Showing 72001 words to 75000 words out of 467220 words

Chapter 25 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12109

da iyayenki abinda ake ciki da kuma abinda ya miki ki qara maggi da gishiri ke kice dukan mutuwa ya miki ma sannan na biyu dole mu binciko ko wacece mu bi ta qarqashin qasa mu watsa auran tun a waje babu yanda za'ayi ta tare a gidanki" Turai ta fada. Haka suka ci gaba da kitsa yanda za'ayi har dare Binta na gidan kafin ta koma wujiga wujiga fuska ta kode saboda kuka ido yayi luhu luhu. Ranar bata ko kalli qafar benen Audu ba, cikin daren ta hada kaya daman Turai ta shirya mata direban da ze kaita Kaduna ai kuwa washe gari Asubar Fari tana jin Audu ya dawo daga masallaci ta dauki Jakar kayanta ta saba Zakariyya a baya ta fice.

Can inda sukayi da Direban ze tsaya taje ai kuwa ta tarar dashi babu bata lokaci suka yanki hanya se Kaduna. Yanda ta wuni ta kwana da yunwa ga tashin hankalin da take ciki ya saka duk ta fita hayyacinta, inda Audu ya mareta yayi shati abinka da fuskar Ajebo, saboda iya sharri har kanta ta buga a bango yayi quli ta karci wasu gurare a jikinta da farce saboda ita kadai tasan meta shirya zata fada idan taje gida.

A Makeken compound dinsu ta kwanta tana malelekuwa wai ba zata iya takawa ba bayan isarsu, Direban kansa bude baki yayi tsabar mamakin kaidin wannan matar. Qalau suka taho da qafafunta sau biyu suna tsayawa a hanya harta fita tayi uzurinta amma shine da zuwansu zatace bata iya tafiya lallai mata ababen tsorone.

Mamansu na Kitchen tana bada umarnin abinda za'a girka na rana ta jiyo ihu da kururuwa a waje babu shiri ta fita tayi tozali da Binta kwance a qasa tana wannan ihu qurjinta ya buga, abinda ya fara zuwar mata shine mutuwa akayi dan haka jiki na rawa ta qarasa ta kamata.
"Na shiga uku na lalace Mama wayyo Allah na" abinda take ta fada kenan sanda Maman suka shigar da ita ciki da taimakon Munira qanwarta. A falo suka barta ta sake kwanciya qasa har wani numfashi take ja tamkar wadda ake zarar ranta.

"Dan Allah kiyi shiru kimun bayanin meya faru Binta, karkisa ka zuciyata ta buga ki gaya mun meya samu Mijin nako" Maman ta fada cikin tashin hankali.
"Meyake faruwa haka? Ke Mamana menene? Accident kukayi ko wanine ya mutu acan?" Alhaji Zakariyya daya taso daga bacci dalilin kuwwar Binta data isa ko ina a gidan ya fada yana isa gareta, ganinsa yasa ta qara rikicewa ta shiga qoqarin miqewa tana miqa masa hannu ya riqota jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali
"Kiyi magana Binta, zakici ubanki wlh idan baki mana shiru kin fada mana abinda ya faru ba" Mama ta fada cikin tashin hankali ta jimqe hannayenta da suke fitar da zufar fargaba.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*

Dakyar ta iya nutsuwa dukda ba sosai ba ta shiga kora musu qaryar data tsara ta haddace dangane da Auran da Audu yayi ba tareda saninta ba kuma akan ta masa magana yayi mata dukan kawo wuqa dakyar ta kwaci kanta shine ta gudo. Yanda ta tsara labarin babu wanda ya isa ya qaryata ta musamman ga shaida nan jikinta ya nuna. Mamaki madaukaki ya kama iyayenta musamman Alhaji daya ringa dubanta kamar me son ya tabbatar da dagaske take ko qarya takeyi.

"Wlh bazan koma ba, sedai ya zaba koni ko ita haka kawai bazanje su shafamun cuta ba kuma idan ya zabi zama da ita Dady ka gaya masa ya maido maka da duk wata dukiya daya samu ta dalilinka ai daman saboda ni ne kuma idan ya sakeni dole ya bayar tunda bata ubansa bace" Binta ta fada cikin gunjin kuka. Alhaji Zakariyya ya wuce bangarensa ba tareda yace mata qala ba ya kasa yarda da abinda ta fada, meya hada Audu da matan banza har ya gano matar Aure a cikinsu sannan da gaske Audu ne yayiwa yarsa gudan jininsa wannan dukan babu kara balle ya taci arziqinsa to kodai shaye ya fara toh?

A can falo kuwa da Mama ta gaji da ihu da kururuwar Binta ta daka mata tsawa tace
"Ki rufe mana baki, Audun ai ba mahaukaci bane da ze kamaki da duka haka kawai waye be san halin tsiwarki ba a gidan nan kuma Aure daman kin sani a rubuce take zeyi, ba wata kika tarar a gidan ba dan haka ba zaki fitar da ran kema za'a kawo miki wata ba. Abinda na jiye miki tun farko a Auran Tifical Bahaushe kenan wanda be yi Ilimin Boko ba balle ya waye da yanda rayuwa take, irinsu Audu a kullum tunaninsu be wuci su samu kudi su tara mata da Yaya ba basu damu da jin dadinsu ba balle walwala ko yanda zayuwarsu zata kasance, ke kikace kinji kingani dan haka yanzu babu wani dalili da ze saka kice zaki dawo mana nan, Munira ma Addu'ar Allah ya kawo wanda zero dauke mun ita nakeyi ballantana ki kaso Auranki ki dawo mun".

"Kai Mama ya zakice haka bakiga abinda ya mata ba se kace ba yarki ba, kuma ko auran zeyi ya rasa wa ze auro is Karuwa haba mana wannan ai ba abune me yuwuwa bama" Munira ta fada aiko ta juya kanta tana cewa
"Idan na sake jin bakinki a nan sena gwabjeki shashasha ai kema ba sanin ciwo kanki kikayi ba

"Ya isa haka Firdausi, ke kuma Mamana ki shiga ciki kiyi wanka Munira ki rakata clinic a dubata, ku dauke yaron nan daga qasa sannan wanda ya kawoki tafiya yayi ko yana nan?" Alhaji Zakariyya saya sake fitowa shirin shirin fita ya fada. Se sannan suka lura da Zakariyya dake kwance qasa abinsa yana bacci Direban ne ya shigo mata dashi ya watsar dashi a qasa tareda jakar kayanta. Ta miqe tana dingisawa Munira ta dauki Yaron suka wuce ciki.

KANO
Rai fes Audu yayi bacci babu damuwar komai tattare dashi illah mafarkin Amaryarsa daya kwana yanayi tareda shirya yanda tariyarta zata kasance nan da sati biyu masu zuwa shima saboda ya bata damar yin shirye shirye ne daga bangarenta dan shi a shirye yake fenti kawai ze saka a sakewa dakin can tazo ta zauna. Rashin zuwan Binta dakin be dameshi ba saboda yasan koda taje qarshe rigima zasuyi, da ya dawo daga sallar Asuba har ze shiga ya dubata kuma ya fasa dan yana so ya koma bacci yasan kuma muddin ya shigan bacin rai ze kwaso dan haka ya bari akan sa hade idan gari ya waye sosai.

Bugun qofar gidan da ake kamar za'a ballata ne ya tayar dashi. Ya ringa sakin tsaki yana tunanin wanene haka? Jallabiya ya saka ya sakko yana mamakin Ina Binta ta shiga ake irin wannan dukan qofar bataji ba ko itace ta fita qofar ta kulle ta waje. Takaici ya qumeshi ganin Lantana me aiki, ya tsani matar saboda kana ganinta kalar munafukai ne da ita. Ta durqushe a qasa kamar zata kwanta tana gaishe shi ya amsa a dake yana cewa

"Wane irin abu ne haka zakizo kina dukan qofar mutane"
"Kayi haquri yallabai kasan dokar Hajiya qarfe bakwai nake zuwa gidan nan to Nazo tun bakwan na buga ba'a bude ba na tafi shine na dawo na sake bayi bugun da qarfi ne ko bacci take kar nayi laifi tace banzo da wuri ba"

Tsaki yayi ya juya ciki, harya fara hawa sama ya dawo jin tanata qwanqwasa qofar Bintan shiru ba'a bude ba, ta matsa ya isa jikin qofar ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar. Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace
"Yaji tayi kenan"
"Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan.

"Alhaji Mairo tazo ne? Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai,
"Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan. Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi.

Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar? Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne? Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa.

A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta.
"Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin
"Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba

Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba.
"Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata.

Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu.
"Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada.

Alhaji ya nisa yana kallonsa yace
"Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?".
Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa
"Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje".

Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace
"Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun?

"Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace
"Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar"

"To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada.

"Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage.

Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan?

Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace

"Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?"

Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa
"Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi"

"Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 18*

Ki bude kunnenki dakyau kiji abinda zan fada, dukiya da kike tutiya akanta ta Abdullahi ce, duk abinda nayi masa kyautace halak malak dan haka ko ki bishi ki koma, ko ki dage ya sake ki zabi ya rage naki amma ki sani sisin kwabo baze maidamun ba dan ya rabu dake ko wani abu saboda dama badan ya aureki na bashi ba, tashi ki bani guri karki qara mun ciwon kan da yake damuna" Alhaji ya dakatar da Binta dake ihun kuka.

Sanin halin mahaifin nata kaifi dayane yasa ta tashi ta koma ciki tana cigaba da kukan ta labartawa Mama yanda sukayi.
"Ahto seki shirya ki koma daman duk tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa ze doka, ke kika zabe shi dan haka dole ki jure duk wasu tazgado dake tareda zama dashi kishiya kuma naga wata kika tarar kowa da halinta zata zauna ai ba kuma kanki ze ajiyeta ba" abinda Mama ta sake gaya mata kenan haka tana ji tana gani suka kama hanya da farar Asuba ba tareda ta hadu da sauran yan uwanta ba wadanda su ta saka ran zasu bata shawarar yanda zata yida

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login