Showing 18001 words to 21000 words out of 467220 words

Chapter 7 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12260

yanda yayarta ta gaya mata kafin tayi wankan Ibadah dukda kunyar idon Audu haka ta shirya shi kuma ya juye ruwan bokiti ya fita dashi ya dawo ya goge gurin tas kafin ya sirka wani ruwan ya dauko fitila ya wuce bayi. Seda yayi wanka shima ya shirya kafin ya kwanta gefen Bara'atu da tuni bacci ya kwasheta, wani irin farin ciki da annushuwa yake ji, daman haka auran yake? Kai dole ashe Abokanan sa su ringa cewa Aure da dadi.
Ya tuna Yakubu ma yana can yana kashe Arna qilan yanzu shi kadai kamar sabon kamu ya fashe da dariya a haka bacci ya dauke shi shima cike da nishadin samu Bara'atun tasa a yanda beyi tsammani ba.

Kiran sallar farko ya farka dan ya rigada ya zame musu jiki tun suna qanana da an kira sallah Malam ze tayar dasu suyi nafila kafin lokacin Asuba su fita masallaci shiyasa jikinsu ya saba duk gajiya duk bacci basa tsallake wannan lokacin se sun farka. Motsin saukarsa daga gado ya farkar da Bara'atu wadda itama bata da nauyin bacci. Ta kasa kallonsa yayi murmushi yace
"Ki kwanta, kiran farko ne". Seta tashi zaune sosai a kunyace tace
"Ai bazan iya komawa baccin ba".

Audu ya dakko baho ya zuba ruwan zafi ya sirka, ya sake hada wani a buta kafin ya kalleta yace
"Toh gashi nan ko zakiyi amfani" yana fadar haka ya dauki wata butar daya cika da ruwa ya fita daga dakin dan bata sarari. Seda ya kalli bangaren Yakubu da suka garqame qofa Asirinsu a rufe babu wanda yasan halin da suke ciki kafin ya wuce Bandaki ya kama ruwa yana cikin daura Alwala aka haskoshi, ya kare fuskarsa tareda kallon inda hasken yake tahowa saga bangaren Goggo Fadi ne, da alama kuma inda yake take nufowa seya dauke kai yaci gaba da Alwalarsa harta iso kansa tana cewa

"Har gabana ya fadi wlh na dauka gamo nayi" banza ya mata ya miqe ta sake cewa
"Aa, angwayene har aka iya miqewa da farar Asuba? Kaga bayan gudan namune ya fara alamun fadawa shiyasa naji tsoron karna shiga da duhu na rufta kafin a kawo mun agaji ma qila na nutse ina Amaryar, ta tashi ko se an kawo Agaji?"
Tsabar takaici harya tsaya ze bata amsar maganarta ta farko amma qarshen yasa ya wuce ba tareda ya ce mata komai ba, wai a kawo agaji ita dai tana tsufa amma se a hankali. Dakin ya koma lokacin Bara'atu ta fita daga ruwan data ji dadinsa sosai ta daura alwala tana tsaye tana tunanin yanda zatayi da ruwan ya shiga dakin. Kamar dazun ya sake juyewa a Bokiti ya dauraye ya fita dashi ya zubar can bakin rariya ya kife bahon qofar Dada tunda ya gama amfaninsa ya koma dakin, seda yayi Nafila kafin aka kira sallah dan haka ya dauki carbinsa ya fita daidai nan Yakubu ya fito daga bangarensa suka rankaya suka tafi masallacin duk su biyun babu me cewa komai suka zama kamar wasu surukai kowanne fuskar sa cike da annuri irin na sababbi Angwaye.

Bayan an Idar da sallah Abokanan su suka tare su da tsokana, nan suka zauna har gari yayi haske kafin suka doshi gida seda sukaje soro kuma suka tsaya saboda jiyo muryoyin mata alamar kowa ya tashi har an fara hidimar gida. Audu ya kalli Yakubu kamar tababbu suka fashe da dariya lokaci daya harda duqewa kowanne shiyasan dalilin dariyarsa. Yakubu ya kalli Audu yace
"Bazan iya shiga gidan nan ba kunya nakeji"
"Ai gara kai daka sha kunu ka wuce ka sakayo qofa shikenan ka gama abinda zakayi a ciki ka fice ni kuwa komai zanyi akan idon mutane" cewar Audu.

Shigowar Aminu ta sakasu shiga gidan dole yana ta tsokanarsu shima, a dakin Dada suka yada zango suka gaisheta kamar yanda suka saba, bakinta kamar ze yage saboda farin ciki, yau din wata ranace ta musamman a gurinta burinta ya cika na ganin Yakubu da Audu a matsayin magidanta sauran mata Autanta Baballiya da tasan ba lallai tayi tsahon ran da zataga wannan lokacin ba. Seda gari ya gama wayewa tangarau kafin kowanne ya koma dakinsa. Bara'atu na kishingide ya shiga ta miqe ya kalleta da murmushi yana cewa
"Aa yi kwanciyarki Jaruma"

Ta rufe fuska da Hijabin jikinta jin abinda yace wai jaruma, to jarumtar me tayi?"
Muryar Inna Hasiya dake magana ta sakashi fita ya dawo ya kwashi fulasan jiya ya kai mata ya tambayi Bara'atu Qaramin fulas din Shayi ko Jug ta nuna masa inda suke ya dauka ya fita ya kaiwa Innan daga can ya wuce dakin Shafi'u inda yayi ajiyar kaya.

Inna Hasiya tayi sallama Bara'atu ta amsa kafin ta shiga da fara'a Bara'atu ta miqe ta karbi kayan dake hannunta kafin ta duqa har qasa ta gaidata ta amsa tana tambayarta kwanan baqunta ita dai se murmushi take Innan tace mata
"Ga ruwan wanka can a kewaye kije kiyo se ki karya sannu ko" ta fada cikin tausasawa. Kan Bara'atu na qasa tace
"Toh Inna, amma Kwandon wankana yana bangaren Yaya Balaraba a can na barshi jiya"

Cikin jin dadin Yayar da ta kira Balaraba dashi Inna Hasiya ta fita da zummar karbo mata, a hasashe dai Hafastu tayi dacen surukai masu tarbiyya da kuma kunya. Seda ta dauki abin karin su Yakubu wanda Bilki ta ware kafin ta kai musu ta kuma karbowa Bara'atun kayan wankanta. A bandakin ta tarar da Ruwa har bokiti biyu, tayi wanka me kyau ta gasa jikinta dan ruwan da zafinsu kafin ta fito tana sunne kai dan Inna Hasiya da Bilki na tsakar gidan, dab da zata shiga daki Goggo Fadi ta taho tana cewa
"Aa Amarsu wanka akayi?"

Bara'atu ta durqushe tana gaisheta ta amsa fuska washe da fara'a, Inna Hasiya da fuskarta ta hade bayan fitowar Goggo Fadin tace
"Tashi maza kije ki shirya karki bushe".
A dakin bayan ta shafa mai ta ciro wata yaluwar Atamfa me ratsin fari dinkin Tazarce riga ta wuce guiwa an tsagata daga gefe gefe se zani ta saka. Ta bude qaramin kwandon da aka zuba mata kayan kwalliyarta. A qyalle ta zazzaga powder ta shafa ta dakko jagira tana niyyar zanawa se kuma ta dakata. Kwalliyar Balaraba ta jiya ta tuna, daga ita har qaqayenta da sukazo daga ruga babu wadda zakaga dambareriyar kwalliya a fuskarta hoda kawai suka saka se kwalli da man lebe kuma sunyi kyau kodan kasancewar su fararene oho?
Dukda cewar a ruga suke amma sun fita ita da nata qawayen wayewa ta ta'allaqa hakan da cewar garinsu Wailari yafi nasu kusada Birni har wasu daga cikinsu sukan kai tallar Nono cikin Kano qila a can suke gano kwalliya irin ta matan Birni wanda daman Audu yana kwatanta mata sam baya son wannan Jagira dasu jambakin da suke cike fuska dashi amma ita a ganinta idan ba tayi haka ba ba kwalliya tayi ba.

Zuciyarta ta shawarta mata ta gwada simple kwalliya irin ta Balaraban dan haka ta ajiye jagirar, brush ta dauka ta taje girarta da take a cike me kyakykyawan yanayi kamar an zanata fitina take sakata dambara baqin jagira akai ta qarawa fuskarta da bata haske baqi. Bayan ta taje girar ta saka kwalli a dara daran idonta, bazata iya haqura da jambaki ba dan haka ta shafa kadan ta kawo man lebe me kyalli da Audu ya sako mata a kayan fitar biki ta dora akai ita da kanta ta ringa sakin murmushi ganin yanda tayi kyau, fuskarta har qyalli take cike da Annuri irin na Amare. Ta mayar da kayan kwalliyar ta feshe jikinta da turare kafin ta ware dankwari bayan ta gyara zaman ribbon din data tufke jelar Shukun da aka mata. Daurin Maryam Babangida tayi wannan kam gwance ita a gurin kashe dauri, ta ringa juyi a gaban Kwabarta me mudubi daga sama har qasa tana dariyar yarinta dan tayiwa kanta kyau Addu'a take Audu ya shigo ya ganta taji me zece.

Motsin qofa yasa ta nutsu ta shiga neman farin gyalen data fitar tareda kayan. Audu ya shigo da sallama hannunsa riqe da Baqar leda babba kana gani kasan gwangwanaye ne a ciki ya kalli Bara'atu fuskarsa ta sake washewa zuciyarsa tacika da alfaharin kasancewar ta mallakinsa ita kuwa se sunne kai take na kunya. Ya kalli kayan karin da aka ajiye musu alamar bata ci ba yace
"Kar abincin ya huce kizo kici" a kunyace ta zauna qasa, ya fitar da gwangwanin Madara Peak dana milo se sukarime iyali kwali biyu ya ajiye mata ya juya da ragowar yana cewa
"Bari na kaiwa su Yakubu".
Kicibus sukayi da Bilki, ta miqo masa Babban farantin silba da aka dora kwanukan samira guda biyu se ledoji farare da aka qullo Madara, Milo da sugar tace

"Gashi farfesun Inna tace nata ne ita kadai ta ci ta shanye romon" ta fada cike da shaqiyanci tana kallon Bara'atun, ta dago kuwa ta maka mata harara, idon Audu ne yasa bata bata amsa ba tunda su din qawayene daman sun saba da caccakar juna. Audu ya karbi Farantin ya ajiye ya kwashe kayan shayin cikin ledar wanda yasan cikin manyan gwana gwanan da yake siyowa Dada duk sanda ze zo aka debo yace
"Maida su na taho mana da namu mantasu nayi dakin Shafi'i"
"Toh Yaya" Bilkin ta karba ta cigaba da tsayuwa dan so take ya fita ta tsokani qawar tata, karantarta yasa yace mata
"Muje toh" ba yanda ta iya ta fita amma dai ze fita ya barsu a gidan yau kam Bara'atu ta banu a gurinta dan dalilin daya sakata kwana a gidan kenan ma.

Tare suka karya da Bara'atun dukda yanda take ta noqewa bayan sun gama ya miqe yana cewa
"Zanje dakin Shafi'i nayi wanka, idan kina buqatar wani abu ki aiko yara su gaya mun"
"A dawo lafiya" ta fada tana miqewa itama bayan ta hada kwanukan da sukaci abinci dasu suka fito a tare bayan ta saka takalmi. Gurin da taga an tara wanke wanke ta ajiye na hannunta Audu kuma ya fita daidai nan Balaraba itama ta fito da nasu kwanukan tasha kwalliya kamar dai Bara'atun, suka sakarwa juna murmushi ta ajiye kayan hannunta kafin suka shiga gaisawa. Dakin Dada suka nufa tare suka tarar suma sun gama karyawa kenan Bilki na tattare guri Baballiya na kwance kamar gawar sababi yana tabara ko kunya bayaji waishi Auta.

Inna Hasiya ta dana masa duka tana cewa
"Dallah tashi ka basu guri su zauna", Dada da bakinta yaqi rufuwa se sannu take musu suka zauna kowacce na sunne kai suka shiga gaishe su. A mutunce suka amsa, tamkar ba surukai ba haka Dadan ta ringa jansu da hira suna amsa mata daddaya cike da kunya Inna Hasiya ta fice tsakar gida se Bilki dake tsokanarsu Dada tana tare musu.
"Kuje ki rakasu su gaida Goggonku" Dadan ta fadawa Bilki, ta miqe suka bi bayanta suna fita ta dafa Bara'atu tana cewa
"Qawata ya kikaji Auran?"
Inna Hasiya ta rafka salati tana cewa
"Kin banu Bilki wannan fitsara har ina sirrin Yayan naki kike kiji kome? To bari Audun yazo daidai yake dake".

Bilki ta ringa dariya su Bara'atu dai se murmushi da haka suka qarasa dakin Goggo Fadi sun tarar da ita da Aminu wanda tun Asuba daya shigo gidan yana can kome suke tattaunawa se Allah. Cike da girmamawa suka gaidata ta amsa itama basu jima ba suka basu guri, bayan sun fito Bara'atu ta kalli Balaraba tace
"Muje kiga dakina nima" suka rankaya Bilki ta wuce gurin Inna Hasiya data kirata. A dakin Balaraba ta ringa santin kayan Bara'atu, hira suka shiga tabawa Bilki ta dawo nan ta tasasu gaba da tsokana suka ringa hira gwanin dadi kafin qawayen Bara'atu suka fara zuwa yan kwadayin ragowar kazar Amarya.

Kazar ta basu Balaraba ma taje ta dakko musu sauran tata dan ita qawayenta tasan yanzu sun kai gida tunda Asubanci me motar da ze mayar dasu yace zasuyi ze wuce Kano dakko kaya. Wuni guda tsakanin bangaren Balaraba da dakin Bara'atu sukayi shi, Inna Hasiya kuwa bata gaji da hidimta musu ba wanke wanke da shara babu yanda basuyi ta basu ba taqi tace su huta. Haka aka ci sati Angwaye da Amare na tsinkar furen qauna hankali kwance. Dukkaninsu sunyi bulbul abinsu kana kallonsu kasan basu da damuwa banda ma matsalar rashin sirri da take hana Audu yanda yaga dama wannan yasa ya quduri a ransa dole idan ya koma Kano kafin ya dawo ya gyara musu bangare a katange kamar na Yakubu dan gaskiya wannan zaman na kwarar sa.

Seda akayi sati hudu da biki kafin hankalinsa ya fara komawa Kano dalilin yan kudaden hannunsa sunyi qasa ga hidimar yauda kullum a wannan rutsin kuma ya sake fahimtar cewar a yanzu ne ma yake da dalilin tashi tsaye ya nemi kudi ka'in da na'in kodan Iyalan da suka fara ajiyewa. Ya fara shirin tafiya, da daddaren ranar ana saura kwana uku ya koma Kano ya samu Dada da zancen ya kamata Yakubu ya koma yaci gaba da karatunsa.
"Dada yanzun nauyi ya hau kanmu, bazan so mu qare rayuwarmu cikin wahala tamkar ta mahaifinmu da sauran yan uwanmu ba kina kallo dai yanda suke fama basu da wata tartibiyar madogara se Noman da sukeyi.
Karatun Yakubu nada muhimmanci na farko Burinsa ne na biyu kuma idan ya kammala ze samu madafar da ze riqe kansa tunda shi ya gaza maida hankali akan Kasuwanci kamar ni kuma gaskiya bazan zuba ido ina kallo da quruciyarsa aikin wahala ya kashe shi ba dan haka kiyi masa magana ya bar duk wani abu daya dauka yazo mu koma Kano ya zana jarabawa yaci gaba da karatunsa".

Dada tayi shiru tana nazarin maganganun Audu tabbas gaskiya ya fada yanzun nauyi ze qarar musu kuma baze yuwu ace shi kadai zeci gaba da daukar ragamar gidan gaba daya ba. Ta numfasa tace
"Zanyi masa magana babu damuwa da yardar Allah".
Hakan kuwa akayi Dada tayiwa Yakubu magana take ya nuna rashin Amincewa da maganar a cewarsa idan duk suka tafi Birni waye ze ringa Kula da Dadan da yaran mutane da suka Auro? Dada tayi dariya tace
"Kai dai kace bazaka iya tafiya kabar matar kaba" Yakubu ya sunkuyar dakai kamar ya nutse dan kunya ya kasa cewa komai se Dada ce taci gaba da cewa

"Kodan saboda su karatun naka nada muhimmanci Yakubu a yanda Audu yayi mun bayani. Idan ka duba kwanannan nauyi ze qarar mana, badi iyanzu idan muna da rai kun dauki Yayanku akwai buqatu marasa yankewa da zasu qaru kaga dan uwanka yana matuqar qoqarinsa akan mu, idan ka gama Karatun zaka samu madogara tunda ga Fa'izu (yaron me gari da shima ya kaishi Kano yayi karatu) kaga yanzu maganar da akeyi yayi hanyar da Gwamnati zata gina mana Firamare a nan qauyan dole za'a nemi malamai, kaga ko wannan aikin ka samu tunda ance biya akeyi ai an samu madogara seka hada da yar sana'ar da kakeyi Asiri ze rufu kodan saboda dan uwanka ka daure ka cika burinka wanda har ya fika damuwa da hakan".

Haka dai Dada da Audu sukayi nasarar tausarsa ya yarda ze koma Kano ya ci gaba da karatunsa, tafiyar Yakubu data taso ya saka Audu qara kwankin tafiyarsa dan su shirya a tsanake. Ana saura kwanaki biyu su tafi da daddare Hashimu da yayi balaguro tun daurin auran su Audu da kwana hudu ya dawo gari. A daren ranar suna zaune a dakin Dada Malam, dan gurin Mairo ne yayi kiransu inji Baba Hashimu. Audu da Yakubu ne sukaje, yana zaune tareda Goggo Fadi suna hira gabansu Kaza ce gasashshiya suna ci Audu da Yakubun suka samu guri suka zauna suka gaishe su. Hashimu ya cire tsinken da yake sakace dashi ya kalli Audu yace

"Naji labarin kuna shirin Tafiya Birni shine nace kafin ku wuce ya kamata mu zauna muyi magana, so nake yi ku siyar mun da barin gonarku ya zama mallakina tunda dai ba nomawa kukeyi ba, abincin ma idan an baku saidawa kuke kun koma cin kalar na Birni se shinkafa da Taliya ko?" Ya qarashe cikin sigar tambaya.

https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*

*FREE PAGE 6*

Yakubu ya nisa yace
"Ban fahimce ka ba Yaya, kaji labarin muna somu siyar da gonar ne ko yaya?"
"Ko daya, ina dai so ne nasiya kuma a shirye nake ko nawa kukayi mata kudi zan biya" Hashimun ya sake fada, Yakubi ze sake magana Audu ya tareshi yace
"Shikenan zamu siyar, Allahya kaimu safiya se a kira su Malam Audi suyi mata daraja daga nan se muga yanda za'ayi" yana gama fadar haka ya miqe dole Yakubu ya bishi ze fara masifa Audu yayi masa alamar da yayi shiru, daga cikin dakin suka jiyo dariyar Goggo Fadi Hashimu kuma yana cewa
"Sunyi kyan kai dan ko basu siyar munta arziqi ba to zasuyi Asararta a banza"

Wannan magana ta daurewa Yakubu kai ya kasa fassara abinda yake nufi a haka suka koma dakin Dada take Audu ya gaya masa dalilin kiran, Dada tayi shiru kafin tace
"To me kuka ce masa?"
"Nace masa zamu siyar da safe zan nemo au Malam Audi ayi mata kudi"
"Amma meyasa Hashimu duk gonakin da suke garin nan se tamu zece ze siya kuma..."
"Dada, dan Allah kar a tada maganar nan, gona yake so ko za'a siyar masa daga nan a raba kudin kowa ya kama abinda zeyida kasonsa" Audu ya katse Dadan se sannan Yakubu yayi magana yace

"Wannan ma ai maganar banza ce, ta yaya zamu siyar da abinda ita kadai muka mallaka ciki muke ci muke sha? Kai me yasa baka lissafi ne kawai abinda kwakwalwarka ta gaya maka kakeyi?"

"Kadaiji da kunnenka abinda ya fada shawara ta rage taka ko ka bari a karbi kudin ko kuma ta salwanta a banza kaga munyi asara da hujja" Audun ya fada yana miqewa yayi musu sallama ya fice daga dakin yana tafe yana tuna Gonar Baffaye wani tsohon Abokin Malam ne da gonarsa take gabas da tasu, bara waccen shekaru uku kenan Hashimun ya nemi ya siyar masa dan harkoki suna ta bude masa babu kuma wanda zece ga inda yake samun kudi Baffayen yaqi, daminar Bana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login