Showing 345001 words to 348000 words out of 467220 words

Chapter 116 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12391

kanzil ba Salim da ze tanka hanashi tayi seda tayie isarta kuma ta fita tana kuka tana jera Allah ya isa duk wanda yaci da rabonsu.

"Badan ma Al?ali baya tsoron Allah ba ai kafin Aisha ni ya kamata na fara zuwa a lissafin gadon Amadu tunda seda ubansa ya aureni kafin ita, wlh bazan taSa yafewa ba tunda dai duk dukiyar ubana ce ake wada?ar da aka ga dama a ciki kuma se kun dawo da ita sa hannunku idan ba haka ba ta zame muku masifa" haka ta ringa faWa data zauna a tsakar gida tana kuka. Masu aiki dai sedai su kalleta su shige lungu suyi dariya, kowa cewa yake hassada na neman zautar da Hajiyar duk wanda kuma kuskure yasa suka haWa ido masifar ta juya kansa ta zageshi tatas haka har aka kira magriba ta ringa abu Waya kamar wadda taci kai. Ana sallamewa daga masallaci ta tafi falon Alhaji Audu. So take ta sameshi goga masa rashin mutunchin data tanada amma tayi rashin sa'a bata tarar dashi a ?asa ba, ta duba saman nan ma baya nan dan haka ta fita tsakar gida tana kwararawa Issa kira ya taho da gudu ta tambayeshi ina Alhaji nan ya shaida mata ya fita a mota tareda direbansa.

Kamar zata ciji kanta saboda masifa haka dai ta koma ciki tana sa?a da warwarar abinda zata yiwa Alhajin, a yanda zuciyarta ta kumbura ta kuma ?e?ashe akan cin mutunchin da yayi mata Wazu ji takeyi tsaf zata iya sha?eshi ya mutu ko zata huta da ba?in cikin da ya ke ?unsa mata duk ranar Allah.

**********
Umarnin da Alhaji Audu ya bata na cigaba da zama a gidan sam beyi mata daWi ba amma haka ta daure ta zauna har cikar wa'adin ranar da akayi rabon gadon tazo. Tamkar tana zaune a kan ?aya haka ta ringaji, Allah Allah take yamma tayi ta tafi gida dan a ranar ta aika da duka sauran kayansu daya rage a gidan da za'a tafi kai yaran Tahfiz ma ta gayawa direban idan ya dakko su can gidansu ze kai mata su Baba Bilki dai kallonta kawai takeyi bata ce mata komai ba.

Bata ga laifin ta na son barin gidan ba domin ita kanta a dole take zaune, sabon da sukayida Ahmad yasa kwata kwata gidan ya fice mata akai idan magriba tayi lokacin dawowarsa yayi ba ita da Fatiman ba harta yaran tana lura da yanda jikinsu yakeyi sanyi se su samu guri su takure suna kallon kofa ayita tambayarsu menene suce babu komai, a irin wannan lokutan kuma yawanci Jafar yake shigar musu wanda ta lura Fatiman bata son haka shiyasa tunda ta la?anci ya maida lokacin kamar dole na zuwa gidan daga inda la'asar tayi zata shige Waki ba kuma zata fito ba shiyasa data ga ta haWa kaya tun safe kasa ce mata komai tayi se ?walla da take sharewa ta kira Momy kuma ta gaya mata tace babu komai, ta barta ta tafi tunda tana so karsu tauyeta suce seta zauna ita kaWai tasan me take ji a zaman gidan ba tareda ainihin mamallakin gidan ba.

Suna zaune a falo Ahmad na bayan Baba Bilkin ta goyashi Fatima kuma tana danna waya, mai adaidaitan da tace Liman ya nemo mata kusan minti talatin shiru take so ta bi ba'asi ta kirashi be amsa ba tayi tsaki tana cewa Baba Bilki
"Kinganshi kamar wanda aka aika wata duniyar, samo me adaidaita kamar wanda ze kira tifa"

"Liman ne fa, Allah yasa ba mantawa yayi ya shiga wata sabgar ba, toh gashi nan ma ?ila naji ana sallama" Baba Bilki ta amsata jin an sallama. Da sauri Fatiman ta mi?e zata shige ciki amma kafin ta kauce har ya shiga cikin falon sukayi katarin kallon juna cikin ido, a tare suka gallawa junansu harara tayi ?aramin tsaki ta shige ciki shi kuma ya ?arasa cikin falon inda Baba Bilki take cewa

"Au ashe kaine. Kana gari dama Jafar kwana da kwanaki se dai muji hirarka a bakin yara?"

Seda ya zauna kafin ya gaidata ba tareda ya amsa tambayar da tayi masa ba. Tana ?are masa kallo tace
"Jafar kana kallon kanka a mudubi kuwa? Kaga yanda ka lalace? Allah ya ji?an Ahmad amma ya kamata kayi ha?uri ka Wauki dangana haka ka rage damuwar daka Worawa kanka kar muje wani ciwon ya kama ka kaima mu shiga uku" Baba Bilkin ta faWa tana matse ?walla. Yayi gajeran murmushi yana mi?a hannu ta kwanto Ahmad. A ?irjinsa ya sakashi bayan daya sumbaci goshinsa kafin ya ce

"An mayar dashi Asibiti kuwa jiyan?"
"Munje, sun dubashi sunce babu komai Alhamdulillahi kuma ko kallonsa kayi kasan lafiya lau yake gashi nan har ya fara murmurewa sati biyu ya fara cike rama".

"Tabarakallah kam, kamanninsa da Yah Ahmad ma sun sake fitowa, ya nata jikin babu wani abu dai ko?"

"Duk fa kowa lafiya an gode Allah sun dai sake ja mata kunne akan ta rage damuwa kuma ta ringa magana shikenan se abinci da suka ce ta ringa ci sosai saboda ya samu isashshen ruwan Nono"

"Bata cin abinci kenan?" Ya sake tambayar ta daidai nan Fatiman ta fito cikin shiri sanye da hijabi dogo har ?asa da ?aramar jakar da tayi mata saura a gidan. Bata ko kalli inda yake ba ta cewa Baba Bilki
"Ya dawo, ga me mashin Win can a waje"
"Toh bari ma tashi nima ai kayan nawa a haWe suke" cewar Baba Bilki ta shige Wakin da suke ta fito da jakarta har sannan kuma Fatiman na tsaye bata motsa a inda take ba seda Baba Bilkin ta fito kafin ta fice daga falon bayan data yiwa gurin kallon ?arshe zuciyarta ta shiga tsinkewa.

Harta aka Waura mata aure da Ahmad bata yarda a ranta zatayi dogon zaman aure dashi ba saboda wancan al'amarin da yake zuciyarta daga sanda ta sanya ?afarta a cikin gidan ta canza niyya ta ?udurce a ranta mutuwarta ce kawai zata fitar da ita daga gidan dan koda wasa bata taSa kawo Ahmad zai rigata mutuwa ba se gashi ubangiji ya zartar da ikonsa Allah kuma baya kuskure, duk abinda ya faru akwai sila.

Tana tafe tana share hawaye da gefen Hijabinta harta shiga cikin adaidaitan ta zauna se kuma ta fito ta cewa Baba Bilki tana zuwa. Fita tayi daga gidan ta shiga gidan Jafar, rabonta data taka ?afafunta a gidan harta manta. Fatiyyah na zaune a falo ta sha kwalliya kamar sedai kana kallonta kasan bata da walwala dan ko sallamar Fatiman bata ji ba seda ta kusanceta sosai. Babu yabo babu fallasa ta amsa mata, a hannun kujera ta Wofana suka gaisa.

"Sallama na shigo muku zamu wuce gida"
"Tohh! Da wuri haka?" Fatiyyah ta faWa tana gyara zama, se Fatiman ta mi?e tana ce mata
"Eh ai yamma tayi, a yayyafe mu idan munyi muku wani abu cikin kuskure" Fatiyyah ta mi?e tsaye itama tana ce mata
"Mu zamu nemi yafiya ai Maman Amal ni me kika taSa yi mun? Allah sarki rayuwa ana tare yanzu kuma za'a rabu Allah ya ji?an Ahmad yasa can ta fiye masa nan"

Ta amsa da "Amin" tana juyawa saboda hawayen dake neman cigaba da zubo mata, duk idan akayi mata gaisuwa sabuwa mutuwar take dawo mata. Ta kasa sabawa da rashin Ahmad kullum ta Allah maimakon sau?i damuwar ta ?aruwa takeyi. Har compound Fatiyyah ta rakata tana cewa zataje gidan nasu idan an kwana biyu

"Amma da kin bar mana ko iya Amal ce" ta faWa da yanayin da kanaji kasan ba har ranta ba. Kai ta girgiza mata alamar Aa ba tareda ta waiwaya ba ta fice daga gidan, tana sakin ?ofa Fatiyyah tayi shewa kamar wata yar tasha kafin ta shige cikin gida da gudu ta kira Hajiya.

Seda ta shiga gidan Alhaji Munzali da gidan Maman Intee wanda yake manne da nasu kusan dai su biyun ne suke mu'amala sosai tasan kuma ba zasuji daWi ace ta tafi ba tayi musu sallama ba. Babba Bilki na tsaye jikin Adaidaita ta dawo suka shiga, har ke keken ya tayar sun fara tafiya kafin ta ankare babu goyon Ahmad a bayan Baba Bilki da sauri ta dakatar dashi tana kallonta tace

"Baba ina babyn?"
Lalube Baba Bilkin ta shigayi har ?asan Adaidaita se kace me neman allura ko wani tsinke can kuma ta tuna ta rafka salati tace
"Yana gurin Malam, wlh duk na rikice na zata ai na goyashi". Komawa sukayi, Baban ce ta shiga falon dan ita a waje ta tsaya tana jiranta. Jafar na kwance kan kujera idanunsa a kulle ya Wora Ahmad Win dake bacci a ?irjinsa yana bubbuga bayansa a hankali, ta matsa kansa tana cewa

"Ashe baka biyo mu ba, yo ba har mun Wauki hanya ba kafin ta tuna ?ila da se mun isa can zamu fahimci mun manta yaron a gida".

Tashi yayi zaune yana kallonta yace
"Ina kuma zakuje?"
"Au baka san yau zata koma can gidansu ba kenan?" Ta mayar masa da tambayar, ya kalli ?ofa kafin ya koma ya kwanta da yaron yana cewa
"Oh ban sani ba, Allah ya kiyaye hanya toh".

"Kawo shi toh mai Adaidaita yana waje tana jiranmu tun Wazu" ta faWa tana ?o?arin Waga yaron daga jikinsa se ya dafe shi yana kallonta yace
"Karki tashe shi mana Baba"
"Ya kake haka ne Malam, tana waje fa tana jirana ga sanyin yamma ya sauko kuma kasan Wanyen jiki ne da ita badan lalura bama ina zata fita war haka?"

"To waya ce ta fita? Ba gidansu zata tafi ba? Taje mana ai ba'a hanata ba Allah ya kiyaye hanya" ya bata amsa hankali kwance yana maida idonsa ya rufe kamar zeyi bacci se Baba Bilki ta ja gefe tana kallonsa da mamakin abinda yake nufi da ri?e jinjirin mutane yana kuma cewa uwarsa ta tafi to ta barshi dawa?

"Kai bana son sakarki fa Jafaru ka bada yaro mu tafi ka wani kwanta ka ?wa?wumeshi shi, kar kaga ina tausayinka se in Sata maka rai yanzun nan tunda kai har yau baka girma ba".

Shirun da taji kusan minti goma Baba Bilki bata fito ba yasa cikin ?ufula ta shiga gidan, tasan baze wuce ya tsaya yana Sata mata lokaci ba tana shiga ta tarar kamar ma bacci yakeyi abinsa dan haka tace

"Wai bacci yakeyi ki tashe shi mana Baba mutumin fa yana jiranmu"

"Idonsa biyu wlh, halin dai ze kwata mun daman ai ruwa ne ya daki babban zakara yayi laushi amma Jafaru ai ba mutunchi ya cika ba"

Se tayi tsaki kai tsaye ta matsa kansa ta shiga ?o?arin janye yaron, yanda ya taso gaba Waya ya tsorata ta, a ?o?arin ta mi?e ta kifa kansa ta dafe kujera da hannu shi kuma yayi azamar janye yaro gefe kafin ya tareta da hannunsa goshinta ya bugi kwandalelen agogon azurfar hannunsa.

"Subhallahi ai kinga aikin zuciya" Baba Bilki ta faWa tana Wagota, dake me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki se kawai ta Sare baki ta saka musu kuka.

"Ki karSe shi mu tafi" ta faWa cikin kuka. Jafar ya mike tsaye da Ahmad Win yana kallonta yace
"Gidanku kika ce zaki tafi ga hanya nan babu wanda ya hanaki su kuma nan ne gidansu, tukunna ma da izininwa kika kwashe mun kayan yara har kina bada umarnin daga islamiyya a kaisu wani gida can? Idan ma mafarki kikeyi ki farka domin babu inda zaki tafi mun da yara, nan ne gidan ubansu kuma anan zasu zauna dan haka kina da zaSi biyu zama ko tafiya, idan kuma kin zaSi tafiyar karki Satawa kanki lokaci domin ba zaki fita da ko yaro Waya daga gidan nan ba tunda ba da su kika zo ba" yana gama zana mata maganganun ya fice da Ahmad yana sake lulluSe shi da shawul din da aka sakashi a ciki.

Sakin baki sukayi duk su biyun suka bishi da kallo harya fice daga falon kafin ta zabura tabi bayansa da gudu Baba Bilki kuwa salati ta hau yi tana tafa hannaye tace
"Yo idan bakayi fitina ba Jafaru ai ayi tantamar kasancewarka jinin Binta. Ni Bilkisu yau naga abinda yafi ?arfin gani na, ?alau ma wannan yaron yake kuwa? Kodai rashin Wan uwansa ya taSa masa saiti ne?"

Ita kaWai take surutunta kafin ta fita tabi bayan Fatiman,
"Ka bani Wana" Fatima data sha gaban Jafar ta faWa, ya mata wani kallo da ta fassara dana wula?anci kafin ya kauce mata ta sake tareshi, cikin kaushin murya yace

"Ki matsa ki bani guri kafin ki ja na miki abinda ba zakiji daWi ba" cikin tsawa itama ta mayar masa tace
"Ka bani Wana ka gani idan da abinda ze haWani da kai, wani yace karka haifi naka da zaka zo kana nunawa mutane fin ?arfi akan abinda baka da iko dashi" se yayi tsam yana kallonta kusan sakan talatin kafin ya sake gewayeta ze wuce ta ri?e abin Waukar yaron badan ya yi sauri sake dam?e shi ba tsaf ze sulmiyo dan be tsammaci zatayi wannan rashin hankalin ba. Zuciya ta harzu?o masa iya wuce ba zato ya kwasheta da marin daya sa ta saki yaron ba shiri ta dafe fuska.

"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un Jafaru lafiyarka ?alau kuwa? Baba Bilki ta faWa cikin tashin hankali tana kama Fatima da mamaki ya sumar da ita a inda take tsaye.

Kai ko Jafaru yada saurin hannu =?$?=?$?

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 28*

*ASSALAMU ALAIKUM*
*YAN UWANA MATA MASU BURIN A KODA YAUSHE SU KASANCE CIKIN GYARA, JIKINSU YA RINGA TAFIYA DA ZAMANI TA FANNIN KYAU DA KAYAN MARMARI MASU HANA IDANUN OGANNI LE?E-LE?E TO KU MARMATSO DOMIN DAI TAFE NAKE DA ABIN ARZI?I KUMA DOMIN KU KA?AI*

*INA GABATAR MUKU DA GADALIN MUTAN NINGI, INGANTACCE KUMA SAHIHIN MAGANI WANDA MUKAYIWA LA?ABI DA TULA-TULA 3 IN 1*

*INGANCCE KUMA SAHIHIN MAGANIN MU TULA-TULA NA GYARAN NONO, IDAN HAR NONO NE MATSALARKI YAR UWA DA YARDAR ALLAH SE DAI KI BAYAR DA LABARI DOMIN TULA-TULA YANA GYARAWA TARE DA TAYAR DA DUK WATA KOMADA YA MAYAR DA SU CAS ABIN GWANIN SHA'AWA. BAMU CE NONONKI ZASU TASHI SU TSAYA KAMAR NA BUDURWA BA, A'A ZASU DAI SU CIKO SUYI KYAU DUK YANDA SUKA YAMUTSE DA YARDAR ALLAH ZASU ZAMA ABIN SHA'AWA GA MAI GIDA. DALILIN KIRANSA TULA TULA E IN 1 KUMA BAYAN GYARAN NONO YANA MAGANIN SANYI TARE DA SAUKAR DA NI'IMA*

*AN SAMAR DASHI DAGA NAU'IKAN ABUBUWAN DA JIKI YAKE BU?ATA, MAI CIKI BATA SHA AMMA MAI GOYO ZATA SHA DOMIN YANA WANKE NONO SANNAAN IDAN ZA'AYI YAYE YANA HANA CIWON NONO*

*KAI TSAYE A TUNTUBI MAMAN ILHAM KADUNA AKAN 08135613021, Muna kaduna muna aika Kaya ko ina a faWin Nigeria cikin Aminci. Kar a manta siyanna gari mayar da kuWi gida TULA-TULA tabbas ne bawai ya?ini ba*

Be ko sake kallonsu ba ya fice daga gidan. Hawaye masu Wumi suka wanke mata fuska ta share su da bayan hannunta kafin ta ?wace daga ri?on da Baba Bilki ta mata da niyyar binsa seta sake kamata tana cewa

"Haba, kuma se ki biye masa? Kema banda kafiyarki ai da duk haka bata faru ba bari na kira Al?ali yanzu tun wuri asan abinyi dan lamarin Jafaru beyi kama da na me hankali ba" ta lalubo wayarta ta dannawa Baba Al?ali kira.

Al?alin na zaune falon Alhaji Audu na sama yana sake yi masa bayanin yanda sukayi da iyayen Fatima. Ya ajie masa takaddun kadarorin yaran a gabansa yana cewa
"Gasu nan se a san me ya kamata ayi dasu. Ina zaton mun gama komai daya kamata abu Waya zuwa biyu sukayi saura na zartar da wasiyyar daya bari"

"Dama akwai wata wasiyya da Ahmad ya bari ne? Na zata wasiyya na gaba da rabon gado ita ya kamata a fara zartarwa" Alhaji Audu ya faWa yana kallonsa, se Al?alin ya gyara zama yace

"Haka ne, amma idan ta shafi gado ba kamar ace mamaci yayai wasiyyar a ciri wani abu a dukiyarsa a bawa wani kyauta,muddin be zarce kaso Waya cikin ukun abinda ya bari ha dole a zartar da hakan kafin a raba sauran abinda ya bari to ita wannan wasiyyar tasabata kuWi bace sannan abu ne bana gaggawa ba shiyasa ma banyi maganarsa da wuri ba to amma kai ya kamata na sanar maka ba kuma wani abu bane illah ya bar wasiyya akan...wayarsa ta shiga ?ara, se ya dakata ya cirota daga Aljihu ya duba me kiran yace
"Bilki ce, ko me ya faru kuma?" Seya Waga da sallama.

Daga can Baba Bilki tace
"Al?ali babu lafiya a gidan nan"
"Subhallahi meya faru? Cikin yaran nr ko kuma ita mahaifiyar tasu?" Ya tambayeta seta bashi amsa da cewa

"Ina fa, Jafaru ne. Wlh ina ganin rashin Wan uwansa ya taSa masa ?wa?walwa, kasan yarinyar nan yau zata wuce can gidan su" Baba Al?ali yayi saurin mayar da wayar speaker dan Alhaji Audu yaji abinda take cewa,

"Hello kana jina kuwa?" Ta faWa jin shiru yace
"Ina jinki Bilki meya faru kuma?"
"Tiryan tiryan ta labarta masa abinda ya faru, cikin rashin jin daWi Baba Al?alin yace mata

"Yanzu ina Jafar Win?"
"Ya fice da jaririn bamu san inda ya tafi ba"
"Shikenan, yanzu kice tayi ha?uri, ku tafi ki rakata gidansu zan kirawo Jafar Win yanzu"

"Mu tafi banda yaron kuma Yaya?" Baba Bilki ta faWa da mamaki, Al?ali yace
"Eh, ku tafi da kansa ze biyota ya kawo mata Wanta. Ko yananda maman da ze shayar dashi ne? Kema rashin dabara yasa har kika bari ta biye masa hakan ta faru, ku tafi kawai ze zo ya sameni kuma ki gaya mata ta kwantar da hankalinta be mari banza ba" ya sake jaddada mata ta kashe wayar a sanyaye ta gayawa Fatiman abinda yace. Da hawaye shaSe shaSe Fatima ta shiga Adaidaitan suka bar gidan bayan da Baba Bilkin ta kulle. A hanya tana ta lallashinta ita dai jinta kawai takeyi bata ce komai ba.

Cikin Sacin rai Alhaji Audu ya lalubi wayarsa Al?ali ya dakatar dashi yace
"Bari na kirashi".

A Sangaren Jafar kuwa gidansa ya wuce da Ahmad dake baccinsa hankali kwance bema san wainar da ake toyawa a kansa ba. Fatiyyah na zaune tana chatting bayan sun gama waya da Hajiya ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login