Showing 180001 words to 183000 words out of 467220 words

Chapter 61 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12156

a ya?in nan haka kike fata fata da mutane" seda ta murmusa. Suka zauna Abdul shiru shirun Abokinsa yace musu yana waving, sukayi waving back.

Badar da take kar a fita se gashi sun shantake suna zuba zance akan movie daya sako mata a flash drive suka bar Afeeya da Abdul da idan ya fadi magana guda se yayi minti takwas be sake cewa komai ba sedai murmushi, irin marasa maganar nan ne har mamakin Abotar su akeyi da Nurain da ko bacci da?yar idan bakinsa yana shiru, seda goma ta buga Afeeyah tace bacci takeji kafin suka tafi gurin Sambo karbo Macdee.

Guda shida Badar ta ce a musu yan 300, Nurain ya buga tsallen albarka yace baze biya ba, ita kadai ze siyawa taya zataci Macdee shida? Sanin za'a kwata hakan yasa Afeeya fita da ATM Winta dan tasan hali tsaf se an gama saka musu ze iya guduwa ya barsu a gun gashi kuwa sunzo suna drama yace sedai ta aje huWu kuWin biyu ze biya ita dai ta bawa Sambo ya cire kuWinsa yana dariyar lamarin Badar da Nurain, sedai basuje gurin ba amma kullum se sun siyar da hali.

"Wadannan yan uwan naki kullum kukazo se sunyi Drama" Sambo ya faWa, Afeeyah tayi dariya tace "saurayine me Mamma?o da Budurwa me kwaWayi"
"Allah ya isa amma kin cucemu" suka haWa baki gurin faWa ita dai ta tsallake ta barsu, bata san ya suka ?are ba dan har ta kwanta Badar ta shigo harda ?arin Kaza guda Waya da Can Exotic guda shida se L&Z one liter. Suka baje suna ci taji ?arar text ta duba taga Alert 5k from Usman Bashir Yabo ta nunawa Badar tace
"Saurayinki ne, kinsan dadin rantawa Bestie kuWi harda extra ze biyaka"
"Dan rainin hankali,, kawai shi se anyi surutu hankalinsa ze kwanta, da kuWin fa a jikinsa har cash ya bani bari ma na tura masa kiga karna manta amma shine ze yarfamu akan Macdeen 1800 kuma ki biya ya wani maido miki da kuWin yaron nan se a hankali".

"Sonki yake shiyasa yake neman fitinarki" Maman Minal data dage akan zancen ta ta sake faWa, Afeeyah tace
"Allah ka nunamun wannan rana Nurain da Badar, bangon gidanku Adon Fire extinguisher zan muku saboda tsaro" duk suka saka dariya harda ita da suke tsokana.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 10*


Da wata irin kasala ta farka da Asuba sakamakon mafarkin data kwana tana yi. Ta kalli Badar dake masifar tun
Wazu take tashita amma ta mata banza.

"Haba Badar ki barta mana" Maman Minal ta faWa kafin taci gaba da cewa
"Kin san dai Afeeya tana riga kowa tashi ko bata sallah se ta farka ta tashemu tunda kikaga yau ta makara se ki mata uzuri".
Badar tayi tsaki tace
"Idonta biyu fa tsabar iskancine idan ba zatayi sallar ba seta faWa ai a barta" fuu taci gaba da juye ruwan zafin da take a bokiti. A kasalance Afeeyah ta yun?ura ta tashi zaune tana cewa
"Zanyi mana", gabanta ya faWi saboda yanda tajini a ji?e, mafarkin da tayi ya shiga dawomata seta kalli Badar data zuba mata ido itama, kamar zatayi kuka amma ta kasa cewa komai.

"Kar dai fa Aljanin darene yazo mata? Mutumin data haWu dashi jiya kwana tayi tana mafarki dashi kuma ta tashi cikin wannan yanayin karfa da gaske Aljanine? kai Innalillahi taga ta kanta ita Afeeya ina ta kwaso Aljanu ta shiga uku" ta raya a zuciyata kafin ta sake yun?urawa tana tattare rigarta a ranta ta ?udurce tana yin sallah zata kira Ummanta ta faWa mata tun wuri, bata taSa irin mafarkin ba se yau gara ta faWa mata koma menene a tareshi tun kafin ya aureta ta shiga uku.

Seda na sauka daga gadon ta kalli shimfiWar stain Win jini da ta gani ya sakata sakin ?affaffar ajiyar zuciya saboda ganin wani abu daban ba yanda tayi tunani ba. Towel ta Wauka ta wuce wanka da Ruwan Badar tana jin tana zaginta amma ban tanka ba. Seda ta kintsa kainta kafin ta cire bedsheet din ta kama inda ya baci ta wanke a baza daman yau zasu haWa wanki, takwas saura suka fita class bayan sun karya har sannan kuma jikinta a sanyaye yake idan na tuna mafarkin jiyan se taji Zuciyarta ta buga kuma wani abun mamaki sukayi waya da Umma da Baffa amma ta kasa faWa mata kamar yanda tayi niyya, abin ne da nauyi kawai Anty Sauda zata kira to ta faWa mata.

A Ajin ma bata da wani kuzari da kuzari Malamin da kansa seda ya tambayeta lafiya take tace kanta ne yake ciwo. Malamin na fita Class Rep Winsu ya tsallaka sit Win da suke, ta kwantar da kanta a kan Desk suka gaisa da Badar da Yusuf ta harari Sahid dan basa shiri kafin ya kalleta yace
"Whitey (haka yan class Win suke kiranta ko Afee whitey saboda haskenta) I have been looking for you since yesterday"

Ba tare data Wago ba tace masa
"Ya akayi?" Dan Sahid akwai dan banzan surutu shima da gulmar tsiya
"Wani mutumi ne, I mean one guy asked me about you yesterday and i told him every detail i know har layinki na bashi, Afee you don do good catch i swear, from his looks gayen nan is Rich, his face looks familiar to me but i couldn't figure out inda na sanshi" Sahid ya fada. Badar ta harareshi tace
"Haka ka iya kai dai ka zama kamar wani kawali kullum cikin haWa yammata da Samari", hausar bata bawai yana jinta dakyau bane Banufe ne dan haka ya kalli Yusuf da suke tare yace

"What is Kalali? Because i know Badariyya, when ever she speak big big Hausa word she is up to no good" dukda yanda nake jina amma seda nayi dariyar maganarsa Yusuf yace
"Tana nufin you are a good match maker"
"Ehen" Sahid din ya sake fada da alamar be yadda da abinda ya fada ba amma se ya maida hankali kaina yana cewa
"He gave 100$"
"Kaji daWi" Afeeya ta faWa tana mi?ewa saboda cikinta daya hautsina, tsallakesu tayi ta fita da sauri can gurin fanfo tana zuwa ta shiga she?a Amai masu wucewa suna binta da sannu. Kamar ta kunno ciwo tana gama aman marata ta ri?e ita da bata Mp se gashi ta gagara tashi tsaye daga gurin seda Badar tazo ta Wagata.

"Muje Hostel kawai daman baki da lafiya amma kika fito?" ta faWa suna tafiya a hankali. Yusuf ne ya kaisu har gaban Amina a motarsa kafin suje ta galabaita juye juye kawai take a cikin motar na azaba dakyar ta iya fita ai kuwa nan gurin Security ta kwanta tana kuka shaSe shaSe kamar wadda zata haihu, abinda bata sababa, bata taSa experiencing ciwon Mara ba se lokacin shiyasa take jinsa wani sabon abu kamar zata maWe.
aka daka saboda ciwo.

"Sannu Afeeya me yake damunta?" Anty Amina daya daga cikin matan security da mmsuke mutunchi dasu ta tambayi Badar,
"Inaga zazzaSi ne" Badar ta bata amsa Afeeya ta nuna musu mararta da hannu, cikin tausayawa Anty Aminan tace
"Wayyo sannu, daure ku ?ara ciki se kisha ruwan zafi da pain relief, Allah ya kawo Afuwa"

"Kuje kuyi aure yara kun zauna kuna fama da ciwo" ?aya matar ta Saro maganar, Badar ta Anty Amina suka kamata ganin an fara taruwa akana kallonta wasu na cewa Aljanu takeyi. A common room suka ajiyeta ta kasa zama kan kujera se a ?asa ta kwanta tana cigaba da mur?ususu, ashe haka Matan suke ji amma ta ringa cewa Bafar raguwa idan tana ciwon Mara yau gashi Allah ya kamata itama kamar fa an hura mata wuta takeji a gurin wannan abu da akwai Azaba.

Ta fi awa a gurin kafin ciwon ya lafa mata lokacin har gashin kanta seda ya hargitse kamar wadda tayi na?uda. A dudd?e ta ringa tafiya har sukaje Waki, duk wanda Badar ta gayawa abinda yake damunta se yayi dariya kafin ya mata sannu dan haka take musu. Sururat ta haWa mata ruwa me zafi takai mun banWaki kafin ta fito Badar ta haWa mata shayi me kauri ta gyara mata gado, kamar wata sarauniya haka suke lelenta suna mata iskanci kuma, tasha Paracetamol ta kwanta bacci ya kwasheta wata Jalalar Mutumin ya sake diro mata a mafarki amma ba irin na daren jiya ba.

Na daWe sosai tana bacci har gurin qarfe biyun rana kafin ta farka ta ji daWin jikinta se abinda ba'a rasa ba. Kamar me ciki ta seda ta sakeyin Amai kafin tayi tsarki da ruwa me dumi sosai ta canza pad ta koma Waki tana tafiya salaf salaf kamar waddata fito daga Labour room.

"Abin nema ya samu" Ummi ta faWa ta harareta kafin ta zauna kan Gadon Maman Minal tana cewa
"Tun jiya Ummi daga zuwa Lecture baki kwana a nan ba?"
"Bayan na fito daga lectures ne na hadu da Surayya shine kawai na bita City tunda yau banida lecture, yanzu ma motar bati na samu shiyasa na taho da wuri" Ummin ta bata amsa kan tabi Cousin Winta city gidan Antynta.

Afeeya ta kalleta badan ta yarda Zaria City tasan baze wuce yawonta na banza ta tafi ba. Ummi bataji ko kadan, ta santa tare sue a English da zasu shiga Level 3 Win nan ta bari ta koma Library science saboda rashin mayar da hankali ana nema a koreta, party da clubbing a Zaria babu inda bata sani ba yanzun a hakan ma ta rage ne zama dasu suna matseta dole ta rage wasu abubuwan da wuya ta fita ta kwana a waje duk yawonta zata dawo Hostel.

"Wlh gidan su Surayya naje idan ma baki yarda na kirata yanzu kiji da kunnenki" ta katsewa Afeeya shirun da tayi dason wanke kanta. Wayar Afeeya ta fara ringing akan gado ta Wakkota tana cewa
"To me kikaji nace Ummi? Duk ma abinda mutum yayi ai dan kansa me kyau ko mara kyau zaka tarar da sakamakonka me sonka ne yake damuwa da abinda kakeyi har yake so ka hau hanyar daidai". Ahmad ne yake kiran kafin ta answer ta ktase se lokacin taga missed call daya mata kafin wannan kiran.

Wani kiran ya sake shigowa, ta Waga yana narke murya dan bata so wayar tayi nisa.
"Fatima kin tashi? Ya jikin?" Ya faWa cikin kulawa, ta kwanta tana cewa
"Da sau?i, ka kira aka ce ina bacci ne?"
"No, dana kira baki Waga ba i called Badar ita ta gaya mun bakya jin dadi ta barki kina bacci i hope you are feeling better now? Kodai zakuje hospital ne kira Ilyas ya kaiku?" Ya sake tambayata a tausashe, a maimakon taji daWin kulawar tasa ma haushi yake bata ya fiya sanyi da yawa ta muskuta tana cewa
"Nafa samu sau?i kuma nasha magani, Ilyas na zata ya bar Zaria ai"
"No yana nan be samu sun canza masa din ba so kuma ma saura two months ya gama shiyasa ya ha?ura" (cousin Winsa ne yaron sister Momy da yake Internship a Shika Asibiti).

"Ayya Allah ya bada sa'a, ya kake? Abujan? Yaushe zaka dawo?"
"Are you missing me?" Ya faWa yana sakin murmushi najin daWi yau Fatima ta tambayeshi wani abu daya shafeshi, kunya ta kamata tayi murmushin ita ma amma bata ce komai ba yaci gaba da cewa
"Se Thursday In sha Allah, kina zumuWin ki ganni ne?"

"Uhm" kawai tace, cikin tsokana yace mata
"Da gobe fa zan taho, sena haWu da wata yar farar Yarinya me irin zubinki, ita take so ta ri?eni na kasa tahowa".

Ba wani son sa take ba ba amma se da zuciyarta ta sosu da abinda ya faWa kishi ya taso mata, a ?ufule tace
"Kace kayi budurwa yar Abuja yar gidan masu kuWi" yanda tayi maganar ita kantaseda ta idar ta fahimci muryar da tayi amfani da ita tayi kauri da yawa ta kuma bayyana kishin daya taso mata ?arara. Dariya sosai Ahmad yayi tayi shiru kunya da takaicin kanta suka rufeta, seda yayi me isarsa kafin yace
"Ashe dai Fatima na kishina haka? Gaskiya naji daWi".

Bata sake ce masa komai ba ya gama surutansa tana ji ganin ta ?i bashi amsa yasa ya canza akalar maganar da cewa
"Haka kawai Tuwo nake sha'awar ci da Miyar Kuka, kamar na tafi Kano yau ma nake ji"

"Ikon Allah Tuwo kuma ka rasa wacce miya seta kuka?" Ta faWa cikin mamaki dan zata iya cewa a matasa dai shine mutum na farko data taSajin yana son Miyar kuka, Yah Malam dinsu cewa yayi ganyen bishiyar Aljanu ne tsaSar hatsabibanci irin na mata suka mayar dashi abinci shiyasa duk me yawan cinsa kwakwalwarsa toshewa take saboda sharri.

"Kuka dai da kika sani, ni ai idan kina so ki burgeni to ki bani abincin gargajiya amma fa with a touch of modernity bawai kuma ayi abu babu sha'awa ba, irinsu dambu, Akubus, Fate, ?anwake babu wanda bana ci kuma a kowanne lokaci zan iya ci be it safe, rana dare duk zan iya cinsu musamman idan an shiryashi ya dace da lokacin".

Kai ta Waga kamar yana ganinta tace
"Na gane"
"Yawwa idan ma baki iya ba se ki koya dan ni babu ruwana da wasu continental dishes da kika ganni shiyasa ma kikaga nake daidaitan se Umma ta sauke abincin dare nake zuwa gidanku dan ba ?aramin daWin girkinta nake ji ba kuma na ci na Anty Sauda ma naji yayi kalar na Umma Allah yasa kema haka kika iya girki"

"Ina koya" ta bashi amsa a ta?aice tana janye wayar daga kunnenta, minti goma sha daya suna magana zan iya cewa basu taSa kaiwa haka suna waya ba idan ma sunyi to befi sau a ?irga ba. Kamar ya shiga ranta taji shima yana cewa
"This is our longest phone call so far, bari na shigar dashi a Diary yau Win ta shiga tarihi".

Ta yatsina fuska kamar yana ganinta kafin tayi magana cikin sauri taji yace
"Ki huta Fatima, i will call you later Jafar yana kiran Waya wayana".

Wani tu?u?in ba?in ciki ya taso mata dajin sunan wanda ya ambata. Ta tsani Jafar Win nan tsana me tsanani da bata san iyakarta ba. Bata ko amsa masa ba ta kashe wayar tqna jan mugun tsaki. Maman Minal da bataji shigowarta ba ta ce
"Lafiya kike tsaki haka?"
"Babu komai" ta bata amsa tana mi?ewa saboda yunwa data faraji. Ta zuba taliyar data gani a tukunya ta hau ci ranta duk a dagule, ta kusan cinyewa Badar ta shigo da alama ta kwaso yunwa dan hannu kawai ta wanke ta dirarwa abincin da Afeeyan take ci seta tsame hannu ta bar mata dan daman ta ?oshi gudun kar su mata masifar da suka saba idan ta rage abinci yasa take turawa da?yar.

"Jibi tuwo zamuci a Wakin nan" Maman Minal data idar da sallah ta faWa, Afeeya ta kalleta, Badar tace
"Ai kuwa mun kwana biyu bamuyi tuwo ba. Bari rana ta lafa s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e muje cefane miyar me za'ayi?"
"Kamar Kuka naji kince ko Afee?" Ta jefawa Afeeyah tambayar, zare manyan idonunta tayi tana kallonta da rashin fahimta dan bata gane inda maganarta ta dosa ba, ita yaushe sukayi zancen tuwo?

Maman Minal Ta mi?e tana ninke sallaya tace
"Zancen tuwo naji sunayi da Ahmad shine naji sha'awarsa nima kinga se ta mana Jibi idan zezo"

"Kai Anty Zahra daga jin muna magana bafa cewa yayi yana so ba labari ne kawai ya kawo maganar ba cewa yayi na masa ba" tayi saurin defending kanta kafin su ?allaba mata abinda bazata iya ba. Badar dake side hannu ta cafe tana cewa
"Aiko yin tuwo Lazim idan ba so yake ba meze saka ya miki zancensa kawai dai be fito kai tsaye bane ke kuma in kinada lissafi ai kinsan me yake nufi Allah ya kaimu jibin dama bamu da Lectures kuma na shinkafa zaki mana Aradu ki tu?eshi da kyau yasa malmala mu kwashi gara abinmu"

"Aiko zaki Wige indai ni zan tu?a miki tuwo, shima ya nemi inda zeci tun dare be masa ba wlh" Cewar Afeeya, Badar ta hayayya?o mata tana cewa
"Wlh se kinyi, ko mu ba zaki dafa mana ba se kin wa Ahmad banza wadda bata san Abin kirki ba. Ahmad Win nan kwanta miki kaWai ya rage ya farayi amma hakan be saka yaci darajar mutunchi kema ki ringa mutuntashi ba kici gaba ubangiji ya miki ni'ima amma kina nema ki butulce masa in bakiyi wasa ba kika watsar da damarki ba fata na miki ba gaba se kinyi kuka da dana sanin rasa shi dan wlh a zamanin nan samun kamar Ahmad Namiji kyakykyawa, me kuWi ga Ilimi da nutsuwa ga hankali kuma ya soki tsakani da Allah bawai da lalataba se an tona ai mazan dai gasu nan ke zaki bada labari dan babu kalar saurayin da bakiyi ba kowa kuma yazo iskanci yake kawoshi koda wanda ya tsaya bayan Ahmad din" Badar ta faWa a hasale bacin ran ya nuna har kan fuskarta.

Kallonta Afeeya tayi bayan data zauna akan gadonta, bata tanka mata ba ta maida kai kan wayarta tana duba number data kirata yanzu kafinkuma ta answer ta katse, ganin ta waje ce yasa ta ajiye wayar ta yuwu Kamfanine ko sacammer. Tana jin Badar na maganganu tayi mata banza dan idan ta tanka se ran kowa ya Saci.

Badar tana yawan faWa mata maganganun da bata jin daWinsu akan Ahmad amma tanayi mata uzuri saboda tasan bada wata manufa take faWarsu ba a ganinta damuwa da lamarinta nema har yasa take tada jijiyar wuya akan abinda ya shafeta amma kuma idan aka kalli maganar tata ta wata sigar tana nuna kamr Alfarma Ahmad yayi mata da har yake sonta wanda wannan yana daga cikin abubuwan da yasa bata sonsa.

Bazata auri Mijin da ya zarce matsayinta ba wanda kowa ze ringa mata kallon cusa kanta tayi ko kuma Alfarma yayi mata daya aureta bata kai Ajinsa ba kamar yanda ?an uwansa ya faWa mata.

"Badar na gaya miki ba sau Waya ba ba sau biyu ba idan kina son Ahmad na bar miki shi kuma zanyi duk iyawata gurin ganin kin same shi. Na sani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login