Showing 21001 words to 24000 words out of 467220 words

Chapter 8 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12195

yayi shuka lafiya har ta fara yabanya haka kawai aka wayi gari komai ya bushe shekarar haka ta qare ko Kara be cire a gonar zancen da akeyi yanzu gonar ta zama tamkar kufai, aciki ne ma ake zaton Gwamnati zatayi ginin firamaren da za'a bude wadda me gari ya bashi shawarar ya bayar dan abinda za'a biyashi ya nemi wata ko qarama ce ya siya.

A labarin daya ringa kewaya gari ance anga Hashimu yana zagaya gonar da dare bayan sunyi zancen cinikin Baffaye yaqi wanda ba'a kwana biyu ba wannan ibtila'i ya fadawa Baffaye, bawai ya yarda da abinda aka fada ba amma kalaman Hashimun na dazu sun saka qara masa hujja nacewar ze iya yi musu mugunta a kan Gonar. Ransa fal da baqin cikin hanyar da yan uwan nasu suka dauka bayan gushewar Malam da bashida burin daya wuce ganin sun hada kansu amma abu ya gagara, haka ya kwana da takaicin abin a zuciyarsa washe gari kuwa qarfe goma na safe gaba dayansu suka hallara yan dakin Goggo Fadi dana dakinsu. An kirawo Dillai a gaban kowa sukayi wa gonar kudi da daraja abinda ya qara qonawa Hashimu rai dan kafin zuwansu seda ya samu daya daga ciki har cin hanci ya bashi akan su kassara farashin gonar, haka ya tishe kudin cas ya basu abinda ya qara bawa kowa mamaki su kam sun rasa a ina Hashimu yake samun kudi haka.

Audu da yan uwansa suka qule a dakin Dada, Yakubu nata fada akan abinda ya faru, Bilki da Aisha ma dai sunbi sahun Audu nayin amanna da siyar da gonar dan har Bilki na cewa daman taji a bakin Mijinta Hashimun na fadar koda tsiya se ya mallakin barin gonarsu ya zama nasa to gara da kayi ta arziqi shikenan.

Audu ya kalli Dada yace
"Yanzu ya za'ayi da kudin nan?"
"Ni a ganina a nemi wata gonar a siya idan yaso ko haya ce a bayar ko kuma a nemi ma'aikata su ringa nomawa ana biyan su lada" Dada ta bada shawararta, Audu yayi shiru kafin ya kalli Yakubu yace
"Kai kuma ya kake gani?"
"Daka zarce hukuncin a siyar da baka shirya abinda za'ayi da kudin ba?" Yakubu ya fada a cikin fada Dada ta daga masa hannu tana cewa
"Bana son haka, karka kuskura ka saka wannan abin a ranka balle har sabano ya shiga tsakaninka da dan uwanka. Kaifa ka gaya mun abinda kukaji ya fada jiya, kasan hatsabibancin Hashimu, ladan hayar da suke bamu kana kallo lalataccen da kwari suka taba ake tattarowa a bamu duk dan a zauna lafiya yasa ban taba magana ba yanzun daya nuna yana so gara a bashi dan qarshe zamu iya rasata baki daya".

Yakubu be iya cewa komai ba tunda Dada ta goyi bayan Audu, qarshe bisa shawarar Audu da Bilki suka yanke cewar za'a tada gini Jikin katanga a fitar da qofar shago ta waje da kuma ta cikin gidan inda zasu zuba duk wasu abubuwan buqata da suke wahala a Qauyen, mutum daya ne yake shiga Kano yayo sarin kaya shima se yafi wata beje ba dan haka abubuwan buqatu da yawa sedai a haqura ayi amfani da wanda ya samu sannan Bilki tace tana so Audun ya ringa aiko mata da zannuwa da sauran kayan kwalliyar Mata daga Kano tana siyarwa dan shima Mace daya ke wannan sana'ar Asabe Dillaliya, sunyi na'am da shawarar, aka kasafta kudin kowa aka fidda masa rabonsa kafin suka sake hadesu Audu ya adanasu cikin kayan tafiyarsa.

Cikin abinda ya masa saura a hannu ya tafi Kumbotso dan yiwo musu siyayyar abubuwan amfani, dayace Yakubu yazo su tafi qi yayi dan har sannan a qule yake dashi, yasa an siyar da Gona kuma ba'a siyi wata ba an tattare kudi wai za'a juya su. Se ya liqis ya dawo Bechi niqi niqi da siyayyar da yayiwo, a qofar gidan ya tarar da magina sun jiqa gefe ga bulo da alama gini ake a cikin gidan. Ne damu dasu ba yayi musu sallama ya shige sedai abinda ya gani ya sakashi dakatawa tareda tsayar da yaran da suka tayashi daukar kaya.

Hashimu na tsaye da Malam Sha'aibu magino suna magana, ga katanga nan da aka fara dorawa daga bakin qofar soron har jikin katangar baya ta gidan da Alama an tasarma raba gidan ne. Bawai Rabawar ne ya bashi mamaki ba Aa yanda aka tada katangar idan aka gine ze zaman su basu da hanyar shiga bangarensu kenan ko kuwa Katanga zasu ringa tsallakawa oho.

Aminu ya fito daga dakin Goggo Fadi kana ganinsa kasan a fusace yake beko lura da Audu ba ya kalli Hashimu yana cewa
"Tun wuri ka dakatar da wannan ginin wai me yasa duk abinda ze janyo tashin hankali a gidan nan shi kakeyi? Yanzu ta ina kake so su ringa shiga barayinsu?"
Cikin ko in kula Hashimun yace masa
"Ko su fasa wata qofar ko su siyi fukafukai duk matsalarsu ce gida ne dole a raba kuma a sannu yanda na raba su da gonar shima gidan seya gagre su zama sun barshi".

Zuciyar Audu ta harzuqa amma ya daure bece komai ba ya wuce da qafa ya tunkude bulon da basu gama kamawa ba aiki Yar katangar da ta fara tsayi ta ruguje ya shige abinsa yaran da sukayo masa dako suka bishi, a fusace Hashimu yabi bayansa har qofar dakin Dada seda Audun ya dire kayan hannunsa kafin ya kalli Hashimu dake numfarfashi ze fara bala'i yace
"Idan ka manta bari na tuna maka soron a cikin rabon gadon mu yake, saboda idan muka ja katanga baku da ta inda zaku fasawa Mahaifiyarku qofar fita shiyasa muka barshi amma da tuni na dade da sakawa an toshe qofa mun canza mata fasali" yana gama fadar haka ya shige ciki ya bar Hashimu da yayi shiru yana tunani, tabbas gaskiya Audun ya fada Soron rabonsu ne tsabar shaidan da yake masa kururuwa yasa ya manta ganin yafi kusa da bangarensu idan kuma suka toshe din da gaske basu da kusurwar da zasu bullawa Goggo qofa dan ta bamgarensu sun fisu yawan dakuna haka zakila Kudun su da yamma jingine suke da gidaje babu damar su fasa qofa sabanin su Audu da suke ta gabashin gidan inda fili yafi yawa kuma babu gini jikin katangar ta bangaren.
Cike da borin kunya ya tafi yana cewa
"To se kuzo kuyiwa soron kudi a biyaku dan babu fashi gidan nan se an raba shi".

A cikin daki kuwa Dada ta girgiza kai mamakin lamarin Goggo Fadi da yaranta ya kasa sakinta a kullum sabon abu suke tsiro dashi to wai me yasa tun Malam na raye basu bayyana halinsu a fili ba se yanzu daya kau? A daren Audu da Yakubu suka tara matansu nan dakin Dada suka qara jan kunnensu tare dukda basu da matsala, lafiya lau suke zaune Dada kuwa a yaya ta daukesu ba surukai ba idan kaga yanda suke gwanin sha'awa. Kamar yanda suka fara girki daya sukeyi kuma a hakan zasu cigaba, Sadiya yar wajen Bilki zata ringa taya Balaraba kwana, da farko Innar Bara'atu tace zata turo mata qanwarta se daga baya kuma tace Babansu ya hana. Daga qarshe Abdullahi mutumin Audu dan gurin Aminu aka bata dukda Goggo Fadi da Hashimu basu so ba, da yake shima Aminun tsayayye ne yayi musu fes yace dan sa ne kuma ya bawa Audu halak malak ko bayan ransa yayi Tijara kafin magana ta Mutu Abdullahi ya dawo dakin Bara'atu lokacin shekarunsa hudu a duniya.

Audu da Yakubu sun dawo Kano cike da kewar Matayensu kowanne yana jin jiki haka suka duqufa abinda ya maido su, sunyi register rubuta jarabawar kammala Sakandire da suka ci sa'a daidai lokacin an fara kwana kadan suka rubuta cikin yardar Allah sakamako ya fito dukkaninsu sun samu sakamako me kyau. Yakubu ne ya tirsasa masa kan cewar seya rubuta dukda yace shi ba karatu ze ci gaba ba amma idan ya ajiye takaddar wata rana zatayi masa Rana. Kudin da suka zo dashi Audu ya zuba suka fadada kasuwancinsu, yayi sarin kaya masu yawa ya aika dasu Bechi an bude shago wanda dama sun bar alhakin aikin a hannun Mijin Bilki Baballiya ne yake zama kuma ba qaramin ciniki akeyi ba dan kusan komai na buqata an kai harda ma sababbin abubuwa a gurin mutanen qauyen ba'a rufa sati biyu is anyi sabon sari an aika idan suka aiko da cinikin da akayi ta hannun Qanin Hayatu Mijin Bilki da yake jan motar kaya yanzun.

Tareda Yakubu suke fita kasuwa, tuni kuma an tayar da ginin filin da Audu ya siya a nan Goron dutse inda yake zama, filin nada girma babu laifi dan haka aka rabashi biyu shida Yakubu kamar yanda daman ya tsara. Gini aka tada daki ciki da falo kowanne se safaya guda daya da kuma kitchen da bandaki ginin bulo, idan ka shigo soron gidan daya ne sannan zaka tarar da qofofi guda biyu na shiga kowanne bangare. Yakubu ya dage akan Audu ya maida hankali gurin gyara nasa bangaren dan shi fa bega abinda ze rabo shi da Bechi ba, koda ya fara Karatu ze ringa tafiya duk hutu irin yanda ya ringayi lokacin yana makarantar kwana dan baze yuwu su tattaro su dawo Kano su bar Dada ita kadai a can ba ko bayan haka sam shi bashida sha'aqar zaman Kano ma baki daya haka dai aka ci gaba da rarrafa rayuwa watansu uku a Kano kafin sukaje ganin Matansu niqi niqi da abin Arziqi dan a watannin ba qaramin Alkhairi aka samu da kudin da aka juya ba ga can Shago da Sana'ar Bilki ma se sambarka.

Sun tarar da matansu da Dadarsu lafiya sumul ga qarin abin farin ciki Balaraba nada shigar ciki, wannan abu yayi wa kowa dadi, satin Audu biyu ya koma ya bar Yakubu dayace seya qara hutawa shi kuwa daya baro dukiya be bar me juya masa ba dole ya koma, kwanansa biyu da komawar shima saqo ya riskeshi wanda yakeyiwa Yakubu cuku cukun samun gurbin karatu ya aiko masa da cewar an samu dan haka Yakubu ya shirya ya tafi Domin har Samista ta fara nisa acan makarantar dole Audu ya juya Bechi. Dan qaramin yaqi sukayi da Yakubu sanda Audu ya gama wassafa masa abinda yake faruwa. Ya rasa me zeyi, ashe wai Audu can Jami'ar Ikko ya nemawa Yakubu gurbin karatun Shari'a ta hannun Tsohon Abokinsu na Magashi wato Hayatu duk a tunanin Yakubu anan kwalejin Shari'a da aka bude a Kano ze nemar masa Gurbin ashe shine dalilin daya sa be gaya masa komai ba akan zancen makarantar.

Yakubu yace ba zeje ba, ya za'ayi ma ya tsallake ya tafi har Kudu da sunan karatu? Idan jami'ar ce baga ta nan a Zari'a ba tunda ta kano basu fara karatun shari'a ba a sannan ko ba wannan bama shi karatun Jami'a ya masa girma a lokacin baze iya ba, seda Dada tayi masa wuji wuji sanna ya haqura.
"Me yasa Yakubu duk qoqarin da dan uwanka yake akanka baka gani ko da yaushe cikin gwasaleshi kakeyi? So kakeyi kuma ku zama kamar su ace babi jituwa bazaku hada kai da baki shawararku ta zama daya ba? Idan kuna haka suma qannenku abinda zasu dauka kenan ni kuwa fatana ko bayan raina ace duk abinda zaku zartar a tsakaninku se kun shawarci juna kuma babu babba ko yaro in har daya ya bada shaqara me kyau da zata amfane ku ku karba ku zartar amma gashi kai da kake babba kai ne duk abinda aka kawo se kayi Adawa da hakan bana so bana jin dadi ka dena hakan" Dada ta fada masa.

Yakubu yayi shiru, har ga Allah baya jin dadin yanda Dadan take goyon bayan duk wani hukunci da Audu yake zartarwa dukda dai ba abu mara kyau yakeyi ba amma yin hakan ze saka ya dauka cewar komai yayi daidai ne ba kuma ze ringa duba muraden waninsa ba in har abinda zuciyarsa ta raya masa kawai shine daidai. A komai na rayuwa shawara nada kyau amma ya za'ayi ya ringa zartar musu da hukunci kamar wasu Yayansa ai ko Baballiya beci ace Audu ya turashi wani gari can karatu ba tareda son ransa ba balle shi da girmansa harda iyali ya ajiye ayi masa wannan abun yanzu haka ze tattara ya tafi ya bar yar mutane har tsayin wane lokaci ze dauka kafin yazo? Nan da Kano ma suna daukar watanni inaga Ikko da tafiyar kwanaki ce kafin kaje, anan cikin qauyensu da akwai Abokanansu biyu da suka tafi neman Arziqi shekara uku kenan zuwansu daya gida kuma sun basu labarin yanda Kudu take tayaya ma ze iya zama a can fisabilillahi amma ya ya iya? Yanda ran Dada ya baci yasan ko yayi mata bayani ba lallai ta fuskanta a fuskar salama ba.

Haka ya fara shirin tafiyar jiki a salube danma Balaraba ta dage da qarfafa masa guiwa tana gaya masa duk saboda ita da abinda zata haifa zeyi wata rana kuma komai ze zama labari a sannu idan yaje garin ma ya gane kan komai zasu iya tafiya tare dan ita akwai Yayanta da yake kai Shanu can Kudun saboda yawan zuwan da yakeyi ya kai matarsa daya can take zaune wannan yasa hankalinsa ya dan kwanta amma idan ya tuna ze tafi ya barta da ciki qila har se abinda zata haifa ya fara zama ko rarrafe ze zo ya ganshi duk se yaji abin ya qara fita a kansa. Haka ya shirya, duk wani abu da ze iya nema na dangin abincin da ba lallai ya samu can ba Dada da Balaraba sun hada masa. Harda dambun nama Dada tayi masa, gasu Yaji, quli quli harda Alkaki Audu ya ringa dariya wai kamar me tafiya qasar waje. Randa zasu tafi Kano Balaraba ta kasa daurewa ta ringa kuka duk ta qara sanyaya masa jiki dakyar ya iya tafiya Goggo Fadi da yan fadarta suka ringa yadawa Dada magana wai ta watsa yara sun tafi Bariki ga Yaran mutane sun auro sun ajiye wannan ai ba daidai bane iya dai bata kulasu ba suka gama jajanta tafiyar su Audun kafin kowa ya dauki dangana sukaci gaba da rayuwa yanda suka saba.

Audu kuwa seda ya raka Yakubu har Ikko, tafiya ce kamar ta yada shege musamman su da basu taba zuwa ba a hakan ma wai dan mota me kyau suka hau basu bi motar Arha wadda ake loda mutane ba. Satinsa daya ya juyo bayan Yakubu ya samu gurin zama ya gama duk wasu abubuwa har ya fara shiga aji. A dan tsukin Seda Audu ya leqa kasuwa ya gano sabgogin arziqi aiko ya qyarawa Yakubu da zarar ya gama gane kan gari ya shiga kasuwar Hayatu ze taimaka masa ya dubo musu abubuwan da ake buqata a Arewa da suke sauqi acan.

Ya dawo Kano cike da kewar Dan uwansa ya kuma cigaba da kasuwancinsa ka'in da na'in, sabanin da da yake share watanni yanzu wata biyu yakeyi yaje Bechi wani lokacin ma wata daya da kadan zeje ya kwana uku ko hudu ya juyo haka ze musu siyayya kuma ya hada harda yan uwansa dukda barakar da suka samu be fasa yi musu ba suma kuma babu kunya basu qi karba ba. Balaraba nata rainon cikinta daya fito sosai yana wata na bakwai sannan. Ba yanda Audu beyi akan suje Kumbotso Asibiti ba tunda su nan babu amma Dada taqi a cewarta Ahalinsu kaf babu wadda ta taba zuwa wani Asibiti kuma lafiya lau suke rainon ciki su haihu duk wani taimako kuma daya kamata tana bawa Balaraban shima zaman Birni yasa har yake wani zancen Asibiti banda ha???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ka a garin kaf wayaga tana zuwa wani Asibiti banda Matar Shafi'i Hedimastan primary su Baballiya da aka bude.

Har fushi yayi amma Dada taqi saurararsa, ya samu Balaraban akan ta shirya a sace ze kaita dan shi fa ya daukarwa Yakubu Alqawarin kula masa da iyalinsa ba kuma yason kowanne tsautsayi ya gifta wani abu ya same su ma se Balaraba tayi dariya tace
"Bana jin komai Yaya Audu lafiyata qalau kamar yanda Dada ta fada in sha Allahu zan haihu lafiya base munje Asibiti ba daga can Rugar mu ma Innata tana yomun aiken saiwoyi babu wata damuwa da yardar Allah".

Badan yaso ba ya barta, watan Haihuwar Balaraba na tsayawa ya dawo Bechi yanda kasan shi za'ayiwa Haihuwar, kwanan sa biyu da dawowa Balaraba ta fara Naquda cikin dare har garin Allah ya waye bata haihu ba duk irin taimakon da Dada da Goggo Fadi tareda Unguwar zoman da suka kirawo suka baya amma abu ya gagara, haka ta sake wuni sur cikin ciwo kuma abin takaici sun hana akaita Asibiti acewarsu dama haihuwar fari akan dade, hankalin Audu ya tashi ganin har duhun Magriba ya fara kawo kai amma Balarana shiru zuwa sannan kuwa ko baa fada ba ka kalleta kasan qarfinta ya fara qarewa. Beyi shawara da kowa ba ya fita neman motar da zata kaisu Kumbotso, duk masu motocin daukar kaya na garin abin takaici kamar hadin baki duk gurin wanda yaje ae yace masa bashi da Mai yau ko aiki be fota ba.

Har gurin Alhaji Magaji yaje wanda a lokacin shi kadai yake da motar hawa a garin amma be samu alfarmar ya taimaka masa su kai Balaraban Asibiti ba ga duhu yayi dan tuni anyi magriba Isha ake shirin yi. Zuciyarsa ta quntata ya rasa abinda zeyi, be taba jin burin mallakar abin hawa na irin na wannan dare. Hankalinsa be qara tashi ba seda Bara'atu ta fito tana kuka hankali a mugun tashe take sanar masa Jikin Balaraban ya qara rikicewa har ta fara zubda jini gasu Dada can duk sun rude suna salati. Suna tsaye nan cikin rashin mafita kamar daga sama sega Kasim, Abokinsa ne amma irin wanda alaqar bata da qarfi sosai. Audu ya sauke ajiyar zuciya yana yiwa ubangiji godiya daya kawo masa Kasim din. Alfarmar Baburinsa ya nema ya bashi haka aka cocciba Balaraba da sam bata cikin hayyacinta Dada ta hau bayanta suka sakata a tsakiya suka tafi Kumbotso aiko wannan abu ya qara hura wutar gori Goggo Fadi ta ringa masifa tana fadar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login