Showing 330001 words to 333000 words out of 467220 words

Chapter 111 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12152

da Sarki yakeyi mata akan tazo su tafi ba. Jafar dakw tsaye bayan sun gama daidaita zaman akwatin ya juya ya kalleta, yanda take tsayen tana kallon motar cikin fitar hayyaci ya matu?ar taSa zuciyarsa.

Acan gidan Alhaji Audu kuwa mutane ne kota ina babu masaka tsinke tun daga waje gurin maza har zuwa cikin gida. FaWar irin halin tashin hankali da Ahalin tareda makusantansu suka shiga Sata lokaci ne. Sanda labarin mutuwar ya isa gidan Momy na falon Alhaji Audu taje ta sameshi akan tana so ta bisu hankalinta ya kasa kwanciya da irin sau?in da ake cewa Ahmad Win yana samu ita sam jikinta baya bata haka. Suna tsaka da magana Alhaji Abdullahi ya kirashi shi kuma Dr Hassan ne daya rasa waze fara gayawa seya kira Alh Abdullahi.

Alhajin na fara salati ta mi?e tana cewa
"Shikenan, ni daman naji a jikina ba baccin tashi yakeyi Wazun ba, Allah ya karSi ba?uncinka Ahmad annabi ya san da zuwan ka, na yafe maka duniya da lahira" ta fashe da kukan daya janyo hankalin jama'ar gidan babu wanda ma ya tsaya tambayar menene domin dai sun san mutuwa ce kawai zata saka Momyn irin wannan kukan kafin wani lokaci zancen ya karaWe ko ina dangi na kusa da nesa sun samu labari, yanda mutuwar ta dake su tamkar mutuwar fuji'a bawai mutuwar majinyacin da daman ana saka masa ran tashi ko tafiya ba. Tun ranar kuma gidan ya fara cika da mutane, ?arfe huWu akayi sanarwar jana'izar ranar litinin amma tun goman safe duk girman farfajiyar gidan ta cika taf da jama'a dole aka s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ake Webo rumfuna da tabarmi aka zuba a waje haka cikin gidan mata ta ko ina ba masaka tsinke.

Hajiya Binta na tsaye a babban kitchen muryarta har tsakar gida saboda shirun da akayi kowa na jiyo sababin da takeyi akan abinci,
"Ba seda nace a raba naman biyu na shine kika juye duka? To wlh kinja musu sedai uban kowa ya ci lami gobe" karaf kwacacam ta ringa hada kwanuka tana gwarawa tana masifa.

"Ai se ku fara zuzzubawa, ku ware na Alhaji da manyan ba?in sa sauran a zuzzuba mutum huWu roba Waya, ke kuma dauki wannan ki kai Wakina" ta nunawa Safiya ?atuwar robar data cika da miya dukta kwashe naman ta jibga a ciki.

Kafatanin yan uwanta da yayayen su, surukanta da ?awayenta duk suna zaune a falon jigum jigum wasu na lazumi wasu sunyi shiru cike da jimami wannan babbaan rashi da sukayi, mutum na mutane. Suna zaune shiru Safiya ta shiga da uwar kula ta dire a gaban su, kafin ma ta matsa Hajiya Ummu na kallonta tace

"Meye wannan?"
"Miya ce Hajiya tace a kawo yanzu za'a mi?o shinkafar" ta bata amsa. A mugun fusace Munira tace
"Fita da ita kafin zuciya ta Webe ni na danna fuskarki a ciki" jiki na rawa ta Wauke kular kuwa ta fice suka ci karo da Binta dake shigowa da kwanon salak ta ce
"Ke ina zaki kai miyar"

"Yanzu Binta banda tsabar rashin hankali da rashin imani ana wannan yanayin ko kawo gawar yaro ba'ayi ba amma ke ta abinci kike? Idan mutuwar Ahmad bata zamar miki ishara ba Binta ke kuwa a duniya meye ze saka ki shiga hankalinki?" Hajiya Salima ta faWa tana share hawaye, Binta ta taSe baki tace

"To tun sha biyu aka ce zasu iso gashi ana neman ?arfe biyu ayi ta zama jungum jungum ciki ba komai ai gara aci a samu ?arfin yin kuka idan an kawo gawar ko?".

Saboda takaici babu wanda ya sake tanka mata a cikinsu, baban ?arin ba?in cikin duk maganar da takeyi ana jiyota daga waje. Cewa Safiyar tayi
"Shigar mun da ita Waki kinji duk su gama munafuncinsu nan da anjima zasu nemi abincin, yo Allah na tuba tunda ubana ya mutu na iya cin abinci jimamin uban waye ze hanani, to gasu nan ma sun iso ga ?arar ambulance nan gara azo ayi abinda za'ayi a dena saka jama'a asarar hawaye haka" ta faWa daidai sanda ?arar jiniyar motar Asibiti ta kusanto gidan.

Hankulan Ahalin TIJJANI BECHI ya tashi, ta faru ta ?are magana dai ta tabbata Ahmad ya rasu kuma gawarsa ta iso gida. Dukda yawan jama'ar dake waje da cikin gidan seda aka buWe hanyar da motar da Fatiman take ciki ta isa har bakin ?aramar kofar shiga ainihin gidan ita kuma motar gawar ta tsaya a ?ofar falon Alhaji Audu, da sauri Jafar ya kukkutsa cikin mutane ya isa inda take tsaye ta kasa motsawa kamar ma bata ganin gabanta saboda Hijabin data ja ta rufe fuskarta gaba Waya. A hankali yace ta biyoshi, yana gaba tana binsa a hankali suka shiga.

Ganin su biyu ya taso da ainihin alhinin dake cin zuciyoyin zuri'ar nan aka fara koke koken gaske domin wanda sukayi a kwanaki biyun na wasa ne, Jafar be barta ba seda ya kaita har cikin Wakin Momy inda take kwance da ledar ?arin ruwa a hannunta, tana ganin Fatiman da Jafar ta sake fashewa da kukan da da?yar aka rarrasheta ta denayinsa saboda jininta daya hau ya?i sauka, kukan Momyn ya maida mata da nata mikin sabo itama ta dur?ushe a inda take ta fashe da kukan daya karya zukatan duk wanda suke zaune a Wakin kowacce ta shiga nuna tata kwarewar gurin rera kuka.

A can falon Alhaji Audu kuwa babu Sata lokaci aka shiga wanke gawar bayan Baba Al?ali ya umarci Dr Hassan daya dubashi ya tabbatar da komai na jikinsa yana nan yanda yake yana kuka ya cajeshi babu wani yanka ko Winki a jikinsa da ze nuna alamar an cire wani abu me amfani daga jikin nasa.

Seda aka shirya shi tsaf kafin Baba Al?ali da kansa ya hau sama ya kira Alhaji Audu. Yana zaune akan gado ya rafka tagumi da hannaye biyu ya zubawa bango ido, bema ji motsin Al?alin ba seda ya taSa shi yayi firgigit se kuma ya shiga muzurai. Al?ali Yakubu yayi murmushi yana kallonsa yace
"Audu, ina jiye maka kar zuciyarka ta gajiya da dakon nauyin da kake Wora mata tayi bindiga ta fashe. Ka taso an gama haWashi saura befi minti sha biyar a kira sallah ba kuma ya kamata a baiwa yan uwansa mata damar ganinsa kafin a fita dashi" yana gama faWa masa haka ya juya yana goge ?walla.

Alhaji Audu kuwa tamkar ya caka masa mashi a ?irjin haka yaji maganar an gama haWashin, numfashinsa na sama yana ?asa, kusan minti goma yana zaune kafin ya lallaSa ya Wora babbar rigar kayan da suke jikinsa ya saka hula sannan ya Wakko wani ba?in gilashinsa na ciwon ido, yakan daWe beyi amfani dashi ba idan ba ze shiga rana me haske sosai ba. Seda ya daidaita kansa da kyau kafin ya sauka ?asan yana tafiya a hankali kamar me tausayin ?asa.

Idanunsa ?ur akan gawar Ahmad da ba'a rigada an rufe masa fuska ba sun dai toshe kunnuwansa da ?ofofin hanci da auduga, wani sanyi yaji ya taho masa tun daga tsakiyar kai ya dire akan ?afafunsa, Momy, Fatima, Hajiya Binta da Hajiya Rabi, Hajiya Balaraba se Baba Bilki da Anty Maimuna data rako Momy da kuma kafatanin yayan gidan maza da mata harda Alhaji Zakariyya duk suna gurin, a jikin ?ofar shiga cikin gida ya hangi Jafar ya basu baya, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi kafin ya ?arasa kan gawar hannayensa na rawa ba tareda tunanin komai ba ya Wagoshi gaba Waya ya rungumeshi a jikinsa yana cewa

"Ban taSa rungumarka da girmanka a sanda kake raye ba, na yi fatan ubangiji ya ara mun dama ko da sau Waya ne na aikata hakan a gareka amma Allah be nufa ba, Allah ya ji?anka babban mutum Allah ya gafarta maka. Ka kasance me ha?uri, me kyautatawa iyaye sannan ka kasance mazumunci, halayenka na gari su bika, Allah yasa aljanna maWaukakiya ta zamo masauki a gareka Ahmad Allah ya dubi bayanka ya shirya maka zuri'arka se mun taho abin alfahari sanyin idaniyar iyaye.

Kukan da Baba Al?ali ya hanasu shi Alhajin Audun ya buWe musu ?ofa gaba Waya falon ya cika da amsa kuwwan muryoyinsu musamman muryoyin matan idan ka cire Hajiya Binta da tayi mitsi mitsi da ido tana kallon Alhaji Audu dake rungume da gawar se Jafar daya hau kansu da faWa yana cewa
"Ku tashi ku fita, ai yace kar wanda yayi masa kuka Addu'ar mu kaWai yake bu?ata akan me zaku zo kansa kunayi masa ihu dallah ku tashi ku fita" ya shiga fuzge gawar daga jikin Alhaji Audun tamkar ma be san wanene shi ba shima kuma ganin yanda Jafar Win yake abu cikin fitar hayyaci yasa ya sakar masa gawar dan uwansa, shiya naWeshi da rufin ?arshen Hussanin na tayashi dan su biyun suka rage masu sauran taurin zuciya, ana fita dashi Fatima da Momy suka suma, Baba Bilki suka budewa sauran masu hayaniya a ?wa?walwa fili daga wannan ta faWi waccen ta bita gida ya sake rikicewa, da?yar dai aka tattarasu aka maidasu ciki aka kulle ?ofar gidan.

A barandar falon Alhaji Audun aka sallaceshi bayan sun idar da sallar la'asar kafin aka sakashi a mota dubban mutane sukayi masa rakiya zuwa gidansa na gaskiya cikeda Alhinin rashin nagartaccen mutum da akayi. Hawayen Jafar basu samu sararin sauka ba seda aka zura gawar a rami, yaga an fara zuba masa ?asa, wani irin kuka ya fasa da seda zukatan mazaje suka girgiza, ya yun?ura tamkar ze faWa cikin ramin aka rike shi, yanda yake kuka yana kiran Yah Ahmad seda ya saka duk wani me imani dake tsayw a gurin zubar da ?walla, aka rirri?e shi har seda aka gama maida ?asar aka rufe kafin ya fizge ya dur?usa a gaban kabarin yana cigaba da kuka, dakyar aka sakashi a mota suna fara tafiya yayi shiru Asharab ya dubashi yaga idanunsa sun ?a??afe alamar ya suma ba shiri suka wuce Asibitin da aka wuce da Momy da Fatima, ita Fatima bayan ta farfaWo jini ya Salle mata ita kuma Momyn bata ma farfaWo ba.

*********************
Tamkar kububuwa haka Hajiya Binta ta baro falon ana tsaka da koke koken da rikicin masu Aljanu da waWanda ciwukansu suka motsa, ba ta damu da matan dake zazzaune ba ta yaye hijabin jikinta ta sa?ale jikin ?ofa ta wuce babban kitchen Win tsakar gidan taci gaba da abinda takeyi, robobin da aka rigada ala zuba abinci tasa aka fara fito dasu, sudai masu rabo iyakar su tsakar gida basuyi gigin tunkarar Sangaren Momy ba, yan uwan Fatima na Sangaren Hajiya Rabi, dangin Baffanta ne se ?annen Umma biyu da sukazo daga Niger Anty Sauda da wasu cousins Win su se Badariyyah da tun ranar da akayi rasuwar suka taho kano ita da Nurain yau da safen kuma Babansu da Momynsu tareda Anty Yusra Yayarta sukazo Jana'iza.
*Assalamu alaikum warahmatullah*

*Amincin Allah ya tabbata a gareku masoyan rubutun Ummu-Maheer, tabbatas ina ji daku ina kuma alfahari daku a duk inda kuke*

*Ina so nayi amfani da wannan damar na gode muku na kuma baku ha?uri a bisa shafuka masu taSa zuciya da suka rigayi wannan shafin, kuyi ha?uri da zubar hawayen da rashin Ahmad ya sanya ku, tabbas duk inda rayuwa take dole akwai mutuwa. Fatanmu a koda yaushe ubangiji ya karbi rayukanmu a lokacin da yake farin ciki da komawar mu gareshi, ina mai sake baku ha?uri da neman afuwarku ga duk wanda rubutuna ya tadowa da tsohon mikin rashin jigo a rayuwar sa na kuma gode ?warai da bibiyata tun daga farkon labarin nan ba tare da kun gajiya ba, muna dab da ?ar?areshi da yardar Allah.*

*Team bati ina gaisuwa, a yi ?o?ari dai azo a sauke bashi. 500 ne kacal a turamun ha??ina a cikin*
*7061838488 opay OR 0709290797 Access bank Maryam Farouk*

*Se a tura shaidar biya zuwa ga 07061838488, WhatsApp only banda kira please Nagode*

*Son so fisabilillah*

*MTM B3 P24*

Kwanci tashi akace a sarar mai rai kwanaki goma sun shuWe da rasuwar Ahmad Bechi a kuma ranar yan uwa na kusa dana nesa da suka zo tayasu Alhini suka ?arasa barin gidan. Kwanaki goman da suka gabata sun kasan ce masu tsanani musamman ga mutane mafiya kusanci da Ahmad Win Momy, Fatima da kuma Jafar wanda se bayan da suka dawo idonsa ya shaida binne Ahmad sannan ne ya gasgata cewar ya barshi har Abada, ba ?aramin dukansa rashin yakeyi ba. Tun bayan da aka sallamoshi daga Asibiti be ko iya zama cikin mutane inda ake karSar gaisuwa, can Wakin su na samartaka ya buWe ya shiga duk wanda yazo masa gaisuwa se dai ya tarar dashi acan.

Ranar cika kwana goma da rasuwar Baba Al?ali ya tara su yake sanar musu Fatima kan mahaifan Fatima sun nemi da su tafi da ita can gida tayi takaba.

"Sun bada uzurin yanayin jikinta da ya?i daidaita dan haka suna so su tafi da ita" Baba Al?alin ya faWa kafin wani cikin waWanda abin ya shafa yayi magana Hajiya Binta tayi caraf tace

"To daman zaman me zatayiwa mutane gayyar na ayya gayyar tsiya ai ko basu nema ba daman jira nakeyi yau ta ?are banji ance komai ba da kaina zan tattarata na kai musu tsiyarsu. Ba yanda banyi in hana abin nan ba kowa ya ringa mun kallon muguwa gashi nan abinda nake gudu ya tabbata, tazo ta zazzaga yaya an kama gado shine suka lashe shi, dake ma duk gayyar mata ce yayan Satan basira ai da se ki jira ki haifi namiji yanda komai ze zama naki kafin ki cinye shi"

"Wacce irin magana ta marasa tunani kikeyi haka Binta? Shin wai ma waya kirawoki nan gurin? Ko kuwa kinada ruwa cikin abinda ake tattaunawa ne?" Baba Al?ali ya katseta cikin fushi seta harareshi ?asa ?asa kafin tace

"Ni ko nake da ruwa kuma maganar data shafi gidan Amadu har se an kirawoni ina matar ubansa kai ne ma za'ace kayi shishshigi tunda dai ai Allah ya bawa Audun nan yaya maza tuli da zasu iya zartar da komai amma komai seka cusa kai kaje kaji da naka matsalolin mana".

Kallonta kawai Al?alin yayi ba tareda yace komai kafin ya maida kallonsa kan Alhaji Audu da yayi shiru a zaune tamkar bayajin duk maganganun da sukeyi. A fusace yace masa

"Ka jawa wannan da?i?iyar matar taka kunne dan wlh duk ranar data kaini bango ba zatayi mana daWi nida ita ba, sannaan kaji abinda na gaya maka iyayen yarinya suna so su dau?i yarsu se kuyi abinda ya kamata ku sallameta" yana gama faWar haka ya tashi fuu ya fice ba tareda ya ?arasa sauran maganganun da yayi niyyaryi ba yana jin Binta na ?arajin ya ce mata da?i?iya, seda Alhaji Audun ya buga mata tsawar da batayi tsammani ba kafin ta tsagaita tayi masa ?ur da ido tana kallonsa. Tun da akayi mutuwar kullum se Audun ya shayar da ita sabon mamakin ba?in daSi'un da bata san yana dasu ba da suke bayyana. Sum sum ta fice daga falon zuciyarta tamkar zatayi bindiga tus ta fashe saboda takaicin abinda ya mata, tsawa a cikin mutane.

Bayan fitarta Alhajin cikin muryarsa data sake cika da izza ya kalli Fatima dake Wigar da hawaye yace
"Kiyi ha?uri kinji, sannan babu inda zaki tafi, zaki zauna a nan har zuwa ki haihu sannan muga abinda hali zeyi"

"Zata koma can gidan Alhaji, zaman ta anan ze zama da takura ta koma gidanta kawai ta zauna" Jafar ya faWa yana kallon Fatiman. Shiru Alhaji yayi kafin ya ajiye numfashi yace
"Shikenan, ta koma can Win idan yaso daga gidan nasu wata tazo ta zauna tareda su. Allah ya ?ara rufa asiri".

A yammacin ranar suka koma can gidan tareda Baba Bilki bayan Jafar ya kira Baffa ya gaya masa abinda Alhajin yace sannan ya nemi idan da akwai wadda za'a turo ta tayata zama Baffan yace Baba Bilkin da suke tare ma ta isa, daman rigimar Umman tace da Anty Sauda da sukace ta dawo gidan amma a shari'ance ma an fi so mace tayi takaba a Wakin Mijinta.

Komawarta gidan ya sake maido mata da komai sabo, ranar basu iya bacci ba dan ba ita ba hatta Baba Bilki a daren tayi kukan da ko rabinsa batayi a can gidan ba. Idan ta kalli guraren da yake zama ko abubuwan da yake amfani dasu duk se komai ya hargitse mata, daman bata iya hawa sama ba balle ta shiga Wakin sa, Abinda ubangiji ya tsara ne ya kasance tilas ko ana so ko ba'a so a karSa da hannu biyu kuma a gode masa.

Bata san cewar tana son Ahmad ba seda ta rasashi, tana kewarsa, duk sanda lokacin shigowar gida yayi ya wuce ba tareda ta ganshi ba gaba Waya duniyar juya mata takeyi taji komai ya fice mata akai. Tayi kuka har hawayenta suka ?afe yq zama sedai tayi na zuciya, duk irin ?o?arin da kowa yakeyi akan ganin ta sake ta koma walwalarta abun yaci tura haka ta rugumi sabuwar rayuwar da shafin ?addararta ya buWe mata ita da yayanta da a yanzu bata da sama dasu. Babban tashin hankalin data fara fuskanta shine yawan tambayar da sukeyi mata akan ina Yah Ahmad? Ance ya mutu kenan ya tafi Aljanna baze dawo ba ko kuma zasu sake ganinsa wata rana? duk sanda sukayi mata tambayar ranar wani take kuka dan bata san amsar da zata basu ba.

*************
"Nifa se yanzu nake jin haushin kaina, to akan me zanyi kuka ma saboda Amadu ya mutu bayan mutuwar tasa itace sau?i na kuma itace makamin cikar burina" Hajiya Binta ta faWa tana kallon Naziru da Zakariyya dake zaune suna kallonta. Sati guda kenan da Zakariyyah ya faWi a banWaki, faWuwar tasa se tazo masa da Alkhairi dan bayan ya suma an kaishi Asibiti daya tashi farfaWowa tunaninsa na baya ya dawo. Naziru dake danna waya ya Waga kai yace

"Allah sarki Ahmad Allah ya gafarta masa amma fa gaskiya anyi rashi a gidan nan. Ga gwaskan da muketa dakon ya kauce mutumin nan ko gezau ita kuma mutuwa ta afkawa wanda babu ruwansa"

"Ai ban san kaima shashasha bane se yau, Amadu kuwa shi yake da ruwa harda tsaki, ai ni wlh se yanzu ma nake godewa Allah, gara da suka cinye shi. Kana kallon abinda ubanku ya ringayi se kace wani zautacce saboda wannan kirikun yaron ya mutu, irin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login