Showing 459001 words to 462000 words out of 467220 words

Chapter 154 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12388

daga gefe, seda ta gyara parking ta fito tana gyara hijabin jikinta ta isa inda suke fuska a sake tayi musu sannu da zuwa. Fathiyyah dake ta yatsina irin ta masu ciki ta amsa mata a sama tana cewa me fito da kayan yayi sauri da alama wani abu take so ta karSa kafin su shiga shidai Jay kallonta kawai yakeyi trying so hard to believe what his eyes are seeing, gabansa ta matsa tana murmushi ta sake ce masa
"Sannu da zuwa Jay" ya buWe mata hannaye har sannan idonsa akan cikinta da yayi tudu dukda be kai na Fathiyyah girma ba amma it is obvious, ta no?e kafaWa alamar Aa kafinta wuce ciki seda ta basu baya sannan ta haWe fuska haushin kanta ma ya kamata to akan me zata tsaya tana wani pretending bayan ba shiri sukeyi ba? Takun da taji daga bayanta yasa ta waiga suka kusa cin karo dan yana dab da ita, da hannu biyu ru?ota ta saitin cikinta, ta bige masa hannayen ta ?ara sauri zuwa part Win ta ya take mata baya, duk yanda ta ringa kokawa dashi seda yafi karfinta ya zare hijabin jikinta bayan daya haWe hannenta biyu ya Wage su sama. Ya ringa kallon cikin, jikinta yayi sanyi ganin hawaye na bin fuskarsa ya saki hannayenta a hankali ya dur?usa a gabanta ya Wora hannunsa biyu akan cikin kamar me tsoron taSawa kafin ya janye ya Wora fuskarsa daidai lokacin da abin cikin ya juya kawai ya rungume cikin ya sakar mata kuka kamar wani gara.

Sakin baki kawai tayi tana kallonsa kusan minti biyar kafin ya mi?e ya rungumeta ta bata hannunsa akan cikin muryarsa na karyewa irin ta me kuka yace
"Amma kin san kin zalince ni kin kuma Wauki ahakin abinda yake cikinki ko? Me yasa Afeeyah? Wane laifi na aikata miki dana cancanci irin wannan hukuncin how could you do this to me ki rabani da jinina for how long have you been hiding this from me?"
Shiru ta masa, ya saketa a hankali ya zauna akan kujera kafin ya jata ya Wora ta akan kafarsa his hands all over the bump, seda ya lalubi idonta ya saka cikin nasa ya kuma hanata janyewa kafin yace
"Tell me, laifin me nayi miki dana cancanci wannan hukuncin?"

Baki ta zumSura bata ce komi ba, yayi ajiyar rai yace
"Shikenan, wata nawa yanzu?" Da yatsunta ta nuna masa takwas, ya buWe ido, bata ankara ba ya shammaceta ya mintsileta a gefen cikinta duka biyu, ta ?wala ?ara cikin azama yayi covering bakinta da nasa ya shiga nuna mata irin kewarta da yayi.
Bayan shuWewar awanni biyu tana naWe cikin jikinsa kamar zata shiga cikinsa, bata san tayi kewarsa har haka ba, ta motsa saboda ri?on da ya mata ko tace cikinta yasa taji ta takura motsinta ya farkar da Jay daya fara bacci ya shiga shafa cikin yana tambayar ta me take so tace babu komai seya gyara mata kwanciya tun tana mutsu mutsu saboda yanda duk ya kankaneta ya hanata sakat harta ha?ura bacci ya Wauketa.

Irin yanda ya lalace mata yini guda yana manne da jikinta seda ya bata tausayi ta kuma fahimci abubuwan da ya ringayi farkon cikin Fathiyyah bawai da wata manufa bane Aa tsabar yanda yake ?ulafucin samun haihuwar ne amma me yasa tsayin shekaru be taSa nuna za?uwarsa nason ya haihu ba se yanzu? Bata manta Ahmad har ya fishi damuwa akan rashin samun cikin Fathiyyah ya ringa ce masa suje asibiti kenan duk kuma sanda take da ciki se yayi zancen Allah yasa wannan karon su haihu tare da matar Jay shi kuwa ko a jikinsa ya kan ce ai Ahmad Win ya haifar musu ko da yake dama mutane ne suke Worawa kansu damuwa, aure, haihuwa da mutuwa lokaci ne dasu su kan wanza babu makawa a sanda ubangiji ya hukunta damuwa ko wani tashin hankali baya hana faruwar kowanne daga cikin su.

Da yammacin ranar yace ta shirya zasuje can gida su duba Hajiya dake kwance bata da lafiya, har a Asibiti ta kwanta kusan sati biyu lokacin kuma taje ta dubata har sau uku kafin aka sallameta harda Ummansu da Anty Sauda dasu Umma FaWima sunje saboda hajiyar taji jiki sosai daga ciwon kai abin ya fara mata da jiri, ranar kuma tana zaune uwargidan Naziru tazo mata tana kuka kamar zata shiWe wai kotu ta yanke masa hukuncin shekara goma sha biyar a prison banda uban tarar da aka cishi dan kusan anyi sizing da yawa daga cikin properties Winsa tashin hankalin da ta shiga yasa ta mi?e tsaye da sauri duhu ya mamayeta ta faWi seda tayi sati biyu a asibiti kafin aka sallameta Allah ya rufa mata asiri jikinta be shanye ba amma bakinta ya mutu ta dena cewa kowa komai se dai ido ko maganar tayi seka matsa kusa da ita sosai akeji.

Seda zasu tafi gidansu Hajiyar kafin ta tuna da Fathiyyah yazo, suka sake gaisawa a gajarce tana ta bin Fathiyyan da kallo yanda take tura ciki tana wasu abubuwa kamar akanta aka fara. Tayi ?iba sosai cikin ya hurata dan duk yanda take ganin kanta se taga Fathiyyan ta kereta yanzu tayi murmushi data tuna farkon cikin da yake mata masifar ta saki jiki tana ta ?iba bayan ko Fathiyyah dake da ciki jikinya be buWe kamar nata ba a ranta tace
"Gara ni na haihu na san yanda asalin jikina yake yanzu za'a gane wadda tafi kyan jiki tsakanin me haihuwa huWu da me Waya ai".

Acan gidan kuwa bayan sun isa yanda suka ga jikin hajiya sam beyi masa daWi ba, ta lafke a kwance kusan komai idan zatayi se an taimaka mata tafiyar da take daurewa tanayi ma yanzun seda sanduna hannu biyu kana kallonta kasan tana da damuwa a tattare da ita sun tarar da Baba Bilki a gunta dan tunda ta kwanta a asibiti kusan Baba Bilkin ita take mata komai bisa umarnin Al?ali tare da taimakon masu aikinta. Ya zauna kusa da hajiyar kamar zeyi kuka yana gaisheta, ya kama hannunta da suka yan?wane duk jijiyoyi ta ko ina yace
"Hajiya ya jiki?" Muryarta na karyewa tace
"Da sau?i" se hawaye duk yanda yaso ya daure kar yayi kukan shima ya kasa kawai ya kife a jikinta ya fara kuka Fathiyyah ta taSe baki Afeeyah ta Wauke kai gefe dan kukan ne taji yana son zuwar mata itama Baba Bilki ce ta ringa ce masa yayi shiru
"Haba Malam, kaida zaka rarrasheta likita fa yace ta kiyayi koke koken nan kana dai kallo jikin ya?i daWi sabida ta?i barin zuciyarta ta huta da tunane tunane. Bata da aikin yi sedai ta zauna ta zurawa guri Waya ido kuma bata magana wlh karka so kaga yanda yaron nan Usaini kullum se yazo yayi ta janta da zance amma banda ido babu abinda take sa masa harfa likitan ?wa?walwa takwaran Al?ali ya kaita ta gani kuma dai ance komai lafiya lau to ciwon damuwa ne dai yake neman kamata ga hawan jini ga dipirishan ai kamar gaske da harta fara warewa muna yar hira amma tun shekaran jiya bansan meya faru fa kaga abu ya sake lalacewa, gaskiya ina ga a haWa harda magungunan islamic kyamis saboda fa da dare zabura ta ringayi jiya kamar me iskoki tana kiran matattu, ni tsoro ma naji seda na kira Yaya Audu yazo nan ya tofa mata addu'oi kafin muka sanu tayi bacci se jiya naji ashe wai Turai ce ta mutu ta yuwu mutuwar ce ta taSata amma ai ha?uri zatayi ta dubi yanayin jikinta in kuma ba so takeyi ta bita ba itama, gaskiya dai ka mata nasiha tunda dai kai tana jin maganarka".

Tashi yayi ya Wauki hajiyar kamar yar yarinya ya kaita Wakin ta ya zaunar da ita akan gado yajingina ta da allon gadon bayan ya saka mata pillows a bayanta sannan ya zauna suna fuskantar juna kafin yayi magana cikin muryarta da bata fita dakyau tace masa
"Ina so na bar cikin gidan nan Jafar, shi kaWai ne abinda ze sa na samu sau?in abubuwan da suke cin zuciyata. Zuwa na yarda na aikata kuskure a rayuwata amma bansan ta yanda zanbi na gyara ba. Ka dubeni yanda na koma lokaci Waya komai na rayuwa ya sauyawa mun, mutanen da nake tare dasu tun ?uruciya muke shirya abubuwa tare duk kaga yanda rayuwa tayi dasu yanzu Turai ko a cikin masu rangwamen hankalin ma cutarta me girma ce ance an wareta ma daga cikin mutane dan su kansu mahaukantan gudunta sukeyi, shekaran jiya aka tsinci mushenta a banWaki cikin kashi kace kace abun dai babu daWin ji balle gani ko gida fa basu iya kawota anyi Jana'iza ba saboda yanda kamanninta suka sauya acan gidan mahaukatan aka mata komai aka binne ta hankali na ya tashi sosai Jafar ina jin tsoron kar nina nayi irin ?arshen Turai ka gaya mun me zanyi na gyara kuskure na na baya ko na samu na rabauta" ta ?arasa tana fashewa da kuka me ban tausayi.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*LAST PAGE*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai, ubangijin daya kimsawa Wan Adam hikima ya kuma bashi fasahar sarrafa tunani da harshe harya samu hikimar isar da sako cikin rubutu. Allah ina gode maka ina sake jaddada godiyata a gareka bisa ni'imomin daka yi mini*

*Rubutu ya bani sababbin iyaye, yayye, kanne, ?awaye har ma da aminai. Rubutu ya haska mun rayuwa ya haWa ni da mutanen kirki na musamman da nake fatan haWuwa dasu har a filin barka. Idan nace zan lissafo sunaye littafi guda yayi mun kaWan haka idan na ware wasu na ambaci sunansu nayi son kai domin matsayinku guda yake a zuciya ta. Ina sonku saboda Allah tamkar yanda kuka so ni, ina alfahari daku ina kuma fatan zumunchin mu ya Wore har abada*

*Bani da bakin gode muku masoyan rubutuna musamman waWanda suka saka kudinsu suka siyi littafin HALI KISHI suka sake dawowa cikin tafiyar MATAR MUTUM. Tabbas kune masoya na ha?i?a masu burin ganin cigabanmu. Ina rokon Ubangiji ya yalwata arzikinku ya buda muku hanyoyin samu yanda kuke kokari sauke nauyi Allah karya hanaku yanda zakuyi a rayuwarku. Nagode da jumurin bibiya, na gode da hakurinku tun daga farko har ?arshen tafiyar nan, ina alfahari daku*

*Yan bati nagode kwarai da soyayyar bayan fage amma ku sani masoyi na hakika shine me burin ganin cigaban masoyinsa ta kowacce siga. Ina rokon ubangiji ya azurtaku ta yanda ba zakuji kyashin sauke hakkin wanda ya isar muku da darasi ya kuma nishadantar daku ba. Littafin Matar Mutum dari biyar ne kacal, a yayin da kika gama karanta wannan page na ?arshe, idan har kin tsinci koda abu guda daya ne na darasi a ciki kiyi kokarin sauke hakkin marubuciya ta hanyar biyan kudin karatu 500 asusun*
*7061838488*
*Opay OR*
*0709290797*
*Access bank*
*Maryam Farouk. Nagode*

Jikin Jafar har rawa yake, ya kiWima da jin mutuwar Hajiya Turai ya ringa nanata innalillahi wa'inna ilahi raji'un yana sauraron kukan hajiya da sam baya masa daWi amma ya barta tayi me isarta kafin ya fara mata magana yana cewa
"Babban ni'ima da ubangiji zeyiwa bawa ita ce ya buWe masa zuciyarsa ta gane banbanci tsakanin gaskiya da akasin haka a kullum shine abinda muke jaddada miki hajiya ki dubi kurakurenki ki yarda kin aikata ba daidai ba sannan ki nemi yafiyar waWanda kika zalunta tun kina da iko. Tabbas ubangiji me rahma ne kuma me jin?ai tareda yin gafara ga bayinsa masu yawan tuba. Duk girman laifin dake tsakaninki da ubangijinki idan har kikayi tuba na ha?i?a tareda kika ro?eshi ze yafe miki baya ga haka ki nemi yafiya da amincin duk wanda kika cutar ko kika zalunta a rayuwarki. Ki sani hajiya Allah baya zalunci ba kuma ya goyon bayan azzalumi haka nan babu afuwa ga cutar da kayiwa abokin halitta idan har ba ka nemi yafiyarsa ba kuma ya yafe.

Kinga ha??i hajiya babban al'amari ne da mutane muke rainashi, magana mara daWi idan ka gayawa wani ta sosa masa rai idan har baka nemi yafiyarsa ba tabbas se anyi muku hisabi haka komai ?an?antar ha??in mutum idan kaci ko ka danne har idan be yafe maka se an fidda masa shi a ranar gobe ?iyama. Dani dake mun san akwai kurakuren da kika aikata tsakaninki da mutane da yawa Wanda ya kamata ace tun da daWewa kin nemi yafiyarsu amma bakiyi ba, nagode Allah da har kika gane gaskiya yanzu kuma lokaci be ?ure miki ba zaki iya gyara kuskurenki sannan kici gaba da ro?on Allah akan sauran da ba zasu gyaru da hannu ko da baki ba in sha Allahu komai ze gyaru".

Tana share hawayen da suka ?i tsaya mata tace
"Nasan ba zasu yafe mun ba ko na nemi afuwarsu ?ila ma su sake samun damar aibata ni dayi mun duk abinda suka ga dama tunda na je gabansu neman yafiya, ina tsoron kar suce ba zasu yafe mun ba zuciyata ba zata cigaba da Waukar nauyin da yake cikinta ba, ?irjina yayi mun nauyi da yawa ina dab da gazawa"
"Allah yana duba zuciyoyinmu ne da niyyarmu akan komai, idan har zuciyarki ta tsarkaka kuma niyyarki me kyau ce ubangiji ze dafa miki ya kuma sanya aminci a zuciyoyinsu su karSi tubanki su yafe miki hajiya. Ki cire tunanin me mutane sukeyi ko me zasu ce akanki, wannan shine babbar matsalarki a rayuwa sanya ido akan wasu wanda shine yake gadar da hassada domin zaka ringa ganin abubuwan da zuciya zata raya maka basu cancanci su sameshi ba dakai ya dace. Ki tsarkake zuciyarki hajiya ki tuna gobenki iya kar yanda rayuwa ta taho daga farko zuwa wannan matsayin da kike idan kika duba zaki gane babu wani abu madawwami babu kuma abinda yake da tabbas. Yanzu muka sani bamu san mr ze faru cikin minti Waya me zuwa ba, kiyi ?o?ari ki ribaci lokacin daya rage miki" ya faWa yana ri?e hannunta.

Ta sake fashewa da kuka tace
"Ya zanyi da ha??in Bara'atu, Hadiza da Ahmad su da basa raye?" Jafar yayi shiru ya rasa abinda zece mata, da?yar ya iya cewa
"Yah Ahmad be taSa ri?arki a zuciyarsa ba, kallon mahaifiya yake miki har kuma ya koma ga Allah da buri shiryuwarki a zuciyarsa su kuma ki nemi afuwar yayansu sannan ki tsananta addu'a tareda neman yafiyar ubangiji. Kinga abinda nake gaya miki akan ki ribaci lokaci kiyi amfani da damarki tun baki sake tsunguma cikin wata nadamar ba".
Sama da awa guda kafin ya fito daga Wakin ya baro hajiyar, Fathiyyah kaWai ya gani a falon tana ganinsa kuwa ta mi?e tana kumbura da ?ananun magana ita an barta a zaune kowa ya fashe fuska babu walwala yace mata
"Ina Afeeyah" ta bashi amsa da
"Ban sani ba" tana murguWa baki, ya wuceta ya fice daga falon a gurin Hajiya Zubaida ya tarar da Afeeyan tana cin Funkaso ya zauna ya gaisheta yana kallon Afeeyan data ?i kallon inda yake se hajiya Zubaida ta mi?e tace musu tana zuwa, tana fita ya sauka ?asa ya zauna a bayanta ya sakata a tsakiyar ?afar sa sannan ya zura hannu yana gutsirar funkason shima duk yanda taso ta zame kuwa ko a jikinsa seda suka cinye tas kafin ya Wagata suka wanko hannu a kitchen sannan ya sake fita ya barta a gurin.

Se bayan sallar isha'i suka tafi lokacin Alhaji ya dawo suka shiga tare su ukun suka gaishesu har ya basu zam zam kowacce roba Waya irin wanda yayi Wawafi dashi. Washe gari suka wuce Abuja shida Fathiyyah dasu Layla saboda Aminu da yace akai masa su suyi hutu kwanansa biyu a can ya dawo suka ?ara kwana biyu sannan suka juya tare da Afeeyah har lokacin kuma hajiya bata san da cewar tana da ciki ba ba kuma tace komai ba da ya gaya mata tare zasu tafi.

Satinsu uku a Paris yammacin wata Juma'a Afeeyah ta haihu, tun daren Alhamis dama take jin yanayin baya mata daWi ta dai daure sanin ko haihuwar ce zata iya kaiwa goben tunda tasan yanayin yanda take zuwar mata koda safe da Jay ze fita ya tambayeta lafiya dan ya lura se fushi take tace masa babu komai, bayan ya fita kuma taji ciwon gaske ya fara zuwa dan haka ta nemi cab ta tafi Asibiti bayan abinda akayi Allah ya sauketa lafiya ta haifo Wanta me tsananin kama da ubansa, ita kaWai ta ringa kuka sanda aka bata yaron, rabon zuwansa ne ya kautar da Ahmad. Seda tayi wanka tana kwance a resting room ita kaWai se nurse kamar mara gata kafin ta kira wayar Jay dukda tasan suna da wasa a lokacin cikin sa'a kuwa kiran na shiga ya Waga yana ce mata ina ta tafi?
"Na dawo gida bakya nan duk na kasa nutsuwa ko wasan ma na gagara yi dakyau i had to excuse my self and come back jikina yana bani kamar kina cikin wani yanayi mara daWi" ya faWa a jere, daWi ya ratsata dagaske kenan yana jin duk yanayin da take ciki a jikinsa bawai daWin baki bane.

Ce masa tayi taje asibiti ya sake rikicewa yana tambayar me ya sameta tace babu komai kawai taje ne amma yanzun ma zata taho yace No ta jira gashi nan zuwa cikin mintuna kaWan kuwa ya isa ya buWe baki cike da mamaki yana kallon Nurses Win reception da suke congratulating nasa sanda ya shiga, kawai bin wata Nurse ya ringayi harta kaishi VIP inda Afeeyan take tareda babynta. Ya rasa me zeyi, tsakanin sanin cikin da haihuwar bema san wanda yafi taking nasa by surprise ba daga wani bangaren na zuciyar sa kuma yaji haushinta sosai amma ya danne me yasa take masa haka? A hankali ya ?arasa cikin Wakin ya wuce inda babyn yake kwance ya Wauke shi yana jin wani abu yana ratsa shi, sanda yaron ya buWe ido ya kalleshi ko ji yayi kamar an masa rahma a duniya, ya rungumeshi bayan da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login