Showing 120001 words to 123000 words out of 467220 words

Chapter 41 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12148

nan gurin.

"Be kamatu na tafi muna riqe da juna a zuciya ba, ina roqon da ka yafe mun idanna maka wani laifi a zaman da mukayi da kai, daga bangarena na yafe maka, iyakar wannan Alkhairin da kayi mun ka zama silar da zan ziyarci ma'aiki ya wanke duk wani laifi naka da yake cikin zuciyata sannan idan ka koma gida ka gayawa Matarka in har taji tsoron Allah ta gaya maka gaskiya ta wankeni daga zargin data saka mutane sukemun na kisan kai na yafe mata idan ba haka ba idan harna mutu ko ita ta rigani mutuwa tabbas shari'armu sedai a qarqareta a gaban Allah dan bazan yafe ba bayan raina a ringa aibata Yayana ana jifansu da abinda ban aikata ba" Bara'atu da be san sanda ta dawo gurin ba ta fada tana kuma gama maganar ta koma cikin Ayari tana daga masa hannu, kamar wanda aka matsawa Remote haka shima ya shiga daga mata hannun, zuciyarsa ta ringa tsinkewa wata faduwar gaba da besan dalilinta ba ta saukar masa haka ya tuqa motarsa ya koma gida yana maimaita zancenta na matarsa ta wanketa daga zargin data dora mata.

A karon farko ya tambayi Binta gaskiyar abinda ya faru? Ya akayi tasan Bara'atu ce ta kashe mata Da? Bintan dake cike fam da tafiyar Bara'atun tayi tsaki kawai ta tashi ta bashi guri. Bara'atun nema take ta zame mata qajaga, ta tunkudeta amma ba zata bar zuciyarta ta huta ba kenan? Abu daya ke sanyaya mata rai idan ta tuna aure ya qare tsakaninta da Audu duk Bala'i dole su haqura sannan ga Yayanta nan zube a tsakar gida suna watangaririya iya rabata dasu da tayi tasan zuciyarta ta quntata, jira takeyi Tagwayen Zubaida su shekara biyu suma tasa ya karbo su subi sahun yan uwansu domin tasha Alwashin babu wata mace da zata mori Audu bayan ita, yaya dai da suka haifa sun samu sedai su jira idan ya mutu su yafici abinda suka samu amma badai a yanzu da yake raye ba.

An kammala aikin Hajji lafiya Mahajjata nata lissafin kwanakin daya rage musu su dawo gida haka nan yan gida nata shirye shiryen tarbar yan uwansu, kwanaki biyu ya rage Jirgin su Bara'atu ya sauka, a daren ranar da zasu tafi Jidda inda daga can za'a maido su Nigeria suna shirye shirye dan sun gama daure kayansu cikinta ya fara murdawa, kamar wasa tun tana jinsa kadan kadan har ta kai ga ta kasa zama cikin abinda be gaza Minti talatin ba da fara ciwon cikin rai yayi halinsa Bara'atu ta amsa kiran Mahaliccinta. Mutuwarta ta girgiza yan tawagarsu gaba daya bama su Bilki kadai ba.

Wata mata ce take fadin
"Dazu take cemun tun da muka hau jirgi tayi addu'a idan har ta kammala aikin Hajjinta lafiya kuma ibadarta ta karbu tana fatan ubangiji ya karbi ranta a binneta a qasar Ma'aiki tace tsoro takeji anya kuwa tayi Hajjinta daidai ashe lokaci yana tafe ubangiji ya karbi shahadarki Bara'atu Yarinyar kirki yarinyavme haquri Annabi yasan da zuwanki" haka akayi jana'izar Bara'atu da Asuba a masallacin Harami aka binneta a maqabartar da ba kowa yake samun wannan Alfarma ba se me tsananin rabo shikenan rayuwar ta qare ta tafi ta bar Binta a duniyar da take ganin ba zata qare ba.

Dawoqar Mahajjata a maimakon murna se Al'amari ya juye na koke koke da Jimami, duk wanda yaji mutuwar Bara'atu seya girgiza hatta da Binta da da take ganin idan aka bata wuqa zata iya dabawa Bara'atun se gashi sanda labarin mutuwarta ya rsketa zuciyarta seda ta tsinke ta kuma girgiza.

Munira qanwar Binta da tazo Kano tun Bayan qaramar sallah dalilin takurar da Mama take mata akan ta fitarda Miji bayan kamar wadda aka sakawa hannu Sauro be taba tsaida ita ba bare yaje gidansu da sunan zance shiyasa ta tattaro ta taho gurin Bintan saboda ta samu sauqi kuma qila ta samu Mijin a nan sanda taji zancen mutuwar Bara'atun kuka ta fasa ta dora hannu tana tumami
"Mun shiga uku Yaya Binta matar nan ta mutu bamu nemi yafiyarta ba wlh inaga haqqintane ya kamamu gashi naqi Auruwa Anty Sakina haka siddan aka koreta daga gurin aiki duk irin hanyar Dady da mutanen daya sani ta kasa samun wani aikin ga Mijinta ibtila'in daya fada masa daman da aikin nata suke lallabawa da tallafin da Dady yake bata to ta rasa aikin ita kanta Yaya Salima cikin garari take masifar yau daban ta gobe daban gashi yanzu ta mutu balle mu roqeta ta yafe mana qazafin da muka mata shikenan haka rayuwarmu zata qare a balbalce ni kenan bazan taba yin aure na na shiga uku na lalace wayyo ni Munira kaicona dana biyewa shedan muka laqabawa Baiwar Allah sharrin kisan rai bata ji ba bata gani ba" magana take cikin ihu da kururuwa wanda mutanen da suke tsakar gida Yan Bechi da sukazo tarar su Bilki duk sun Jita, Audu na kan Baranda dan jiri ne yake neman kadashi tun sanda labarin mutuwar ya riskeshi shiyasa ya zauna a gurin ana masa fifita se ga wata sabuwa yana jiyowa daga dakin Binta.
*PROMO PROMO PROMO*
*Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi*

*Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*.
*Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah*
*1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package*
*2-Qafarka qafata package*
*3-Kankat package*
*4-Da kuma Mini package*

*Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha*

*Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* >?t?>?t?
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*

*Siyan Nagari Maida kudi gida*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 29*

"Ke Munirah meye haka? Baki da hankaline kike daga murya baki san bamu kadai bane a gidan nan?" Binta ta fada a rikice tana qoqarin toshe mata baki Muniran ta fizge tana cigaba da cewa

"Ki barni Yaya Binta abin kukane ya sameni dole nayi, daman Yaya Ummu seda ta fada, tace akwai ranar da zamuyu kuka muyi Nadama, seda tace tun muna da sauran lokaci mu kwance qullin da muka daura a lokacin ban dauki maganarta da muhimmaci ba, haka kawai muna zaman zamanmu muka jazawa kanmu masifa ta hanyar shiga haqqin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba muka bata mata suna kuma mukayi silar mutuwar Auranta gashi yanzu ta mututu ta bar mu a duniyarda nauyin haqqinta a kanmu nidai Allah ya isa tsakanina daku kun cuceni wlh" ta sake fada muryarta a sama tana rusa kuka.

"Alhamdulillahi! Dadina da gobe saurin zuwa, Allah nagode maka daka matsi bakin Azzaluman bayinka suka tonawa kansu Asuri, kaiconku wlh, kaicon Zuciya me cike da Mugunta da Zalunci irin taku. Yanzu ai ga duniyar nan gaba daya bama gidan Audu ba ta tafi ta bar muku se ku shinfida tabarma ku cigaba da zama kuna kasa abinda kukaga dama a cikin duniyar, amma ku sani wlh cutar da kukayiwa Bara'atu bazata barku ku zauna lafiya ba, yanda kuka saka rayuwarta cikin qunci da takura harta koma ga mahaliccinta da yardar ubangiji haka zaku qare taku" Bilki ta fada idanunta na tsiyayar da hawaye, ta waiwaya ta kalli Audu daya runtse ido kamar yayi bacci a inda yake zaunen tace

"Baka da banbanci kaidasu, yanda zasu qare rayuwarsu suna girbar sharrin da suka shuka kaima haka zaka qare taka kana Nadamar zamanka da Bara'atu"
"Ke Bilki menene haka? Da wanne kike so yaji dan Allah?" Aminu ya katseta. Bata kulashi ba taci gaba da kukanta. A cikin daki kuwa Munirah na gamsheqar kuka Binta na tsaye akanta ta harde hannye gaba daya kanta ya qulle ta rasa abin da zatayi a lokacin, ji take kamar ta rufeta da duka shegiyar yarinya ta kwance mata zani a Kasuwa yanzu da wace kalma take so ta gyara kwabar da tayi mata?

Tana jiyo sanda su Aminu suke fadawa Audu zasu wuce saboda kar suyi dare a hanya.
"Ka daure ka shiga daki ka kwanta, rayuwar kenan daman farkonta da qarshenta dan taqin kadan ita dai Bara'atu tata ta qare kuma In sha Allahu munayi mata kyakykyawan zaton tana Babban masauki addu'a kadai zamu cigaba da bibiyarta da ita kafin tamu tafiyar ta riskemu Allah yasa kuma abinda ya faru a baya ya zame mana darasi a rayuwarmu gaba daya" Aminu ya sake fada masa daga nan suka fara haramar wucewa Bechi.

Cikin yanayi me ban tausayi Audun ya miqe, dakyar ya iya ce musu Allah ya tsarw hanya ya daddafa ya haye samansa a falo yayi zango ya kwanta rigingine a qasa wani zafi da radadi yake ji daga can cikin zuciyarsa, numfashinsa ya ringa fita da sauri da sauri tamkar wanda yayi gudu a, a sannu ya baiwa Idanunsa damar fitarda abinda suke muradi, hawaye ya gangaro ta gefen idanunsa zuwa cikin kunnuwansa, tamkar me tsoron wani ya jishi ya saki kuka kamar mace, kuka me tafe da abubuwa da yawa a cikinsa. Cikin muryar da bata fita yake cewa

"Dana san mutuwa zakiyi Bara'atu da ban rabu dake ba, inama ina da damar maido da baya, dana canza zaman da mukayi zuwa mafarkinki, dana san rayuwarki ba zatayi tsaho ba da...da...." Ya kakare yama rasa abinda ze fada se kawai yaci gaba da kukansa a hankali kewar Bara'atun me nauyi tana dirar masa. Kalamanta na sallamar da tayi masa suka ringa dawo masa kamar sannan take maganar, tace ta yafe masa amma bashida tabbacin Allah baze kamashi da laifin cutar da ita ba wai meya shiga kansa shi? Meyasa ya kasa tantance gaskiya da qarya a zamansa da Bara'atu? Me yasa ya gagara yi mata uzuri ya ringa Muzguna mata yana tozartata? Yanzu gashi ta tafi ta bar masa duniyar dai, tayi masa nisan da baze taba taddota ba.

Seda yayi kuka me isarsa kafin ya tashi dalilin kiran sallar Azahar da ake tayi yana layi kamar wanda ya shawu ya dauro Alwala, baze iya sauka ba dan haka a nan yayi sallarsa addu'arsa gaba daya ta nemarwa Bara'atu Rahmar ubangiji ce, yana nan zaune yayi zuru zuru kamar wanda ya kwana zawo, motsin hawowa saman ya jiyo, ya waiwaya ya kalli qofa daidai nan Binta ta shigo da Try a hannunta ta doro kulolin abinci jikinta sanye da Zurmemen Hijabi har qasa fuskarta tayi jaa ta kumbura kamar wadda tasha kuka ta qoshi.

A gabansa ta ajiye Try din ta zauna se ji yayi ta fashe da kuka tana hailala da salati, yayi zukudi yana kallonta kawai.
"Mun shiga uku mun lalace Ashe Bara'atu mutuwa zatayi daman? Me yasa yarinyar nan bata haqura munyi zaman lafiya anyi rabuwar arziqi ba?" Yeeee ta sake rushewa da wani kukan.

"Binta" ya kirata cikin kaushin murya, tayi dif daga kukan munafurcin da takeyi ta kalleshi, cikin sautin daya fi na farko ya sake ce mata
"Zan sake tambayarki menene gaskiyar abinda ya faru ranar sunan Zakariyyah?"

"Wace gaskiya kuma wai kake buqatar sani bayan abinda nida yan uwana muka shaida maka tun a waccen ranar? Allah ya jiqan Bara'atu kawai ni daman tun tuni ai nace na yafe mata idanma wannan kake tunani" ta bashi amsa ba tareda ta kalli idonsa ba babu tsammani kuwa taji saukar yatsunsa a kuncinta irin marin nan na bazata seda ta wantsala gefe tana zare ido kafin ta taqarqare ta fasa qara tana kiran
"Ka mareni"
"Na marekin, kuma dukan tsiya zanyi miki yanzu muddin baki bani amsar abinda na tambayeki ba sa'innan na koraki gidanku" ya fada yana miqewa tsaye PPP ll ya razana Bintar bata taba ganin ya birkice haka ba, Bay's play llp ta fara ja ganin yana neme neme da alama abinda ze doketa dashi din yake nema hakan yasa tace

"Zan fada maka wlh, nidai na shiga bandaki ina fitowa kawai na tarar da ita ta zauna akan Jaririn"

"Har yanzu kina da bakin yimun qarya ko?" Ya fada yana nufota da wayar Radion daya zare, ta yunqura zata gudu Hijabin jikinta ya tadeta ji kake timm ta fadi a qasa be ko bata damar biqin radadin faduwar ba ya shiga zabga mata Bulaliya ta ko ina a jikinta. Dukanta yake kamar ya samu qato dan uwansa yana fadin "ba zaki fadamun gaskiya bako?"

Dadai ta tabbatar da gaskiyarta ce zata kwaceta a hannunsa dole ta fada,
"Wlh sune, basu fadamun daman ya mutu tuntuni ba se bayan da aka gama mana shari'a wlh ba laifi na bane kayi haquri ka kyaleni".

Be barta ba seda hannayensa suka gaji zuwa sannan ko motsin kirki bata iyayi ya mata lilis fatar jikinta duk ta fashe nan ya watsar da bulalar ya shige daki ya barta tana jan numfashin wahala dan kukan ma ta kasa cigaba da yinsa. Wanka yayi ya fito ya tsallajeta yayi waje abinsa, Munira na bakin qofar, tunda ta jiyo ihun yar uwar tata ta taho sedai tsoron karta shiga ya hada da ita yasa taci burki a gurin.
"Kar na dawo na tarar daku cikin gidana daga ke har itan" ya fada mata. Ta sauke ajiyar zuciya da be taba lafiyarta ba, seda ya sauka daga qasan kafin ta shiga, yanda taga Bintan ta tsorata ta kamata Binta ta fashe da kuka saboda Azaba ta ko ina jikinta radadi yakeyi mata.

Hudu ta gota sanda Munira ta hada musu yan abinda zasu buqata Binta ta coccogala suka fita daga gidan Audu saboda tsoron abinda ze iya biyo bayan zamansu Alhalin yace su tafi. Gidan Turai suka nufa dan babu halin Tafiya Kaduna a wannan lokacin, suka hadu suka ringa jimamin al'amarin.
"An auna arziqi dabe furta ya sake ki ba ai, lokaci kawai zaki bashi ya danyi fushinsa ya sakko komai ze daidaita" Turai ta fada.

Binta dake kwance magashiyyan Zazzabi na nuqurqusarta a haka ma wai taje Chemis an bata maganin rage radadi dana zazzabin shine taji dama dama.
"Yanzu ta mutuma amma tsinanniyar matar nan ba zata barni na zauna lafiya da Mijina ba Allah ya isa tsakanina da Bara'atu" ta fada tana sakin kuka. Munirah tace
"Yanzu ashe ba zaki saduda ba Yaya Binta? Wannan abun be isa ya zame miki ishara ba?"

"Zanci uwarki idan kika sake saka mun baki a magana" ta fadawa Muniran daga nan tayi shiru tana jinsu da Turai suna maganganu akan matakin daya kamata su dauka, ita dai Allah ya gani tayi nadama kuma tana fatan itama Bintan ta ganr gaskiya tun lokaci be qure mata ba sannan da sun je gida dole ta warwarewa Iyayensu komai daya faru saboda ayiwa tufkar hanci, muddin Binta bata rabu da wannan matar da alamu suka nuna ita take sake dorata a hanyar banza ba ba zata taba komawa ga Allah ba. Washr gari suka tattara suka wuce Kaduna, Binta bata tsammaci abinda ta gani bayan da Munirah ta fasa kwai ba, gigicewar da Salima da Sakina sukayi ba kadan bace Ummu ko fadi take
"Kun gani ko? Kunga abinda nake jiye muku ko? Yanzu wa gari ya waya? Gashi nan ta mutu ta bar muku duniyar kuji da dakon haqqinta".

Alhaji Zakariyya wanda yake fama da ciwon bugawar zuciya kusan shekara hudu kenan da ciwon ya ta'azzara masa abu kadan yake tayar masa dashi wannan tashin hankali daya riskeshi na abinda Yaran nasa suka aikata ya sake motsa masa ciwon sosai, ita kanta Maman Seda Hawan jininta ya tashi, Allah ya sani daga ita har Mijinta babu me muguwar zuciya da baqin rai irin wanda Yaransu suka gwada. Rashin lafiyar Alhajin tasa basu bi takan Binta ba qoqarin yanda zasu cetoshi kawai sukeyi a sannan.

AUDU
Tattara yaran yayi ya maidasu Bechi bayan da Binta ta bar gidan harda Zakariyya da bata tafi dashi ba, rayuwa ta masa quncin da be taba zaton ze tsince kansa a makamancinsa ba, komai ya sukurkuce masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinsa shi kadai yake rayuwa a gidan abinci sedai ya siya ko yaje gidajen Abokanansa yaci. Be bi takan Binta ba balle yasan me take ciki dukda har yanzun be yanke hukunce dangane da cigaban zama da ita ba ko akasin haka cikin wannan yanayi ya share watanni biyu, Yakubu yazo Kano ya tarar dashi gashi nan shi ba me hankali ba shi ba zararre ba, dukda cewar yana da fushinsa a zuciya amma akace Jini ba wasa ba ya tausayawa Audun.

Shi ya ringa tausarsa ya nuna masa cewar kuskure dai ya rigada ya aikata a rayuwarsa yanzu abinda ya rage masa shine ya gyara sannan rabuwa sa Binta ba shine mafita ba a yanzu tunda dai ya fahimci wacece ita ya kuma san tuggu da makircin da take shirya masa a gida seya hankalta ya kuma san me yakeyi, sannan ya bashi shawara da ya hade kan gidansa, yaje ya maido da Zubaida ta raini Yayanta a gidan ubansu yasan kuma ita zata iya riqe Marayun Bara'atu ta hada da nata saboda zancen yace ze maidasu Bechi ma be taso ba ya kuma jaddada masa ya tashi ya koma makaranta ya nemi ilili na boko dana Muhammadiyya saboda Ilimi shine gishirin rayuwaz daga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login