunna"

"Haka Amadu ya ringa rawar ?afa akan yarinyar nan se kace da gwal akayi mata nata nata abin ko tafi sauran mata" hajiyar ta faWa tamkar ta manta dawa take magana. Kunya haWe da dariya suka kama shi lokaci Waya amma ya kanne dukda haka cikin ransa seda ya murmusa a zuciyarsa yace
"Ai ba zaki gane bane kawai hajiya, she get back she get front and her soup is different". Har suka isa gida hajiyar na mita shidai murmushi kawai yake yayi nisa ma a tunani abin gwal Win da hajiyar ta tuna masa yana sauketa ya kirata video call suka Wanyi hira kafin ya tafi gida washe gari kuma ya koma Abuja ?ara kwana Waya the next day ya koma Paris har ya tafi kuma basu haWu da Alhaji ba dan yana Bechi shida Hajiya Zubaida.

Wato seda Afeeyah tayi matu?ar kai zuciyarta nesa akan al'amarin Wokin wannan cikin, yanda me cikin da uban ciki suke abu seka zata akansu aka fara haihuwa a duniya ta ringa tunanin wannan da a guri Waya suke kenan Zuciyarta bugawa kawai zatayi saboda ba?in ciki. Dare ko safiya cikin face time call suke, duk abinda yakeyi hankalin sa na kan ya gama ya kira Fathiyyah, hirarsa kuwa kaf ta koma zancen babyn da za'a haifa ne gashi ya isheta da tambaya me dame masu ciki suke so meye basa so me za'ayi kaza me ya kamata ayi idan kaza yazo tambayoyi harda na rashin hankali ta?i amsawa kuma abu ya zama jidali. Ko bacci idan sukayi wayarsu take haka ze tashe ta ya tambayeta Fathiyyah tace ?????&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&?&'abu kaza zata ci babu matsala taci ko Aa? Fama take da kanta amma yanda idonsa ya rufe akan cikin Fathiyyah yasa sam be fahimci cewar itama tana wani yanayi ba a maimakon haka ma idan yaga ta canza fuska ko ta?i biye masa suyi zancen ciki seya fara faWa tun tana daurewa da daitaga abun bana ?are bane tace ita dai ya cireta a shirginsu ta gaji.

Iya ha??in ta da suke shiga ba dare ba rana sanda ya kamata ace yana gida ya bata lokacinsa sannan zasu durfafi waya ana nuna masa ciki ko suyita iya shegensu karar da yake mata da baya waya a gabanta da Fathiyyan ma yanzu ya dena sedai idan taga ba zata iya sauraro ba ta shige Waki ta bashi guri Allah ya taimaketa ma yanayin nata cikin yazo mata da rashin son damuwa sau tari kwanciyarta takeyi ta barshi idan ya gama lalacewa da babyn nasa ya shiga ya sameta. Watansa Waya da zuwa ya sake komawa yayi kwana uku ya dawo ita ta zata ma tare zasu tafi ya mayar da ita ya Wakko maman baby to bata san dai meye dalilinsa na ?in yin hakan ba ba kuma ta tambayeshi ba haka suka cigaba da gurgura rayuwa yau fari gobe ba?i tana kuma cigaba da rainon cikinta da yabi jikinta tamkar sauran, ta ?ara ?iba da haske har yana mata mitar dole ta fara workout ba zata zauna ta zama wata giwa ba sedai ta jishi da kunne kawai. Watansu huWu a Paris a lokacin a lissafinta cikinta ya doshi wata biyar kenan yaci ace ta fara awo hakan yasa tace masa tana so zataje Asibiti.

Ranar da yace zasu je kuma tafiya ta tasar masa zeje Manchester dan haka ya haWata da driver ya kaita. Seda tayi komai daya kamata aka mata registration na antenatal da sauran parenting classes da suke bawa mata masu ciki training kafin ta koma gida tana jiran ya dawo finally ta gaya masa dai tana da cikin nan itama, washe gari kuwa ya dawo a ranar kuma yace mata ta shirya washe gari zasu tafi Nigeria Fathiyyah bata da lafiya ta faWi a toilet an kwantar da ita a asibiti. Yanda ya gigice ya bata tausayi dukda be faWa mata komai bayan faWuwar ba ta ringa Addu'a a zuciyarta Allah yasa ba abinda ya samu cikin jikinta cikin ikon Allah kuwa da suka isa suka tarar da ita garas dan badan ance wai ta faWi bama ita bata ga alamar wani rashin lafiya a tattare da ita ba dan an sallameta ma sun koma gida tun a jiyan sun tarar da Hajiya Binta da Hajiya Ummu se Hajiya ?arama da Sarah sunzo dubata. Daga yanayin kallon da Hajiyar ta mata tasha jinin jikinta ai ko tana zama tamkar Hajiya dama tana jiran lokaci ne da zata amayar da abinda yake cikinta. Ta ringa mata tijara akan me taje? Ko ta biyo sahu ne Wan aiken da suka tura be isar da sa?on yanda suka so ba shine tazo ta ?arasa da kanta toh kurwar jikanta tafi ?arfinta duk maitarsu nan gani nan bari ba abinda suka isa su masa.

Afeeyah ta ringa kuka, a duniya kalmar maita da hajiya take jifanta da ita tana mata ciwo, tana ji tana cewa
"Ai ko wannan ciwon ?afar dama an gaya mun kece to wlh ko sakar mun ?afa ni ba Aisha bace ko Amadu da kika cinye koshi Jafar Win da kikaga na sakar miki ba fin ?arfina kukayi ba a ankare nake daku duk wanda ya taSa shi wlh sedai shi ya mutu" ta ringa sakin maganganu abu dai babu daWi kamar ta manta a gidan surukai suke daga Hajiya Ummu dai har su Sarah aka rasa wanda ze iya ce mata komai kunya kamar su nutse a gurin se yan uwansu Fathiyyah da suka zo dubiya ne dan an gama yayatawa dangi su suka ringa bawa Hajiyar ha?uri Fathiyyah da mamanta nata murmushi ?asa ?asa tarkonsu ya kama.

Tun zuwan Jay na farko tayi nacin ya tafi da ita yace Aa bazeyi risking babynsa ba tayi ha?uri har se cikin yayi ?wari tukunna duk zuwan da zeyi kuma da uzurin da ze bata har dai ta fahimci kawai baya son tafiya da ita ne tunda har cewa yayi ko sun tafi babu abinda zata iya yi masa a condition Winta baze iya takura mata ba saboda baby dan haka tayi ha?uri kawai ta zauna da taga tayi tayi amma bata samu yanda take so ba shine suka kitsa zancen wai ta shiga banWaki taga ba?ar mage tayo kanta mamanta ta kira Hajiya ta gaya mata shine fa ta kira Jafar Win tana rusa kuka wai an turawa Fathiyyah magen maita dan a salwantar da ciki in har yana son gamawa da ita lafiya ya tattaro Fatima ya dawo da ita gida ya Wauki Fathiyyah dan idan har wani abu ya samu cikin Fathiyyah ba zata yafe masa ba. Babu wanda ta gayawa a gidan ta Azazzalo Sarah suka taho a jirgi ita kuma Hajiya Ummu ta biyo train daga Kaduna suka haWu a gidan Hajiya ?arama.

Cikin kuka Afeeyah ta fice daga falon can suka haWu da Jay yana ?o?arin shigowa dalilin text Win da Sarah ta aika masa tace yazo da sauri, ya rungumeta. Ta sake fashewa da kukan daya dake shi sosai ya ?ara ?arfin ri?on daya mata ya Wora haSarsa akanta yana shafa bayanta ya jata suka fita. Sun daWe a mota yana rarrashinta ta kasa yin shiru ga magana tana so tayi amma zafin kalaman hajiya da suka haWu da pregnancy hormones suka sa kukan yafi ?arfinta ta kasa cewa komai har seda tayi me isarta kafin bacci ya kwasheta a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Seda su Hajiyan suka fito kafin ya kwantar da ita ya fita daga motar ko kallonsa hajiyar batayi ba ta shige gaban motar da suka zo ta mi?e ?afafu zuciyarta na tafarfasa. Tayi rantsuwa idan har wani abu ya samu cikin Fathiyyah se tayi shari'a da Fatima dan ita ba Aisha bace tana ji yana cewa Hajiya Ummu zasu biyo su gidan Hafsa yanzun tace karya soma.
"Muddin ba so kake na mata abinda za'a ringa yawo dani a gari ba karka kuskura ka kawo ta inda nake, ka tattara ta ta wuce gidansu kuma karka haura gobe a ?asar nan in ba haka ba zamu gauraya" ta faWa tana numfarfashi. Duk wani bala'i daya sameta akan wannan tsinanniyar yarinyar ne tunda ta shigo rayuwar su komai nata ya lalace duk abinda ta saka gaba bata sake yin nasara ba.

Seda suka isa gidan Hafsa kafin Hajiya Umma ta ringa bala'i kamar zata kama da wuta, tace mata
"Badai ke baki da hankali ba? Duk abinda ya faru be saka kin nutsu ba yanzu wace hujja ce dake da zaki kira yarinyar nan mayya? Yanzu idan magana ta tashi tayi ?ararki dame zaki kare kanki zaman da kikayi a hannun yan drugs be sa kin hankalta kin guji sake shiga abinda babu ruwanki ba ko? To wlh tallahi babu wanda ya isa ya kirani shaida keda kika janyowa kanki duk abinda ya biyo baya ke zaki sani ina kallon uwarta na girgiza kai wato kin basu leakage to duk masifar da suka taro sedai ta ?are miki ke dasu kin manta nan Asabe ma?ociyarmu a Malali da tayiwa Maman Ade sharrin maita sanadiyyar zuwanta gidan yari kenan harta mutu ba'a gama shari'ar ba zaki gane baki da wayo idan magana ta tashi".

Sarah tace
"Ni wlh Mama gani nake ma ?arya sukeyi lafiyarta ?alau kawai shiri ne"
"Yo ai tunda muka shiga na gani ?alau take haWi ne kawai kinga yanzu ai ta sake haska musu hanya ta basu ?ofar kawo ko wanne iskanci da gangan ma zasu iya salwantar da cikin suce ita ce to nidai babu ruwana dama kar wanda yace ai ina gurin akayi" Hajiya Ummun ta sake faWa. Hajiya tayi tsuru tsuru tunda ta tuno mata da zancen Asabe da maman Ade, bata manta ba irin haka Asabe tace Maman Ade Mayya ce ta kama wani yaro a unguwar su shari'a dai har Asabe ta mutu ba'a ?are ba nan da nan hankalinta ya tashi data tuna zaman da tayi a NDLEA inda ma Waki me kyau take harda Ac amma ji ta ringayi kamar a kabari take balle ace an kaita kotu da wace ?afar zata gidan yari?.

****************

A hankali ta buWe ido jin motar ta tsaya, ya Wagota ta zauna sosai yana kallon idonta daya kumbura ba ?aramin kuka tasha ba can ciki yace mata
"We are home". Ta kalli cikin gidan daya zarce a kwatanta kyansa, tunda suka hau jirgi daga Abuja ta sake komawa bacci ita ba zata iya tuna sanda suka sauka bama har suka shiga mota tayi ?asa da idonta sababbin hawaye na neman ?wace mata, wato maganganun hajiya sun zafe ta matu?a shi kansa Jay Win ba?in sa take gani yau da ace ya gaya mata zargin da suke mata me ze saka ta bishi har aci mata mutunchi a gaban kishiya da danginta? Ya rungumeta aiko ta fashe da kuka harda shashshe?a hakan yasa direban dake jira su fita ya mayar da motar gurin ajiyeta ya fita daga motar ya basu guri. Jay ya rasa me zece mata, a hanya Sarah tayo masa voice na duk abinda ya faru dukda tun jiyan dama hajiya ta fara cewa Afeeyah ce dama ai mayune so suke su cinye cikin tunda ta fara maganar ya dakatar da ita ashe bata ha?ura ba shine tazo tayi a gidansu Fathiyyar. Dakyar ta tsagaita suka shiga gidan, seda yayi kamar ze rasu kafin ta ha?ura da kukan amma ta?i kulashi. Duk irin haWuwar da part Win ta yayi bata bi takan komai ba ta haye gadon Wakin daya kaita ta kwanta tana mayar da numfashi, seda ya fita ya bata guri kafin ta tashi tayi wanka tayi sallah kanta na mata ciwo sosai.

Washe gari bayan ya lallaSa ta sun shirya yayi mata sallama ya koma Abuja, bata wani damu ba dan haushinsa takeji sosai akan abinda aka mata jiya tana bu?atar ya bata sarari ko kiranta data ringayi bayanya tafi bata ce masa komai daga uhm se umm har da suka koma Paris Win tareda Fathiyyah babu wata jituwa tsakaninsu a can Win ma tsakaninsa da Fathiyyah se a hankali tayi fushi dalilin da sukaje wai be ko damu da halin da take ciki ba ya Wauki Fatima suka wuce Kano kuma ya dawo yana mata masifa akan abinda ya faru se kace ita ta saka hajiyar tayi abinda tayi sukayi faWi in faWa a maimakon taji daWin binsa se abun ya zama ba haka ba musamman daya kaita asibiti antenatal yayi musu bayanin ta faWi yana so a dubata sosai a tabbatar babu wata matsala dan be yarda da Asibitin da sukaje a gida ba dukda ance har Waurin bakin mahaifa an mata
Dr data dubata tace musu komai lafiya babu wani abu da aka mata wannan ya tabbatar da maganar Sarah da tace mata ?arya Fathiyyah take lafiyarta ?alau aiko ya ringa mata jidali yana cewa ya zata ta canza hali ashe kwanton Sauna tayi yanzu menene ribarta idan ta sake assasa matsala tsakanin hajiya da Afeeyah?

Ta ringa kuka tana bashi ha?uri akan itama ba laifinta bane ta rasa yanda zatayi ne hankalinsa ya dawo kanta tayi iya ha?urin da zata iya ta gaza shiyasa haka dai suka cigaba da zaman sama sama, ga tight schedules yasa be samu sararin zuwa Nigeria ba har seda sukayi wata uku acan har sannan kuma babu jituwa tsakaninsa da Afeeyah musamman da take ganin ya tafi ya share guri ya zauna bayan ita Fathiyyah duk karshen wata ya ringa zuwa yana ganinta hakan ya sake tabbatar mata da bata da wani muhimmanci a gurinsa idan ba morarta zeyi ba seta tattarashi ta watsar ta kama yayanta dan tun bayan data dawo da kwana biyu suka koma gidan haka taci gaba da rayuwarta tana rainon cikinta da babu wanda yasan dashi se se yan gidansu se kuma Maimuna da suke zumunchi sosai tunda suna kusa yanzu ita kuwa bame magana bace ko Momy bata gayawa maganar ba musamman da Afeeyan tace mata shi kansa Jafar Win be sani ba.

Bata san da zuwansu ba wata ranar Asabar da safe ta dawo daga kai yara Tahfiz ta tarar da mota ana sauke kaya Jay da Fathiyyah na tsaye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login