Showing 171001 words to 174000 words out of 467220 words

Chapter 58 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12249

aureta bazan bari ba, bata isa ta shigo ta lalata abinda Allah haWa ba, babu matar da zata lalata zumunchin da yake tsakanina dakai kuma Mayyace Ta kama maka Soul, first thing tomorrow morning Bechi zan tafiz ai da muna Yara ance da akwai Sarkin Mayi acan, I'm going to report her to him duk ma inda ta kai Kurwanka seta dawo dashi I promise".

Fatima ko tayi tsaye da waya a kunne tana sauraron Jafar, ta ma kasa fahimtar kalamansa da inda suka dosa, ta fahimci ba muryar Ahmad bace abinda take tambayar kanta waye wannan???

Zagin Mahaifinta da yayi shi ya karya mata zuciya har bata san hawaye ya fara saukar mata ba seda Badar ta taSata akan su tafi taga tana kuka da waya a kunna wannan yasa da sauri ta zare wayar ta saka a speaker don a zatonta ko wani Bad news ake gaya mata daga gida nan ta tsinci faWan Jafar da Ahmad dan lokacin ya gama zazzaga mata tijara Ahmad ya kwace wayar.

"Atleast he stood for you, shi kuma ko wanene wannan da yake i?irarin indai yana raye ba zaki Auri Ahmad ba Bi'iznillahi da ransa yanaji yana gani zaki Aureshi sedai ba?in ciki ya sa ya haWiye zuciya ya mutu. Ke kuma banza kin tsaya kina kuka, me yasa baki cuccusawa uwarsa Ashar ba? Dallah muje ni kar kisa na huce haushi na akanki kin wani tsaya kina kuka wlh na Wauka mutuwa aka kira a gaya miki daga gida, daman idan baki nemo mana number sa munci Kutumar ubansa ba to naki zanci SoloSiyon banza kawai".
Badar ta ringa masifa iyakar ?arfin ta har suka isa ?aki ita kuma Fatima tana kuka. Yar Matsiyata, mayya daya kirata yafi komai yi mata ciwo a rai, shi be san ba son Yayan nasa takeyi ba bare har yaci mata mutunchi akansa? Koda ace tana son Ahmad wannan dalilin ya saka ko zata mutu seta rabu dashi wlh.

Wayarta ta Wauka take tayi blocking ta kumayi deleting number Ahmad, an gama chapter sa domin ba ayi wasu Ahali fa zasu wula?anta mata Baffanta ba kuma ko Ahmad ne Autan Maza sedai ta mutu batayi Aure ba.
MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 8*


Sosai Ahmad ya Wauki fushi da Jafar akan abinda yayiwa Fatima, dukda shi Jafar Win ya sauke kai ya bashi ha?uri inda suka sake fafatota da yace se ya kira Fatima ya bata ha?uri ai ita yayiwa laifi nan fa Jafar Win yace muddin ba Momy bace bazeyi ba, sedai idan sanadin haka yasa Ahmad yace shi ba jininsa bane amma wlh baze bata ha?uri ba, da niyyar sati uku yazo Nigeria dalili wannan Sarakar yasa kwana goma yayi a daddafe ya tafi kuma duk gida seda aka gane akwai matsala tsakanin Jay da Yah Ahmad Win nasa dan muddin yana gari duk inda zaka gansu tare suke amma wannan karon kowa sabgarsa yakeyi.

Momy ta tambayi kowannensu akan meya faru amma sukace mata babu komai, ta haWasu tayi musu Nasiha akan karsu bari shaiWan yayi tasiri a cikin zukatansu, su Win sun kasance abin misali cikin zuri'ar Audu Bechi karsu yarda seda girma ya fara zuwa kuma su kama wata hanya ta daban.
"Na san abu biyu shaiWan yake saurin samun gakaba akan mutum ta dalilinsu, Mace da KuWi, karku bari Waya daga ciki ya haWaku kuyi ?o?ari ku sasanta kanku" tace musu duk suka amsa mata da "In sha Allah" amma suna fita kowa ya kama gabansa.

Ahmad yanda ya kasa samun Fatima a waya shiya sake dugunzuma hankalinsa har yake ?ara tasirin fushin Jafar a zuciyarsa, Allah ya sani yana sonta, so me tsanani da yake jin tamkar idan be sameta ba ze iya rasa ransa. Daya kasa samun wayarta tilas ya shirya ya tafi Zaria abinda ya ?ara tunzura Jafar shi kuma tsanar Fatiman ta ninku a zuciyarsa tunda har ta zama silar ruguza Ala?ar sa da Ahmad yayi rantsuwa ba zata shiga zuri'arsu ba domin Allah kaWai yasan abinda zata haifar musu. Shirin komawa ya shigayi duk da kwanakin daya niyyata basu cika ba kawai gara ya tafi dan baze jure abinda Yah Ahmad yake masa akan Mace ba, Macen ma wadda bata kai matsayin ace Ahmad Win ya haukace haka akanta ba.

Har hasaso kamanninta yakeyi ?ila wata ba?ace mummuna da fuskarta kamar ta shafa Ba?in Man da Babanta yake ta'ammali dashi, kai Yarinyar nan ma dole asiri tayiwa Ahmad kuma tilas ya karyashi.

Hajiya kuwa ranta ?al tamkar zata taka rawa data fahimci yanda abu yayi zafi tsakanin Jafar da Ahmad. Dubunta Hansin ta bawa Turai taje mata gun Malam akan ayiwa musu Farra?u domin taga alamun Amadun yana neman yasa kwaSarta tayi ruwa kuma aiki yaci. Duk wani buri da tanadi da take dashi akan Jafar in har yana tareda Ahmad ba zata samu cikar burinta ba Jafar kuma shine makamin ?are danginta a yanzu. Tana da shiri da kuma tsarin ganin ya zama makwafin Alhaji. Da akwai matattarar sirrin Alhajin inda duk wani abu mai muhimmanci daya shafi rayuwarsa yake da wanda su suka sani harma da wanda basu sani ba takaddun Kadarorinsa na gida dana ?asashen waje duk a nan ya ajiyesu.

Wata Safe box ce a cikin Wardrobe Winsa ta kaya. Safe ce da akayita da wani irin matakan tsaro ta yanda duk tsiya da bala'i muddin ba wanda ya kulleta ba shi kaWai ze iya buWewa babu ta yanda za'ayi lalata tsaronta kuma ba zata fasu ba. Tasha ta saita Kemarar wayarta ta yanda zata Wauko mata ?alamisan da Alhajin yake buWe gurin dasu amma abu ya faskara kamar ma ba wani abu da yake dannawa se daga baya ta fahimci kwayar idonsa ce mabuWin gurin, kenan babu ta yanda za'ayi ta buWu indai ba shine da kansa ba.

Hankalinta yana ?ololuwar tashi idan tayi tunanin yanzu ace ya faWi ya mutu ta yaya zasu buWe gurin su kwashe wasu abubuwan da bazasu so ace sun fito a rabon gado ba sedai ita da Yayanta su handame?

Da fari taso ta tattauna maganar da Zakariyya da Naziru taji ko suna da Mafita, sedai ta fasa hakan saboda ta sani a yanzu ita dasu shegen Sama ne uake dukan na ?asa, kowanne ?o?arin ya gina kansa yakeyi idan kuma ya samu dama ya tattare komai shi kaWai shoyasa ta fasa sakasu a cikin shirinta. Jafar kaWai ta aminta da sakashi gaba akan cimma wannan ?udurin nata, shi take so ya zama magajin Alhaji domin tayi ammanna duk cikin Yayansa babu wanda ya aminta dashi har zuwa yanzu ya sanar dashi ta yanda za'a buWe ma'ajiyar bayan ransa.

So takeyi ta sake cusa Jafar Win jikin Alhaji ta fili data baWini ta yanda ze Amince dashi ya dam?a wannan Amanar a hannunsa ya zama shine Magajinsa, ita kuma da wannan damar ta samu Jafar Win ya gama sanin komai game da Alhajin shikenan burinta ya cika domin se yanda tayi da Jafar Win da kuma dukiyar Alhaji sedai wannan muradi nata baze cika ba muddin Jafar yana tare da Ahmad, shi yasa bataji komai ba da Turai tace ta bada kuWi zata je mata inda suka kai sunan Abba T saurayin Hajiya ?arama domin dukda dukan daya sha a hannun Yakubu be ha?ura ba, ya dawo amma a can gidan Haj Turai sukeyin Hira ko kuma su fita yawo gari maganar da ake yanzu ma Bayan sallar Azumi yace Iyayensa zasu zo tambayar masa Auranta. Babu wanda ya san zancen a gidan kosu Naziru Hajiyar bata gayawa ba tace sedai aji komai katsahan tunda har a yayan cikinta akwai masuyiwa Hafsatun ba?in ciki.

Ahmad na Zaria Jafar ya tafi dan tarewa yayi a Hotel kullum haka ze je Samaru ya wuni a Faculty of Art yana bibiyar ta inda ze gamu da Fatima amma ta?i yarda su haWu se ranar daya kwana uku ne ya samu nasarar ganinta sammako ya buga tun bakwai yaje ya zauna a bakin Class Win da zasuyi Lecture, a gurin wani Guy ya samu Time table Winsu bayan daya nuna masa hotonta ya tabbatar masa ya santa bata zuwa Class kwana biyu amma na goben ya tabbatar zata zo indai tana Makaranta dan Malamin baya wasa Individual Attendance yake Wauka and is automatic carry over idan mutum yayi missing wannan tasa ya tafi da wuri, 8 zasu shiga amma 7 bata gama rufawa bama ya kafa ya tsare a bakin ?ofa.

Yana tsaye a gurin suka zo ita da Badar da wasu yammata biyu, bata ganshi ba se Badar ce ta nuna mata shi tana cewa
"Kinga Ahmad"
"Ahmad?" Ta maimaita da mamaki tana kallon inda take nuna mata se gashi kuwa a tsaye ya zuba hannaye a Aljihu yana binta da kallo suna hada ido maganganun Jafar suka fara dawo mata tamkar a lokacin yake faWarsu wannan tasa tayi saurin Wauke kanta ta doshi class Win da sauri dan ba zata bari ya tareta ba amma kafin ta shiga yasha gabanta.

"Ka matsamun na wuce" ta faWa ba tareda ta bari sun haWa ido ba saboda yanayinsa da yake neman karya mata lago ya samu galaba akanta.
"Zan jiraki a waje ku gama" ya faWa a sanyaye yanajin tamakar ya rungumeta saboda So, taja baya saboda kusancinsu yayi yawa tana cewa

"Karka jirani dan ko ka zauna bazan saurareka ba"
"Shikenan, zan shigo Ajin na ro?i Lecturer ya bani dama a gaban kowa nayi magana dake hakan ya miki?"

Yanda yayi maganar ta fahimci ze aikata abinda yake nufi dan haka tace
"Karka shigo, ka jirani a waje"
"Good girl" ya faWa yana mata murmushin ?arfin Hali, kansa ciwo yake masa be taSa zaton haka so yake dagaske ba. Fatima ta wuce, Badar ta matso fuskarta Wauke da fara'a, she is lively ko yaushe fuskarta a washe take kamar ta Ahmad Win muddin ba an tsokalota bane.

"Hi" ta faWa tana waving masa,
"Hello Badar" ya mayar mata yana Waga mata hannun shima bakinta har kunne jin ya ambaci sunanta, ashe dai Fatima ta bashi labarinta.
"Karka damu, just give me your number, kaje ka samu comfortable guri ka zauna i will bring her to you damun gama Class" ta faWa tana bashi wayanta. Ya karSa ya shigar da Digits Winsa kafin ya mayar mata yace
"Nagode Badar, i will be in Shinkafi Elite, zan jiraku a can"

"Ayt, se munzo" ta sake Waga mishi hannu kafin ta shiga Ajin ta zauna kusada Fatima dake le?ensu ta window, duk a kan Idonta Badar ta bashi wayarta tana ganin yanda suke ta wani Murmushi duk seta tsargu. Badar batace mata komai ba har akayi Lecture aka gama suka fito, tana lura da yanda take satar kallon gurin da alama Ahmad yake nema amma bata ganshi ba A zuci Badar tace
"Munafuka kawai tana so tana kaiwa Kasuwa".

Suna tafe duk Fatima bata da laka, tunani takeyi ko ya tafi? ?ila ya ha?ura da itan kawai tunda har ya karSi number Badar.

A hanya Badar tace su biya ta Shinkafi su siya Chips tace ta ?oshi amma Badar ta nace se sunje in yaso ta siya ita kaWai.
"Kije can ki zauna kinga akwai layi kafin azo kanmu" ta nuna mata Table Win dake kusa dasu, Fatima tayi tsaki, can ?arshe ta wuce seda ta zauna kafin ta lura da Ahmad ne a gurin. Zabura tayi zata mi?e ya dafe hannunta, karo na farko da hakan ta faru tsakaninsa da wata Mace da ba Muharramarsa ba. Cikin sauri ya saki hannun nata se kuma ya mi?e tsaye ganin tana shirin barin waje yace

"Kwana na uku ina yawo cikin makarantar nan, na kasa samunki a waya, idan na canza layi na kira ki da kinji muryata seki kashe daga ?arshe kindena Amsa duk wata number dana kira da ita why Fatima? So kikeyi zuciyata ta buga na mutu kowa ya huta? Dame kike so naji? Da Matsalarki koda rigimar Jafar? Wlh ko ki tsaya muyi magana yanzu ko kuma ba biki har cikin Hostel, Bet me I'm fuc***g serious zaki sha mamakina yau".

Kuka Fatima ta fasashe masa da shi kawai ta zauna tareda kwantar da kanta akan Table ta shiga rera shi. Ahmad ya zauna ya harWe hannaye yana kallonta ba tareda ya hanata ba. Badar kuwa saya karSi order ta tafiya tayi Hostel.
Seda Fatima tayi kuka me isarta Ahmad na zaune ya na kallonta kafin ta tsagaita ta fara zazzage masa abinda yake ranta wanda Jafar Bechi yaci ace ta gayawa sanda yake zaginta amma ta huce akan Ahmad Win.

"Kiyi ha?uri dan Allah kuma ki manta duk wani abu daya faWa shima cikin fushine and he regretted everything he said, zan haWaku a waya ze baki ha?uri komai ya wuce" Ahmad ya faWa kamar zeyi mata kuka.

"Ni na ha?ura sannan kaima na ha?ura dakai, Brother ka ya gaya mun what i need to know about your Family, na sani daman ba zasu soni ba saboda ni Talaka ce amma ka sani ka kuma gaya masa tabbas mahaifina Talaka ne amma ba Matsiyaci bane domin yana da wadatar zuciya kuma sana'ar sa da yake zagi Halal yake nema Haram ba sannan ba yawon Maula yake gurin wasu mutane ba balle ya samu damar zaginsa ya ?as?antar dashi. Nasan mutunchin Iyayena dan gaka bazan bari wani ya taka darajarsu ba, ko beyi rantsuwar bazan Aureka ba na rigada na yankewa kaina wannan shawarar sannan ka gaya masa Maita daya dangantamu da ita, nasan ko nayi shari'a dashi a duniya ba za'a bi mun ha??ina ba saboda shi Wan masu kuWi ne amma zamuyi shari'a a Katun da ba'a bada cin hanci" ta faWa sababbin hawaye na sauko mata.

Duk yanda Ahmad ya zata abin ze zo masa da sau?i ya zarce haka, taurin kaine da ita kamar mutanen farko ta ri?e maganganun Jafar Bechi se maimaitasu takeyi.

"Amma Fatima ko Allah daya halicce mu baya kama wani mutum akan laifin da wani daban ya aikata muddin ba sunyi tarayya a cikin aikata laifin ba. In har akan Abinda Jafar yayi miki ne na baki ha?uri kuma in har zakiyi mun Adalci kin san bani na sakashi ba, ki faWi kanki tsaye cewar bakya sona, ba kya ?aunata kawai dan rajin kanki ba saboda abinda Jafar yayi miki ba. Na dade da fahimtar haka, amma na kasa cire rai dake bansan me yasa zuciyata ta kasa ha?ura dake ba, ina Addu'a akan Allah ya zaSa mun mafi Alkhairi a kullum kuma ji nakeyi tamkar ana ?aramin sonki, duk yanda nakeji akanki wlh zan jure kuma zan ro?i Allah ya yayemun muddin kika furta da bakinki bakya Sona ba kuma zaki aureni ba nayi miki Al?awarin daga nan gurin ba zaki sake gani na ba zan kuma fita daga rayuwarki koda Sonki ze zama Ajalina zan ha?ura dake Fatima".

*************

A YEAR LATER

Gudu gudu sauri sauri take tafiya saboda ta kusa makaraz fata takeyi Allah dai ya rufa mun asiri ta samu ta shiga Ajin nan kafin Dr Abolude ya rufe, ba rasa ajinsa ba wannan banzan halin nasa na marking note se kace a primary ko secondary school shine abinda yake bawa kowa haushi dashi balle ita yau da rubutun ya zamar mata biyu, ga nata gana Badar dole taje da wuri ta samu sit a gaba, layin wanka ne ya bata mata lokaci saboda Monday ce kusan kowa na block dinsu nada Ajin safe.

Qiris ya rage ta hantsila daidai Basket ball court saboda wani mutum da tun fitowarta daga Amina Hall ya zura mata ido kamar me shirin ganin yayan hanjinta, taja tsaki ta dauki Jakarta data zame ta fadi a ranta tana mitar wannan kallo haka taci gaba da zabga sauri a karo na biyu ta sake yin gaba tana shirin gangarawa daidai Senate building saboda mutumin dazu data gani tsaye gabanta kamar Aljani. Batasan sanda ya biyota ba harya tare mata hanya, zuciya ta harziqomata amma bata tankashi ba ta sake rabeshi ta wuce a kato na biyu se ji tayi daga bayanta ance

"Sihh, jimana yammata". Raita ya ninka da baci, a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce irin wannan kiran wulaqancin da maza sukeyiwa yammata ba, se kace wata mota ko Mashin a ringa maka wani Sihh wasu tantiranma har fito suke kamar masu kiran kare. Taci gaba da tafiyarta kamar zata tashi sama ga haushin mutumin ga na bata mata lokaci da yake tayi dan ta tabbata yanzun kam ta makara sedai ta maqale a bakin window idan batayi sa'a ba. Karo na uku ya sako fadowa gabanta, wannan ba?ar Wabi'a ta mutumin da abin takaici take baya ko tunanin zata iya faWuwa tunda batasan da shi ba ya ringa diro mata kawai kamar wani jifa.

"Dan Allah ki saya" ya faWa yana kallonta se a sannan ita ma ta kalleshi fuskarta babu alamar rahama amma can ?asan ranta seda ?irjinta ya buga saboda se yanzu ta kalleshi da kyau. Wani zabgegen mutum me ?irar ?arfi jiki a murWe dan a yanzu da yake tsaye gabanta shigarsa ta nuna motsa jiki yakeyi, rigace Armless jikinsa da wandonta wanda da kaWan ya zarce guiwa kayan suka qara bayyana surar ?arfinsa, bata tantance fuskarsa ba dan bata kalleta sau biyu ba, yanda ya kankane mata hanya yasa ta raina kanta da tsahon da take ta?ama dashi dan wata yar firit ta ganta a gabansa.

"Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faWa da sautinsa daya sa ta gaza tantance wane yare ne shi, sake daga kanta tayi ta sake kallon fuskarsa, a zubi za'a kirashi Bahaushe ko kuma Hausa Fulani amma a zubin jiki dai yafi kama da Irin zabga zabgan Igbiran nan ko Inyamurai haka fatar jikinsa da take da haske dukda ba fari bane amma a goge take tar yanda kasan ya hada jini da fararan fata.

Tsaki ta zabga data kalli sumar kansa da tasha gyara irin na Yan Ball din nan itako yana daga irin abinda ta tsana dan duk girman mutum idan ta ganshi da irin Askunan nan kallon wanda be san kansa take masa ba. Tuna abinda yake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login