Showing 333001 words to 336000 words out of 467220 words

Chapter 112 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12119

yanda suka shiga suka fita shida uwarsa ya samu ya shiga jikin Alhaji kaida ya cigaba da rayuwa me kake tsammani a gidan nan? Inaga wata rana duk se ya saka Alhaji ya kore mu yace mu bi duniya. ?iri-?iri yabi ya kankane Jafar ya hanashi cigaba, duk yanda naso mu haWa kai da yaron nan mu gina gobenmu ya?i saboda huWubar tsiyar da yake masa to dai gashi Allah ya mun maganin komai se inga ta tsiyar Aisha.

Lokaci kaWan ya rage kowa da komai ze sake dawowa hannuna yanda yake tun usuli, amma fa se mun dage dan ya?in yanzu zefi na baya wuya saboda abubuwa sun canza an shammaceni da yawa amma komai ze gyaru" Hajiyar ta faWa tana kaWa ?afarta me lafiyar.

***********
Rayuwa ta fara mi?awa har anci wata guda da rashin Ahmad sati uku kuma da komawar Fatima can gidanta. Jafar ne tsaye a kansu, duk wani abin bu?ata shi yake samar musu dashi shiga goma fita goma ze tambayi Baba Bilki me suke da bu?ata? Babu dai wata matsala ko? Dan Fatima ta gagara sakewa dashi balle har ta iya tattauna wata magana dashi. Ko gidan ya shiga idan tana falo zata shige cikin Waki, idan kuma tana Wakin daman ba zata fito ba har se ya gama abinda yakeyi ya tafi. Baba Bilki tayi mata mitar harta gaji ta barta.

"Bansan abinda ya haWa ki da Jafaru ba amma koma menene nake ga yaci ace yanzu kin watsar da komai, idan a baya beci albarkacin Yayansa ba ai yansu kya dubi Wumbin ?aunar da yakewa yayanki tasa ki sakar masa fuska. To wama yasan me gobe zata haifar?" Haka Baba Bilkin take mita sedai ta jita da kunne kawai amma ba zatace komai ba.

A be shiga gidan da yawa ba a rana ya shiga sau biyar, shi yake kai yaran makkaranta ya Wakko su sannan ya kaisu Islamiyya dake nan cikin unguwa ce babu nisa tareda yaran gidan Alhaji Munzali suke dawowa. Ana yin magriba kuma ze shiga ya tambayi me suke so? Wani lokacin da anyi isha'i ya deSe su su tafi yawon siyo kayan ?walama ko kuma ya tafi shi kaWai ya siyo musu idan ya dawo ya zauna suyi homework suyi hira bazebar gidan ba se sunyi bacci.

Shige da ficen nasa ita takura mata yakeyi da kuma yanda yake son sakota a shirginsa ya ringa tambayarta ya take babu wata matsala ko ya wannan ya wancan ko ba zata tanka ba se yayi ta mata magana musamman idan ya tarar Baba Bilki na mata mitar rashin cin abinci ko tayi shiru tana tunani ko kuka haka ze zauna ya fitittika yana masifa har cewa yake idan ta bari wani abu ya samu cikin jikinta baze yafe mata ba, se kace cikinsa.

Kwanan Ahmad talatin da biyu da rasuwa Fatiyyah ta dawo Kano, sanda akayi rasuwar sunzo tareda yan gidansu kwanansu biyu da zasu tafi ta biyu bisa goyon bayan Hajiya Binta bayan da tayi ?aryar bata da lafiya. Yanayin ciwon nata yayi kama da laulayi ciki koda Mamanta tace ta zauna Hajiya ta fitittike tace ba zata zauna ba ta bisu su tafi haka kawai ta zauna mayu na zuruftun zuwa yiwa yar uwarsu gaisuwa gidan a samu wata ta lashe mata Wan tayi tun beyi ?wari ba toba zata dau?i ganganci ba.

Tafiyar tata bata damu Jafar ba dan idan ta zauna ma takura zata zame masa a yanayin da yake ciki kuma haushinta yakeji sosai saboda yanda kwata kwata bata nuna damuwarta akan ciwon Ahmad ba harya rasu. Sannan ya Wauka zata zama cikin sahun farko na mutanen da zasu nuna damuwarsu a gareshi saboda rashinda yayi amma ta shayar dashi mamaki ace matarsa har seda suka kwana biyi da dawowa Najeriya kafin wai ta biyo yan gidansu sukazo gaisuwa kuma ta sake cewa zata bisu su koma shiyasa da zasu tafi barin gidan yayi dan baya so su haWu bare ta sake Sata masa rai be kuma kirata ba idan ma ta kirashi se yaga dama yake amsata be san da zata dawo Win ba ma ya fita kawai ya koma gidan ya tarar da ita.

Kamar kuma yanda yayi hasashe tana dawowa Fatiyyan ta fara kunno masa da sababbin futuntunu. Tunda akayi rasuwar basu wani zauna da Hajiya ba. Kullum yana zuwa gidan ya gaishe ta sannan ya duba Momy kuma Hajiyar bata taSa cewa wani abu ba amma Fatiyyah na dawowa ko kwana biyu ba'ayi ba tunda taje gidan ta samu Hajiyar ta karanta mata ?arya.

Hankalin Hajiya yayi mugun tashi sanda Fatiyyan ta sanar irin hidimar da Jafar yakeyiwa Fatima da yayanta.
"Kullum ta Allah a be kashe musu kuWi ba Hajiya ya kashe dubu Wari biyu ko fi, yafa zamar musu direba ko ina shi yake kai yaran kuma koda yaushe yana can gidan a can yake wuni bacci ne kawai yake shigo dashi gida kuma ko ya kwanta banda mafarkinsu dana Ahmad Win babu abinda yakeyi haka zakiji cikin dare yana surutai yana kiran sunansu se kace wanda suka asirice" Fatiyyan ta faWa tana share hawayen munafunci.

Hajiya ta aje numfashi tace
"Lallai, wato Aisha dagaske takeyi ba zata rabu dani ba, amma babu komai ina nan juyawa kansu akwai shirye shiryen da nakeyi da zarar na cimma abinda yake gabana zan juya kanta daga ita har shegiyar Fatiman zanyi maganinsu. ?adda kama kawai nakeyi shiyasa na Wauke kaina akansa na barshi yake abinda yaga dama amma zasu gane kurensu lokaci kaWan ya rage". Da Fatiyyan ta tafi kasa zama tayi ta tafi gurin Alhaji Audu.

Taso ta Wan bada ?afa ayi koda sadakar Arba'in ne amma kuma taga alamar a garin neman gira zata rasa ido gara tayi komai da sauri ayi wadda za'ayi gayyar ta watse.

Sanda ta shiga Alhajin na zaune akan kafet Hajiya Rabi na daga gefensa tana matsa masa ?afarsa da ta Wan tasa, ba iyakar ?afar ba duka jikinsa ma ya kumbura kamar wanda sanyi ya hura ta samu guri ta zauna bayan data bankawa Rabin harara ita dai tunda tayi mata kallo Waya ta maida kanta taci gaba da abinda takeyi.

"Ciwon ?afar ne ya tashi kenan Alhaji? Sannu ai an sha zama kusan sati biyu fa kullum kana naWe akan tabarma wuni guda ana abu Waya, Allah dai ya bada lada ya ji?an Amadu yau fa har kwana talatin da huWu lallai tafiya ta mi?a" ta shiga zuba kamar lalatacciyar radiyo. A ciki Alhajin ya amsa da "Amin". Hajiya Rabi ta kwashe magungunansa daya sha da man zafin data shafa masa ta wuce sama dasu, Hajiyar ta sake binta da harara kamar idonta zasu faWo. Ta tsani ta buWe ido taga wata mace a cikin gidan tareda Audun bayan ita. Aisha da Rabi sun zame mata jaraba, ta iya korar Zubaida tsohuwar kilali da Hadiza gogaggiyar Bazawara, Bara'atun da tasan Audu naso kamar ransa itama seda ta fitar da ita daga gidan amma waWannan biyun sun zame mata ?arfen ?afa ta rasa yanda zatayi dasu.

?wafa tayi a fili kafin ta gyara zama tayi ?asa da murya kamar ta Allah tana kallon Alhaji tace
"Niko ina taso na tambayeka, an kuwa biyawa Amadu basussukan da ake binsa kafin aka rufeshi? kasan fa bashi yana hana mutum kwanciyar kabari kar muje muna nan muna abin mu shi yana can a tsaye kuWaWen jama'a sun hanashi ajiye ha?ar?arinsa, ah to, irin wannan kurWa- kurWa daya ringayi Allah kaWai yasan yawan kuWaWen jama'ar da suke a hannunsa".

Kallonta kawai Alhajin yakeyi cike da mamaki harta kai aya yama rasa abinda zece mata, ta karkace tana sake mi?e ?afarta ta ?arfe dan bata lan?wasuwa tace
"Ahaf, ai dama na hasaso haka, ba lallai ace kun tuna kunyi abinda ya dace ba. Ita kuma Aisha gudun kar abinda zata samu na rabo ya ragu ai ba zata tuna muku a samu a sauke masa nauyi a fitarwa da bayin Allah ha??in su ba balle kuma waccen matsiyaciyar matar tasa wannan ko tasan wani da yake binsa kuWi ai ba zata faWa ba Soyewa zatayi".

Seda ya furzar da iska kafin yana kallonta yace
"Binta kenan, to ai shi Ahmad Allah ya taimakeshi a rayuwarsa be iya rakice rakicen rigima ba, kuma kurWa- kurWar duk da yayi da guminsa ne babu sisin kowa a ciki, idan ma da wanda yake binsa bashi tun kafin ya bar ?asar nan ya biyasu dan munyi cigiya kuma har yau babu wanda yazo yace yana binsa bashi sedai waWanda shi yake binsu kuma da yawa sun maido dashi kaWan suka rage wanda basu bayar ba"

"To madallah, ai haka ake so. Gara suyi su kawo a raba gado a sallami kowa dandai kasan shima gadon nan nauyi ne, kuma ance a gaggauta saukewa mamaci shi, to amma da zaka ce babu wanda yake binsa bashi halan ka manta da kuWin fili dana ginin kantin da kayi masa? Ko kuwa an shiga an fita an mantar dakai za'a hau kan dukiyarmu ayi rubda ciki?" Ta sake faWa tana tsareshi da ido. Seya ajiye ruwan daya Wauka zesha ya kalleta da kyau yace

"Dukiyarku keda wa?"
"Kwarai kuwa dukiyarmu nida yayana dan dai kasan yau ka faWi ka mutu nafi kowa kaso a cikin dukiyarka, banda ma zuciyar musulunci tsaf zan iya rufe ido nace duka komai nawa ne tunda dai ubana nane silar komai" Bintan ta bashi amsa har tana buga cinya da gatsine hanci. Mamaki ?arara akan fuskarsa yace

"To ai se ki jira ma mutu kafin kiyi fiffi?ala akan dukiyar. Binta bafa yanke talauchi mahaifinki ya bani ba, ba kuma bishiyar kuWi ya shukamun nake tsinka ba wasu yan kuWaWe ne ya bani naja jari yalwa da bun?asar da sukayi nasibine daga Allah da kuma jajircewar da nayi gurin juya dukiyar harta zama yanda take a yau ba wai shuka kuWin da ya bani nayi ba balle kice sune suke ta yaWo ina ci.

Idan lissafi za'ayi ko iya kuWaWen dana kashe aka saka miki wannan ?afar ?arfen sun zarta abinda kusan shekaru hamsin kenan kina goranta mun akansu. Idan aka haWo da wahalhalun da nayi dake da yayanki tun ?uruciya kinga ai ciko ne ya biyoki, kar ma a lissafa da wanda aka sata bada sani na ba, yau ko shi mahaifin naki be isa yace shi yamun arzi?i ba domin rabo nane Allah ya saka a jikinsa tilas ya bani dukda harya bar duniya rana Waya be taSa gaya mun magana mara daWi ba balle yayi mun gori, albarkacinsa kike ci shiyasa kika Wauki tsayin lokacin nan kina mun abubuwa ina sharewa badan bazan iya Waukar mataki akanki bane ba"?

Zabura tayi tana cewa
"Saboda nabi diddigin ha??in mu shine zaka gayamun magana Audu har ka nemi la zagi ubana? ?arya nayi ba ubannawa ne silar Arzi?in naka ba? Me kake dashi da? Badan shi ba da ?ila yanzu talauchi ya rigada ya kasheka, idan ma kana raye da a shekarun ka na yanzu ka daWe da zama tsumma, har kuma saboda butulci irin ma Wan adam ka iya buWe baki ka barranta kanka dashi, to ko kaso ko karka so Arzi?in da kake ta?ama dashi na ubana ne badan niba da baka same shi ba kuma billahillazi Aisha tayi kaWan taci wannan fili ita kaWai, idan ma asirceka tayi ka zauna kama waWanda maganganun ko a cikin ruwa akayi asirin nan se an nemo shi an karya domin taci ?arya ta kwana da yunwa taci wannan dukiya tunda bata ubanta bace" tana gama faWar haka ta tashi tana cangala ?afa ta bar falon ranta na tafarfasa.

Sanyin da tayi tarko ne domin so takeyi ta san duk yanda zatayi Alhajin ya karSi super market Win Ahmad Win ya mallakawa Waya daga cikin yayanta, shi yasa harta Wauke ido ta bar Jafar na abinda yaga dama tsakanin gidan da gidan Ahmad amma yanzu tunda sabgar babu arzi?i zata tsefe ta koma Bintan ta kuka koda tsiya koda tsiya tsiya duk wata kadara ta Alhaji da take a hannun Ahmad se an fito da ita, mutum ta samu ta biya yake mata binciken sirri duk inda su Al?ali suka saka ?afa suka fita suna tattaro abunda Ahmad Win ya bari tamkar akan idonta akeyi, ba kuma zata yarda da rainin wayo ba domin lissafin da takeji ya shallake ace wannan Wan tatsi-tsin Ahmad Win ne ya mallake su, tabbas a Wan lokacin daya shiga jikin Alhajin ya samu dama daya ja abubuwa sosai shine za'a raina musu wayau to zata ji zata gani.

Kamar kububuwa haka ta shiga falonta, Alhaji Zakariyya na zaune akan kujera Sarah ta zubo masa abinci yana ci Hajiyar na shiga tace
"Yawwa gara da kazo, ke kuma dan abu ya kazan ki fita ki bamu guri munafuka me ba?in jini, duk yammatan gidan nan aunyi aure harda na bayanki gasu nan zasu tashi amma ke shegiya kamar mujiya duk wanda yazo seya gudu fita ki bani guri kafin na make ki". Ita dai Sarah ta fice tana jin babu daWi, duk me yayi zafi irin wannan aibatawa da Hajiyar take mata? A iya saninta dai babu abinda tayiwa Hajiyar tun akan ruwan kanwar data zubar mata shikenan ta tsaneta a kullum bata da aiki se zaginta da kwashe mata albarka, maganar aure kuma ai lokaci ne, data kawo wanda take so har an saka rana Hajiyar ta shiga ta fita seda ta lalata saboda bekai wanda Maimuna zata aura arzi?i ba, ita kuma tayi al?awarin sedai ta mutu batayi aure na amma ba zata taSa yarda ta biyewa Hajiyar tayi irin auren Hajiya ?arama ba dan duk bala'in son zuciya irin ma Hajiyar da bala'i ya isheta da kanta tace a sako mata yarta shi kuka mijin yace besan zance ba yanzu ma ya fara zama da ita.

Saran na fita Hajiya ta zauna tana kallon Alhaji Zakariyya tace
"Ya kamata mu koma garin nan, akwai matsala sosai".

Cikin rashin fahimta ya kalleta yace
"Wani gari kuma Hajiya?"
"Gurin wancan macucin malamin daka kaini mana aka mun fashin miliyoyin kuWaWe na babu biyan bu?ata, dole mu koma kodai ya mun aikin da zai ci ko kuma ya biyani kuWi na dan ba asararriya bace ni" t faWa kamar zata rufeshi da duka. Fuska ya yamutsa yana kallon sama kamar me tunani kafin yaja abincinsa yaci gaba da ci, Hajiya ta sake fusata tayi kansa kamar zata dakeshi tana cewa

"Wato ga mahaukaciya ina maka magana ka shareni ko?"

"Wai ke da waye haka Hajiya ake jin muryarki tun daga waje?" Yakubu ?arami ya faWa bayan daya shiga falon, ta juya tace
"Nida wannan mutumin mana, tsabagen ya mai dani wata butacen se kace wadda nake haushi na masa magana yaja abinci yana ciba tareda ya bani amsa ba".

Yakubu ya zauna kusada Alhaji Zakariyyan ya Waga kai ya masa kallo Waya kafin yaci gaba da cin abincinsa,Hajiya ta sake harzu?a tace
"Ka gani ko? Ji fa yanda ya kalleka kamar yaga kashi, Zakariyya zanci ubanka fa. Naga alamar warkewar taka da sabon salon iskanci tazo maka to zan rafkeka in saita maka ?wa?walwar dan naga alamar bata zauna dakyau ba har yanzu".

"To dai gara idan magana ce mai muhimmanci ki nemi wani kiyita dashi dan wannan da kike gani ya warke ne be warke ba" Yakubu ya faWa mata, rage kaifin muryarta tayi tace
"Ban gane ba? Me kake nufi? Kamar ya ya warke be warke ba?"

"To saitinsa ne yake gocewa kuma yanzu, ai dama likita yace yana bu?atar lokacie tsayi ya samu cikakken hutu har ?wa?walwarsa ta dawo aiki tamkar da, a maimakon ki barshi ya huta yana dawowa hayyacinsa kika cigaba da lafta masa hayaniya da damuwar da kuka Worawa kanku. Nima jiya Zayyad Winsa yake gayamun sun maida shi Asibiti saboda irin abin nan da yakeyi kuma an ce musu yanzu kuma ?wa?walwarsa ce takeyin farfaWiya na Wan lokaci, ai ki godewa Allah ma da ba faWuwa yakeyi ba abin ya tsaya a iya gushewar tunani"

"Shikenan na shiga uku na lalace ni Binta, daga wannan se wannan da wanne zanji?" Ta faWa tana zama a ?asa kafin ta rushe da kuka kamar wadda akayiwa mutuwa.



*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

Barkanmu da sallah, Allahya maimaita mana

*BOOK 3*
*PAGE 25*

A ranar da Ahmad ya cika kwana Arba'in da rasuwa sabon taro akayi a gidan, taron kuma ya sake motso musu da rashin da sukayi, aka yi koke koke da addu'oi kafin zuwa dare kowa ya watse ya koma inda ya fito. Babu wanda zece yaga idon Hajiya ranar, kamar ma bata gidan dan tun randa sukayi yar hatsaniya da Alhaji Audun bata zama kullum idan ta fita da safe se yamma lis take komawa gidan ta kuma dena kula kowa sabgar gabanta kawai takeyi.

Jafar ne ya mayar dasu Fatima gida bayan isha'i, ita bata so zuwa gidan Alhaji Audun ba saboda yan uwanta da zasu zazzo mata itama amma babu yanda ta iya Ummansu tace washe gari duk wanda yayi niyyar zuwa se suje can gidan nata. A hanya suna tafiya ta jingina kanta jikin kujera tana sauraron surutun da Amal takeyi Jafar yana biye mata. A wani gurin siyar da kayan ?walama ya tsaya, suka fita tareda yaran suka barta ita kaWai dan sun baro Baba Bilki acan gidan suna aiki se jimawa za'a maido da ita.

Bata san tsayin lokacin da suka Wauka a ciki ba saboda nisan da tayi cikin tunani, wata irin kewar Ahmad ke cin zuciyarta. Bata taSa tsammanin tana son sa ko zata so shi kwatankwacin abinda takeji a zuciyarta bayan data rasashi ba. Hannaue biyu ta saka ta rufe fuskarta ta fashe da kuka me tsuka zuciya, Jafar dake tsaye a wundo dake saitinta ya ?ara ?arfin bugun da yakeyi se sannan ta farga ta shiga goge hawayen da gefen hijabinta kafin ta sauke gilashin ba tareda ta kalle shi ba.

"Wane flavour kike so na Ice cream?" Ya tambayeta muryarsa a dakushe. Kai ta girgiza masa alamar babu, be sake magana ba ya ba ya koma cikin shagon babu jimawa suka fito da ledoji da yawa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login