Showing 318001 words to 321000 words out of 467220 words

Chapter 107 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12179

yanzu tana kallonsa a matsayin miji ba?

Motsin buWe ?ofa da sallamar Hajiya Rabi ne ya fargar dashi, ya kalleta harta zauna gefen gado fuskarta bayyane ?arara da damuwa tace
"Wai me yake faruwa? Momy ta fita tana kuka ina tayi mata magana ma bata kula dani ba kuma da safe da kuka fita ance jikin Ahmad ne ya tashi ciwon ne yayi tsanani ko me ya faru?"

A maimakon ya bata amsar abinda ta tambayeshi shi seya kafe ta ido yana cewa
"Rabi, shin kema zaman yayanki kikeyi a gidan nan ko kuwa har yanzu kina mun kallon mijinki?"

"Sakinta kayi?" Ta faWa tana dafe ?irji, seya girgiza mata kai yace
"Ban saketa ba tukunna, ki amsa mun tambayar da nayi miki amma"

"Murmushin ya?e tayi tana kallon gefe tace
"Inda ace ni nake da gatan Momy da wallahi na daWe da barin gidan nan Alhaji ko ka sakeni ko baka sakeni ba amma ina zaune ne kawai saboda tawa jarabtar Allah be bani jajirtattun iyayen da suka damu da damuwata ba waWanda idan na kai musu koke na zasu tayani ya?in neman yancina sannan ina duba makomar Yayana idan na fita na barsu in ba haka ba da ko gudu ne zanyi na koma wani guri can da babu Wanda ya sanni na ?arasa rayuwata cikin farin ciki amma nasan duk yanda iyayena zasu tilastani na zauna dakai dole su ha?ura idan har ya zamana babu sauran zama a tsakaninmi, dan Allah idan ka tashi sakinta ka haWa dani ka sama mana yan ci tare".

Kallonta ya ringayi tamkar ya ga sabuwar halitta daga ?arshe yace mata ta fita ta bashi guri, ya tallafe kai da hannu biyu yama rasa dame zeji, haka ya ringa malelekuwa tsakanin gado da kan kafet, duk ?arfin magungunan hawan jininsa da yake sha suna sakashi bacci daren ranar be runtsa ba, shiga goma fita goma ze bugawa Babba Al?ali daya tare a Asibitin waya, tun da yamma bayan ya farka aka mayar dashi Asibitin Dr Hassan kamar yanda Alhajin ya bada umarni, Muhammad ma sunyi magana ya sanar masa yana iyakar ?o?arin sa gurin ganin an samu damar fita da Ahmad Win cikin lokaci.

Acan Asibiti kuwa baibai suka ninke Fatima akan gaskiyar ciwon Ahmad Win, saboda kar hankalin ta ya tashi sosai likitan da kansa ya shaida mata cewar ciwon ?oda ne yake damun???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Ahmad, rashin ganowa da wuri ne ya saka shi jin jiki haka amma ta kwatar da hankalinta domin har an samu wadda tayi daidai da jininsa za'a dasa masa. Dan ma dai Alhajinsu yace baya so ayi aikin anan Asibitin sedai a fita dashi turai ayi acan, amma karta damu babu komai da anyi aiki lafiya ze samu sau?i tamkar wani abu be taSa samunsa ba.

Allah sarki ta ringa kuka kamar zata shiWe ta kuma yarda dagaske musamman da aka karSi passport Winta sannan aka mayar dashi can Asibitin Dr Hassan da ya farka kuma daga dogon baccin da yayi yanayin jikin da sau?i harta samu damar yi masa ?orafin me yasa ya Soye mata yace ai gashi yanzu ta sani, haka suka washe gari tun gari be gama haske ba Asibitin ya fara cika da dangin Ahmad, yayan gidansu mata har Wanda suke aure a wasu garuruwan da yayan Baba Al?ali dana sauran yan uwansu se gasu tamkar ana biki duk wadda ta shigo kuma seta fashe da kukan tashin hankali tana maganganun da Fatiman ta gaza gane kansu.

Ahmad dai yana bacci tun bayan da aka sakeyi masa wata allura dan cikin dare bayan bacci ya Wauke ta da taimakon maganin baccin da Nurse ta bata a shayi bata sani ba bisa umarnin Dr Hassan domin itama jikinta na bu?atar hutu tana kwanciya nasa jikin kuma ya rikice har seda aka canza masa Waki suka mayar dashi ICU, da safen ce mata sukayi saboda yan zuwa dubiya aka kaishi can dan kar a dameshi, itama ta window ta le?a shi yana baccin ta koma falon Amenity room Win da aka fara kwantar dashi anan yan dubiyar suka zo suka tarar da ita.

Tun tana ?o?arin yi musu bayanin da akayi mata dangane da ciwon Ahmad Win har lissafin kanta ya ?wace ta fara dena gane komai dalilin kalaman da taji sunayi, yanda suka cika Wakin kowa da kalar nata kukan yasa ta sulale ta fice dan tana da bu?atar yin tunani me zurfi domin ta fahimci kamar ba iyakar gaskiyar maganar aka gaya mata ba akwai abinda ake Soyewa Wanda ba'aso ta sani.

Can waje ta fita ta samu guri ta zauna, bata jima a gurin ba ta hangi Aminun su Ahmad Win tareda wani da ta sanshi amma ta manta sunan sa cikin sauri suka shige ciki dan haka basu lura da ita ba kusan minti goma Aminun ya fito hular dake kansa sanda ya shiga a hannunsa yana firfita, daga can gefenta ya nemi guri ya zauna ya buga waya, harta yun?ura zata masa magana ganin har sannan be lura da ita ba seta fasa saboda abinda taji yana faWa a wayar.

Tasan dai Ahmad Waya ne a gidan kuma shine dai yake kwance a Asibiti yanzu haka, jiki da bakinta sukayi mata nauyi har Aminun ya tashi daga gurin tana ji yana gayawa wanda suke wayar akan ya kira kowa ya gaya masa amma banda Jafar kar a gaya masa yanzu.

Tana hangoshi seda ya shige motarsa ya tayar kafin ta samu karfin mi?ewa tsaye, taga ko gudu tayi ba zata kamoshi ba harya kai get se kawai ta juya cikin Asibitin tafiya take kawai tana jefa ?afarta badan tasan inda take zuwa ba har seda taci karo da wata Nurse ta ri?eta kafin ta fahimci a inda take se kawai ta fashe mata da kuka kamar wadda aka cewa Ahmad Win ma ya rigada ya mutu.

***********

Baba Bilki ta zuge akwatin data zubawa Fatima yan kayayyakin da zatayi amfani dasu, tana share hawaye ta kalli Fatiman dake kwance tace
"Na gama ko akwai abinda kike bu?ata?"
"Babu komai Baba nagode Allah ya saka da Alkhairi" ta faWa a sanyaye muryarta a dashe kafin ta yun?ura da?yar ta tashi, seda ta dafe bango jirin da yake hajijiya da ita ya lafa mata kafin ta fara takawa a hankali kamar me irga sawunta ta fita daga Wakin Baba Bilki na biye da ita da akwatin kayanta.

Bata aminta da gaskiyar zancen data tsinta a bakin Aminu ba seda Momy ta tabbatar mata, a lokacin ta gasgata cewar ba kowacce damuwa akeyi wa kuka ba domin tunda tasan ainahin Abinda yake damun Mijinta kuka ya ?auracewa idanunta, bama tasan me taji ba ko takeji a tsayin kwanaki goma da sanin abin ita dai tasan tana rayuwa amma baya ga nan bata san me take ba ta dai godewa Allah daya lamunce mata take iya ambatonsa, ta rame ta Washe Hatta abin cikinta ya motse tamkar babu shi dukda anyi mata hoto an tabbatar da yana raye sedai bata saka rai dashi kwata kwata saboda duk abinda aka zana mata ta kiyaye domin lafiyarsa ta gaza aiwatar dasu.

Idan kaga yanda ta koma a Wan lokaci seka rasa waye mara lafiyar tsakaninta da Ahmad Win dan dukda cewar ciwo ya gama ragargazarsa annuri da fara'a tareda barkwancinsa basu barshi ba.

Kowa mamakin ?arfin hali da dauriyarsa yakeyi, shike cikin ciwo amma makusantan sa ne da kuka da fargaba tamkar ma babu abinda ya dameshi koda yake ya rigada ya sare da rayuwar, ita Fatima tama kasa ce masa komai akan ciwon bata ma san ta inda zata kamo ta fara masa maganar ba, iyakar abinda yake ciki ya ishe shi. Da kanta ta lissafa tsayin lokacin da take zaton ciwon ya bayyana a jikinsa, da ace mutum nada ikon juya lokaci data koma ta gyara.

Bata manta lokacin daya ringa zaryar Asibiti a lokacin yace mata murar da yake yawan yi ce ta dameshi a sannan ma yaui tafiya ne ya dawo daga Russia yace mata sanyin daya kwaso ne haka yayi ta zaryar Aaibiti daga kano har Zaria Shika daga ?arshe yace mata wai Asthma ce dashi tun sannan ko turaren wuta zata saka seta tabbatar haya?in ya fita tsaf kafin ya shiga gurin sannan ta rage ta'ammali da kayan sanyi shine ma silar daya siyo musi fankoki na tsaye suka rage amfani da Ac ashe duk bagarar da ita yayi, tafiye tafiyen da ya rinyi ba shiri duk ashe na yawon neman magani ne sau tari daya fara ?orafin gajiya da ciwon jiki se yace mata zeyi tafiya harta ringa mitar shida zirga zirgar cikin gida ma ta gajiyar kuma ya ?ir?iro zuwa wata ?asa? Har ta kai idan zeyi irin tafiyar seya jangwaleta da faWa ta yanda ko ze tafin ba zata yi mita kota hanashi ba ashe duk a sannan shi kaWai yasan halin da yake ciki tsayin wannan lokacin shi kaWai ya san raWaWi da Azabar daya daWe yana sha ya kuma Soyewa kowa saboda karya saka su a damuwa tabbas Ahmad jarumi ne.

Kwanan sa biyu a Asibitin ya addaba se an sallameshi ya dawo gida, lallaSashi sukeyi dole Dr Hassan ya yarda ya maida shi gidan kusan kullum can yake wuni bayaga Nurse daya ajiye me kulawa dashi dukda dai ba wani abu akeyi masa ba, idan ciwon ya motsa ne ake masa allurai da zasy rage masa raWaWi, a iya abinda Allah ya sanar dashi dangane da likitanci yasan Ahmad ya kai matakin da cigaba da Wura masa wasu magunguna ba abinda zeyi illa ya ?arasa kassara inda be ida mutuwa ba a jikinsa, jiran lokaci kawai yakeyi ko fita dashi waje dan Alhaji ya matsane amma da ze yarda da shawararsa gara a barshi a gida cikin yan uwansa ya mori kwanakin da suka rage masa a duniya duk da al'amarin na ubangiji ne yana iya juya komai a sanda yaso se dai bisa ga horewar da yayi musu ta fahimtar ciwo da matakin da yake iya zama karshen rayuwar Dan Adam to tabbas Ahmad yana gargara.

Gefen Hijabin jikinta ta saka ta goge hawayen da ya tsatstsafo mata tamkar tayi kwalli da barkono tsabar yanda idanunta suka bushe, a falon ?asa suka tarar da Ahmad tareda Alhaji Babannan, shi kaWai ne bata gani ba a cikin yan gidansu tun bayan kwanciyar Ahmad Win a Asibiti se Jafar wanda a yanzu ta gasgata besan komai dangane da ciwon Ahmad ba yanda ya rufe kowa haka shima ya rufeshi.

Ta rusuna ta gaishe shi ya amsa yana mata sannu tana jin gajiyayyun idanun Ahmad Win akanta amma ta gaza kallon koda sashen da yake.
"Ubangiji ya ?ara miki juriya shi kuma Allah ya bashi lafiya, Hassan ya gayamun Asibitin da zakuje basu da na biyu a duniya, da yardar Allah za'a dace ze samu lafiya Alfarmar annabi da Alkur'ani" Baba Bilki dake kuka ?asa ?asa ta amsa da
"In Allah ya yarda Allah ya biya bakinka ya amsa".

Salim yayi sallama ya shigo daga bakin ?ofa ya gaishe su kafin yace su yake jira.
Alhaji Babannan ya mi?e yana bawa Ahmad hannu yace
"Zan wuce in sha Allah zamu haWe a Abuja kafin ku wuce"

"To ka kaini can gidan seka wuce Yaya" Ahmad ya faWa yana kallonsa, yayi jim yana kallon sama kafin ya amsa masa da "toh, ina jiranku a waje" ya tattara babbar rigarsa ya fita Ahmad ya rakashi da murmushi kafi Salim ya shiga turashi akan wheel chair suka fita. Seda yabi ma'aikatan gidan duk sukayi musabaha, masu raunin cikinsu suka fara hawaye kafin aka sakashi a motar Alhaji Babannan Win kamar yanda yace Bilki da Fatima suka shiga motar Salim Win, har zasu fita ya tuna da wani abu yace ya tsaya, ta window ya kira Salim ya faWa masa abinda ze Wakko masa sannan ya karSi wayarsa dake hannun Fatima.

Haka ya ringa gaisawa da makwafta da masu gadin unguwar har suka fice kowa na masa fatan Allah ya tsare da kuma dacewa da abinda aka tafi nema, da suka isa gidan Alhaji Audu kuwa yasha mamakin ganin motoci birjik a ma'ajiyar gidan, daga kan securities masu uniform har sauran ma'akatan gidan kamar waWanda basu da lafiya, haka suka wuce su bayan sun gaisa Baba Bilki da Fatima suka Shige cikin gida su kuma suka shiga falon Alhaji Audu inda ake jiransu tareda Alhaji Babannan wanda a hanya Ahmad Win ya ringa sakarwa kalaman da suka sa ya kasa musa masa daya ce su shiga cikin gidan tare, abin mamaki kuma abin farin ciki tun daga kan Alhaji Babangida har zuwa Autansu Abdallah mata da maza Jafar da Zakariyya ne kawai bab, hatta Naziru da ganinsa ya zama se masu sa'a yana zaune a gurin se kuma Yayan Baba Al?ali da sauran Yayayen Yayyensu falon ya cika ma?il kamar sallar idi.

Yawo ya ringayi da idanunsa akansu fuskar sa Wauke da murmushin da be taSa gushewa daga fuskarsa ba ?arshe ya sauke akan Alhaji Audu dake kishingiWe kan kujera tamkar wani sarki fuskar nan ba yabo ba fallasa kamar ko yaushe. Dada na ganin Ahmad Win ta fashe da kuka kamar sauran matan na jira suka mara mata baya, cikin faWa Alhaji Abdullahi yace su tashi su shige cikin gida wane irin sakarci ne haka?

"Kayi ha?uri Yaya amma kuka ya zama dole bazamu iya hana kanmu ba, ku godewa Allah ku mazane kuna da jarumta da ?arfin zuciya ba kamar tamu ba" ta faWa tana rufe baki Mu'allim ya kware baki wiwi ya fasa musu ihu, kamar Faisal na jira ya samu wanda ze buWe musu ?ofar yan maza kuwa ya kama wai Aminu shi babba ya fara cewa suyi shiru
"Zaku sake karya masa zuciya sallama mukazo yi muyi masa fatan Alkhairi ba wai mu saka masa damuwa a zuciya ba dan Allah ku dena" ya ?arasa yana sakin nasa kukan shikenan falon ya zama kamar gidan mutuwa dan har Baba Al?ali hawayen ya shiga sharewa ganin sun hargitse gurin ya saka Alhaji Audun yin gyaran murya ya zauna da kyau cikin bada umarni yace matan su fita su basu guri.

Da WaWWaya suka ringa ficewa suna waiwayen Ahmad da yake ta murmushi shine kuma abinda yake sake karya musu zuciya, seda suka fice gaba Waya ya sake kallon mazan dake sharar hawaye yace
"Kuma ku bisu zamanku bashi da amfani tunda kun zama Waya ku da su Win" nan suka saita kansu sannan ya sake kallon inda Ahmad Win yake Alhaji Babannan na tsaye a bayansa yace

"Yusuf baka ga gurin zama bane ka tsaya a nan?" Kansa a sama ya tura Ahmad din tsakiyar falon kafin ya samu guri can gefe kusada Hussaini daya ?wama ba?in gilashi yana danna waya. Murya na rawa Baba Al?ali ya buWe musu taro da Addu'a daga nan ya sake jadada ma?asudin taruwarsu a gurin ya rufe da yi musu yar gakeriyar nasiha akan rayuwa da zumunchi. Da yace Alhaji Audu yayi magana cewa yayi bashida abin cewa se kuma ya zabura yace

"Ko bana sonku kamar yanda da yawanku kuka saka hakan a zuciyarku ku sani ina da ha??in haihuwa akanku, wannan ya zama na farko kuma na ?arshe idan ma a nan cikinku akwai me wata cuta daya Soye tun wuri ya bayyana ta dan bazan yakewa koma wanene ya sake Waukar alhakina akan ciwon da bansan yana dashi ba"

"Amma dai ka yafe mun Alhaji" Ahmad ya faWa cikin sanyin murya, Alhajin ya kalli gefe kafin yace
"Baka mun komai ba, kuma koda kayi na yafe ba kai kaWai ba gaba Wayan ku duk wanda yayi mun wani abu na yafe masa, Allah yayi muku albarka baki Waya Allah ya tashi kafaWun dan uwanku ya bashi ikon aiwatar da ?udirinsa na Alkhairi" yana gama faWar haka ya mi?e duk suka bishi da kallo ganin ya shige ?aramin falonsa.

Shiru ya gifta tsakani kowa da abin da yake sa?awa a ransa kafin raunatacciyar muryar Ahmad ta katsesu inda yake cewa

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 21*

"Ina neman alfarma a gurinku. Dan Allah mu taru mu manta baya, muyiwa junan mu uzuri kamar yanda muka taru gaba Waya a nan yau bisa rajin kanmu ba tilastawa ba kuma dole aka kira kowannen ku ba ina fatan ya zama silar samun daidaiton da nake ta fata da buri a tsakaninmu.

Fatana na ?arshe a rayuwata shine kan zuri'ar mu ya haWu guri Waya, mu tabbatar da zumunchi mu zama abinda mutane suke hasashen mu akai. Daga nesa mutane suna mana kallon tsintsiya me maWauri daya muyi ?o?ari mu tabbatar da hakan. Kuyi ha?uri duk abinda ya faru a rayuwarmu ba laifin kowa bane haka zanen ?addarar mu yake dan haka karmu cigaba da Worawa kowa laifi muna tauye rayuwarmu daga jin daWin dake tattare da zumunchi.

Rayuwar nan gajeriya ce, cikin ta?aitaccen lokaci komai yana iya canzawa. Kuna kallon yanda ?addara tayi da Yaya Zakariyya, gani, bama fata amma bamu san me ubangiji ya sakw tanadarwa waninmu a gaba ba. Biyayyar mahaifa tilas ce bawai zaSi ba, bana zaton muna da karSaSSen uzuri a gurin Allah da zamu ri?a harya hanamu kyautatawa mahaifinmu, koda ace yana kan kuskure wannan ya rage tsakaninsa da mahaliccinsa ne amma mu a matsayin mu na Yaya tilas mu kyautata masa iyakar iyawarmu mu sauke ha??in da Allah ya Wora mana nasa.

Dan Allah koda sau Waya a shekara ku ringa haWa irin wannan zaman sannan ku kyautata mu'amalarku, bani da tabbacin zan sake zama tareda ku kamar haka amma ko a ina nake ina fatan farin ciki da kwanciyar hankalin da zaku samar ya tarar dani" ya tsahirta saboda ?irjin sa daya masa nauyi kusan minti biyar ya Waga kansa sama yace

"Idan ban dawo ba na bar amanar iyayena da iyalina a hannunku, ban Waukewa kowa ba koda ace ba ku yarda kun jiSanci lamuran junanku ba dan Allah ku kula da bayana. Karku bari Momy da Jafar suyi kewata, yayana kar suyi kukan maraici na rashin uba. Ina so su san tasirin Ahali suyi farin ciki tareda Alfaharin kasancewarsu Jinin TIJJANI BECHI

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login