Showing 291001 words to 294000 words out of 467220 words

Chapter 98 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12215

a baya suka isa falon. Yana zaune a ?asa Binta na gabansa ta du?a kamar tana masa raWa suka shiga tana ganinsu ta fara washe baki tana cewa

"Ikon Allah, ana zancenku se gaku. Yanzu nake so na tashi na samu me kaini na gano ?afafu sun sakani gaba tunda akayi haihuwar nan nake cewa zanzo Allah be nufa ba se gaku to maraba lale, bari na gani wacce ce tayi Shirin kwace mun miji na korata waje wadda zata gidan Yakubu kuma itace ?awata. Babu wanda ya kula wasan nata kowa ya nemi gurin zama Fatima dai can bakin ?ofa ta lafe domin bata manta karonsu sa Hajiyar ba, harga Allah tsoron ta takeji irin tsoron da akeyi wa mahaukaci me duka.

Hajiya bata ha?ura ba ta matsa gaban Momy zata karSi babyn hannunta se Momyn ta maze tamkar bata gane me take nufi ba ta tashi ta bawa Alhaji Audu ita ya karSa da Bismillah se itama Hajiiya Rabi tayi saurin mi?a masa ta hannunta ya haWasu biyun.

"Lallai jini ba ?arya ba, kagansu tamkar Yayunku suna jarirai manya dasu masha Allah, fuskokinsu kuma kaga kamar ?an uwanka lallai ka biya tukuicin ?auna" Alhajin ya faWa yana kallon yaran, Hajiya tayi zuruf tace

"Dani suke kama kenan?"
"Da Jafar dai, ke kuma a wa zasuyi kama dake Binta?" Alhajin ya gatsa mata magana yanda ta buWe baki fuskarta ta tattare alamun bala'i taso ta kafa wani abun ya tokareta duk ya basu dariya seda suka murmusa. Alhajin ya kalli Fatima yace
"Sannu Fatima, Allah ya Wayyaba" Mony da Hajiya Rabi suka amsa da Amin banda Hajiya dake kokawa da Sacin rai kamar wadda ta haWiyi kunama, lallai Audu yaga makwancinta amma zatayi maganinsa akwai Shirin da takeyi.

"Yaya sunayensu ko bakayi musu huWu ba ba?" Alhajin ya sake tambayar Ahmad, zeyi magana se ga Jafar yayi sallama ya shigo fuskar nan a haWe kamar haya?i,
"Eh daman bari nayi se munzo kayi musu" Ahmad ya bashi amsa Alhajin cikin faWa yace
"Har kwana biyar me kake jira da bakayiwa yayanka huWu ba ba? Idan kai ba zakayi ba baga Wan uwanka a kusa ba se ku bar yara babu suna to me kuke ce mus"

"Haba Alhaji, kai da aka girmama aka kawowa ai se ka amsa kayi meye na faWan" Hajiya Rabi ta shiga maganar, Binta dai se harara, bata so ta sake magana ya kuma dizgata a gaban Kishiyoyi da shegiyar yarinyar data tsana. Yarinya se kyau kamar Aljana, ta haihun ma amma jegon tamkar ?ara gyarata yayi tayi fresh.

"Mi?awa Jafar yaran Alhajin yayi yace
"Kai yi musu huWu ba bana son shashanci" ya karSi babbar yayi mata seya mi?awa Alhajin yana cewa
"Takwarar Momy ce"
"Toh wannan se kayiwa uwarka takwara" Alhajin ya faWa yana mi?a masa Wayar, Momy, Hajiya Rabi harda Fatima suka zaro idanu lokaci guda jin abinda Alhajin yace ayiwa Binta takwara? Yo mutane na takwara ne domin tabarakin kyawawan halayen me sunan wane wanda yasan ciwon kansa ne zeyiwa Binta takwara bayan ko yayanta kaf Nazira ce take da Binta itama Mijin ne yayi mata kara amma ko Matar Yakubu data haihu baya baya Hajiyar da kanta tace ya saka sunanta yace mata toh, ranar suna se tayi an raWa Aisha. Ta ringa tsine tsine kuwa harda kwato ghana must go data kai ta kayan takwara.

Murmushi Hajiya Binta ta saki harda gyara zama tana kallonsu Wai-Wai irin lokacin ramuwa yazo, Jafar ya kalli Ahmad daya sunkuyar da kai kafin ya shigayiwa yar huWuba kamar yanda Alhaji yayi umarni


Wash hannuna, toh Allah ya raya Binta yasa ta kwaso halayen kirkin takwara idan da akwai =?(?=?(?=?(?=?(?

"The moment you've all been waiting for has finally arrived! Our Milk Cake Masterclass is here! Don't miss out on the opportunity to learn the art of creating the perfect milk cake from Mcubes Bakery.

This is a money back guarantee class! We will not let you go till you are satisfied with the class. The milkcake that make a statement...99.9% positive review...no fails. Get into the milk game with the best milkcake in kano WE ARE READY TO TAKE YOU ON THE BEST EXPERIENCE <؉?=?O?

Ina masu son su koya perfect milk cake koh kuma suyi upgrading recipe dinsu toh kuzo kuyi joining class din mu yanzu! It s money return granteee! Improve your business now by joining us!
Ga promo kuma
15k early bird !
20k Reg Fee!

Limited spots available, DM to reserve yours.
http://Wa.me/2348134606093

Group enter the link below +?

 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/BAY5WE5skLg0N9rf8x3gcW

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 11*

Alhajin ya sake mayarwa da yarinyar kansa a ?asa yace
"Ga Bara'atu"
"Jafaru, a gidan uwarka sunana ya koma Bara'atu? Meye ma hakan na shuga uku ni Binta a ina ka samo wannan sunan kuma?" Hajiya data mi?e da sauri kammar wadda ta zauna akan kunama ta shiga taratsi tana tafa hannaye, ta juya kan Momy tana cewa
"Aisha tayani ganin ikon Allah, kai yau ni Binta naga lukutar masifa Jafaru kanka ?alau kuwa?"
"Ai yayi kara matu?a da hakane ma babbar ya kamata a sakawa Bara'atun tunda duk gaba take damu a gidan nan gaskiya ka kyauta Jafar" Momy ta faWa hankalinta kwance tana murmushi, Bara'atun ma ita sunan Babbar Yayar sune mace me karamci da tsananin ha?uri dan haka ita sunan ya mata daidai.

A fusace Binta ta juya kan Alhaji ganin Aisha ya manna mata hauka tace
"Baka ce komai ba, kana ganin rashin mutunchin da aka mun"

"Allah ya rayata yasa ta gaji ha?uri da kawaici irin na me sunan" Alhajin daya kafe Jafar da ido tunda ya ambaci sunan yarinyar be ko dubi Bintan ba ya faWa bayan daya sauke ajiyar zuciya, rai fes Momy ta sake amsawa da Amin Hajiya Rabi ta tayata Ahmad dai kansa na ?asa yana murmushi, tamkar Jafar Win ya shiga ransa. Yana ta jinjina abin a ransa yana so yayiwa mahaifiyar su Alhaji Babangida takwara dalilin irin labarin zamanta a gidansu daya samu a bakin Baba Bilki, yana da buruka a ransa na ganin kan zuri'arsu ya haWe abinda yasa beyi gaggawar aikata hakan ba gani yayi kar ya zamana yayi rashin Adalci ace Fatima ta haifi yara biyu mata be saka mata sunan mahaifiyarta ba seya bari akan idan Allah ya sake basu wata macen ze saka mata Bara'atu toh yanzu gashi Jafar ya aiwatar da tunaninsa. Gurin da Fatima take zaune ya kalla, so yakeyi yaga yanayin fuskarta akan wannan hukuncin dan basuyi shawarar sunan da za'a saka musu ba, tu kafin ta haihu yace mata Alhaji ze bawa zaSi bata sake tayar da maganar ba. Murmushi ta sakar masa sanda suka haWa ido, ya lumshe nasa idon kafin ya furta mata I love you ba tareda sautin maganar ya fito ba itama ta mayar masa seya maida kai ?asa yana murmushi tareda sauraron Hajiya dake tilawar rashin mutunchi ta inda take shiga bata nan take fita ba wanda takeyi dasu Win kuma daga Alhajin har Jafar babu wanda ya nuna alamar yana sauraron abinda take cewa.

"Wannan masifa har ina? Mata ta mutu amma ban huta ba se yaushe Bara'atu zata barni na sha?i iska me daWi a duniyar nan ace a rasa wanda zeyi mun wannan tozarcin se kai Jafaru?" Hajiya ta faWa tana rushewa da kuka taci gaba da cewa
"To billahillazi se dai ka bita kushewa can ku ?arata, kuma kowa ya shirya a gidannan se an sanni aka wula?anta bazan yarda ba, badai Bara'atu ba? Yanda ta ta rayu ta mutu a ?as?ance itama haka zata bi mu zuba mu gani" fuuuu kamar iska ta kwashi jiki zata bar gurin Momy tayi saurin matsawa ta kwashe yaran daga cinyar Alhajin ganin Bintan na neman yin tafiyar yaji dasu tana cewa
"Alkhairi da haske na dabaibaye da rayuwarsu da yardar Allah mugun ido ko baki baze yi tasiri akansu ba ta wuce dasu Hajiya Rabi ta mara mata baya Fatima ma ta bisu a ranta tana jinjina Al'amarin Hajiya Binta".

Shiru ya ratsa falon kafin muryar Alhaji ta katsesu yana kallon Jafar yace
"Kaje gidan gona a Wauki shanu guda biyu ayi musu ?auri sannan a Webi raguna huWu kowacce a yanka mata biyu" sun gode, Allah ya ?ara girma" Jafar Win ya faWa yana mi?ewa kamar daman akan ?aya yake zaune Ahmad mya rufa masa baya suka fita bayan da yayiwa Alhajin godiya.

"Me yasa zakayi haka, sunan Hajiya fa yace a saka kayi gaban kanka?" Ahmad ya faWa bayan da suka shiga mota, kallonsa Jafar Win yayi yana murmushi yace
"Kawai ji nayi hakan ya kamata Shikansa Alhajin seya fi jin daWi akan sunan Hajiyar. Amma wai wacece ma Bara'atun? Nifa a bakinsa nake jin sunan shiyasa kawai na saka mata"

"Are you serious baka ma san ko wacece ita ba kawai ka sakawa yar mu sunanta?* Ahmad ya faWa yana kallonsa da mamaki, cikin yanayi na rashin damuwa Jafar yace
"Ban santa ba, kawai ina yawan jinsa yana kiran sunanta, i felt like ko wata tsohuwar soyayyar sa ce da yake missing, kasan ni kuma i do respect lost love, shiyasa kawai nayi tunanin idan yana ganin wata me irin sunanta ze samu relief tunda ni nasan ba zaka yarda kayima tawa Soyayyar takwara ba" ya ?arasa maganar idanunsa suna canza kala.

"Ikon Allah, toh sannu Wan gado. Bara'atu sunan mahaifiyar su Yaya Babangida da Yaya Babannan ne, ita ce matar Alhaji ta farko kuma first love Winsa" Ahmad yayi masa bayani, ya taSe baki irin bawai abin ya dameshi ba kafin yace

"Ban sani ba ai, amma dai yana sonta sosai fa saboda na kamashi lokaci babu Adadi da picture a hannunshi yana kiran sunanta"

"Hmm" kawai Ahmad yace dan shi yasan komi akan labarin zaman Hajiya Binta da Bara'atun a bakin Baba Bilki dama sauran matan Alhajin anan ya gane cewar matsalar gidansu ba ?arama bace ba kuma ba zatayi saurin gyaruwa ba kamar yanda yake hasashe a baya, ashe rayuwar da suka tashi suka gani ba komi bace illa Waurayar abinda ya faru a baya. Idan yaga Hajiya Binta yanzu kallon mamaki da tausayi yakeyi mata, a ransa yana mata fatan ta shiryu ta gane kura kurenta na baya kuma ta gyara su, baya mata fatan ta koma ga Allah da tarin ha??o?in mutanen data zalunta.

"Bari naje, akwai sa?on da zan amso a Airport" Jafar ya katse masa shirun da yayi se ya saki ajiyar zuciya yana kallonsa yace

"Yawwa that reminds me, yaushe zakaje ka maido da matarka?"
"Nace ta tafi ne?" Ya bashi amsa yana barin wajen. Ahmad ya bi bayansa da sauri yana cewa
"Wai kai meyake damunka? Da farko ma meya sake dawo da waccen yarinyar rayuwarka ba kace tayi aure ba akan me zata ringa kiranka cikin dare?"

Tsayawa yayi kamar ze bashi amsa se kuma ya juya kawai ya tafi, Ahmad ya bishi da kallo, tun bayan auransu da ya koma Europe rayuwar sa ta fara daidaita shine yanzu zata sake dawowa ta lalata komi. Ajiyar zuciya yana kallonsa harya fice daga gidan cikin motarsa kafin ya shiga takawa a hankali ya koma gurin Momy.

HAJIYA BINTA
Tamkar me na?udar da aka sakawa ruwan tayar da ciwo ya wuce ?a'ida haka ta ringa safa da marwa cikin Wakinta ri?e da waya, tayiwa Turai kira yafi saba'in yana shiga amma bata amsawa. Wula?anci da tozarcin da akayi mata yau ba kaWan bane tilas kuma ta Wauki mataki, baya ga laifin Jafar ba akan abinda yayi domin tasan ba a hayyacinsa yake ba kuma wannan ne babban abinda ya tayar mata sa hankali ta yanda tayi sakaci har akaci galaba akan Jafar Win, ?an da duk wani burinta da tanadinta yake a kansa sedai kuma sam al'amura basa tafiyar mata a yanda ta tsara akanshin ta rasa a ina matsalar take? gashi yanzu tana kallo an shammaceta ana kuma neman a kaita ?asa ta sanadiyyarsa. Turai ce Abokiyar kukanta, ita ce kuma wadda zata lalubo mata mafita gashi yanzu tana nemanta amma ta gagara samunta koda yake laifinta ne, kamar yanda suke da Turai ace ta kasa yi mata uzuri a dalilin ankon data musu da kishiyoyinta lokacin bikin su Jafar Win haka ta kasa ha?uri bayan tijarar da tayiwa Turan a nan gidan seda ta bita har gidanta tayi mata rashin mutunchin da kashedin babu ita babu ita kuma ko mutuwa taji tayi tazo kan gawarta bata yafe, ba zagin cin mutunchin da batayi mata ba ita a sannan ko tunanin irin tarin sirrikanta da Turan ta sani bata kawo abinda tayi mata ze saka ta fitar dasu ba oho ta daiyi bankaurarta ta gama tun sannan kuma ko a waya Turai bata sake nemanta ba balle ta tako inda take tsayin shekara guda kenan da motsi se gashi amfaninta ya taso mata bagatatan.

"The moment you've all been waiting for has finally arrived! Our Milk Cake Masterclass is here! Don't miss out on the opportunity to learn the art of creating the perfect milk cake from Mcubes Bakery.

This is a money back guarantee class! We will not let you go till you are satisfied with the class. The milkcake that make a statement...99.9% positive review...no fails. Get into the milk game with the best milkcake in kano WE ARE READY TO TAKE YOU ON THE BEST EXPERIENCE <؉?=?O?

Ina masu son su koya perfect milk cake koh kuma suyi upgrading recipe dinsu toh kuzo kuyi joining class din mu yanzu! It s money return granteee! Improve your business now by joining us!
Ga promo kuma
15k early bird !
20k Reg Fee!

Limited spots available, DM to reserve yours.
http://Wa.me/2348134606093

Group enter the link below +?

 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/BAY5WE5skLg0N9rf8x3gcW

Da taga kiran wayar baze yuwu ba se kawai ta shige Waki ta yafo gyale tana share hawaye kamar yarinya ta fita tsakar gida tana neman direban da ze kaita gidan Hajiya Turai, tana tsaye Ahmad da Fatima suka fito suma Sarah da Maimuna na biye dasu Wauke da yaran, tamkar idonta ze cire ya faWo ?asa haka ta ringa bin Fatiman da wani kallo me cike da tsana kafin ta juya kan Sarah cikin hargagi kamar zata tsinke harshenta take ce mata
"Dan Abu ta kazan ubanki ina zakije? Zaki yarda wannan abin na hannunki ko sena ci*****"

Caaaa ma'aikatan dake zirga zirga sukayi mata da ido dukda dai ba sabon abu bane halin Hajiyar amma na yau ya basu mamaki. Ahmad ya saka hannu ya karSi yarinyar daga hannun Sarah da har idonta ya tara ?walla, muryarta na rawarkuka tace
"Dan Allah yaya ku jirani, fita zatayi suna tafiya zan fito mu tafi muma" murmushi yayi mata ya wuce gaba Fatima da jikinta yake rawa tabi bayansa Maimuna kam ko a jikinta domin kata'in Hajiya tamkar shan maganin bature yake a gurinsu, Safe Rana dare babu bashi se sun sha shi. Seda ta tabbatar sun bar gidan kafin ta shiga mota tana zazzagawa direba masifa suka tafi gidan Turai kusan minti goma bayan da. Ahmad ya tabbatar da tayi nisa a hanya kafin ya juyo suka Wauki Sarah da har ta cire ran tafiya tare dasu. Daman tasan Hajiyar ba zata yarda ba shiyasa bata ma faWa mata zata bisu ba bari tayi sedai ta nemeta ta rasa idan se an gama shagalin suna zata dawo tasan zata sha masifa dai da zagi amma yafi mata akan ba?in cikin da zata kwasha idan Hajiyar tace zata hanata zuwa sunan twins Win Yah Ahmad.

Bayan dogon ban baki da ban ha?uri harda dur?uso da neman gafara kafin Turai ta saurari Binta, duk kiran da tayi mata tana gani bata amsa ba saboda abinda Binta tayi mata ko a mafarki bata taSa zaton ze faru ba, bayan kuma duk wannan uban tijarar rashin mutunchin babu kunya yanzu da damuwarta ta matsota shine ta kwashi ?afa taje gidanta Binta kenan me abin mamaki. Sun tattauna, kafin tace mata ta shirya kawai ta saka rana suje gidan Sabon Malam data samu duk wata damuwarta ze yaye mata kartaji komai, akan haka suka rabu bayan kwana biyu zasuje gidan Malamin da ko musu batayi akan zuwan ba tunda dai kissar da take ta?ama da ita yanzu bata aiki idan kuma tace zata tsaya kallonruwa toh tabbas kwaWo zeyi mata ?afa.

*********
Lafiya lau akasha taron sunan Aisha da Bara'atu wanda akayiwa la?abi da Layla da Nayla, ansha bidiri Mejego da babies Winta sun zuba kyau, Yan uwa da Abokanan arzi?i daga garuruwa sun halarci taron sun kuma tayasu murna tareda kyaututtukan da bazasu ?idayu ba, yara sun shaida su yan gatane dan iyakar bajintar da Jafar yayi a uban kayan barka daya yi musu kamar za'a buWe shago, harda Wannkunne da abin hannu na gold da wani dutse me kama da diamond a jiki se tarkacen kayan wasa danginsu mota da sauran tarkacen kayan wasa Waki guda suka cika da kayan Barkar Jafar wanda ko tsinke be burge Fatiman daga ciki ba dan har seda Ahmad ya nuna rashin jin daWinsa kafin tayiwa Jafar Win godiya.

Yayan gidansu Ahmad matan duka sun halarci taron sunan haka matayen wasu daga cikin mazan bayan Matar Sarki da suke Waki Waya matar Dr Hassan taje, se Matar Yakubu dukda irin takarar da Hajiya tayi masa be bi takai ba dakansa ma ya kaita har yayi hoto da yaran ya saka a status se Matar Aminu. Matar Alhaji Babangida da yaranta dai sunje musu barka shima kuma ya kirashi a waya Aliyu kuma ya bashi uzurin matarshi ta tafi Umarah shidai sun gaisa har kuWi ya aika masa yace a siyawa babies riga su Alhaji Hussaini kuwa ko message Win daya aika masa na sanarwar haihuwar beyi tsammanin ya buWe ba haka Alhaji Babannan wanda se daga baya daya samu labarin abin kirkin da aka musu kuma se gashi ya kirashi a waya, kwana biyu tsakani ya zo shida matarsa da abin arzi'?i ni?i ni?i sukayi barka, kusan silar ?ulluwar zumunchi tsakaninsa da Ahmad kenan.

Dama be tsammacin ganin wani daga gidan Naziru ko Zakariyyah ba balle ita uwar gayyar Hajiya da kamar zata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login