Showing 144001 words to 147000 words out of 467220 words

Chapter 49 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12210

duka yace
"Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi kaWai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a ?asa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa

"Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga Waki kafin nayi maka baki"

"Allah huci zuciyarki ni ban faWa dan kiyi kuka ba, Waki kuma sedai kiyi ha?uri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama faWa mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace. Abincin daya gani a gyare ya Webi iyakar abinda ze isheshi ya sha?o plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da faWe faWen maganganu marasa daWi akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal Win daya Wora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba. Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya ?ure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce Waki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje Wakinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa.

Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta ba?in cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari ?al.

"Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu haWin kai idan ya hau kujerar? Jiyan nan fa kar kaga tijarar daya mun a gidan nan ya zubar mun da mutunchi a gaban ma?iya" nan ta bashi labarin yanda sukayi da Yakubu jiya, Zakariyya ya jijjiga kai yace
"Haba kema Hajiya wani sa'ilin se ki ringa abunda be kamata ba, yanzu saboda Allah wannan tarbiyyace? Ko yar wani kikaga zatayi abinda be kamata ba ai hanawa zakiyi amma kike ingiza yarki ta aikata wannan ba daidai bane sam wlh kuma koni da ace na tarar da yaron sena ballashi wlh itaka kuma se naci uwarta dama ana yawan kawo mun zancen bataji na zata hassadace kawai akeyi mata ashe da gaskene to dan ubanta kawai zamu nemo koma waye mu aurar da ita mu huta kafin ta janyo mana abin kunya a gari".

Baki sake Binta ta ringa kallonsa har ya kai aya kamar zatace wani abu kuma seta haWiye ta bar maganar tace
"Ai shikenan, zancen ya wuce, yanzu dai a aikamun da kasona a akawun kai a kawomun kash kawai na ringa ganinsu inajin Wuminsu kusa dani"

"Miliyan dari ukun za'a kawo miki cash Hajiya?" Zakariyya faWa cikin mamaki, ta harareshi tace
"Bangane dari uku ba? Wai nawane kuWinma da kake kiran wata dari uku za'a bani?" Cikin Waga murya tayi maganar yayi saurin yi mata alama da tayi shiru saboda motsin taSa ?ofa dayaji, Yakubu Bechine ya shiga fuskar nan a turSune kamar ta Audu, Binta ta lafta tsaki tace

"Dallah rabu dani yaji mana, nama zata wani barene ze shigo"
"Barka da safiya Hajiya, Zakariyya Sannu" ya gaishe su daga tsayen da yake. Hajiyar ta harareshi bata amsa ba dan a cike dashi akan abinda yayi jiya Alhaji Zakariyya kuwa wani banbarakwai yaji daya kirashi Zakariyya gatsal kamar wani sa'ansa, yanzun shigowarsa ya haWu da Ahmad ze fita shi kuma, seda ya kusa kaiwa ?asa kafin ya gaishe shi kuma da Yaya ya kirashi ya amsa masa a wani wula?ance yana shan ?amshi kamar wanda yazo masa maula kuma yaron ko a jikinsa ya wuce abinsa har yana masa fatan fitowa lafiya daga gidan se yanzu Yakubu ?aninsa ciki Waya ze masa wannan gaisuwar se kace wasu Abokanai? Koda yake ai Yakubun ma ya mutuntashi tunda Faisal da ido kawai ya kalleshi sanda ya shigo ita kanta Hajiyar be tsammaci ya gaisheta ba ya fita dan da ganinsa lokacin ya tashi ma daga barci.

"Tambayarka nake nawane kuWin?" ta sake nanata masa seya sauke ajiyar zuciya yace
"To nidai abinda yace mun kenan kuma baze yuwu a saka kuWin lokaci Waya ba saboda kinga yanzu EFCC ta tsaurara da binciken shige da ficen kuWaWe a Account Win mutane kar mu jefa kanmu a matsala gara a ringa sakawa da goma da biyar har ayi balancing"

"Zezo ya sameni kuwa, a gidan ubanwa kasafin ya zama dari uku? Nida nake lissafin kusan dari bakwai shine zaku cemun wata dari uku? Nifa shiyasa na?i jinin haWa sabgar kuWi da Naziru dan macuci ne, tsayin lokaci kullum yace ana juya kuWin za'a turo ina nan galahanga kenan kuna can kuna sharafinku se yanzu zaku Wan yafutamun abinda kuka ga dama shiyasa naji ance ka siyawa Matarka motar Miliyan Ashirin shi kuma yana rabon kujerun Umarah ko ni dana hada pulan Win ban san komai ba kun ninkeni a baibai" murya a sama take maganar babu War ko shakkar wani ya jita Zakariyya kuwa daga inda yake zaune har zufa ta fara keto masa ta tsoron kar wannan fallasar ta Hajiya ta janyo musu tonon Asiri tun ba'aje ko ina ba, muakutawa yayi cikin rage sauti yace mata

"Yanzu dai kiyi ha?uri na gaya miki yace ze zo kuyi magana tafiyar gaggawa yayi zuwa Legos amma Litinin ze dawo ba jimawa zeyi acan ba"

"Ai ko bezo ba ni zanje har gida na sameshi, yo hauka akeyi mu damfari ubanku sannan ku zagayo nima ku cuceni" ta sake sakin wata maganar

"Dan Allah Hajiya kiyi ?asa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faWa,
Yakubu daya haWo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a mana?isar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an Webi kuWin ba ya zata lissafi kawai suka ?ara masa. KwankwaWe shayinsa yayi ya taso yana cewa

"A fitar dani ko wallahi na fasa ?wai"
"Dan uwarka ka yanka Kaza ?arewar fasa ?wai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haWe seka gane baka da wayo wlh"

Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace
"Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ?ishin ?ishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa".

Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ?ulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruWe se kokawa take da waya

"Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta mi?a masa wayarta tana cewa
"Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ?ullata".

"Aikuwa ba zaki same shi a waya yanzu ba dan suna da wasa ?arfe sha daya, lah lokaci yayima an fara ina tsaye bari kawai na kalla a nan" Yakubun ya bata amsa bayan ya dire mata wayarta a gabanta ya matsa gaban Cinema Tv bango guda wadda Jafar ya sakawa Hajiyar saboda tace wai bata ganinsa dakyau a tsohuwar tata.

Tv na daidaita kuwa kamar me daukar hoton wasan Kwallon da ake yasani ya haskowa Hajiya Binta fuskar JAFAR BECHI tarr kamar ze fito ta cikin gilashin Tv. Zabgegen saurayi irin ?irar Yayan AUDU BECHI, dogone sosai jikinsa nada Wan kauri dukda ba za'a sakashi a layin masu ?iba ba amma a murWe yake koda gani ba se an gaya maka yana motsa jiki dakyau ba. Fatarsa nada haske sosai dukda ba fari bane sedai hutu da zaman Turai ya bashi wata kala me kyau kuma me wuyar samu a cikin mutane, ba wani shahararren kyan fuska yake dashi ba Aa daidai Misali ne irin na Maza gayu da yanayin muhalli da wankan da yakeyi ne yasa har Mata suke iya sakashi a jerin Maza masu kyau wanda ake gwarama kai akansu , ga duk wanda yasan Hajiya Binta Musamman a zamanin ?uruciya kai tsaye ze tabbatar da JAFAR din jininta ne dan zubin fuskarsu daya idan ka cire Idanun Gidan BECHI daya samu se labbansa wanda Binta tace irin na Alhajinsune, duk tana jika dai da itan yake kama kenan.

Jafar Win na tsaye a coner ya take kwallo da ?afarsa ta hagu idanunsa kuma na kan saitin inda yake so ya bugata. JC ce a jikinsa Jaa me ratsin fari ta club din Arsenal wadda ke dauke da Number 7, a bayan rigar an Rubuta JAAY, wani murmushi yake saki daidai sanda Referee ya busa whistle gaba Waya yan ?wallo suka shiga tara tara kowa na jiran ya jefo ta inda yake ya kama, baya yaja kaWan ya buga ball Win daga inda yake ta ringa kurWaWawa ta tsakakanin ?afafuwan yan wasan aka rasa wanda ze taketa har seda ta dangana da cikin raga shikansa Goalkeeper kamar an ri?e masa hannu da ?afafuwa ya kasa tareta har ta shige, ihun yan kallo na cikin Tv tarefa na ZAKARIYYA BECHI da YAKUBU BECHI ya cika falon, Hajiyavkanta da take cikin ruWu fuska a Waure bata san sanda ta saki dariya ba tana cewa

"Ai na sani, sedai idan ba Jafaru na ba be taba kama kwallo ya saka ba tareda ya kaita raga ba, kai Allah dai yacigaba da tuntuWo maka Albarka Wan nan Allah ya cigaba da tsole idon ma?iya" ?a guda tilo kenan cikin rayayyu tara da take dasu wanda take Waga hannu ta ro?ar masa nasara a gurin Allah ta kumayi masa addu'ar fatan nasara tareda saka Albarka, yana kuma ganin hasken hakan domin Uwa duk yanda take Uwa ce kuma tasirin harshenta nada girma.

Jafar Win me shekaru Ashirin da bakwai a duniya yanzu ya kai matsayi mai girma a duniyar kwallon ?afa. Matashin Dan wasa ne da ake ji dashi a faWin duniya wanda kowanne Club suke zawarcinsa, idan ka cire Messi da Ronaldo JAAY shi yake take musu baya a duniyar kwallon ?afa a yanzun. Ubangiji ya hore masa baiwar sarrafa kwallo, duk rintsi duk tsanani idan JAAY ya karbi kwallo seya kaita ga inda ya hara kafin ya ha?ura, juriyarsa da Nacinsa da kuma ?o?arinsa na haWakan Yan Team Winsa Abokanan taka ledars shiyake ?ara masa ?ima a idon duniya domin kowa ya shaida wannan jajircewar tasa ce ?ashin bayan cigaba da Nasarorin da duk wani club dayake taka leda a ciki yake samu.

Cikin farin ciki suka haWu suna kallon Wasan, harda Hafsatu da Sarah dake bacci ihun su Yakubun ya taso su ko karyawa basuyi ba suka haWu aka cigana da kallon.

BECHI FARM
Kamar yanda Alhaji Audu yace Ahmad ya sameshi a gidan gona haka ce ta kasance, Alhajin ya riga Ahmad isa saboda ba?i da yayi ze gana dasu acan wanda shine musabbabin daya saka yace Ahmad ya tarar dashi a can Win, sanda ya isa Alhajin na tsakiyar tattaunawa dan haka yayiwa kansa masauki a daya daga cikin falukan da suke gidan gonar idan kaga tsaruwarsu zaka Wauka a cikin gida kake ba wai gidan gona ba. Yana zaune cikin zullumi rungume da takaddun tsarin abinda yake so ya gudanar, zuciyarsa fal wasi wasin yarda ko akasin haka daga gurin Alhaji, idan Alhajin be yarda da bu?atarsa ba a ina ze samu gurin da ze aiwatar da aikinsa tamkar wanda yake nema a gurin Alhajin?

Gajiya yayi da zama da tunani ya tashi ya fita yana zagaya gidan gonar, sashen tsuntsaye ya tafi, acan ya shantake yana kallon Halittun ubangiji, tsuntsaye gasu nan kala kalanda Alhajin yake kiwo danginsu Dawisu, Aku, Kanari da sauran tsuntsaye masu tashi kala kala a keji nan su ga kuma tattabaru nan irin ?asashe daban daban Jikinsu kaWai abin sha'awa. Kukan tsuntsayen da surutun masu kula da gurin ne ya Webe masa kewa har besan lokacin daya Wauka ba seda wani daga cikin yaran Alhajin yayi kiransa.

Masaukin daya tarar da Alhajin yafi kowanne haWuwa a gidan gonar, yana zaune kan Luntsumemiyar Rolar chair two sitter irin zaman da yayi da suturar da take jikinsa kamar wani basarake seya cike kujerar gaba daya kwarjininsa ya cika falon. Tamkar beran da ruwa yayiwa duka haka Ahmad ya raSe daga gefen kujera yana gaida Alhaji.

"Ka tashi ka zauna a sama, meye haka kakeyi kamar wanda yazo Maula?" Alhajin ya faWa cikin muryarsa me razana Maza. Ahmad ya sake yin ?asa dakai cikin tsantsar ladabi yace
"Aa Alhaji nan ma yayi, be kamata kana zaune akan kujera nima na zauna ba"

"Umarni na baka ba shawara ba" ya sake faWa a dake, wani sashi na zuciyarsa kuma yana tsinkewa, Ladabin Ahmad daban ne kaf a cikin Yayansa 28 yayi zarra wanda yake take masa baya kuma Jafar ne wanda zama da Ahmad Win ya washsheshi shima ya rabautu da kyawawan Wabi'u.

Kamar wanda ya zauna akan wuta haka Ahmad ya Wosana mazaunansa akan kujerar jininsa yana sake tsinkewa, falon yayi shiru, motsin ?ofa da aka buWe ya saka Ahmad Win zabura kamar mara gaskiya ganin Kuku ne ya shigo yana tura abinda ake Woro abinci akai yasa ya maida kansa ya sauke Ajiyar zuciya a hankali. A nan tsakiyar falon kan Ledar da Kukun ya shimfiWa ya jera abincin daya shigo dasu. Seda ya gama ajiye komai daya kamata kafin ya juya ya fita bayan ya sanarwa da Alhaji komai ya kammala.

Alhajin ya sauka ya zauna a ?asan ya tokare hannunsa Waya da Tum Tum ya shiga serving kansa abincin Ahmad yayi sauri ya sauka ya karSa. Ganin duk ire iren abincin da Alhajin yake ci yanzun ne dangin Alkama dasu Acca se kayan ganye sakamakon Sugar daya gamu dashi ya saka masa komai madaidaici yanda ze iya ci kafin ya koma ze zauna Kukun ya sake shigowa da madaidaicin Tray ya ajiye a gaban Ahmad Win ya sake fita.

"Ga irin naku nan" Alhaji dake cin Funkaso da akayi da garin Alkama da wata miyar tanta?washi ga shayin Goruba yana kurSa ya faWa.
Ya buWe baki da niyyar yace ya ?oshi amma kallon da Alhajin yayi masa ya saka ya buWe abincin. Soyayyar jollof din Basmati ce se kaza guda gasashshiya da kuma coslow. Favorite Win Ahmad kenan shinkafa balle ga Kaza mutuniyarsa a gefe daman be karya ba ya fito dan haka tuni ya manta da surukutarsa da Alhajin ya hau zuba loka. Seda suka ?oshi ?at, Kuku ya sake zuwa ya kwashe komai ya dire musu kayan marmari da tataccen ruwan Inibi me sanyi, Alhaji nata satar kallon Ahmad kamar yanda shima yake satar kallon Alhajin.

Dukda wata magana bata shiga tsakaninsu ba har suka gama cin abincin amma duk su biyun yanayin ya musu daWi domin wannan shine karo na farko da suka taSa haWa muhallin cin abinci tun tasowar Ahmad Win sedai su hangeshi sunaci da Hajiya tareda Yayanta, sanda suna yara idan ta kira Jafar yazo suci abinci suka tafi tareda Ahmad Win haka zatayi ta zaginsa ta koreshi shi kuma Jafar ya saka kuka yabi bayansa wata rana haka da duka zata tisa Jafar Win seya zauna dukda bazeci abincin ba domin basa raba kwano da Ahmad da suka fara girma kuma da lokacin cin abincin wanda sukafiyi da dare ya kusa ze ja Ahmad su bar gidan ma doke ta ha?ura ta barshi kuma duk abinda akeyi Alhajin be taSa magana akai ba, ashe haka cin abinci tareda Mahaifi yake da daWi? Ya raya a ransa.

"Ina sauraronka, menene abinda yake tafe da kai?" Alhajin ya soko ainin abinda ya tarasu. Ahmad ya zaro takaddun daya zo dasu. Filla filla yayi musu a gaban Alhajin zane ne a jiki da guntayen rubutu yayi ta maza ya shiga yi masa bayanin abinda yake shirinyi. Tsarin taswira ne na katafaren Shopping Mall dayake da ?udirin buWewa, burinsa ne tun yana yaro provision store yake bashi sha'awa. Sanda suna Goron Dutse kafin su taso har Tireda ya kafa a ?ofar gidansu yake siyar da alawowi harda su Maggi da Omo, sau Biyi Audu yana sakawa a jijjigeta amma idan aka cire Yau in Allah ya yarda kwana biyu yayi yawa zega sabuwa a karo na uku harya niyyata ze cire ranar a kan Idon Ahmad Win yace masa

"Dan Allah Alhaji karka ciremun, idan ma kuWin haya kake so na ringa biya zan baka idan na tara kuWi jarina yayi yawa, so nakeyi idan na girma na gina babban Shop da za'a ringa siyar da komai da komai" wannan maganar ta sanyaya masa jiki tasa ya fasa abinda ya niyyata wanda a sannan ma Binta ce tace masa Aisha ta saka Ahmad ya buWe tiredar saboda aga gazawarsa ace ya kasa daukar Wawainiyarsu, maganganun Yaron kuma se suka tuna masa da sanda ya daura Wambar cika nasa burin sanda yake yaro yanzu da Ahmad Win yake nuna masa abinda yake so yayi se abinda ya faru kusan shekara Ashirin kenan ya dawo masa.

A nutse ya ringa kallon komai yana kuma sauraron bayaninsa, ya fasalta masa guri da girman filin dayake da bu?ata danyin ginin.

"Shin kana da kuWin da zaka gabatar da duk wannan aikin daka Wauko?" Alhajin ya tambayeshi, Ahmad ya haWe yawu kafin yace

"Da akwai tanadin da nakeyi dukda nasan baze isheni nayi koda rabin abinda nake da buri ba a yanzu, amma a hankali ina sha Allah ina saka ran zan samu"

"Ok, to me kake so nayi maka kenan?" Alhajin ya jefa masa tambayar me kama da rainin wayo, jikinsa yayi sanyi dan be hango alamar samun nasara ba amma ya daure yace

"Wannan filin na cikin gari inda ake ajiye manyan Motoci da nake so idan da Hali a bani Aro tunda an dena amfani dashi".

"Aro?" Alhajin ya tambayeshi kamar da mamaki, kansa na ?asa ya Waga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login