Showing 195001 words to 198000 words out of 467220 words

Chapter 66 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12245

cikin katafaren Bedroom Winsa yana taje Quater Million Sajen dake kan fuskarsa yayi ?aramin murmushi kafin yace
"How are you my love?", zare ido tayi kamar tana gabanshi kafin cikin tsiwa nace
"when did i become your love? Don't call me that again"
"The first time i set my eyes on you, i know you are my lost but found true love" Jay ya faWa yana Waura agogo, fita zeyi, kiran da ya mata bata Wauka ba shine ya shiga wanka yanzu ya fito yana shiryawa ya sake kiranta.

Baki ta tura amma kalamansa sun mata daWi, wato da confidence yake komai nasa babu wani Wari Warin irin na Ahmad shi gaba gaWi yake faWar abinda yake a zuciyarsa.
"Hey sweet, are you there?"
"Uhm" ta iya furtawa kawai dan ta rasa bakin magana. Ta kasa gane kanta da wannan stranger Win, bala'in jin daWin magana dashi take kusan zata iyacewa a class hankalinta duk yana kan wayar da sukayi da Asuba, bata sanshi ba bata san waye shiba ba amma har cikin ranta ji take kamar sun shekara dubu tare.

"I'm going out, dama na kira ne naji muryarki nayi miki barka da Juma'a, i might be late out though, will you wait for me ba zakiyi bacci ba har na dawo muyi magana?" Jay ya faWa tamkar me barwa matarsa sallahun ze fita wani guri, mamaki ya sake kasheta amma cikin tsiwa kuma ta mi?e tsaye tana kakkaSe jikinta tace

"To ni meye haWina dakai kuma da zan?i bacci na jiraka?"
"Abinda nake so muyi magana akai kenan, ina so kisan meya haWaki dani yau" ya bata amsa a tsume jin zata fara masa rashin kunya, wai kuma se shakkarsa ta shigeta harta gyara harshenta tace
"Karma ka kirani dan bacci na zanyi koma zan kashe wayar kawai tunda kai idan ka fara kiran mutane se kace sunci bashinka baka ha?ura se an amsa"
"Wait for me please" ya faWa da taushin daya saka ta Waukewa na sakanni, yayi miskilin murmushi, ya gama gane lagonta ba ita kaWai ba yammata da yawa muryarsa na cikin abinda yake saurin kassarasu shiyasa ya la?anci salo salo da yake amfani dasu gurin ladaftar da masu kunnen ?ashi irinta.

"Will you?" Ya sake faWa da sautin dayafi na farko taushi, tsikar jikinta ta hau zuba, kai ta ringa Wagawa kamar ?adangaruwa kawai kafin dakyar tace masa
"Toh, amma kar yayi dare da yawa"
"Till i call, bye, I love you" ya sakar mata maganganun kafin ya kashe wayarsa. Taji I lobiyu tabi kashi Miliyan amma bata taba jin wadda ta gamsar da ita irin wannna da bata da tabbacin da gaske yake ko ?arya ya sharara ba.

Da yamma ta suka fita karatu sai bayan Magriba suka dawo rabi da rabin hankalinta nakan Jay dayace ze kirata, dukda yace se dare amma fata take ya sake kira da yammar. Suna hanya Nurain ya kirata akan ya shigo Makarantar.
"Ina my Badar? Wayarta baya shiga?" Ya tambayeta. Ta saci kallon Badar data ?urawa hanya ido kamar me neman wani abu kafin tace
"Gata muna tare, ka jiramu a white sit mun kusa isowa"
"Alright Bestie" ya kashe wayar.

A nan gurinsa suka lalace suna hira har gurin tara dukda hankalin Afeeya rabi da rabi ne a gurin Badar ce suke kurSar madarar soyayya da Habibin nata ayi faWi. Tara da rabi tace ita zata shige ciki yunwa takeji Nurain yace suje su siya abinci a Baescope.
"Wlh ba zamuje ka sake yarfamu irin na ranar nan yau ban fito da kuWi ba" Afeeyah ta faWa yayi dariya yace
"Haba da kenan, yanzu ko wani na gani ze yan?wana Baby na Badar ai se inda ?arfi na ya ?are balle nida kaina.

Suka tafi a motarsa, a can sukaci ya siya musu Ice cream suka dawo.
"Bestie meya faru ne? Fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa?" Nurain ya tambayi Afeeyah ganin duk walwalarta ta gushe. Tunda suka je gurin yake lura da yanda ta tsume abincinma tsakurarsa tayi bayan ita tace tana jin yunwa jefi jefi kuma tana duba waya tana tsaki.
"Babu komai Bestie I'm just too tired, bari na baku guri dan nasan Badar tsuntsun soyayya baze barta ta gaji ba" ta wuce Badar na zaginta.

Harta gama shiri ta hau gado badan tana jin bacci ba sedan ranta babu daWi Jay be kira ba kamar yanda yace. Ta rufe idonta tana jin kamar ta fasa kuka, su Ummi suka tambayeta lafiya tace kanta ne yake ciwo kowa ya mata sannu suka barta.

A zabure ta mi?e jin wayarta ta fara ringing, a jikinta taji cewar shine, ta dire daga kan gado tana neman hular da zata saka takalmi ma wari da wari ta zura ta fita har suna karo da Badariyyah.
"Wai Afeeya wane salon munafunci kika samu na ba zakiyi waya a Waki ba?" Badar ta faWa tana ri?e ?ugu, Afeeyan ta harareta tace
"Yo aike ke tashen munafunci yanzu, ki gama cika baki Allah ya sawwa?a me zaki ci da Bestie na ashe mu kika mayar shashashu kuna can kuna tsinke furen ?auna"

"Ya ranki?" Cewar Badar tana fari da ido, Afeeya ta girgiza kai kawai ta fice. Dukda dare ga uban sauro haka ta samu wani sa?o ta lafe ta bi kiran Jay daya katse, be amsa ba ya kashe ya kirata back
"Irin Ahmad ta raya a ranta" muryarta na amsa kuwwa a kunnenta ta manta da wani batun Amadi bawan Allah ta fuskanci Jafaru.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 13*


"Assalamu alaiki" ya faWa cikin murya me sau?i kamar wanda yake cikin nishaWi sosai. Ta amsa can ?asa, yayi murmushin daya saka kunnenta fara ?ai?ayi kafin yace
"Na kiraki morethan ten times baki amsa ba, you are lucky ina cikin farin ciki yau amma da sena hukuntaki"
"Toh" tace masa,
"Oh toh ma zakice kawai? U are not apologing, Any way how is my sweet baby doing? Ya Juma'a?"
Ta karkace ta gyara zama kafin tace
"Komi lafiya"
"That's great" ya bata amsa se sukayi shiru na kusan minti biyu kafin ya sake cewa
"Afeeya, i hope you remeber me?"
"Nidai idan zakayi magana ka dena kiran sunana and i don't remember you i don't think we have ever met" ta faWa da shagwabar da batasan tayi ba saboda yanda yake kiran Afeeyan gaba Waya wani yanayi yake sakata.

"Babe karki Kashewa Hajiya ni da wannan shagwaSar taki" ya faWa, yanda yaja Babe Win ya sakata jin wani sanyi yana ratsa mata Sargo har seda ta haWe jikinta tanayin kamar kanta na haya?in shau?i. Allah ya sani Ahmad na iyakar yinsa gurin riritata yana faWa mata kalaman soyayya amma batajinsu kamar na wannan mutumin.

"We met on Monday, kina sauri zaki tafi class i followed you to your department a gurin Class Rep naku na samu number ki so you are this popular ina cewa Afeeyah yace ya sanki, i hope you are known for the good not for the other way?".

Shiru tayi masa dan idan yana magana bata so ya dena, sautin muryarsa is killing her,
"Afeeyah" ya kira sunanta ta amsa da
"Uhm".

Shiru yayi kafin yaja numfashi yace
"Kafin muyi nisa Afeeya let me make this clear to you, ina da saurin fushi like the smallest thing you couldn't imagine can trigger my temper. Na tsani na yiwa mutum magana yayi shiru ko ya amsa mun da uhm ko body language, I prefer kayi mun magana ko zagina zakayi and bana son nu?u nu?u da boye boye na tsani ?arya da munafunci, i love bold and straight forward person in dai kika kiyaye wannan zamu zauna lafiya, lastly I'm a lover boy, i love to be loved and be pampered, kinga idan kina riritani kina shayar dani madarar love na rantse har ?afarki zan ringa lasa tsabar biyayya".

Bata san sanda ta tuntsure da dariya ba saboda maganarsa ta ?arshe wai lashe ?afa kamar wani maye kai wannan mutum da abin dariya yake ma wlh. Tayi dariya sosai shi kuma yayi shiru yana sauraronta seda ta gama dan kanta tace
"You are so funny wlh"
"Some times" ya bata amsa kafin ya sake cewa
"I should make a proper introduction of my self now. Sunana JAFAR but the world knows me as JAY, Bahaushe ne ni haifaffen Kano amma rainon Turai, na bar Nigeria when i was 13 na tafi Manchester nayi joining Football Academy. I'm a professional footballer, shekarana 11 ina taka leda yanzu professionally, I'm currently playing with Arsenal, ina buga number 7 or 9".
I'm from a polygamous family, inada siblings da yawa sosai i think that's all that you might want to know now about me for now, may be with time zaki ?arasa sanin komai a kaina".

A duk bayanin nasa babu abinda yayi catching attention Winta kamar sunansa da kuma profession dinsa, JAFAR kuma FOOTBALLER? Samun kanta tayi dace masa
"Kai kaWaine Jafar musulmi kuma dan Nigeria da yake buga kwallo a Turai?"
"No bani kaWai bane, akwai Jaybee a Tottenham se Jay Jay a Leinster, but they are all half Nigerians me yasa kika tambaya?" Ya maido mata seta sauke wata ?arfaffar ajiyar zuciya yanda kasan wadda aka ritsa da bindiga ta samu ceto koda yake da tunanin da yake zuciyarta ai har gara ace bindigar ce, indai ba mantawa tayi ba Jafar ?anin Ahmad ma ?wallo yake yi a turai idan ya zama shine Jay da take magana dashi ai she?e kanta kawai zatayi ta mutu, zuciyarta ta aminta da cewar Jafar Win Ahmad yana cikin Wayan biyun waWancan daya faWa ko Jaybee ko Jay Jay tunda bata san mamanshi ba, ta yuwu halfcast ce kamar yanda yace suWin half Nigerians ne amma ba wannan JAY Win bane ba, babu yanda za'ayi ya zama JAY ma.

A yanzun haka suna da aikin da sukayi sharing da Jafar Win yasa kaso Arba'in na zumuWin da takeji akansa ya disashe, zuciyarta har wani harzi?owa tayi da tunanin abokin faWan nata, Jay da yaji shirunta yayi yawa yayi gyaran murya yace a sanyaye kamar bashi ba yace

"Afeeya lafiya kikayi shiru ko da akwai wani abu ne"
"Babu komai, kawai sunanka da profession dinka sunyi kama da na wani abokin rigimata" ta bashi amsa, muryarsa har ?ara sauti tayi kamar a fusace yake tambayarta
"Wanene shi? Meye ya haWaki rigima da Namiji?"
"Cousin Wina ne" ta samu kanta da yanko wannan Jibgegiyar ?arya da seda ta faWa sannan takaicin kanta ya kamata to saboda me zatayi masa ?arya? Haka kawai taji bazata iya ce masa ?anin saurayinta bane ba, daga can Jay ya sauke numfashi yana cewa
"Your cousin is a footballer too, wane club yake?"

"Nima ban sani ba, amma kamar a Arab countries Win nan yake" ta faWa saboda last tima kamar daga Qatar taji Ahmad yace yazo shiyasa ta bayar kawai tacan Arab countries yake ?wallon. Bata taSa ganinsa a fili ko a hoto ba balle ta kwatanta masa shi, a waya suka taSa magana sau Waya wadda yaci mata mutunchi se jefi jefi idan yana gari ta kan jiyoshi tareda Ahmad har ya gasa maganganu itana ta rama. Har sannan murya babu walwala Jay ya sake ce mata
"Oh i see, i hope there is nothing between you two? Bama shi ba da farko if you know you are committed to relationship wanda iyayenki suka shiga tell me?"
"Babu" ta bashi amsa a sanyaye kamar me tsoron yace ya fasa kulata.

"Amma dai Mace kamarki ba zata taSa rasa suitors ba, ina da kishi beyond your imagination. Bana so nayi sharing abinda nake so da wani, that is why i hate someone saboda the person stole the most precious thing to me" ya faWa cikin jin haushin Fatiman Yah Ahmad kafin yaci gaba da cewa

If you know you are in to any relationship just call it to end saboda me guri yazo kowa ya tafi kawai"
"Late comer ya kwace maka budurwa ko?" Ta tambayeshi kishi na neman kamata itama.
"Forget it, kawai kiji abinda na gaya miki. Allah i will not accept sharing you with anyone. I love you fisabilillah and i want Marry you Afeeyah. I want to settle down hopely by the end of this year kuma dake nake so nayi aure will you do me the honor and be my beloved wife?"

Ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi, kalamansa sun shigeta har tsajiyar zuciyarta wani yamm takeji a jikinta. Cikin nutsuwa irinta wanda ya san kan soyayya da yanda ze farauci zuciyar mace a karon farko ya ringa tsarata. Tayi shiru tana sauraronsa, tayi nisa cikin hakaito kamanninsa, se ta ringa ji kamar kafin haWuwarsu a makaranta. Sana'arsa data sani a yanzu ta bata satar amsa tabbas tana ganin fuskarsa a wasu guraren kamar posters, jikin Baburan Adaidaita sahu da sauran gurare. Ta tuna Sani Abokin Yayanta Jay ake masa dalilin son da yakeyiwa ?an ?wallo Jay, amma ya akayi bata ganeshi ba? Koda yake ba wai kallon Ball takeyi ba shima shahararsa ce da kuma yanda su Yah Malam kullum basu da aikinyi se magana akansa tasa ta ri?e sunansa da fuskarsa amma kuma data ganshi a fili ya canza mata.

Be rabu da ita ba seda ya tabbatar ya isa duk inda ya kamata a cikin zuciyarta kafin yace taje ta kwanta dare yayi. Be tambayeta komai akanta ba, ta ringa jin wani iri, ta sani surah da kyan fuskar da Allah yayi mata ne ya ruWi Jay zuwa gareta idan har yasan ainihin ita wacece tabbas ze gujeta, Sanannen mutum a duniya kamarshi bazeyi tarayya da yar Talaka kamarta ba balle har suje ga batun aure.

Yanda ya ringa nanata mata Hajiyarsa tana sonsa ya tabbatar mata da Mama's boy ne, yace a gidansu sunfi su Talatin, daga kuma few things daya faWa mata akan familynsa ta fahimci suma suna da ire iren matsalolin da da yawan Manyan gidajen masu hannu da shuni wanda suka tara Iyalai da yawa suke fuskanta, wasu har a social media zakaga suna raba hali. Yanda ta fahimta suna da matsala irin ta yan ubanci a gidansu, ta tuna Ahmad shima gidansu suna da yawa amma kuma bata taSajin ya gaya mata wata Saraka a tsakaninsa da yan uwansa ba, sudai Allah ya taimakesu toh.

Kwana tayi tana juya maganarsa da yake ce mata
"Amma kinsan san dana ganki banyi zaton zanji kinyi hausa ba because you look Asian, da akwai wata girlfriend da nayi Zoya she is from Korea amma Dad Winta ne Korean mum Winta is Arab from Iran so she has that Iranian look and Korean skin, oh my God you need to see her, i have never seen someone as beautiful as she is se ke dana ganinki kunyi kama sosai wlh tsayi kawai zata fiki".

"Ikon Allah" ta fada a zuciyata bangare daya kuma haushin wai girlfriend Winsa da taji ya ce ya kamata har bata san sanda bakinta ya furta
"Oh saboda nayi kama da Ex Girlfriend Winka yasa ka kulani kenan?"
"Ko Waya, sanda nake tare da ita ma she was the one pushing the relationship and i supported her just because she was nice, Zoya was the most beautiful soul i have ever met in my life tana da kirki na ?arshe ta so ni she really wanted to marry me kuma ko ni i lokacin idan da zanyi aure it will be her but unfortunately she lost her life in a plane crash ta tafi ganin Mamanta a Iran from London bata da lafiya tafiyan da bata dawo na kenan sukayi hatsari shekara biyu kenan and since then i remain single".
Ita da kanta ta yarda akwai mutanen da kirkinsu yake sakawa dole kayi mu'amala dasu kamar Ahmad, ta kwatanta a ranta ace shi ya mutu, irin yanda taji yasa tayi saurin kawar da tunanin daga raita

Washe gari dakyar ta iya tashi baccin da bata samu isashshe ba, sun daWe suna magana da Jay a waya sannan data kwanta ta kasa bacci tayita bitar hirar da sukayi. Shida da rabi ta idar da sallah tana Azkar ya sake kiranta ta Waga fuskarta da murmushin da batasan ma tanayi ba suka gaisa.
"Zan fita ne nace bari na fara kiran Baby na naji ya ta tashi, or you are still in bed?" Ya faWa salonsa dake kassarata. A shagwaSe tace
"Aa na tashi nayi sallah Azkar nakeyi yanzu".

"Kinyi mana addu'a ko?" Ya tambayeta ta Waga kai kamar tana gabansa se ya sake cewa
"Zan fita Training ki kula da kanki i will call you when I'm back ok?"
"Allah ya kaimu" ta bashi amsa a sanyaye dan se taji bata so ya ajiye wayar. Be sake magana ba ya kashe tana ajiyeta kiran Ahmad ya shigo seda ta harari wayar kafin ta ansa.

AHMAD

Yana zaune a gefen gadonsa, shigowarsa kenan daga masallaci tun Asuba kwana yayi da tunaninta, tunda ya farka da Asubar yaso ya kirata amma ya daure ya bari gari yayi haske.
"Fatima, meya samu wayarki jiya ta?i shiga na kira yafi sau goma?" Ya faWa bayan data Waga wayar. Muryarta a kumbure kamar me bacci alhalin haushine ya cikata tace
"Bacci nayi da wuri, kuma ban sani ba ta shiga DND se yanzun dana tashi na cire".
"Haba nayi mamaki duk hankali na kuma ya tashi amma yanzu na samu nutsuwa tunda lafiya kike, ya school Win toh?" Ya faWa har yana sauke ajiyar zuciya se kuma tausayinsa ya kamata wato So Jarabtace wanda Allah ya dorawa kaWai yasan wahalarsa gashi itama idan batayi da gaske ba tana neman afkawa komar wanda ze wahalar da ita.

Ta mi?e tana ninke sallaya tace masa
"Lafiya lau nake, ya hanya? Kun koma Kano ko can kuka kwana?"
"A cikin Kano mukayi sallar Magriba ma" ya bata amsa ta haye gadonta tana cewa
"Masha Allah kunyi sauri gaskiya toh sannunka"
"Yawwa kema sannunki" daga nan suka Wanyi shiru se ya sake cewa
"Bari na barki zaki koma bacci ko yau weekend nima cikin gidan zan shiga na gaida Momy se na dawo na kwanta an jima idan Allah ya kaimu zanje gurin Baffa kina da sa?o ne?"
"Aa, babu" ta bashi amsa se yace
"Toh shikenan ki kwanta we talk later"
"Bye" daga haka ta kashe wayar taja bargo dan bacci be isheta ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login