Showing 33001 words to 36000 words out of 467220 words

Chapter 12 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12243

ya kuwa miqe a zabure ze kurma ihu Audu ya zare masa ido dole ya nutsu ya hau sosa inda ya haureshin yana tura baki girman Banza yake dashi amma ya ringa abu kamar qaramin Yaro. A gaba Audu ya tasashi seda ya tara masa ruwan wanka ya kuma zuba masa wani a Buta yaja masa kunne akan karya kuskura ya kunna musu famfo ya lalace kafin ya koma falon ya harde kamar gidansa ya shiga cikin Abinci yana ayyana abubuwa dayawa a ransa. Yana da manyan burika da yake fatan Allah ya cika masa.

Ze ginawa Bara'atu irin wannan Aljannar duniyar, ya hasko kansa yana tuqa mota irin wadda aka dauko su a ciki ha ma'aikata ko ta ina idan ya wuce su ringa zubewa suna gaishe shi dan shidin mutum ne me Izza yana so a girmama shi matuqa. Seda yayi damkafin ya tattare sauran gefe ya rufe, can dakin ya leqa ya hango Baballiya kan gado yayi rashe rashe yana bacci ya girgiza kai kawai yana murmushi, falon ya koma ya kishingide kan kujera bacci ya sace shi besan tsayin lokacin daya dauka ba sunansa da ake kira ya farkar dashi ya hau murza ido.

"Sannunku, na tayar dakai ko?" Tunde ya fada fuskarsa da Fara'a. Audu ya zauna sosai yana cewa
"Aa babu komai ina zaune ma bansan bacci ya dauke ni ba"
"Ai kun sha gajiyar hanya, daman Alhaji ne ya dawo sannan kuma anyi Magriba shiyasa ma yace a kirawo ku masallaci" Tunden ya sake fada. Audu ya kalli qaton Agogon dake jikin bango kafin ya miqe da hanzari ya wuce dakin Tunde kuma ya fita. Seda ya dalawa Baballiya dukan gaske dan ya gaji da kiran sunansa yana jijjiga qafarsa kafin ya miqe yana soshe soshe. Audu ya wuce yayo Alwala, a bakin gadon ya ganshi ya sake kifewa aiko ya kuma kai masa mari ya farka da gudu ya fada bandaki. A rayuwarsa zece be taba bacci me dadin na yau ba. Yana ganin babu wata Katifa data kai tasu ta gidan Yaya Audu dadi da laushi seda ya hau wannan yaji ashe shi akan sumunti yake kwana.

Yanda Alhaji ya ringa haba haba da Audu har seda abin ya bashi kunya, mamakin daya sake kamashi ganin tamkar duk mutanen gidan sun san labarinsa,
"Aboki nane na Kano da na gaya muku" abinda Alhajin yake fada kenan kowa se ya fara
"Ikon Allah shine sannu da zuwa ya hanya" a haka sukayo sallah suka dawo cikin gidan kai tsaye Alhaji dake riqe da hannun Audu ya wuce dashi Asalin ginin da suka wuce dazun.

Falo na Alfarma da ya qawatu da jere tamkar a qasar turawa. Alhajin ya zauna kan Kujera Audu yayu qasa ze zauna ya riqo shi yana cewa
"Haba zauna nan sama mana, kaima samu guri ka zauna" ya fada yana kallon Baballiya daya zubawa chandler ido kamar ze kamota. Qofar glass din dake cikin falon ta bude, wata farar Mace kalar Madara ta fito cikin kwalliya ta kece raini tamkar me tafiya biki qamshinta ya baza gurin ya hade da sanyin Ac dana freshner da aka saka. Fuskarta dauke da murmushi take takowa tamkar yanda shima Alhajin dake kallonta yake murmushin.

"Lale maraba da baqin Kano" ta fada tana zama gefen Mijinta. Audu ya zame ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarshi Hanya, seda ya mintsili Baballiya kafin ya shiga hayyacinsa ya gaisheta itama. Da daddaya yaran sa suka fara shigowa falon, Namiji daya fara shigowa wanda zasuyi sa'anni da Audu se mata guda biyar da suka biyo bayansa gaba dayansu farare ne tamkar Alhajin da Hajiyar gasu yan gayu abinda ya burgeshi dasu yanda suke da fara'a sunata haba haba dasu babu kyama ko nuna banbancin sun fisu matsayi.

A kan qaton Dining din gidan suka zauna duka sukaci Abinci dukda Audu yaqi da farko Amma Alhaji yace se sun zauna shima Dansa ne kuma baqonsa a dole ya dan tsakuri abincin dukda damab cikinsa a cike yake har sannan Baballiya kuwa be kwari kansa ba yaci iyakar geji, har addu'a Audu ya ringa masa a zuciyarsa ta cewar Allah rabashi da lalacewar ciki irin yanda ya zage yana narkar Abinci kamar kwancen Yunwa koda yake sabon dandano yaji a harshen sa. Seda suka gama cin abincin gaba daya suka koma cikin falon. Alhaji ya kalli iyalansa yana cewa

"Wannan shine bawan Allahn dana baku labari ya taimake ni a Kano, duk tsayin lokacin nan babu ranar da ba zanyi Addu'a Allah ya sake gama fuskokinmu ba se gashi ubangiji ya karbo Addu'ata"

"Aiko dai ranaku daddaya ne Dady bazeyi maganarka a gidan nan ba, babba da yaro dan gida da me aiki babu wanda be haddace Abokin Dady na Kano ba ni na dauka zanga wani tsoho irinsa ashe ma Dan Saurayi ne" Daya daga cikin yammatan ta fada wadda kuma da alama duk ta fisu kaudi da iyayi. Baze iya fadar ko ta nawa bace a jerin haihuwa saboda su biyar din kusan kansu daya, da gani irin haihuwar kwanika ce kuma da yake suna da garin jiki shiyasa suka tashi kai daya.

Namijin ya kalleta yace
"Kodai kin qyasa ne kike kiransa wani dan saurayi?"
"Kai Yaya" ta fada tana rufe fuska alamar kunya, Alhaji yayi dariya cike da nishadi ya nuna Namijin yana cewa
"Wannan shine babban Da na Jamal, likita ne ya kammala karatunsa shekara biyu data wuce a Jami'ar qasar Ingila harya fara aiki kuma ina kan kammala gina masa Asibiti nasa na kansa daze cigaba da kulawa dashi, wannan Sakina kenan ita take bi masa se Salima, Ummulkhairi, Mamana Binta se kuma Auta Munira" ya qarasa yana shafa kan Autar da ita ce bata kai girman sauran ba. Ya sake nuna Sakina,Salima, da Ummu yace

"Wadannan duk suna da Aure Sakina nada Yara biyu ragowar nada daddaya kaga jikokina hudu kenan, saboda zuwanka yasa duk suka zo Mamana da Auta kadai suka rage se Yayansu"

"Masha Allahu" Audu ya fada yana sake kallonsu gasu nan abin sha'awa. Sakina ce tace masa Mijinta yana zuwa Kano da akwai Yayansa acan yake zaune shi a unguwar goron dutse. Audu ya washe baki jin an an bato unguwarsu yace
"Wurin ina a Goron dutse? Ai anan nima gidana yake"

Da mamaki Alhaji ya kalle shi yace
"Oh daman a cikin Kano kake da zama?" Ya shafa kai yana cewa
"Eh a nan nake gwadago, da ina zuwa ina komawa gida amma yanzu bayan rasuwar Innarmu nayi qaura gaba daya da Iyalina muka koma cikin Kanon"

Take fara'ar dake kan Fuskar wadda aka ambata da Binta ta bace, yanda ta hade ran lokaci guda yasaka kowa ya fahimci sauyin nata banda Alhaji da ke jajantawa Audu rasuwar Dada yayi masa ta'aziyya ya dora da cewa
"Kace kana da Iyali? Ikon Allah"
"Kwarai kuwa Alhaji, idan watan Sallar tsofaffi ya kama shekarata biyar kenan da Aure ina kuma da Yara biyu Maza"
Alhaji da Hajiya suka hada baki gurin cewa
"Ikon Allah ashe harda zuri'a, kai amma abu yayi kyau masha Allahu Allah ya raya yayi musu Albarka, wannan dai qaninka ne ana gani base an tambaya ba" ya fada yana nuna Baballiya dake zuba gyangyadi, bayan ci ai se a kwanta kuma a huce gajiya.

A fusace Binta ta miqe, Mamanta dake ankare da ita ta kalleta tana cewa
"Ina kuma zakije ana hira?" Tayi kwalwal da ido kamar haqaye zasu zubo mata tace
"Kaina ne yake ciwo Mama kwanciya zanyi" bata ko jira me zata ce mata ba ta wuce har tana hadawa da sassarfa saboda yanda take qoqarin fashewa a gurin, wani irin tuquqin bacin rai takeji data rasa na menene. Ta rasa gane meye hadinta da wannan dan qauyen da daga jin yace yana da mata zuciyarta ta fara kumbura wannan shi ake kira da daukar Dala babu gammo kenan.


*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*FREE PAGE 10*

Qarfe tara na bugawa daya daga cikin ma'aikatan ya shigo cike da ladabi ya sanarwa da Alhaji Mijin Sakina da Mijin Ummu na waje Alhajin yace yayi musu iso. Irin alaqar da ya gani tsakanin Alhajin da surukan nasa ya burgeshi. Wato su Yan boko komai nasu da birgewa yake (nada kenan da suka hada Boko da Addini se rayuwar ta zama me burgewa da ban sha'awa ba Yan Bokon yanzu da suka dauki fitsara a matsayin wayewa ba). Ya tuna lokacin da Mahaifinsu na raye, ko a masallaci baya hada sahun sallah da Mijin Mairo da Amina wai surukuta daga gaisuwa babu wata magana da take qara shiga tsakaninsu babu wata shaquwa a tsakani su kuwa bayan gaisuwar gashi har an zarme hirar aiki suna fadawa Alhan abubuwan da suke ciki. Ya nuna musu Audu wanda sun gaisa tun shigowarsu yace

"Ga Abdullahi nan shine baqon da matanku suka zo wa sannu da zuwa" aka sake maimaita gaisuwa data fi tada, matan kuwa tuni kowacce ta shige cikin gidan se gata da mayafi da jaka se yaga kamar har hoda da gazal suka qara da turare dan suna shigowa falon ya sake rikicewa da sabon qamshi, sukayiwa Iyayensu sallama suka fice harda Salima wadda su Ummu zasu sauketa dan unguwarsu daya, a yanda Yaji Mijinta Soja ne baya gari.

Bayan fitarsu Mama ta miqe itama tana cewa Mijinta bari ta shiga ciki taga koda abinda za'a qara kawowa su Audun, ta kalli Baballiya dake zuba gyangyadi tace
"Kaje ka kwanta abinka dan idan ba'ayi wasa ba Yayanka da Alhaji yau kwanan hira zasuyi"

Alhaji yayi dariya yace
"Kamar kin sani, a kawo mana shayi dan muji dadin hirar" ta wuce tana dariya. Alhaji ya kalli Audu yace
"Gaba daya murnar ganinka tasa na manta na tambayeka dalilin zuwanka Kaduna, ko kuwa dai ziyara kawai ka shirya kawo mun?"

Audu ya sosa qeya yana murmushi yace
"Kusan haka Alhaji, Allah ya nufi zamu sake haduwa shiyasa ya kawo mun tafiyar babu shiri" ya nuna Baballiya yaci gaba da cewa
"Wannan yaron ne ya dage akan aikin soja yake so yayi, nayi tambaya acan aka gayamun da akwai Jami'a ta karatun Sojoji da aka bude a nan Kaduna shiyasa na shiryo na taho dashi dan muji ya tsare tsaren makarantar yake".

Alhaji ya gyada kai cikeda gamsuwa yace
"Aiko kazo akan gaba dan suna cikin dibar dalibai ne idan banyi kuskure ba a cikin satin nan nakejin kamar zasu rufe ma dan haka gobe idan Allah ya kaimu zan hadaku da Tunde ya kaiku can NDA din, Abokina General Hanna Balogun shine mataimakin shugaban makarantar nasan babu matsala da kunje zeyi muku duk abinda ya kamata".

Murna ta cika Audu, wato ubangiji ya soshi da rahma shiyasa ya bayyano masa da katin Alhaji Tijjani, ya ringa masa godiya Alhajin yace
"Haba Abdullahi, ai tsakaninmu babu godiya Allah ne ya hadamu kaga kuwa duk abinda nayi maka ai banfadi ba domin kai ka fara taimako na".

"Binta ta shigo da qaramar sallama hannunya dauke da qaramin Try da aka fora butar shayi ta qarfe irin ta buzaye da qananan kofuna suma na qarfen guda biyu akai, Alhaji dake bawa Audu taqaitaccen tarihinsa shidin mutumin Paki ne tanan Kaduna Mahaifinsa haifaffen nan ne mahaifiyarsa Baturiya ce tun zuwan turawa Mahaifinsa suna cikin na farko farko da suka karbi Karatun Boko har ya samu damar tafiya qasar Ingila acan kuma ya hadu da mahaifiyarsa Janet sukayi Aure su uku suka haifa shine na biyu akwai Yayarsa Ketrina se qaninsa Muhammad, su biyun sun bi Addinin Mahaifinsu banda Babbar Yayarsu dukda daga baya dabda Mahaifiyar tasu zata rasu ta karbi Musulunci shekaru biyar da suka wuce kenan ta mayar da sunanta Fatima amma ita Ketrina Allah be nufa ba suna dai yi mata fatan karbar shiriya kafin mutuwa ta risketa.

Binta ta Ajiye Try Alhaji ya kalleta yace
"Sannu Mamana, ban lura ba dazu ashe kin tashi ba'a qarasa hira dake ba"

Ta dan yatsina fuska cikin salon sangarta tace
"Dady kaina ne yake ciwo shine naje nasha magani"
"Sannu Allah ya sauwaqe" Alhajin ya fada cike da kulawa Audu dake kallonta irin kallon qurilla yana hango siffar Turawa a tattare da ita se yanzu ya gano dalilin da yasa Yayan Alhajin har shi kansa suke kamar wanke hannu ka taba, jikin da suke dashi kuma gurin mahaifiyarsu suka gada kenan tunda a cike take qosasshiyar mace bawai irin shirgegeiyar nan da tsoka da kitse yayiwa yawa ba.

Tsakin data buga a daidai saitinsa ya maidoshi hayyacinsa, ya sosa kai, Alhaji dake ankare dash yayi murmushi kawai Binta ta wuce tana qunquni. Kadan yasha shayin dalilin Alhaji ya matsa masa suna sha yana tambayarsa Kasuwa da irin harkokin da yake tabawa.
"Har yanzu kana siyar da Man kuwa?" Alhajin ya tambayeshi. Audu ya kurbe dan saurab shayin cikin kofinsa yace
"Aa wlh, tunda na bar Bechi na saki harkar dan dama dalilin farata saboda haihuwa data zowa matar yayana cikin dare muka rasa wanda ze kaimu Asibiti duk masu Ababen hawa sukace basu da Mai hakan yayi sanadi har aka rasa jaririyar wannan yasa na fara sana'ar daman kuma Baballiya ne yake zama a gurin to yanzu muna tare babu wanda zeci gaba da kulawa dashi shiyasa na bari"

"Yanzu se bige bige kenan kakeyi?" Alhaji ya sake tambayarsa, Audu ya danyi jim kafin yace masa
"Eh" dan se yaji kamar maganar bata dace ba a tunani da izza irin tasa yana ganin sana'arsa ta wuce a kirata da Bige bige, shida yake da Jarin kusan Dubu dari tasa ta kansa a wancan zamanin banda na Gadonsu da yake juyawa gaba daya idan an hade kudaden da ya zuba a Kasuwa sun kai dubu dari uku ai kuwa ya zarce ace yana bige bige.

Alhaji ya nisa yace
"Yanzu dai ku gama da abinda ya kawo ku tukunna zamu san abinda ya dace ayi, meye matakin karatunka tund???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a naji jar turanci ka iya sosai?"
"Iyakacina Sakandire Alhaji" Audu ya bashi amsa, gani kamar ya gaji da hirar Alhaji yace suje su kwanta sa qarasa da safe, seda akayi da gaske kafin Baballiya ya tashi dan kan kafet ya baje yake jan Rago son ransa. Da sukaje kwanciya ya ringa tuna Bara'atunsa da yara suna can gashi babu waya ballantana ya kira ya sanar musu sun sauka lafiya da halin da suke ciki. Ya rufe ido, Binta ta shiga yi masa gizo.

A yanzu da yake qara shekaru da wayewa tareda sanin kan duniya kwakwalwarsa cike take da burika da mafarke da yake son cinma. Tun Asali yana da qawazucin auran mace me garin jiki, bawai qatuwa ba Aa cikakkiyar macen da babu qashi a jikinta. A irin shekarun da akeyiwa Mata aure a sannan kuwa yasan cewar baze samu irin kalar da yake da burinba, daga baya ya gane cewa se bayan Matan sun haihu jikinsu yake budewa su koma irin yanda yake kwadayin, tunda Bara'atu ta haifi Babangida yake baza ido yaga ta fara qiba saboda Balaraba tun qibar ciki bata sace duka ba tana nan yar duma duma da ita ga Ikko data karbeta tasa ta qara wani kyau idan ka ganta ba zakace Matar Yakubu Bechi bace to hakan yayi ta fata daga gurin Bara'atuntasa sedaihar yau data yi haihuwa biyu tana nan tamkar yar matashiyar Budurwar daya aura qirjinta ne kadai zece abinda ya qara girma daga yanda ya aureta gani yake ma kamar qara qanqancewa takeyi idan suka fita se a ti ga dauka qannensa ne ita dasu Abdullahi wannan abin yana damunsa kuma iyakar dadi daze saka jiki budewa yana siyo mata.

Duk daren duniya se sunci Balangu ga fura da zasu dora da ita banda sauran cimaku masu rai da Lafiya amma sedai su suyi bindin bindin har Babangida idan ka gansu girmansu yafi shekarunsu amma banda ita kuma mahaifiyata nada qiba, Babanta kansa ba siriri bane ya rasa inda ta gado rashin Auki ita, ganin Binta ya tada masa da tsohon tsumi da kwadayinsa na Auran mace irinta. Sedai da yake wargima guri yake samu ita zuciyar batayi gigin hasaso masa ita a matsayin tasa ba, Aa yana lissafin samun wata me dama dama kamarta dukda yana matuqar qaunar Bara'atu baya kuma jin akwai wata mace da zata kamo qafarta a zuciyarsa sedai ya dibar mata wasu shekaru da muddin bata kai muradinsa ba ze qara Aure, badan baya sonta ba ko ya raina Halittarta Aa sedan kawar da qawazucinsa ya kuma kade hankalinsa daga kallon manyan matan da zuciyarsa take so.

Haka ya kwana yana mafarki harma ya qara Aure ya samo yar duma duma. Washe gari haka aka sake kiransu cikin gida sukayi karin kunallo tareda Iyalan Alhajin. Dankali kadai suka iyaci daga shi har Baballiyan se Burodi da ruwan shayi, tare suka fita da Alhaji seda Tunde ya sauke shi a gurin aiki kafin suka wuce NDA wanda Alhajin ya rigada ya sanar da Abokinsa zuwansu dan haka basu sha wahala. Anyiwa Baballiya duk wani sikirinin daya kamata sun karbi takaddunsa sun kuma gaya musu zasu sanar da ranar da za'a fara tirenin a gidajen Radio da kuma Talabijin dan haka su ringa saurara.

Da wuri suka koma gidan, A tsakar gidan suka tarar da Binta da Munira wadda da alama itama dawowarta kenan daga makaranta dan Uniform ne a Jikinta suka gaisa har yayi mamakin sakin fuskar Bintan yau sabanin jiya da tunda ta tashi da sunan ciwon kai taketa fushi har dazu da safe kafin su fita. Seda ya leqa ya gaida Mama tace za'a kai musu Abinci yanzun yayi godiya ya wuce masauki a ransa yana tunanin daya san da wuri zasu gama da sunyi sallama da Alhaji kawai sun wuce Kano, amma babu damuwa gobe zasuyi Asubanci da yardar Allah su tafi.

Da la'asar yana zaune gurin megadi suna hira Baballiya ana daki ana shan Ac tsabar tsiya hancinsa ya toshe saboda rashin sabo amma yaqi haqura wai idanya tafi babu tabbacin ya sake ganin ta. Binta ta qarasa gurinsu Audu tasha kwalliya da Atamfa dinkin tazarce, tana da tsayi da jiki ba qaramin kyau kayan ya mata ba ga kalar Atamfar da take da duhu ta sake haska farar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login