Showing 12001 words to 15000 words out of 467220 words

Chapter 5 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12381

ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace.

Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu. Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba. So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata. A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni. Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo a qurarren lokaci basu shiryi tafiyar ba.

Ranar Juma'a aka daura Auran, na Yakubu aka fara daurowa da safe a can Rigarsu Balaraba suka dungumo da Amarya da yan uwanta, se bayan sallar Juma'a aka daura na Audu da Bara'atu. Murna kam ba'a cewa komai a gurin Dada da tasha kwalliya cikin kayan da Audu ya dinka mata, haka qannensa Bilki da Aisha sun sha Anko Baballiya kuwa shaddarsa iri daya data angwaye wanda dama Audu ya dinka musu da niyyar suyi fitar bikin Yakubu se gashi abu yazo a daidai. Qarfe tara suna can Majalisa da Abokanai ana ta shaqiyanci sega Baballiya da gudu yake fada musu wai an Kawo Amaryar Yaya Audu. Kowa yayi mamaki dan ko jiya da yaje gurinta seda suka sakeyin maganar tace masa Innarta tace se daga baya zata tare tunda abin yazo babu shiri Babanta kuwa Magriba nayi ya tada ballin se an kaita, an ce masa babu daki yace ta rakuba a na Babarsa da ya san be shirya auran ba yayi haka yan uwa suka rakota ita kam ko a jikinta dan ko cikin Rumbub gidan aka ce ta zauna shiga zatayi tunda dai burinta ya cika ta Auri Audu.

A dakin sa aka sauketa da qawayenta da zasu kwana, daren ranar Audu tunanin yanda zeyi kawai yake, da yasan za'ayi haka da ya ququta ko babu dabe itama an tayar mata da daki ko ciki dayane, haka dai gari ya waye, da hantsi yan uwan Balaraba suka gama mata jere tsaf irin na yar gata harda Kumbo nan suka fara shirin tafiya bayan sun qara damqa Amarta a hannun yan uwan Yakubu. Daga bangaren Bara'atu dai babu wanda yazo se qawayenta da suka kwana.

A can gidansu ana ta taqaddama tsakanin Babansu da Innarta akan yace ko tabarma baze kai mata ba tunda bata bi abinda yake so ba, ita kuma ta rantse se yayi, da yasan haka ne seya bata lokaci ita da take son auran zatayiwa yarta komai amma yanzu banda kwanuka babu abinda ta tanada dan haka dole ya fito da kayan gado danbaze barwa yarta abin gori ba bayan ba rasa abinda zeyi mata yayi ba gashi tun rana bata daga ba labarin jeran da akeyiwa Balaraba ya fara bazuwa a gari dan itama Babanta Attajirine a rugarsu kuma itace Auta a mata dan haka sun mata bajinta.

Hayaniyarsu har dakin Ilu Abokin Audu da suka kwana a gurinsa maqota suke dasu Bara'atun kuma dakinsa jingibe yake da dakin Soron su Bara'atu inda Innar tata da Baba suka shiga wai suna sirri saboda yan biki dake ciki se gashi Audu yaji komai, sulalewa yayi ya tafi cikin garin Kumbotso saboda yafi masa kusa akan yace ze tafi Kano, yasan gurin lokaci lokaci yana zuwa dan har Aboki yake dashi kai tsaye gurinsa ya tafi bayan sun gaisa be bata lokaci ba ya zayyane masa abinda yake tafe dashi na batun kayan daki saboda garinsu Babu Kafinta meyin kayan katako, gadon qarfe kuma a gurinsa shi da yake zaune a birni yake ganin kayan gado da akeyi na Alfarma ya fitar masa yayi.

Nura ya kaishi gurin wani Kafinta da ake ji dashi a Kumbotso dan a Kano ya koyo aiki wasu kayan ma daga can yake dakkowa ya kawo. Ya numa masa wani Gado Lamba 1 da Kobud dinsa me biyu ta yan gayu dan harda mudubi a jikin murafenta ga kuma mudubi shima me durowa uku a jiki kayan sunyi kyau gasu Ruwan Hoda irin kalar da Bara'atu take so sedai kudin da aka saka musu a yanayin da yake ciki sun masa yawa ga Katifa da ze siya da pillo, aka tirza aka tisa dakyar dai kaya suka siyu, shima seda Nura yayi masa ciko daga baya zasu warware tunda suna haduwa A Kano, aka loda masa su a A kori kura da dundumemiyar katifa da pillow biyu harda Abin shimfida dana rufa ya kama hanyar gida.

Sanda ya dawo yamma tayi rana na gabda faduwa, a waje ya bar masu mota ya shiga ciki nan ya tarar da Dada da yan uwanta da basu wuce ba suna ta kiciniyar kwashe yan kayayyakinta ana shigar dasu dakinsa nasa kuma suna waje da alama dakinta za'a mayar dasu daman ba wani shirgi ne dashi ba Gadon qarfe ne da wata Katifa da yake ta saka ranar canzata tunda ba kullum yake kwana a kai ba se yayi ta mantawa se akwatinsa guda daya. Kunya ta kamashi yanda aka faka kayan a gefe, kenan Dada dakinta zata basu kuma wannan Gadon za'a sakawa Bara'atu

"Yawwa ga Audu" Matar Yayan Dada da basu yada zumunchi ba ta fada dan tun safe ake nemansa an rasa shi ga babu waya bare aji inda ya tafi. Dada ta yafa gyale ta yafice shi suka yi soro, Goggo Fadi, Maryo da sauran Maqwafta yan tsogumi da suka baza tabarma, sun gama kallon dakin Balaraba suka fito aka kafa gulmar ana jira aga me za'a sakawa Bara'atu ita kuma,
"Koda yake ina dakin ma?" Fadar Goggo Fadi, Maryo ta karkace baki tace
"Dukdai qaryar Birnin ta qare, ayita zuwa ana burga a bikin jama'a ga nashi ya tashi ko dakin da za'a ajiye Amarya babu idan da gaske da kudin ai daga tsaida rana yaci a dora ginin Bulon sumunti ma bana qasa ba" suka tafa da matar Hashimu dake kusa da ita.

Dada kuwa suna zuwa zaure tace
"Ina ka tafi Audu bayan kasan halin da ake ciki babu inda dan uwanka bw zaga a garin nan ba amma ba'a ganka ba Jama'a har ana cewa ka gudu". Dariya ta kwace masa yace
"Na gudu kuma Dada naje ina kamar wani mara gaskiya?"

"Oho dai duk ba wannan ba, Hasiya tazo ta gaya mun Baban Bara'atu yace bazeyi mata kayan daki ba, da ace mun san da tariyar nan da tuntuni mun fara shiri amma yanzun ma se ayi amfani da abinda Allah ya hore, na bar muku dakina tunda kaga yafi girma ni se na koma na Malam, Babana kuma ya shiga cikinsu Idrisa (Yaran Yaya Baba da suke zama a gidan) kafin muga abinda Allah zeyi, idan an kwana biyu filin can na gefe seka shigo mata dashi ayi bandaki da gurin girki irin na Yayanka kaga shikenan a sannu Allah ze hore duk kuyi muhalli irin wanda kuke buri, wancan gadon naka ma gaskiya Audu ba'a bawa Amarya ba ga Katifa duk Babana yaci qaniyarta idan da sarari ko katifa ce ka siyo da ledar daki a shimfida mata".

"mma Dada da baki fita daga dakinki ba wancan dinma ya isa ta lallaba kafin muga abinda Allah zeyi" Audu ya fada, Dada ta juya tana cewa
"Kaje dai muga ko katifar da Ledar zasu samu" ya tsayar da ita yana cewa
"Shaf na manta da Ledar wlh sedai ko Bilki taje yanzu inda za'a samu, leqa kiga ga kaya nan dai na samu dukda dai nasan basu kai yanda akeyi ba".

Dada ta leqa, baki ta saki ganin kaya tuni kuma yara da matan Unguwa da sukazo shiga gidan suka baibaye motar ana kallo dan ba'a taba ganin irinsu a garin ba.
"Audu, Kano kaje har ka dawo wannan kaya haka?" Dada ta fada cikin mamaki, Audu yayi murmushi yace
"A turo Bilkin ta samo Ledar tunda ita akw fara shimfidawa ko anjima zan miki bayani.

Dada ta koma ciki bakinta a washe yaqi rufuwa ta tura masa Bilki. Gidanta ta tafi ta dakko ledar data siya take shirin canza ta dakinta bata rigada ta shimfida ba dama ta bari se an gama hidimar Biki nana da nan aka hadawa Amarya daki ga gado na Alfarma kamar wani gidan zoo haka mata keta leqawa masu gyaran daki na korarsu dan sun hanasu yin aikinsu yanda ya kamata tuni kuma labari yakai wa Innar Bara'atu, ta fashe da kuka tana cewa

"Allah na gode maka daka nunawa masu gulma da munafurci qarshensu" tun safen suke qullawa da warewa da yan uwanta akan yanda za'ayi, ta hada dan abinda ya samu, Gadon katako taso tayiwa Bara'atu dan ance Amaryar Yakubu ma shi aka mata amma abinda suka hada baze isa ba kuma wanda za'a tasa ya tafi Kumbotso a yammar shine aiki har sun saddaqar a dauki na qarfen anje shima me siyarwar wai baya nan abin duniya duk ya mata yawa sega wannan labarin farin cikin dukda tasan wata sabuwar gulmar za'a samu ace Miji ne yayi mata ko babu komai sabon salo ne dan babu yarda Miji yaso haka a garin har yayi mata kayan daki.*Batoul Fashion and Boutique* online store ne na sai da kayan 'yan gayu dandasa-dandasa na gani na fada, na kece raini a taro, masu tashin kan Habeeby d'? Kuma masu sa kishiya kwalla=?? @&
Muna da Laces, Atampa, Voiles, Shoes, Bags, Gowns, Veils and Jewelry masu kyau a farashi me sauqi, Muna Bada sari Kuma Muna siyar da daidai, Muna hada lefe masu Aji=?%?
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCOYAR*
*WATA KISHIYAR*
RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*

*FREE PAGE 4*

Haka rayuwa taci gaba da garawa, iya wuya Audu ya dukufa gurin neman Halalinsa kuma ubangiji ya sanya masa Albarka a abun duk abinda ya taba nan da nan se ya karbeshi sedai kuma wani ikon Allah daya fara ganga ganga se sana'ar ta turgude sedai ya saketa ya kama wata wannan yasa aka koma yi masa laqabi da Audu sana'a Goma dan da yawa suna ganin kawai zafin nema ne ya saka komai seya taba. Wata shida shida yake kai ziyara gida idan kuma ya tashi tafiya haka ze hada tsaraba tuli ya kaiwa yan uwansa harda yan Dakin Goggo Fadi da tun abinda ya faru akan Gona aka koma zaman doya da manja idan ka cire Aminu shikadai ne suke mu'amalla dashi yayi Aure har matar ta haihu sun samu Abdullahi yaron idan ka ganshi se kace Audu ne ya haifeshi su Yaya Hashimu kuwa ana fama da baqin rai amma hakan be hana idan Audu yaje da kayayyaki ya basu babu kunya su karbe, a kwai zuwan da yayi Malam babban dan Yaya Baba yace ze bishi Birni Goggo Fadi tayi kicin kicin ta hana a cewarta baze tafi dashi ya koyo masa fitsara da rashin mutunchi irin nasa ba dukda Yaya Baban yaso hakan amma babu yanda ya iya Audu ya koma cike da baqin cikin Yakubu da duk zuwan da zeyi seya masa magiyar ya koma yaci gaba da karatunsa amma yaqi.

Shekaru uku suka shude a sannan Audu nada shekaru Ashirin a duniya ya zama cikakken saurayi ta kowanne fanni, neman Kudi kuwa se abinda ya qarun masa, tuni an aurar da Aisha Yakubu ma yakai kudin aure a can rigar su Dada ya samo budurwa Balaraba kyakykyawar bafilatana har an tsayar da rana watan Azumin tsofaffi wata uku kenan masu zuwa shirin Auran yasa Audu ya qara qaimi gurin neman kudi, a cikin gidansu suka yanki fili Yakubun ya gina daki ciki da rumfa saboda gurin yana da yalwar tsakar gida kowa dai yasan yanda akw gini a zamanin da, mutum daya na iya faro gida yaya su tasa duk suyita yankar fili suna tada dakuna a ciki suma.

Hada qarfi sukayi shida Audu sukayi ginin dan shima yana taba Dinki kuma da yake yazo da zamananci za'ace ba kamar yanda aka saba a karkarar ba se ya zamana yayi suna har daga maqwaftan qauyukansu ana kawo masa dinkin. Tsaf suka gina daki dukda ginin qasane amma anyi Sumunti da daben qasa wanda daga Kano Audu ya taho da simintin haka dakin Dada ma an daga mata shi anyi dabe da fulasta, dakinsu da suke ciki a da wanda yake Rabon yaran Goggo Fadi ta zugasu sun karbe wai Hashimu ne yake ajiyar Hatsi dan yanzu ya siyi gona tasa daban yana nomawa kuma a tasun ma haka zeyi bake bake idan an girbe yafi kowa kwasa wannan dalili yasa Audu ya gyara Asalin dakin Malam wanda suka mayar na ajiyar shigi shima yayi dabe da fulasta ya zama gurin saukar sa idan yazo, da ana aikin ma so yayi da ayi katanga a raba gidan tunda har Bandaki sukayi dan Asalin na gidan a barayin Goggo Fadi yake sunyi wani tun rashin lafiyar da Dada tayi bayan rasuwar Malam akayi mata bandaki daga kusan dakunan ta yanzun ma kuma anyi a gefen dakunan Yakubu wanda Audu yace za'a dan kewaye masa bangaren saboda sirri.

Ya koma Kano da niyar se bikin Yakubu ya rage sati biyu ze dawo kafin nan ya sake roro abinda za'ayi hidimar biki. Da akwai Malam Mudan dan Bechi ne amma yana yawan shiga Kano dan baya rufa wata biyu beje ba ta hannunsa Audu yakeyin aike ko su aika masa daga nan.
Wata sabuwa ce ta bullo daga bangaren Bara'atu yarinyar da Audu yake mutuwar so yake kuma burin aure, tun dama dai Babanta ya matsanta matuqa akan ta fidda miji, duk sa'anninta an musu aure har sun fara haihuwa kullum ta Allah se yayi wannan mitar amma Inna tayita danneshi saboda ita tana son Bara'atun da Audu to wannan karon yace ya gaji duk danginsu babu yarinyar data taba shekara goma sha Shida a gida se a kanta kuma bawai bata da masoya ba dan haka seji kawai Inna Hajara tayi ya karbi kudin auran Bara'atun da saka rana wata uku kusan lokaci daya ze kama dana Yakubu kenan.

Bara'atu tasha kuka hankalinta ya tashi batayi qasa a guiwa ba tayi tattaki ta samu Yakubu dukda yar kunya da suke a matsayinsa na yayan saurayinta haka ta ringa masa kuka akan yaje ya gayawa Audu karya bari a aura mata wani ba shiba, yana komawa gida kuwa ya sanarwa da Dada tace yayi shiri ya taho Birni dan daman tasan za'ayi haka, duk sanda Audun yaje seta masa zancen ya kamata yasan me suke ciki da Bara'atu se yace mata ba yanzu ba yana so abubuwa su qara daidaitar masa akwai shirye shiryen da yakeyi.

Dole Yakubu yayi tattaki ya tafi Kano wanda rabon shi da zuwa tun hutun makaranta wanda daga shi be sake dawowa ba shekaru hudu kenan. Yakubu Kano be zarce ko ina ba se Tsohuwar makarantar Allonsu wato makarantar Gwani Musa dan yasan Audu bashi da wani masauki se can, sedai yayi rashin sa'a Malam ya sanar masa tuni Audu ya bar nan, ya kan dai kawo musu ziyara lokaci lokaci dan ba'afi sati bama yazo kuma Almajirai suna ganinsa a Kasuwar bakin Asibiti idan sunje yawo yace musu yanzu a Goron dutse yake zaune bedai san takamaiman wani guri a can din ba. Yana zaune a bakin Masallaci yana jira ko Allah ze kawo daya daga cikin yaran da sukace sun san inda yake zama a Kasuwa su rakashi sega Hayatu, yaron gidan da Audu ya yiwa aiki wanda Babansu ya kaisu makarantar Boko a lokacin.

Cikin mamakin ganin juna suka gaisa yace suje gida a can yaci Abinci yanata kallon Hayatun daya zama kalar yan gayu da gani ya fara jiquwa a Boko.
"Tunda ka tafi makarantar kwana shikenab bamu sake haduwa ba shekaru kusan takwas kenan amma banji dadi da Audu yace mun ka bar Boko ba, kaga ni yanzu haka ina shekarar qarshe a Jami'ar ABU zaria ina karantar Engineering da ace ka cigaba kaima yanzun ko baka gama ba kana kan hanya" Hayatun ya fada. Yakubu yayi murmushi kawai amma bece komai ba, duk wanda ze so masa da yayi Boko a bayan kansa ne dan mafarkinsa ne ya zama Alqali tun besan me hakan yake nufi ba. Ganin bazeyi magana ba yasa Hayatu cewa ya tashi suje ya kaishi inda Audun yake dan shi suna haduwa sosai har inda ya kama hayar shago yake zaune a can Goron dutsen ya sani.

A kasuwa suka samu Audu yamma tayi anata hada hadar kasuwa dan a sannan ma ake cin kasuwar sosai, kayan yaji yake siyarwa a sannan da sauran kayan qamshi zuwan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login