Showing 30001 words to 33000 words out of 467220 words

Chapter 11 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12158

wanda zaka riqr ze gagara ne?"
"Audu yayi murmushi kawai jin abinda tace ya tashi ya fita bayan ya Ajewa Aminar saqon maganin ciwon qafa yace ta kaiwa Dada, haka suka koma Bechi aka bar su Bara'atu a sabon guri.

Sannu sannu rayuwa taci gaba da tafiya, Balaraba ta yada wanka har taje Bechi daga nan tayo Kano ta kwanarwa su Balaraba Biyu kafin suka kama hanya da Audu daze rakata dan Yayanta Iro ya tafi da Shanu matarsa kuma tana da ciki ta kusa haihuwa wannan yasa Iyayensu sukace ta zauna ta haihu tukunna ta koma. Seda Audu yayi sati ya dawo rayuwa taci gaba. Sosai kasuwancinsa yake garawa. Kudin gonar su da suka siyar ya qara jari da shekara ta zagayo sun ninka kansu wannan yasa ya shawarci Bilki data kawo musu ziyara akan me ya kamata suyi, sun yanke cewar su nemi qananan Gonaki a ringa siya ta yanda a hankali kowa ze mallaki tasa aci gaba da juya kudaden kamar yanda yakeyi yana kuma fitar da riba yana bawa kowa saboda buqatu, gidansu ma Bilkin cewa tayi suyiwa su Hashimu tayi ko zasu siya dan ya mayar da gurin Rumbu kayan gonarsa yake ajiyewa a ciki Audu yace mata Aa su barshi saboda idan sunje su samu gurin sauka ze dai saka a gyara gurin a hankali.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*FREE PAGE 9*

Ranar wata Talata Bara'atu ta sauka a Asibitin Murtala inda Audu ya yankar mata katin Awo tun bayan dawowarsu Kano ta samu Da Namiji murna gurin Audu dasu Baballiya ba'a magana, wata maqociyarsu Baba Larai da suke mutunchi da Bara'atun tun tarewarsu ce tayi mata biqin kwana biyu kafin Audu ya tattarasu suka tafi Bechi, se ganinsu sukayi da jinjiri aka ringa murna a gidansu ta zauna seda akayi suna yaro yaci sunan Malam wato Tijjani suke kiransa da Babangida, Raguna biyu manya Audu ya yanka haka ya mata kayan barka irin na Birni duk inda ka shiga a Bechi labarinsu akeyi, lafiya lau tayi wankanta kwananta Hamsin da Haihuwa suka dawo Kano rayuwa taci gaba da garawa cikin ludufi da Amincin ubangiji.

Kasuwancin Audu kam yana habaka dukda dai har sannan yana kan canje canjen sana'a dalili da duk wadda ya fara tabawa da an kwana biyu se abin ya fara sakin hannunsa tilas yake sake cafkar wata sana'ar ya dora wannan dalili yasa yana da ido acin kusan duk wata sana'a da ake juya kudi a samu riba, ba babbab ba qarama duk yana tabawa ita kanta Bara'atu be barta a zaune ba ya sakata tana taba sana'oi na mata na cikin gida kuma tana samu babu laifi ga Kitso da daman ta iya shima tanayi shiyasa idan suka tashi zuwa Bechi Sallah, Biki ko suna bayan abinda Audu ze bata haka itama zatayi ta Alkhairi wa yan uwanta da nasa, gida su kuwa baya rabo da dangi duk wanda ya samu dama ze zo Kano ya kwanar musu biyu ya koma.

Yakubu na Ikko abinsa tunda Balaraba ta bishi seda suka shekara biyu kafin suka zo lokacin ya rage masa shekara daya ya kammala karatunsa kenan. Daga shi Har Balaraba idan kalle su seka qara, Yakubun ya waye ya zama wani baqin Bature hatta shigarsa ta canza zuwa coat baqa da farar yar ciki irin dai shigar su ta masu karatunshari'a ita kanta Balaraba Turanci har ya kama bakinta saboda suna tsakiyar wanda zo in kashe ka basu sani ba da Hausa. Ga Dada data jima da yayewa tayi kubibi abinta fatarta me haske irinta uwarta har sheqi take saboda zama cikin lullumi ga cin naman ruwa da suke se tsohon cikin da take dashi haihuwa ko wanne lokacin dalilin dawowar tasu ma kenan.

A Kano suka sauka suka ringa yiwa Juna tsiya ita da Bara'atu da itama take dauke da ciki na Biyu watannin Babangida goma sha daya ta samu ciki sati daya kenan Inna Hajara ta dauke mata shi tunda ta kusa sauka amma ba bisa son ran Audu ba. Seda suka kwana biyu suka huta kafin suka tafi Bechi gaba daya niqi niqi da tsaraba daga can Balaraba taje garinsu su kuma suka juyo Kano seda ta gama kwanakinta ta dawo.
Zamansu gwanin dadi, idan safiya tayi Mazajensu suka fita Kasuwa inda Yakubu yake bin Audu Baballiya da Abdullahi su tafi makaranta duk wadda ta riga gama aikin bangarenta zata shiga gurin yar uwarta, nan ma girki daya suke kowa ta dibarwa iyalanta.

Wannan karon ma Balaraba ce ta fara haihuwa ta sake samun Mace kwana biyar tsakani Bara'atu ma ta haihu ita kuma Namiji wannan Dalili yasa Audu da Yakubu da duk sukace babu wadda zataje gida aka hade taron suna, ranar kwana bakwan Balaraba akayi mata yanka yarinya taci suna Maimunatu amma taro seda da dan Bara'atu Yusuf dayaci sunan babanta ya kwana bakwai akayi Yan Bechi sunzo da dangin Balaraba an sha buduri sosoi taro ya watse se yan zaman wanka da kowacce aka kawo mata daga gida Yakubu ya koma Ikko saboda makaranta haka suka cigaba da wanka Balaraba na yada wanka taje garinsu da Bechi tayi musu sallama Audu ya kaita tasha da Yayanta suka bi Yakubu Bara'atu kuma taci gaba da rainon Babannan da Babangida wanda Audu ya kafa kwarzaba seda aka dawo masa da Dansa ga kuma Baballiya da Abdullahi abinsu gwanin Dadi suke zaune.

Bayan Baballiya sun rubuta jarabawar kammala sakandire wadda tsallaken Aji akayi masa saboda girmansa akayi sa'a kuma yana gane karatun daman yana Aji Takwas suka baro Bechi dan haka suna zuwa Kano Audu yasa aka kaishi Aji biyu na babbar Sakandire, ya dage akan shidai aikin soja yakeyi, tun Audu baya daukar abinda muhimmanci har nacin Baballiyar yasa shi tambayar yanda ake shiga makarantar sojojin. Wani Maqocinsa a Kasuwa ya tambaya dan yanajin yana fadar da akwai qaninsa daya tafi aikin soja, shiya gaya masa qanin nasa yana makaranta a Kaduna shima wani Dan uwan mahaifiyarsu ne dayake zaune a can ya samo masa kuma ance daya gama ze fito a babban soja ne ba kurtu irin wanda mutanen mu a wancan lokacin suke zuwa suyita wahalar banza ana kashe su a yaqe yaqe ba.

Wannan dalili ya saka Audu shirin tafiya Kaduna kai Baballiya makaranta. Yace masa ya shirya kayansa kala hudu zuwa biyar a jaka ya kuma hada takaddunsa, Bara'atu ta ringa musu dariya tana cewa
"Dukda dai bamyi karatu ba amma nasan ba haka taka ake kai mutum makaranta ba dole se anbi matakai ka nemi gurbi idan ka samu kafin ka tafi ko?"

"To ai nima ba cewa nayi zan kaishi kaitsaye ba, zuwa zamuyi can muji yanda tsarin komai yake saboda ban gsu da bayanan Labahani ba besan takan komai ba kawai shirme yake gayamun gara muje kinga idan abin babu wahala kinga ba se anyi jeka ka dawo bazan baro shi can kawai" Audu ya bata amsa. A daren tana hada masa nasa kayan Babannan dake wasa ya zubo da wata jaka da Audu ya cukuikuye takaddar kammala sakandirensa ya jefa a ciki da takaddun gonakin da suka siya a Bechi, ta tattare ta mayar tana masa fadan ya fiya qiriniya, Babangida ne ya daga wani qaramin kati ta bata ankare dashi ta mayar ba ya fita dashi. Audu na qofar dakin inda ta baza musu tabarma saboda zafi suna Hira dasu Baballiya da murna tasa ya kasa bacci.

Abdullahi Babangidan ya kaiwa katin hannunsa, ya haska da yar fitila yana karanta abinda aka rubuta a jiki kafinya miqawa Audu yana cewa
"Baba ga abinka Baba ne ya dauko"
Audu ya karbi katin ya haska shi tunaniya tafiyi na menene, duk sonya tuna kuma ya kasa, Kaduna daya gani a Address din dake jiki ya sakashi bawa Abdullahin yace ya miqawa Ummansu ta saka masa cikin jakar da ze tafi dashi, komana wanene yana da yaqinin zeyi masa amfani tunda zashi Kaduna.

* MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na *GHT wato good health treatments
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri *

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*

*Seda suka hau mota har sun wuce Zariya kafin katin ya fado masa take kuma ya tuna inda ya samo shi, wannan Alhajin daya taba taimaka ya basu Mai shekaru kusan uku kenan nasa ne. Farin ciki ya kamashi, a ransa ya ringa Addu'a Allah yasa yana raye kuma yana Kadunan idan sunje ze neme shi su sada zumunchi. Ikon Allah kenan, qila rabon su sake haduwa yasa Babangida binciko katin dan ko da kudi bazece ga a inda ya ajiyeshi ba, zaton sa ma ya fadi tun a ranar. Haka suka sauka Kaduna, Baballiya nata dan banzan raki wai tafiyar Nisa ya gaji Audu ya balbaleshi da masifa yana cewa a haka zeje aikin sojan qato dashi amma se ragonci kamar Mace.

Ganin yana nema yayi masa kuka ya sakashi neman gurin me abinci a cikin tasha ya siya masa, suna zaune yana tunanin ta ina zasu fara, gashi la'asar harta kawo kai dan motar da suka hawo se a hankali kamar sun hau Jaki. Wani akwatun waya ya hango wanda ake biya ayi kira ya miqe yana laluba Aljihunsa inda ya saka katin Alhaji Zakariyya ya tafi gurin. Ya bada lambar aka kira masa, kiran farko ba'a daga ba seda akayi na biyu muryar mace cikin harshen turanci ta ratsa kunnensa.

Gyara nasa harshen yayi suka gaisa kafin ya shiga tambayar mamallakin lambar wanda a katin yaga an rubuta Zakariyya, "wa za'a ce masa?" Ta tambayeshi yace mata
"Kice masa Audu Bechi ne" Audu ya fada duda yasan babu tabbacin Alhajin ya gane tunda ba gaya masa sunansa yayi a wancan lokacin ba idanma ya tuna ya taba haduwa da shi kenan.

Matar tayi shiru kamar me tunani kafin tace ya riqe waya tana zuwa. A can bangaren sakatariyar Alhaji Zakariyya ce ta dauki wayar wadda take a cikin ainihin office dinsa, ta sani lamba ce da yake magana da mutane masu muhimmanci dan haka duk wanda ya kira tabbas yana da muhimmanci gurin Ogan nata. Kwankwa qofa tayi, Alhaji Zakariyya ya bata damar shiga. A taqaice ta sanar masa da kiran daya shigo din, sunan Bechi data fada kawai ya sakashi zabura kamar wanda akace anga Dan uwansa daya bata. Fuskarsa a washe har haqoransa sun bayyana cikin son tabbatarwa yake tambayarta
"Kikace BECHI"
"Yes sir, haka yace sunansa Audu Bechi" ta bashi amsa.

Alhaji Zakariyya ya daga kan wayar dake ajiye kan teburinsa wadda take a hade da ta teburin sakatariyar, Audu nacan saqale da waya a kunne cikin jiran tsammani yaji sallamar Alhajin kamar daga sama har wata Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga gaishe shi.

"Har na fitar da rai da zaka kirani, kullum da tunaninka nake kwana nake tashi, na kasa manta Alkhairin dakayi mun" Alhajin ya fada cikin tsananin murna. Audu yayi murmushi yace
"Haba dai Alhaji dan wannan abin ka kasa mantawa tsayin shekaru?"

"Kai kake kallonsa a qanqanin abu, badan Allah ya kawo ka ka taimakemu ba a wannan rana bansan ya zamuyi ba. Ya bayan saduwa ya Kano? Kasan tun wannan ranar ban sake zuwa Kano ba amma duk idan naji wani zece sena bada sallahun a dubamun kai a wannan hanyar gashi bansan sunanka ba ballantana ko yan karkararku a tambaya" Alhaji ya sake fada. Audu ya jinjina kai cike da mamaki kafin yace

"Ikon Allah, nima yau Allah ya kawoni Kaduna shiyasa na taho da katin nan nace idan baka mantani ba na kiraka muyi zumunchi"

"Kace kana Kaduna?" Alhaji ya fada har yana miqewa, Audu ya nanata masa kafin ya fada masa yana Tashar Kawo tareda qaninsa, Alhaji be bashi damar sanar masa da abinda ya kawo su ba yace ya tambayi me wayar Adireshin gurin da suke ya kuma jira a nan ze tiro direba yanzu a kaisu masauki ai baqonsa ne shi. Haka ya zauna a gurin, ba'ayi ci mintina ashirin ba sega Direban Alhaji da sukaje Kano tare Audu na ganinsa ya gane shi ya qarasa gurin fuskarsa dauke da fara'a.
"My brother" ya fada yana buga kafadar Audu ko ba'a fada ba cike yake da farin cikin ganinsa. Shi ya daukar musu jakar kayansu suka tafi inda ya faka wata luntsumemiyar mota yayin waccen shekarar suka shiga Baballiya se zare ido yake.

Suka ringa ratsa titunan Kaduna da gine gine masu kyau da burgewa a nan kuma Audu ya tabbatar da cigaban da Kaduna tafi Kano ta bangaren tsarin birni wanda ake fada su zauna kasuwa suyita tafka musu yau gashi ya gani kuma ya yarda. Gine ginensu a tsare ga Titi ko ina Malam Baballiya ko kasa rufe baki yayi dan wasu ginin ma be taba ganin kalarsu ba saboda ko a Kanon daga makaranta se gida se ranakun hutu da Audu kan tafi Kasuwa tare dasu babu inda ya sani shiyasa Aljannar duniyar da yake gani yanzu ta mugun tafiya da tunaninsa. A unguwar Sarki inda katafaren gidan Alhaji Zakariyya yake kutsa cikin wani gida.

Gini ne na Alfarma wanda ko a yanzu kwaskwarima kadan za'ayi masa ya tafi daidai da zamani. Gurin da aka tanada dan ajiye motoci Direbam da yanzu Audu yasan sunansa Tunde ya faka motar. Seda ya dallewa Baballiya qeya kafin ya dauke idonsa daga kallon taswirar gidan tamkar kwayoyin idonsa zasu zazzago. Tunde ne yayi musu jagora har zuwa can gefen gidan inda sukaga qofofi guda hudu jere ya bude ta farko ya shiga suka take masa Baya Baballiya ne kan gaba Audu na daga baya saboda ya tsammaci bangaren matan gidan aka kawo su dukda sunbaro wancan qaton ginin me Bene qila na megida ne can amma ga mamakinsa cikin madaidaicin Falo yaga sun shiga. Tunde na murmushi ya nuna masa qofa dake cikin falon yace

"Ga daki nan, ku shiga kuyi uzurin da zakuyi bari a kawo Abinci" daga haka ya juya ya fita. Audu ya ringa kallon Falon dake malale da Kafet irin wanda daka taka qafarka zata lume a ciki ga wasu shimfida shimfidan kujeru na Alfarma, ya taba ganinsu sau daya a gidan wani Hamshaqi a Kano daya kaiwa Takalma wanda suma yana siyar dasu yanzu. Wani qamshi da sanyi ya ringa ratsasu, ya kalli Baballiya dake nan kamar gaula har digar da yawu yake tsabar kallo kafin ya zauna akan kujera kamar me tsoron ace ya tashi. Babu dadewa Tunde ya dawo da wani mutum a bayansa ya saka Apron da hular girki hannunsa dauke da wani qaton Try har mamaki ya kama Audu na tunanin yanda ya iya daukar wannan Try da hannayensa biyu ba taredaya nemi taimako ba.

"Ya naganku a nan ga jakarku ma baku kai ciki ba?" Tunde ya fada yana tsince jakar su Audu da Baballiya ya watsar a garin qauyanci. Cikin dakin ya kai musu Kuku kuma ta aje kayan hannunsa ya fita ya sake kawo wani madaidaici dabe kai na farko ba daga nan ya fita ya barsu Tunde ma ya fita bayan ya jaddada musuga abinci nan suci su qoshi tamkar suna gida. Kiran la'asar da akayi ya saka Audu miqewa ya shiga dakin. Nan dinma lailaye yake da Kafet ga gado na Alfarma da sif irin ta cikin Bango se mudubi daga gefe. Qofar da yake zaton itace ta bayin ya bude ya shiga.

A zuwansa Lagos sun taba zuwa gidansu wani Abokin Yakubu da suke karatu tare a can ya koyi kunna irin famfon daya gani anan idan ba haka ba da yau an sha kunya. Ya kunna Famfo ya tara hannu da niyar Alwala yaji ruwan zafi sabanin na sanyi. Wannan dalili ya sakashi canza shawara, sosaiya ya gaji jikinsa na ciwon wahalar mota dan haka ya dakko soso dan yaga sabon sabulu a kwalinsa ya koma bandakin ya tara ruwa me zafi a bokiti ya sheqa wanka a bandakin yan gayu yayi Alwala ya fita. Tsaf ya shirya yana jinsa kamar yau ya fara wanka a rayuwarsa. Idanbeyi qarya ba fatarsa har wani sulbi tayi taji sabon sabulu. Anan yayi sallah seda ya idar ya tuna da Baballiya sukazo ya fito falon, nan ya ganshi Baje kan kafet yana bacci ga Abincin daya kacaccala nan ya barsu bude se zuba munshari yake kamar wanda yayi awanni da kwanciya baccin.

Tsabar takaici besan sanda ya kai masa hauri da qafa ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login