Showing 348001 words to 351000 words out of 467220 words

Chapter 117 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12172

sanar mata Fatima ta tafi bayan sun gama wayar ne kuma tahau whatsapp tana sana'arta ta chatting, voice note take ta yiwa ?awayenta tana gaya musu Fatiman ta tafi.

Haka nan tunda Ahmad ya rasu ta rasa sukuni akan Fatiman. Dukda tasan abu ne me kamar wuya wai gurguwa da auran nesa amma hankalinta ya kasa kwanciya yanda ?awayenta suke ce mata za'a iya cewa Jafar ya aureta saboda yayanta. Wannan ya hura tsanar Fatiman me girma a zuciyarta, yanda kuma Jafar Win ya Wauki al'amarin ta girma ya sake saka hankalinta tashi take ganin ze iya amsa tayin idan anyi masa dukda kuma tana ta tabbacin yuwuwar al'amarin sedai idan Hajiya bata numfashi a doron ?asa. Wannan yasa take kaiwa Hajiyar duk wani labari data san ze Sata mata rai akan Fatiman ko Jafar, so takeyi ta sake tunzurata akan al'amarin ta yanda duk bala'i ba zata taSa amincewa da haka ba. Ba ?aramin daWi takeji akan bijirewa umarnin Hajiyar da Jafar yakeyi akan Fatima ba, ta san hakan ze sake munana ?iyayyar da takeyi mata ne ta yanda dai kome za'ayi mugun fatan da mutane suke mata baze tabbata ba.

Da kallo tabi Jafar Win harya haye sama da jariri a hannu kafin ta tashi da sauri ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tabi bayansa. A Wakin sa ta tarar dashi ya shimfiWe Ahmad Win yana gyara masa kwanciya, tana shiga yayi mata alamar data fita, ta tsaya ya balla mata harar data saka dole ta fice ta kasa zama a falon duk ta rasa tunanin me ma zatayi me Ahmad yakeyi a gurin Jafar? Bata da mai bata amsa dan haka ta fita tsakar gida. Bata damu da matsatstsiyar shigar jikinta ba ta kira me gadinsu, ya ?arasa yana sunkuyar da kai gefe.
"Maman su Layla ta tafi ne ko tana nan?" Ta tambayeshi tana yatsina fuska. Cikin ladabi ya bata amsa akan sun tafi, seta juya da sauri ta koma ciki.

Jikinta har rawa yakeyi ta shige Wakin dake ?asan ta dannawa Hajiya kira. Tashinta daga tsakar gida kenan bayan data gama tata rashin mutunchi zancen tafiyar Fatiman nema ya sanyaya mata rai harta koma cikin falonta ta zauna tana jiran Faisal data ya karSo mata sa?o a tasha. Tana ganin kiran Fatiyyita Waga dan yanzu sun Winke sun zama Aminai. Ta lailayo ashariya me dan?o da mai?o bayan data saurari abinda Fatiyyan take faWa,

"Gani nan zuwa gidan kar ki ce masa komai yan zun nan zanzo" ta faWa tana mi?ewa ta rarumi wani zani ta yafa tana jirkitawa ta fice daga falon. Har zata shiga gurin Alhajin se kuma ta fasa seta dawo tukunna ta wuce tsakar gida tana fafarawa direbobi kira. Kafin su kai gidan ta antayawa direban dakw tu?ata ashar tayi cikin tifa haka dai suka isa gidan.

Jafar kuwa Fatiyyah na fita ya mayar da mu?ulli ya rufe ?ofar. Wanka ya shiga bayan daya kunna suratul ba?ara a wayarsa ya rage sautin kafin ya ajiyeta daga gefen Ahmad Win. Tun yana wankan yakeji ana kiransa dan haka ya hanzarta ya fito, missed calls uku ya gani na Baba Al?ali dan haka yabi bayansa.

"Malam Jafar kana ina ne?" Al?alin ya tambayeshi kamar babu komai. A da?ile yace
"Ina gida Baba"
"To idan babu damuwa kazo nan gidan ku ina son magana da kai" ya bu?ata ya amsa masa da "toh" kafin ya kashe wayar ya shiga shiryawa bayan ya gama ya Wauki Ahmad Win da mukullin motarsa ya fita.

Fatiyyah na nan ta kasa zaune ta kasa tsaye taga fitowarsa, ya nufeta, har ya buWe baki ze mata magana se kuma ya fasa ya koma saman se ganinsa tayi ya sakw sakkowa da baby carrier babba irin 3 in 1 Win nan, kamar sokuwa tabi bayansa dan be ko sake kallon sashin da take ba ya fita daga falon, tana kallo ya kwantar da yaron a gefe ya gama installing car sitter kafin ya sakashi a ciki sannan ya shiga motar ya tada ita ya fice daga gidan.

"Me hakan yake nufu?" ta tambayi kanta a fili sedai bata da amsa seta juya da gudu ta koma ciki haushin kanta ya cikata data zama kamar wacce ya asirce ta kasa masa magana har ya fita. Yanzu bata san inda ya tafi ba gashi Hajiya tana hanya idan ta kirata tace ya fita ?arshe ita zata saukewa kwandon masifar har ta dau?i waya zata sake kiranta ta ajiye se kawai ta wuce Wakin ta tana wassafa abubuwa iri iri a ranta.

Jafar kuwa bayan daya fita daga gidan wani tunani yayi dan haka ya kira direban yaran yace masa idan ya Wauko su ya wuce ya kaisu gidan Maimuna. Daya gama magana dashi ya kira Maimunan itama ya gaya mata za'a kawo yara amma ko Alhaji ne da kansa ya kirata karta kuskura tace suna gurinta zeje ya mata bayanin komai tace masa toh. Ana kiran sallar Magriba ya isa gidan nasu dan haka daya ajiye mota seya rasa ya zeyi da yaron, baze kaishi cikin gidan ba kuma dai baze yuwu ya shiga masallaci dashi ba, Sarah ya kira yace ta fito, can gefe ya mayar da motar ta yanda babu wanda ze gane da mutum a ciki tana zuwa yace ta shiga ta zauna kafin yayi sallah, bata musa masa ba ya wuce ya barta a gurin ana idarwa ko Azkar be tsaya yi ba ya dawo, tun daga nesa yake jiyo kukan yaron ya ?arasa da sauri ya buWe motar ya karSe shi ze rufeta da masifa tace

"Yunwa yake ji Yaya, kuma na duba ko ruwa babu balle a bashi".
Shiru yayi yana jijjiga yaron da se ?ara wage baki yake yana ihu duk hankalin mutanen compound Win yayi kansa, yasha kunu ya zaro Atm Winsa ya bata yace
"Kije da motar kiyi sauri ki siyo masa madara da feeding set, bari na samu zam-zam a gurin Alhaji na bashi"

"Wai ina Anty Fatiman toh" ta tambayeshi bayan data karSi katin, ya banka mata harara seta kama kanta ta zagaya mazaunin direba baki alaikum ta tafi abinda sakata.

Kafin su isa falon Alhajin kukan Ahmad ya rigasu, Baba Al?ali yayi murmushi ganin yanda Jafar Win ya shiga a firgice yana faman jijjiga yaron Alhajin kuwa harara ya banka masa fuskar nan a hade kamar hadari
"Wuce ka kaishi ciki gurin mata" Alhajin ya daka masa tsawa, yayi diriri a tsaye kafin kuma ya juya ya fita. Hajiya Rabi ce ta karSe shi tana cewa
"Meya faru? Ina mamar tasa?"
"Tana can gida dan Allah Anty ki saka shi yayi shiru a bashi ruwa yanzu Sarah zata kawo madara a haWa masa".

Yanda yake tsala ihu kamar wanda ake yankawa yasa ta wuce dashi da sauri tana cewa
"Kamar akwai madarar su Khadija da suka manta a gurin Momy, Allah yasa ma dai yasha" ta shige falon Momy dashi.

Alhaji Audu be bar Al?ali yayi magana ba ya dirar qa Jafar da faWa kamar ze doke shi.
"Akan me zaka Waukar mata yaro sannan saboda rashin tunani har ka iya dukan mace, yar kace ko baiwar ka da zaka mare ta?"

Kamar irin yaran nan masu yar banzar zuciya haka Jafar ya ringa kumbura daga zaune Yana haWiyar zuciya, Baba Al?ali ya tare Alhajin yana cewa

"Ya isa haka, ba faWa zaka balbaleshi dashi ba, kamata yayi muji menene hujjarsa ta aikata abinda yayi, me yasa kayi haka Jafar? Akan me zaka raba jariri da mamansa?"

Abin tausayi kuma abin haushi yana buWe baki da niyyar yin magana se kawai ya fashe musu da kuka kamar wani yaron goye. Duk se suka buWe baki kawai suna kallonsa aka rasa me cewa wani abu. Seda yayi kukansa ya gode Allah kafin ya goge fuskarsa ya haWe kai da guiwa yana ajiyar numfashi, Al?ali ya tashi ya dakko ruwa me sanyi a fridge ya bashi ya KarSa yasha dan yana da bu?atar shi kafin ya sake ce masa

"Me yasa zaka hanata tafiya da yaronta?"
"To waya ce ta tafi ita? Idan ba zata zauna ba akan me zata tafi mana da yara wani gida bayan ga gidansu? Idan ma tana so ta tafi me yasa ba zata gaya mun ba tunda ai kowa yasan dai nine Babansu kuma ko Yah Ahmad a gabanta ya faWa ni ya barwa amanarsu ya gaya mata duk wani abu da zatayi akansu seda amincewa ta akan mr zata banzatar da maganarsa tayi gaban kanta?" Ya faWa cikin fushi kamar ya manta da waWanda yake magana dasu, Alhaji Audu yayi mici mici da ido yana kallonsa, Baba Al?ali dai ya sakeyin murmushi yace

"Toh banda abinka Jafar me yasa zata zauna? Tana da bu?atar rayuwarta taci gaba, ta manta da baya. Idan taci gaba da zama a cikin gidan tunanin baya baze bari ta samu nutsuwar shirya gobenta ba. A kullum zata cigaba da kwana tana tashi ne da tunanin Ahmad hakan kuma ze dakusar da ita ta yanda zuciyarta ba zatayi sauri buWewa ta karSi wani sabon sa?o ba, sannan ko ba bayan haka kana so taci gaba da zama uwarka tana zuwa tana ?are mata tanadi ai gara ta koma can gidansu cikin yan uwanta ta samu walwala kaga nan da Wan lokaci ?ila Allah ya kawo mata wanda ze maye gurbin Yayan ka data rasa tayi aurenta daga nan kaga kana da hujjar da zaka ?wace yaranka idan ma abinda kake bu?ata kenan".

Yanda kasan ashar Baba Al?alin ya ?unduma masa haka ya Wago a razane ya kalleshi, ko meya tuna kuma yayi saurin saukar da kansa ?asa Al?ali yayi dariyarsu ta wanda suka san kan duniya yace

"Ko ba haka ba?"
Kamar wanda aka cusawa tsumma a baki Jafar Win yace
"Nidai in har zata tafi gidansu to bada yarana ba ba zasu rayu a wani gida daban ba sedai ta zauna a gidanta idan kuma ta zaSi tafiya gidansu to ba zata tafi mana da yaro ko guda Waya ba".

"To yanzu na tambayeka, idan ta bar maka yaran ya zakayi dasu?" Al?alin ya faWa ya wani sake tamke fuska yace
"A gidana zasu zauna mana"

"Ita matarka kunyi da ita zata ri?e maka sune?" Ya sake jefa masa wata tambayar, se yayi jim kafin yace

"Ai ni nake auranta dan haka dole tabi duk abinda nake so in har tana son zama dani"

"Sannu isashshen mai gida, to sa ace ita matar taka kafi ?arfin ta kana tsammanin uwarka zata barka ka ri?e su ne ita?" Se yayi rau da ido kamar ze saki wani kukan kafin yace

"Toh ai komawa France zamuyi"

"Kai da Allah rufewa mutane baki bana son shashancin banza da wofi" Alhaji Audu ya hayayya?o masa kafin yaci gaba da cewa

"Laifinka ne ma dakake lallaSa shi yake wa mutane maganganun shirme. Saboda dai kai baka da saiti a ina ka taSa ganin an raba uwa da jaririnta kuma da ranta bawai ta mutu a kawai don san rai? Idan ma kana da lissafi ina laifin kace zaka karSi manyan amma harda jariri ji yanda ka Wauki alhakinsa kai a rikice shi a rikice ita matar taka adalcine haka kawai ka kwashi yara ka kai mata har kana wani cewa dole ta ri?e su idan tana son zama da kai to bana son sakarci da rashin tunani karka kuskura kuma na sake jin ka tayar da maganar rabata da yaranta muddin ba aure tace zatayi ba wannan kam da kaina zan saka a karSo su amma ba yanzu ba ka tattara shi maza maza ka mayarwa uwarsa tun kafin ranka ya Saci".

Shiru yayi yana sake Sata fuska, Al?ali yace
"Su kuma sauran yaran suna ina?" Yayi shiru seda Alhajin ya daka masa tsawa kafin yace
"Suna gidan Maimuna"
"Sace su kayi ka kai aka Soye maka kenan? To ka kyauta" Alhajin ya sake faWa. Sarah tayi sallama ta shiga falon, tana kallon Jafar Win tace

"Yaya ya?i shan madarar fa ruwa kawai yasha kuma Anty tace yunwa yakeji sosai".

Harara ya galla mata Alhaji yace
"Idan baka kula da amana ba ai ka kashe amanar, zaka tashika mayar mata dashi ko sena Sata maka rai yanzun nan?"

Tamkar kububuwa haka ya fice daga falon cikin fushi, yana dosar cikin gidan ya fara jiyo kukan Ahmad Win, ya dafe kai kafin ya ?arasa da sauri. Anty na ganinsa ta mi?a masa shi tace
"Kayiwa Allah ka mayar dashi gida kalli fa har muryar sa ta disashe saboda kuka" ya karSe shi kamar zeyi kukan shima ya shiga jijjige, Momy dai bata ce komai ba, Baba Bilki ta kirata ta gaya mata yanda akayi itama dai ce mata tayi su rabu dashi da kansa ze kawo mata yaron.

"Yanzu ba abinda za'ayi masa yayi shiru?" Ya faWa yana kallon Momy kamar zeyi kuka, tayi murmushi tace
"?umin mamarsa da abincin daya saba sha kaWai ze saka yayi shiru yanzu, kaje ka kai mata shi idan yasha ya ?oshi ko a jarka ne seta zubo muku wani saboda dare karya hanaka bacci tunda ya?i karSar madara".

Yana jin abinda Momyn ta faWa ya juya da sauri ya bar falon, Hajiya Rabi tayi dariya tace
"Rigimar Jafar da yawa take, ko a ina aka taSa haka oho? Itama dai data yi ha?uri ta Wan ?ara lokaci zuwa ya koma idan ba haka ba kewar zatayi masa yawa".
Momy dai bata ce komai ba taci gaba lazumin da takeyi.

********
Alhaji Audu ya ringa kallo Al?ali tamkar lokacin ya fara ganinsa harya gama labarta masa abinda ya faru be iya cewa komai ba seda Al?alin ya ce masa
"Kayi shiru baka ce komai ba" sannan ya ajiye numfashi yace

"Amma me yasa baka taSa faWamun ba se yanzu? Ai da tun farko bazan bari ayi auran ba. Ta yaya za'ace Ahmad da Jafar sun haWa soyayyar mace guda? Kuma ka bari Waya ya aureta a maimakon duk su ha?ura kowa ya nemi wata?"

"Idan duk sun ha?ura shi kuma rabon waWanda yaran da aka haifa a kaishi ina?" Al?alin ya faWa yana kallonsa se daya furzar da iska daga bakinsa kafin yace

"A jikin wata ze haifesu mana. Ashe shine dalilin daya saka sam auran yarinyar nan ya gagara kwantamun a rai, ina ma ace na sani tun da wuri lokacin Ahmad yana raye"

"Da se kayi me idan ka sani da wurin?" Baba Al?ali ya faWa, Audun yace
"Sakin ta zan saka yayi, ?ila da yanzu ya tsira da rayuwarsa rabo be kashe shi ba".

Al?ali ya girgiza kai a ransa yana ayyana a gurin Audun duka yayansa sukayi gadon wauta da Wanyen kai, se ya ce masa

"Idan ka saka ya saketa kana tunanin hakan ze canza abinda Allah ya riga ya rubuta ze faru kenan? Kuma da kake wata magana babu wani rabo da kashe Ahmad, iyakar rayuwar da Allah ya rubuta masa a duniya kenan koda sila ko babu dole ya mutu.

HaWuwarta da Jafar da abinda ya faru a baya ubangiji ya fimu sanin manufarsa tayin hakan, duk kuma abinda ya faru a baya ya rigada ya wuce, yanzu abinda yayi saura gare ka shine kawai kayi ?o?arin cikawa Ahmad wasiyyar daya bari akan Jafar ya auri matarsa kuma ya ri?e masa yaransa. Nasan abin ba me sau?i bane amma ka sani jihadi biyu zakayi a lokaci Waya, cika burin Ahmad bayan ransa da kuma samarwa Jafar muradin zuciyarsa daya daWe yana dakon soyayyar ta".

************
Da?yar ya iya kaiwa gidan saboda kukan da Ahmad yake tsala masa kamar ze toshe masa dodon kunnuwa, duk ya rikice kansa ya Wauki ciwo a haka ya ?arasa gidan saboda yanda ya ke a rikice be iya tsayawa neman izini ba sallama kawai yayi ya faWa musu gida.

Ummansu Fatiman na zaune tareda Baba Bilki se Umma Halima Yayar Baffansu suna sake mayar da zance, ita dai Fatima tunda suka shiga ta wuce Wakin da aka gyara mata bata sake fitowa ba. Baba Bilki na cewa
"Yanzu zaku ganshi ai na ce mata ta kwantar da hankalinta ta?i ji ina Jafar ze iya da tiri tirin jariri, fitinace kawai irin tasa dukda dai na fahimce, maganar gaskiya zeyi kewar yaran nan ganinsu na Webe masa kewar mahaifinsu ni kaina ji nakeyi kamar in zauna kawai anan wlh mun rigada mun saba bazan ji daWin zama babu su ba, mutuwa kenan, babu ruwanta idan ba dan haka ba aida ta bar mana Ahmad" ta shiga share ?walla da gefen hijabinta, kukan Ahmad yayi musu sallama duk suka mi?e ganin Jafar kamar an jefo shi ya shiga wurga idanu yana neman Fatiman fahimtar haka Ummansu ta nuna masa Wakin da take tace
"Tana ciki, kawo a mi?a mata shi".

Tsallake su yayi ya shige Wakin, tana tsaye dan tunda ya tsayar da mota kunnuwanta suka fara jiyo mata kukan yaron, kusan karo suka ci daya shiga tayi saurin ja baya ta bashi hanya. Jikinsa har rawa yake ya mi?a mata shi yana cewa
"Kiyi sauri ki bashi tun Wazu yake kukan yunwa".

A maimakon ta karSe shi seta balla masa harara ta juya ta zauna gefen gado kafin tace
"Bazan karSa ba kasan yanda zakayi dashi".

Baki sake yake dubanta ya rasa ma me ze ce mata se kawai ya isa inda take ya Wora mata yaron dake neman shiWewa akan cinyarta, cikin halin ko in kula ta janye jikinta kamar zata kada yaron,ya ri?e shida sauri a zuciye ya daka mata tsawa yace

"Baki da hankali zaki kayar dashi?" Marin da na miki be saka kin dena yi masa ganganci bako? Ki karSe shi tun kafin ranki ya Saci".

"Kai Jafaru wai menene haka kakeyi fisabilillahi? Ke kuma ki karSe shi mana bakya jin irin kukan da yakeyi?" Baba Bilki ta shiga Wakin tana faWa. Shiru tayi bata tanka ba haka bata karSi yaron ba, jikin Jafar har wata tsuma yakeyi ya kasayin komai se kallonta kawai yakeyi. Jin kukan ya?i ya tsaya Ummansu da Umma Halima suka le?a suga me yake faruwa.

"Zuciya yayi ya?i karSa ne?" Umma Halima ta faWa seta shiga tafa hannu ganin Fatiman zaune abinta ta haWe fuska tana muzurai tace
"Me zan gani Afeeyah kurmancewa kikayi ko Yaya da zaki zauna yaro na tsaga kuka irin haka amma ko a jikinki kamar bakya gurin?"

"Kwace shi yayi yace bazan je ko ina da shi ba, har mari na yayi akan zan karSi Wana. Tunda ya karSe shi ai ya shirya yanda ze kula dashi ne, ni ku gaya masa ya fitar mun Waga Waki" ta faWa kamar zata fashe da kuka Ummansu ta saWaWa ta bayanta bata an kara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login