Showing 165001 words to 168000 words out of 467220 words

Chapter 56 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12193

ne shi yasa tayi shiru hakan kuma yake jurewa baya fushi yana cigaba da lallaSata.

A cikin haka suka koma makaranta wanda taji daWin hakan sosai saboda ko babu komai zata huta da zuwan da yakeyi sannan zata samu uzurin da zata ringa gujewa wayarsa yanzu dan a gida Idan ya kira Umma data fahimci Ahmad Win be samu karSuwa gurin Fatiman ba ita take takura mata tayi ta mata faWa idan ta bar wayar tana ?ara ko yazo ta tsaya nu?u nu?u ta?i fita. Ta kance mata wula?anci babu kyau, bata san abinda Allah ya tsara ba kuma ita bataga makusarsa ba da zatace beyi mata ba dan a zuwansa na biyu ya shiga har ciki ya gaidata itama data ganshi ta fahimci nutsuwa da Kamalar da Malam yace yana da ita. Yaro ne amma Allah ya hore masa nutsuwa da dattako daya zarce shekarunsa kuma duk wasu iyaye na kwarai tabbas zasuyiwa Yarsu sha'awar samun Miji me kulawa tamkar Ahmad Win.

Bayan sun koma makaranta haka zeyita kiranta ba zata Waga ba, tun su Badar basu sanda Ahmad ba dan bata gaya musu ba har suka gane dalili wata raba ya kirata tana sallah Badar ta amsa wayar suka gaisa ya kama sunanta shikenan hira ta Sarke, Fatima bata so ba domin muddin Ahmad yayiwa Badar tasan ta shiga uku, takura kam ko ruwa me daWi ba zata barta tasha a dalilin Ahmad ba shiyasa take ta Soyewa gashi yanzu Badar Win ta ganoshi.

"Dukda banga guy Win nan ba tun daga voice Winsa nasan ya haWu, wato Afee kin iya catching Big Boys matsalar duk yan iska ne in disguise Allah yasa dai wannan na Allah ne dan wlh daga magana a waya harya burgeni yana da nutsuwa ga kirki, waye shi? A ina kuka haWu" Badar ta tambayeta bayan ta gama waya da Ahmad ta bashi uzurin abinci zataci shi kuma ya shaida mata ze fita Jafar ne yazo ze Wauko shi daga Airport.

"Ya samu hutu ne shine yazo Gaisuwar Rasuwar Brigadier General Baballiya Bechi, ?anin Alhajinmu sa sukayi Hatsarin jirgi last two weeks ai kinji labari ko?" Abinda ya gaya mata da duk ya saka taji kunya kenan. Sanda akayi rasuwar ta gani a SM, kuma anyita surutun a gari kan set up ne akayi musu ba wai Accident bane ba ance akwai wani sirri da suke shirin bankaWawa na wata bada?ala data faru shine kafin nan masu laifin suka kawar dasu, tunda taga Bechin a ranta ta kawo yana da ala?a da Ahmad kuma ta gani ya saka a Status harya tura mata cewar an masa rasuwa kunyar data ji yanzu irin gaisuwar da tayi masa ta
"Allah ya ji?an rai" kawai tace, babu wani sympathy babu nuna concern na cewar Kawunsa ne na kusa ya rasu tana ganin shiyasa yanzu yake gaya mata Jafar yazo dan tasan Mutuwar me muhimmanci ce a gurinsu tunda har na wata ?asar ya taho ita kuwa ba wanda ta gayawa a gidansu ma balle ko a waya su masa gaisuwa.

Hoton Ahmad kawai ta nemo ta mi?awa Badar data addabeta da waya, cikin Mamaki take kallonsa tace
"Ahmad Bechi? Wlh Afee kinyi Miji kinsan kirkin mutumin nan kuwa?"

"A ina kika sanshi?" Ta tambaya tana tsare Badar Win da ido wani abu da bata taSa tsammatar zata jishi akan Ahmad Winba ya taso mata wato kishi.

"A IG mana, ai ina following Winsa" b
Badar ta bata amsa. Seta tsume fuska tace

"Shine har kika san kirkinsa daga ganinsa a IG kuma"

"Ai mutumin kirki baya Suya, kuma idan da kinsan yanda mutane suke yabonsa da bakiyi mamakin dan nace yana da kirki ba, kin san yanda yake taimako kuwa? Ke dai Allah yana sonki Afee, kinga ya canza miki da abinda yafi duk shegun da kika rasa Alkhairi wlh ki gode masa"

"Allah ya saka mu a danshinku Afee, ke kam Allah ya taimakeki da jinin manyan mutane, Bechi Family fa?" Ilham roommate Winsu ta faWa nan suka shiga hirar caaa caaa kowa na tofa Albarkacin bakinsa.

Ahmad
?arfe biyu ya fita Wakko Jay wanda suka samu delay na jirgi daga Abuja zuwa Kano, tun daren jiya ya sauka daga London, ya biyo jirgin Abj to Kn na sha biyu da rabi na rana basu taso ba se biyu da wasu mintina uku saura suka sauka a Kanon. Beyi mamaki daya kira Yah Ahmad yace masa already yana cikin Airport Win ba. Be taSa barin sa yayi jira muddin yana gari shi ze zo ya Waukeshi kafin Jirginsu yayi Landing Ahmad ya isa Airport wani sa'ilin har Abujan yake zuwa ya taro shi su taho Kanon Tare.

Cikin tsananin murna da Wokin ganin juna suka rungume juna kowanne yana jin soyayyar Wan uwansa na sake ratsa Jini da jijiyarsa.
"Kullum ?ara girma kakeyi da fresh, look at you, idan muka jera za'ace kai Yayana ne na uku ma" Ahmad ya faWa cikin zolaya yana kallon Jay daya Sata fuska irin na sangartattun yara wai yace masa tsoho. Kuma da gaskiyar Ahmad Win, A tsaye Jay yake gansansan kamar ya haWa jini da samudawa koda yake jinin Binta da Audu fa kowanne ba baya bane a garin jiki.

Suna tafe suna hira gwanin sha'awa har suka isa gida. Hajiya na tsaka da shiri domin wannan karon ta rantse gayya zasuyi suje taro Jay Win se Kano gaba Waya ta san da ya dawo. Idan zezo gida babu wanda yake sani, ko a jirgi badda kama yakeyi saboda ya tsani irin taro da hargowar da mutane sukeyi duk sanda suka ganshi a cika guri ayita ihu ana Waukar hotuna dashi ayi blocking masu uzurirrika shiyasa kusan shekara biyar kenan ya canza salon zuwansa Nigeria, hatta da manager sa na nan wrong schedule yake bashi dan shi yake sanarwar Jay Win na tafe ya haWa masa mutane shiyasa ya zaSi boye zuwansa, Ahmad kaWai yake gayawa se idan ya dawo a kwashi tsiya da tsiyataku da Hajjaju dan idan zezo Yau ce mata yakeyi se Jibi sedai ta ganshi kamar dirar kirsimeti.

Zuwansa na ?arshe waccen shekarar na buWe Shagon Ahmad daman bata san da zancen ba ganinsa kawai tayi, ta zabga tijara ta kuma ce Alhaji yayi mata tsakani da Ahmad ya fita a sabgar ?anta, ta yaya za'ayi idan ba mugunta ba ya saka ya baro gurin sana'arsa dan yayi Asarar miliyoyin da ake biyansa? Ta kuma ce zancen Ahmad shi kaWai ya Wauko shi daga iyafot ya kau, duk in ze sake zuwa zuga za'ayi dangi da Abokanan arzi?i aje a taroshi jama'a su san yana da gata ba wai ace kamar shi sananne a duniya idan zezo gida ya ringa shigowa kamar ?an fashin da ake fako a kama.

Shine dalilin daya saka ta haWo Jama'a kenan dangi da Abokanan Arzi?i, jira takeyi ayi La'asar su Webi motoci a tafi Iyafot Wauko Jafaru, yau Win har kwalliya taci, ta saka Sabuwar Atamfarta Super Sheraton, kusan shekarar ta uku a Winke, da siyanta kuma zatayi biyar ko Shida ta sallah ce da Alhaji yayi musu sauran da yuwuwa sun dade da bayar da tasu amma ita se Yau Allah ya nufa zata saka shima da fari wani Lace ta saka, sabone amma ajiya tasa Winkin ya fita a yayi, tun ana style me Umbrella da hannu me Worin KafaWa, ga wata uwar boader Lace da aka tattara a wuya da bakin Hannu, da ace Zallar Lace Win aka Winka mata ko ya shekara goma zata saka abinta dan babbane, Design Win Lace kuma baya tsufa sedai Winkin jikinsa ya nuna shekarunsa.

Turai ce ta kalleta sanda ta fito ala dole ta ?ure gayu ga Sar?ar Zinare irin design Win Saudiyya damSasheshiya ta sauka har kan ?irjinta, jan hannunta Turai tayi da sauri suka koma Waki tana cewa

"Haba Binta, yanzu saboda Allah da wannan shigar zaki tafi tarar Jafar Win se kace wadda ta fito daga riga? So kike ki ja masa abin magana a Wauke ku hoto a yaWa a a duniya duk suturunki keko ki rasa wanda zaki saka se wannan Matsiyacin Lace Win dan girman Allah ina zaki kai ubannin suturun da kike dasu ne?"

Hajiya ta yamutsa fuska tana kallon Turai tace
"Karki gaya mun mara daWi mana, me Leshi na yayi? Ina a gurinki na siyeshi ko a lokacin ai ya haura Wari balle yanzu indai ba cutata kikayi ba kuma"

"Shekararki nawa da siyansa? Ni wlh har na manta da nayi irin Leshin nan bana zaton wadda na bawa ma har yanzu yana nan be zama tsumma ba, yanzu dai duk ba wannan surutun ba su Hajiya Rafi'a da Hajiya Zuwaira duk suna falo yanzu suka iso se kin raina kanki idan kikaga kwalliyarsu, yayayenau kansu da sukazo dasu bakiga yanda suka sha kwalliya ba se ke da ake taron saboda ke ce zaki fita a haka kamar mara kan gado dan Allah wuce ki sauya Kaya, ki nemo na mutunchi wannan rakwacam Win sar?arma kiyiwa girman Allah ki tattarosu muje gurin Alhaji Mansur a narkasu, a maida miki ?irar zamani".

Badan taso ba shine ta canza da Atamfar dukda itan ma Turai tace ba tayi ba, gafa kayan nan a jibge amma ta bari ta zaSa mata ma tace Aa, da babu gara babu daWi Atamfar ?inkin doguwar rigane an mata Bead work a wuya da bakin hannun, Sar?ar ce dai tace ba zata cire ba, tilas Turai ta barta, a neman mayafi kuma aka tafka abin kunya dan Hajiya dai bata da Mayafin fita Taro, ?arshe se a gurin Momy Turai taje da kanta ta Aro mata Jaka da Takalmi kuma aka samu a gurin Hajiya ?arama.

"Wlh Binta ki canza hali, wannan tsumulmula har ina? KuWi kina dasu kamar su kasheki amma ace ko jikinki ba zaki iya kashewa ba wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu tsabagen zubar da ?ima Gyalen da zaki saka ki fita kunyar ?anki ma baki dashi se an aro a gurin kishiya wannan abin takaici har ina?"

Turai ta dasa mata mita, Binta dake kiciniyar Rataya Jaka a hammata ta buWe baki zata bata amsa suka jiyo ihun Yara ana oyoyo Uncle Jay, Hajiya ta zabura tayi waje dan ta tabbatar da abinda take jiyowa, Jafar Win da ta gama haWa jama'a da motoci zasu tafi tarowa ko kuwa wani daban suke nufi????
*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*

*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*

*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*

*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*

*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*=?
?
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY =؅?=د?*

*Address =?G?=?G?:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 7*

"Jafaru, ni uwarka ka yaudara wannan karon ma kace mun biyar na yamma jirginku ze sauka seda na gama tattara jama'a zamu tafi taronka mu nunawa Duniya gatanka shine zaka tozartani Ko La'asar bata rufa ba ka diro a gidannan wato ka sanar da Amadu shi da yake ?anin ubanka yaje ya dauko ka ko?" Hajiya ta faWa tana zarewa Jafar idanu. Sakin Yaran Yayyensa da suka ru?un?umeshi suna masa oyoyo yayi ya nufeta fuska Wauke da murmushi cikin shagwaSa yana cewa

"Haba Hajiyata, dawowana lafiya ai shine komai yanzu, maimakon ki tareni da warm hug se ki farayi mun faWa kuma?"

"Ka matsoni sena kwasheka da mari wlh, kai kuma me kama da dido dido, sau nawa zan faWa maka ka fita daga sabgar Jafaru? Shin wai Aisha ta haifamin shine ko Yaya? Nace ka fita daga sabgata data Yayana Amadu amma ka?i kaji shin ana dolene? To kaji da kunnenka duk bala'i da tuggunku sedai ya ?are muku amma babu tsafi ko Asirin da zeci Jafaru wlh balle har kuga ya samu nakasu. ?aukaka da cigaba a rayuwa yanzu ya fara ganinta duk nasan shirinku da li?e masan da kakeyi ba wai ban sani ba Asirin da kayi ka lashe masa zuciya ma ina kan karyashi kuma idan na juyo takanka ba zaka ji da daWi ba"

"Haba Binta wannan wane irin abune kikeyi dan girman Allah? Meye amfanin wannan faWe faWen da kikeyi? Jafar dai gashi ya dawo lafiya me kuma kike da bu?ata?" Turai ta katse Hajiya daga Hauragiyar da takeyi se kuwa ta zabga mata harara tace
"Babu ruwanki Turai, idan ba zaki tayani ba to kija bakinki kiyi shiru"

"Allah ya sawwa?a miki, Sannu da zuwa kaji Jafar yi wucewarka can ?akinku, idan kuma zaka fara shiga ku gaisa da iyayenka da suka zo tarbarka toh, sannu da hanya" Hajiya Turai da bataji kashedo ba ta faWa tana nunawa Jafar Palour Binta wanda jama'ar ciki sukayi shiru suna saurar abinda yake faruwa a wajen, Mutan gidan kuwa daman sun san za'a rina dan haka abin bezo musu a bazata ba. Jafar ya kalli Hajiya dake tsaye kamar sojanniya se numfarfashi take tana dannanwa Ahmad da yayi ?asa da kansa harara, cikin sigar rarrashi Jafar Win yace mata

"Please mana Hajiyata, ki saki fuskarki, change of schedule muka samu na flight and na manta ban sanar miki ba. Believe me Yah Ahmad ma be sani ba seda na sauka Kano. You Know i Miss you so much shiyasa ba zan iya jira ba kuzo da yawa ba shiyasa kawai na kirasa nace yazo ya Wauko ni amma ba laifinsa bane Allah nike da laifi amma kiyi ha?uri bari na koma Abuja kawai gobe sena dawo kizo keda jama'arki ku taroni" ya faWa bayan daya isa dab da ita. Hararar da takewa Ahmad ta mayar kansa kafin tace

"Billahillazi karka Wauka kaci banza baka isa ka tozartani a banza ?awayena su tafi suna gulmata ba sannan na ?yakela muje cikin"

"Ai wanan unnecessary drama taki ce zata saka a tafi ana gulmar taki, sabida Allah meye abin tashin hankali a nan? Daman banda Waurawa kai ke kika saba taroshi ko yaya? Wlh Yaya Binta bakya gudun abin magana da abin sakawa kai ciwon kai a duniyar nan, duk inda zaman lafiya yake kin SauWe masa" Munira ?anwarta da batayi niyyar magana ba sedai ganin Abin na Yayartata na neman zarce misali yasa ta fito tana mata maganar. Fuuuu Hajiya ta shige Waki Jafar ya kalli Ahmad yace
"I'm sorry Yah Ahmad ni na jawo maka"
"Kaidai jeka kafin Hajiya ta canza maka wannan fuskar taka babu ruwana bari naje wani guri bazan jima ba zan dawo" Ahmad ya bashi amsa yana juyawa ya fice daga gidan.

Dukda yayi ?o?arin danne Sacin ransa Amma Jafar Win seda ya fahimta, ya sani dole kalaman Hajiyar su sosa masa rai shi kansa beji daWi ba amma yasan idanyace wani abu baya ga kalmar lallaSi da banbaki a yanzu ?ara tunzurata zeyi tayi musu zazzafar Tijara a gaban mutane.

Jiki a sanyaye ya bi bayan Hajiyar, Ya?e kawai ya ringayi yana gaisawa da tarin matan dake zaune falon Hajiyar, ya so ya gane wasu amma ya manta sunayensu wasu kuma sababbin fuskane a wajensa dan Hajiya badai tara
?awaye ba ga Yayayensu da suka kwaso sekace Biki keyi yanzu da tana nufin waWannan jama'ar zata kwasa su tafi ?aukoshi daga Airport Win?.

Abinda ya sake Sata masa rai yanda Yayan ?awayen Hajiyar suketa wani abu kamar masu shafar Jinnu, se Waukar hotuna suke da video ana sakoshi a ciki wasu ma yaga kamar Live sukeyi a IG suna faWin gasu a gidansu Jay sunzo taron shi. ?asa ?asa yake jan tsaki yana dur?ushe tsakiyar Mata kowacce da kalar soki burutsun hirar da take jefa masa da tambayoyi kamar sun aikeshi ya dawo, ba Hajiyar ba ba ?awayen nata ba babu wadda tayi tunanin a gajiye yake ko yana da bu?atar yaje ya huta seda Hajiya Turai ta fito daga Kitchen taje tana shirya abincin da za'a rabawa Jama'ar da Hajiya ta tara abin Allah arzi?in Jay yau ba ?aramin Better tasa aka shirya a gidan ba harda Rago aka gasa.

"Kana tsugunne Jafar ai se ?afafunka su gaji tashi kaje ka huta kaida ka shawo tafiya" Turai ta faWa, ya saci kallon Hajjaju da ta zauna ta haWe fuska tana juya ?afa da gani lissafa yanda zataci ubansu daga shi Har Ahmad Win daya rusa mata shiri takeyi.

"Tashi kaje mana kake kallona da wasu idonka irin na Ubanku" ta faWa tana zaburo masa. Ya mi?e yana shafa kai, daidai nan Faisal Bechi ya shigo yana kwalawa Hajiya kira yana cewa
"An fa gama saita komai har Photographer ya iso Allah dai yasa ma a barku ku shiga Airport Win irin wannan gayya se kace masu taro Governor.." Se kuma ya dakata saboda ganin Jay a gabansa, ya buga tsalle kamar yaro ya Waneshi yana ihu.

"Get off me my friend, kai baka zaka girma da shirme ba ko?" Jafar ya faWa yana tureshi. Bakin Faisal kamar ze yage yace
"Welcome brother, ni na sani sedai ba Jafar Bechi ba wlh se kayi disappointing Hajiya amma fa ka kwafsa kai kasan irin Grand welcome da aka shirya maka kuwa yau?"

"Matsa na wuce" Jafar ya tureshi jin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login