Showing 246001 words to 249000 words out of 467220 words

Chapter 83 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12497

jansa hakan yasa ya mi?e dan dole yana mata mitar abinda takeyi. Ko a jikinta ta tasashi gaba, ta waiwaya ta gallawa Ahmad dake nan tsaye yana kallon ikon Allah harara kafin tace

"Waya sani ma ko kaima har sun lasa maka, to wlh nafi ?arfin ?aramin maye irinka manyan ma nan zasu ganni su barni". Dariya ta bashi dan har seda ya murmusa kafin ya zauna akan gado bayan da suka fice ta tasa Jay a gaba. Kwanciya yayi rabin jikinsa na kan gadon ?afafuwansa na ?asa ya tallafe kansa da hannu biyu ya zubawa POP dake Wakin ido. Meya samu Jay? Wane abu ya fara ko kuma yake aikatawa daman can dabe sani ba? Meya janyo sauyawarsa tun bayan daya dawo yake abubuwa ba tareda ya sakashi a ciki ba? Shi damuwarsa ba rashin including nasa da Jay bayayi a sabgoginsa bane ba Aa yanda yake abubuwan a ?udundune ne kamar mara gaskiya. Jay da ko ?ofar gida muddin yana nan baze fita shi kaWai ba seya rakashi amma shine ya iya tafiya har Abuja ba tareda rakiyar Ahmad Win ba, wannan be bashi mamaki sosai bama akan zuwa gidan Baba Al?ali da yayi nan ma shi kaWai. Yanzu sun fita lafiya ya dawo cikin wani yanayi daya kasa fassarashi. Babu wata alama a tattare dashi da zata nuna maye ko wani abu makamancin haka sannan daka kalle shi kasan baya cikin hayyacinsa, Fargabarsa da damuwarsa yasan menene yake damun ?an uwansa a yanzu.

Fatima ta faWo masa a rai ya zaro wayarsa daga Aljihu ya kirata dan yaji ya anta ciwon kan amma bata amsa ba se ya soka wayar a chaji ya tashi, seda ya cire T shirt Win jikinsa ya mayeta da Jallabiyya kafin ya fita dukda goma ta gota ya shiga cikin gida. Momy da Maimuna tareda Sarah autar Hajiya Binta suna zaune a falo, Momyn na kallo su kuma suna aikin filling Samosa.

"Manyan yan kasuwa" ya zolayesu bayan daya zauna suka gaishe shi. Sarah tace
"Dan ma Yaya ka?i ka bari mu fara kaiwa Mall Winka ai da wlh da yanzu munfi haka"

"Wannan jagwalgwalon ze bari ku kai musu?" Momy ta faWa se yayi saurin cewa
"Haba ba jagwalgwalo bane Momy gyare gyare mukeyi shiyasa ma ban amsa musu ba amma da mun gama bayan frozen har soyayye zasu ringa kaiwa ai naci naji da daWi kuma na yarda da tsaftarsu".
Sarah da Maimuna suka tafa cike da jin daWi kafin suka shiga tattare kayan aikinsu dan daman sun gama suka wuce kitchen. Bayan shigewarsu Momy ta kalli Ahmad tace

"Ina kukaje da Jafar ne uwarsa ta shigo Wazu tana ta hayagaga da faWar maganganu?" A ta?aice ya bata labarin fitarsu zuwa dawowarsu da kuma abinda ya faru yanzu a waje. Momy tace
"Allah ya rufa asiri toh, ta yuwu ko bashida lafiya musamman tunda ya dawo be zauna guri guda ba yana ta stressing kansa ga Ranar kwanakin nan da zafi ba irin wadda ya saba da ita bace, daman Wazu ina falon Alhaji Babanku ya kirashi yake gaya masa Jafar yaje gurinsa akan maganar zuwa tambayo masa aure ko?"

"Eh haka ne" ya bata amsa ta sake cewa
"A ina ne?"
"Wlh ban sani ba, yau mukayi zamuje kuma ya tafi ya barni"
"Au kaima baka sani ba? Koda yake ai na fuskanci kwanakin nan uwarsa ta matsa masa ni tunda ya dawo ma sau biyu ya shigo falon nan
"Uhm" kawai yace mata jin haka yasa itama tayi shiru da maganar can ta sake cewa

"Toh ya kukayi da ita Fatiman? Babanta yace a bashi sati huWu me tace maka akan hakan?"
"Bamuyi maganar ba Momy amma daman Baban nata yace ai wanda zasu karSi auran ne basa nan shiyasa yace a basu lokaci amma ko Wazu ma mun haWu yace yana gaishe ku"

"Toh muna amsawa, ya kamata dai a fara abinda ya kamata dai toh, bari kaga wasu Atamfofi Wazu *UMMU-MAHEER 07061838488* ta turasu a group Winta *BUYERS BATIK/ALIZA BATIK* ne kyau garesu quality kuwa ba'a magana gasu unique designs babban abin da yake burgeni dasu seka gama yayin Atamfar nan baka ci karo da me irinta a gari ba gasu basa koWewa sedai ka gaji ka bayar kai *BUYERS BATIK* fa ta haWu" ta ?arasa tana mi?a masa wayar.

Ba wani sanin kan Atamfa yayi ba dan yafi ganin kyan Lace shi a jikin Fatima nema Atamfar take burgeshi amma yana ganin *BUYERS BATIK* Win ta tafi da imaninsa. Ya ringa scrolling yana duba designs Win da duk babu na banza a ciki, harya hasaso su jikin Fatima dan kalolin duka zasu karSeta. Ya maida wayar yana cewa

"Amma sunyi kyau Momy"
"?warai ma kuwa, guda nawa za'a Wauka?" Momy ta tambayeshi se yace

"Ki zaSi wanda kike so se ki Waukarwa Maimuna ma nawace?" Ya mayar mata cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa. Ta harareshi tace
"Tun yaushe muka zaSi tamu, maganar lefenka nakeyi guda nawa za'a saka ko kuwa seta ?are sannan?" Se ya hau shafa kai irin na yaji kunya kafin yace

"Ai duk sunyi kyau ma"
"Se a saka duka design goma ce" daga nan suka cigaba da tattaunawa wanda duk maganar auransa Momyn take sako masa.

Jay kuwa bayan sun isa falon Hajiya kwanciya yayi akan kujera tana ta aikin mita ta tafi can kitchen Winsu na baya inda suke hura Itacen da ita ta saka dole ake amfani dashi ta samo garwashi a cikin kasko. Tsabar magana tana zuba maganin a wutar seda haya?i ya turni?eta ta fara tuttula tari har bata san sanda ta ture kaskon nata ba gaushin ya zube Allah ya rufa asiri akan Tiles ne carpet ba. Kansa kamar ze tsage masa haka ya tashi ya Wakko ruwa ya kashe garwashin ya bawa Hajiyar tashi bata daddara ba faWi tajeyi
"Shikenan ashe ba kai kaWai sukayi galaba akanka ba harda ni"

"Dan girman Allah Hajiya ki bari, ni lafiyata ?alau na gaya miki gajiya nayi kawai bacci bake da bu?atar nayi yanzu" yanda yayi maganar ya saka Hajiya binsa da kallo shi kuma jin bata ce komai ya juya yana tafiya da?yar saboda yanda zuciyarsa tayi masa nauyi Hajiyar kuma bata dakatar dashi ba. Kan gado ya kwanta ya rufe idonsa, wayarsa ta shiga ?ara a Jikinsa yaji cewar itace. Wani Sari na zuciyarsa na rasa masa ya amsa ya tambayeta dalilinta na aikata musu abinda tayi inda Wayan yayi galaba ta hanyar hanshi amsa wayar. Jin muryarta a yanzu babu abinda ze ?ara masa se ba?in ciki da damuwa. Har yanzu gani yakeyi kamar bada gaske bane, dukda a zahiri yaga komai ba gaya masa akayi ba amma so yakeyi ya ?aryata hakan ya cewa zuciyarsa ba gaskiya bane ko kuma komai be faru ba.

Idanunsa suka sauka kan wayar Ahmad da yake chaji ya yun?ura da?yar ya Waukota kansa na sara masa kamar ze tsage biyu. Number wayarta ya shiga dialing yana fatan ya zaman babu ita a wayar sedaj yana saka 0803 numbarta ce ta farko data zo a suggested contacts ga sunan da Ahmad ya mata saving dashi FATIMA da manyan ba?i se Jan Emoji me alamar zuciya a gaba. Ya runtse idonsa da ?afin ya buWe WhatsApp a hankali ya ringa bin chats Winsu kamar mr bitar karatu yana cike guraben maganganunta da ire iren daWaWan kalaman da take amfani dasu gurin magana dashi wanda saSanin haka chat Win nata da Ahmad babu wani armashi balle soyayya a ciki. Ya ga hotunanta da basu da yawa idan aka haWa da wanda ta tura masa shi daga haWuwarsu zuwa yau Win, wato yarinyar first class ma?aryaciya ce, ma ha'inciya kuma Azzaluma.

Ya tuna wayarsu ta farko data tambayeshi ko shikaWai Jay Wan Nigeria dayake ?wallo, me yasa tun a sannan be taSa hasaso cewar ita ce ba?

Maida masa da wayar yayi jikin chaji ya kwanta rubda ciki ya danne kansa da pillow. So be kyauta musu ba daga shi har Yah Ahmad su rasa wadda zasu so se wannan Azzalumar mara tsoron Allah. Shi ya gama tabbatarwa ma da tasan su, tasan gidansu Waya shirya komai tayi ya kuma godewa Allah daya saka ya ganota tunda wuri kafin tayi nasarar karya zuciyar Wan uwansa da babu komai cikinta face tarin Alkhairi da son kyautata mata. Yana jin Ahmad ya shigo lokacin kuma wayarsa ta sake Waukan ?ara a karo na babu Adadi amma be amsa ba se Ahmad ne daya shigo ya janyo wayar daga gefen kansa inda ya ajiyeta yana cewa

"Na gaya maka ka dena aje waya kusada kanka idan zakayi bacci bakaji kuma duk wannan ?arar yanzu se kace baka ji ba toh Afeeyah ce kar gobe kazo kana mun kukan ta ?i amsa wayarka".

Da hannu yaja wayar ya latseta gaba Waya ta mutu ba tareda ya amsa ba, Ahkad yayi sororo yana kallonsa, da kuma ya tuna ba matsalarsa bace se yaci gaba da abinda yakeyi ya gama yayi shirin kwanciya yabi lafiyar Gado. Zafin jikin Jay daya matseshi ne ya farkar dashi daga bacci dan shi bashida nauyin bacci ko kaWan, ya taSa Jay Win, zazzaSi ne rau a jikinsa har numfashinsa hucin zafi yake fitarwa amma bacci yake wanda da gani bana daWi bane. Ruwa ya samo me madaidaicin sanyi da ?aramin Towel ya ji?ashi ya fara shafa masa a fusak, Jay ya saki ajiyar zuciya ya buWe ido da?yar ya kalli Ahmad Win kafin ya lumshe su. Da taimakon ruwan daya shafa masa da Maganin daya saka ya tashi yasha a lokacin zafin jikin ya ragur masa se Azababben ciwon kai da yakeji kamar ?wayoyin idonsa zasu fito, kafin safiya ya fita hayyacinsa Idonsa yayi Jajir ga jijiyoyi a goshinsa kamar zasu faso su fito, yanda jikinsa ke karkarwar sanyi bayan yayiwo Alwala ya saka Ahmad dakatawa sukayi sallah a Wakin sannan ya kamashi suka fita a duku dukun suka tafi Asibiti.

"Wai me ya same ka? Lafiya kau muka rabu jiya meya sameka a can in da kaje kuma?" Ahmad ya tambayeshi. Cikin dauriya yace masa
"Inaga Malaria ce, kwana biyu sauro ya cije ni"
"Sedai a gidansu Afeeyan ka kwaso Malaria dan mudai gidanmu babu sauro, kafin kazo seda akayi fumigation kuma still kullum se an saka magani, kuma Malaria ce zata kwantar da mutum haka lokaci Waya? Zamuje Asibiti dai koma menene yake damunka da baka so na sani zasu gayamun" Ahmad ya faWa, shidai Jay be sake ce masa komai ba fama yak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e da jinyar fili data zuciya, abune goma da Ashirin yayi masa rubdugu lokaci Waya. Yarinyar daya Wora dukkan buri da tanadinsa akanta, Macen da yake So tamkar ransa, da ita yake fatan ?are rayuwarsa lokaci daya ta rikiWa ta dawo Macen daya fi tsana a duniya, tun saninsa da ita yake jin ?inta tun kafin ya ganta yasan wacece ita, abinda tayi musu a yanzu ya sake linka tsana da ?iyayyarta me tsanani a zuciyarsa. Ya gane dalilin daya saka jininsa da ita a matsayin budurwar Ahmad ya ?i haWuwa, Soyayyar da sukayi a rashin sani wannan ya karSeta a matsayin sakayyar abinda yake gayawa Ahmad dalilin soyayya da ita, Ubangiji ne ya nuna masa isharar cewa shi yake ?unsa So a zuciyar bayinsa bawai yin kan mutum bane ba amma ya tsinewa dalilin zuwansa Zariya da har yayi silar haWuwarsa da wannan Annamimiyar yarinyar me suffar salihai.

Asibitin Dr Hassan ya kaishi, basu tarar dashi ba se Dr Michel da yayi night duty shine ya dubashi. Ahmad yana waje yana jiransu dan daya shigar dashi fitowa yayi ya basu privacy. A ciki bayan Dr ya gama auna Bp sa saboda ciwon kai da yake shi yake damunsa kuma ido da fuskarsa ma sun nuna hakan. Cikin tsanaki ya kalleshi yace
"Bp ka yayi high sosai also rate na heart beat naka ya zarce misali me yake damuka?"

"Forget about it Dr, kawai ka bani necessary assistance and please don't tell anyone about it ka cewa Yah Ahmad Malaria ne yake damuna" Jay ya faWawa Dr Michel, Dr ya zura masa ido ya buWe baki da niyyar sake masa magana Jay ya haWa hannaye biyu alamar ro?o yace
"Please, do me this favor"
"Fine amma dole koma menene ka cireshi daga ranka saboda lafiyarka ta daidaita ka sani this will not be good for your career and..."

"I know Dr i will try my best" ya sake katse shi. Dr ya girgiza kai kafin ya danna ?ararrawar kiran Nurse se gata ta shigo. Paper daya rubuta prescription wa Jay ya bata ta tafi ta haWa komai ta kai Wakin da zasuyi admitting nasa zuwa Bp ya daidaita sannan ta koma ta gaya masa. Da kansa ya kamashi suna fita Ahmad ya tayashi har zuwa Wakin, ruwa ya saka masa wanda ya zuba Allurai a ciki harda ta bacci babu daWewa kuwa bacci yayi gaba dashi. Cikin damuwa Ahmad ya shiga tambayar Dr me ya samu ?aninsa yace masa Malaria ce. Ganin ya samu bacci yasa ya koma gida, Alhaji ya fara sanarwa Jay bashida lafiya yana Asibiti

"Toh Allah ya bashi lafiya, se a sanarwa uwarsa ai" Alhajin ya bashi amsa, se yaji abin wani banbara kwai ba yanda Alhajin ya saba ruwa da tsaki a lamarin Yayan Hajiya ba, koda yake daman ko a cikinsu basu fiya jituwa da Jafar Winba saboda rikici da taurin kansa sak irin na Alhajin ne dukda yanda Hajiya take so ya zama yafi kowa shiga jikinsa amma abin yaci tura shiyasa take ba?in ciki da shirin da sukeyi da Ahmad a yanzu. Daya gayawa Hajiya kuka ta ringa zundumawa harda tumami a ?asa tana kiran ta shiga uku ta lalace shike nan magauta sunci galaba akanta. Ta tattara ta tafi Asibiti can ta tare ita da jama'arta da surukanta data ringa wa waya tana gaya musu suzo an jefe Jay gashi kwnace magashiyyan a gadon Asibiti, Turai ta tafi mata tambaya dan su binciko wanda ya taSa Jafar Win, Momy da Anty sunje sun dubashi da daddare se sannan Ahmad ya koma saboda Hajiya da take a gurin tana ta faWar maganganu akansa, Alhaji ne yace shi yaje ya kwana da Jafar ita da jama'arsa kowa ya watse ya koma gida. Daze tafi ya tafi masa da wayarsa wadda yaga Missed calls Win Afeeyah sunfi Ashirin ga messages nan birjik na ban ha?uri akan laifin da besan me ta masa ba.

Ya jefa wayar a Aljihu, besan password Winsa ba daya buWe wayar ya kirata ya sanar mata abinda yake faruwa kodan hankalinta ya kwanta. Yana dabda shiga Asibitin ta sake kira ya amsa cikin nutsuwarsa yayi sallama.

FATIMA
Tana shiga cikin gida kaitsaye Wakinta ta shige tana jiyo Umma da Baffah suna magana Baffa yana cewa
"Wlh Ru?ayya ban taSa zaton haka zanji nauyin yaron nan ba, badan fa ya rigada ya ganni ba juyawa nayi niyyaryi amma babu dama"

Umma tayi shewa tace
"Malam, ai baka ma soma jin kunya ba se ranar daya fahimci yaudarar daka shirya masa kaida yarka, billahillazi in bakayi wasa ba seka gagara fita na wasu kwanaki saboda zancen mutane da nunaka da za'a ringayi". Sama sama take jiyo mahawarar Baffa da Umman, ta zauna kan katifa tana dafe da ?irjiz seda ta nutsu kafin ta latsa kiran layin Jay tana so taji ina ya tsaya tunda Allah ya taimaka ta sallami Ahmad yanzu se yazo. Wayar ta ?araci ringing be amsa ba ta sake kira nan ma dai shiru seta ajiye a zuwan ko yana hanya idan ya iso ze kirata amma shiru shiru har sha Waya babu Jay babu dalilinsa kuma be biyo kiranta ba zuwa sannan kuma hankalinta idan yayi dubu ya tashi to me ya faru? Kar dai yazo ya ganta tareda Ahmad shiyasa yayi zuciya ya tafi kuma ya?i amsa wayarta.

Data sake kira tana fara ringing aka katse, cikin sauri ta sake gwada kiran a zatonta ko garin ya amsa ne ya katse ita bama zata iya jira ya kirata ba sedai a karo na biyun aka shaida mata wayar a kashe take. Ta kwanta lamo hawaye na zubowa daga idonta, rejecting yayi kuma ya kashe wayar dan karta dameshi ta tannata yazo ya ganta tareda Ahmad kenan.

Tsohuwar wayar dayace ta dena amfani da ita ta Wauka ta saka sim ta kunna Data, WhatsApp ta shiga dan ta duba ko yana online bata tsaya duba duk sa?onnin da suke ta tuntuWowa ba ta wuce kan number sa. Mamaki ya kamata ganin Dp sa ya sauka sannan babu about hakan kuma tasan yana nufin yayi blocking nata kenanseta saki wayar a ?asa ta rushe da kuka, Umma na tsakar gida tana tattare kaya saboda hadari daya taso har an fara iska ta jiyo kukan nata da sauri ta le?a Wakin,
"Lafiyarki Afeeyah? Kukan me kikeyi me ya sameki?" Umma ta tambayeta. Cikin kukan tace mata

"Jafar ne Umma" Umman taja wani shegen tsaki ta sakar mata labule ta cigaba da abinda takeyi ranta na suya, idan ta buWe baki zagi zata zunduma mata shiyasa tayi shiru. Afeeyah tasha kuka ta gode Allah a daren kafin safiya ta Wora da kiran layin Jay da jera masa Texts na ban ha?uri da rantsuwar duk abinda ya gani yake tunani ba gaskiya bane ba amma shiru kamar an shuka dusa be amsa kira ko guda ba haka be bata amsa ba. ZazzaSi ne da ciwon kan gaske itama ya lafketa haka ta wuni a Waki Umma bata bi ta kanta ba seda Allah ya taimaketa Anty Sauda taje ita ta bata abinci da magani tasha harta samu ?arfin cigaba da kiran Jay Win. Kiran ?arshe da tayi shine Ahmad ya amsa, ta saki ajiyar zuciya me ?arfi sanda taga sakanni sun fara tafiya.

Muryar Ahmad me sanyi ta ratsa kunnenta, ba muryar Jay bace seda ta zare wayar ta duba dan ta tabbatar da wata kirane taga number Jay ce. Cikin muryarta data dashe dalilin kuka ta amsa sallamar kafin tace
"Dan Allah Jafar fa? Yana kusa?"
"Bashida lafiya yana kwance a Asibiti" Ahmad ya bata amsa, a rikice tace

"Yaushe? Meya sameshi? Wane Asibiti yake?"
"Relax, malaria ce inaga sauron gidanku ne basu san ba?o ba suka cijeshi, yanzu zan shiga gurinsa zan bashi wayar seya kiraki ok?" Ahmad ya faWi. Ta sake sauke ajiyar rai, muryar kama take mata da ta Ahmad amma babu dalilin da ze sanya Ahmad ya samu wayar Jay
"Nagode toh

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login