Showing 222001 words to 225000 words out of 467220 words

Chapter 75 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12124

cewa ba Alhajin ne kaWai a gurin ba, tayi sak kafin ta shiga rirri?e hijabi duk ta diririce da gani base an faWa ba kunya ce tayi mata rubdugu.

Alhaji ya nunata da hannu yana kallon wanda yafi sauran kalar ji?uwa da kuWi yace
"Gata nan, ita ce Surukar ?an naka". Wanda aka nunawa Hajita ya kalleta babu yabo babu fallasa kakar yanda sauran ba?in suke kallonta kowanne da yanayin da yake kan fuskarta yace
"Sannu Hajiya, ya me jiki? Ya kuma naki jikin?"

Babban abun ma shine bata san uban waye cikin surukan nata ba amma dai iyakar zubar da kai yau tayi ta tafka abin kunyar da ita da kanta yau ta gagara naWe tabarmar kunya da haukan data saba ae jan Hijabi takeyi ita ba abin ta cire ta maidashi daidai ba duk ta rasa abinda zatayi. Momy tayi sallama cikin kyakykyawar shiga ta Abaya ta yafa yalwataccen Mayafi akai bayanta Maimuna ce da me aikinta Amirah kowacce da dogon Hijabi sun Wauko manyan Trays. Har ta kalli Binta ta wuce ta samu gurin zama kan kujerun da suke daga gefe kaWan, su Maimuna suka ajiue kayan hannunsu suka gaida ba?in kafin suka fita sa'annan suka shiga gaisawa da Momy cikin dattako da mutuntaka.

"Itace Matata ta biyu Mahaifiyar Ahmad" Alhaji ya gabatar da ita. Baban Sirikin Binta yayi murmushi yace
"Ga kama nan kuwa har jikin ma irin nata yayi baza'ace ita ta haifesu ba" Alhaji Audu ya Wanyi murmushi sega Hajiya Rabi nan itama ta shigo a kamalance da sallamarta ta zauna suka gaisa.
"Ga kuma Amaryata" Alhaji ya gabatar da ita". Hajiya Binta ta muzanta iya muzanta, wannan abu da Audu ya mata ya kaita wuya amma kamar wadda aka zubawa glue aka li?e a gurin da take ta kasa gaba ta kasa baya haka ta gagara magana.

Momy da Hajiya Rabi suka mi?e a tare suka musu sallama suka fice, tun a hanya da suna dawowa daga Asibiti ya sanar da Hajiya Rabi, Alhaji Tamim Uban Mijin Hajiya ?arama yace yana tafe ze shigo dubashi dan yana Kano, ya sanar masa sun wuce gida basa Asibiti ya sameshi a can, shi yace ta gayawa Momy wadda take fushi dashi kan abinda ya faru. Sau Waya taje dubashi Asibiti amma kullum zatayi girki safe rana dare akai masa ita kuma Hajiya Rabi can zata wuni da dare ta dawo Ahmad ya Kwana dashi.

Abinda yasa yace a gaya mata zuwan ba?in yasab ba zata rasa abinda zata fitar dashi kunyarsu ba dan bata rabo da abubuwan motsa baki tunda yamma ce ba lokacin cin abinci bane ba gashi kuwa data tashi zuwa tazo musu da abubuwan taSawar da ruwa da Lemo. Shi ya manta ma da Hajjajun seda ta shigo, yanda yaji kunya kuwa dai ba'a cewa komai amma ya godewa Allah da ba ita kaWai yake aure ba, sedai a tafi da ita kaWai a baki domin sauran matansa sun fitar dashi kunya.

Kamar sun manta da tsayuwar Hajiyar a gurin Alhajin ya musu Bismillah suka Wan taSa abinda aka kawo musu. Alhaji Tamim da Abokanan tafiyar tasa wayayyun mutanene suka shiga hirar kasuwanci inda ko wannensu yafi kauri. Hajiya ta gama tsayuwarta kafin ta mi?e ?afafun da da yake cangalawa ta fice kamar kazar da ?wai ua fashewa a ciki. Tana fita ta haWu da Faisal ta tsareshi da tambayar suwaye a Falon Alhaji.

"Baban Abba T ne" ya bata amsa, seta Wora hannu biyu aka kafin kuma ta sauke da sauri har tana neman harWewa ta wuce cikin gidan da saurin bala'i. Jikinta har rawa yake ta kira Hajiya ?arama, bata bari sun gaisa ba ta shiga surfa mata bala'i harda Allah ya isa akan.
"Kin huta yanzu ai se su dawo suyita bada labarin sunzo sun tarar da uwarki kamar mahaukaciya" ta faWa tana rushewa da kuka kafin tayi cilli da wayar. Audu ya cuceta da be gaya mata su waye zasu zo ba yanzu yaja taje ta zubarda mutunchinta, surukin Hajiya ?aramar ne kawai ya gaisheta amma tana gani da Aisha da Rabi suka ahiga duka harda sauran Abokanansa suka gaisa a mutunce ba irin tata gaisuqar daya mata ta jeka nayi ka ba. Ta sake zuge tazugen rashin mutunchi ta ayyana yanda zataci kan uban kowa a gidan tunda taga alamar raini ya fara shiga tsakaninta dasu kuma ba zata lamunta ba amma yanzu bari ta fara gamawa da zancen Yakubu tukunna shine ?ayar da ya tsaya mata a wuya. Ta Alhaji Audu me sau?i ce saboda tana da maganinsa a hannu, wurudin da Turai ta bata zata cigaba dayi tana banka masa yana sha ya dawo hayyacinsa dan taga alamar yana neman yafi ?arfinta.

FATIMA
Ko a jikinta lissafin kwanakin zuwan Jay kawai takeyi wanda ita dashi sukeji kamar su janyo kwanakin su rage musu tsaho. Wani irin so da sha?uwane a tsakaninsu, yanda suka damu da junansu suke tarairayar juna seya baka mamaki ba zaka ce soyayyar gani Waya bace kuma a waya akeyinta. Hatsaniyar da kayi a gidansu Jafar Win ce ta kawo tsaiko a zuwan nasa ya ?ara kwanakin zuwansa Nigeria da sati Waya akan yanda ya tsara dan abin ya faru yaSa shi ya kuma Sata masa rai matu?a, idan yace zezo a lokacin da abun be idasa lafawa ba rigima zata dawo sabuwa ne domin dukda cewar baya son Fatima baya son auranta da Ahmad amma hakan bashi yake nufin ze zuba ido a Tozarta Ahmad ba, shi laifin Fatiman nema ya sake ninkuwa a zuciyarsa domin ta dalilinta ne aka yiwa Ahmad Win haka kuma ta zama silar da take neman sake janyo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu saboda abinda ya faru dole ze sake tsanata gaba tsakanin Yayan Hajiyarsu da Su Hassan sannan a silar auranta Alhajinsu ya kwanta a Asibiti.

A ?a'ida saura kwana uku yazo ranar yace mata an samu matsala se wani satin ze zo. Be gaya mata dalili ba, yanayin muryarsa da taji ta sakata tsurewa kodai wani abu tayi masa saya saka ya Waga zuwan? Cikin rawar murya kamar me son fashe masa da kuka ta tambayeshi dalili. Ya sassauto daga tunzurin da zuciyarsa take kai yace mata
"Babu komai, gidanmu ne babu lafiya an samu yar hatsaniya shiyasa kawai na Waga zuwan nawa saboda ze iya maido da ?urar data lafa".

Bata fahimce shi ba amma tunda dai ba ita ta masa laifi ba ai da sau?i. Ta ringa masa shagwaSa da sangarta harda kukanta akan ya fasa zuwa jibi bayan ta fara shirin tarbarsa, wannan ya sanyaya masa zuciya ya shiga rarrashinta da mata Al?awarurruka idan yazo kafin sukayi sallama ya ajiye waya.

'Ga mata nan irin su Afeeyah birjik a duniya akan Me Yah Ahmad ze nacewa waccen yari yar da babu komai tattare da ita se ba?in talauchi da sharri, daga maganar auranta ji abinda ya faru to inaga kuma ya aurota ya ajiyeta a gidansa ai se abinda Allah yayi kawai. Abin haushi da takaici kuma wai duk bada?alar nan da akayi yanda Ahmad yace ko gezau beji soyayyarta tayi rawa a zuciyarsa ba tana nan daram dam shi dai yayi Allah wadai da So ?aya tak irin na Yah Ahmad' Tunanin Jay.

AHMAD
Yana tsugunne gaban Alhaji bayan daya gama Salla masa magungunansa yasha ya kuma gwada masa Bp da abinda Dr Hassan ya kawo ya kuma koya masa yanda ze ringa masa kullum da safe shi kuma da yamma yake zuwa ya sake dubashi, Sati guda kenan da dawowar Alhajin babu inda yake fita saboda jikin ya?iyi masa yanda yake so, zuciyarsa a ?untace take, duk sanda yayi shiru abinda ya faru waccen ranar ne yake dawo masa dallah dallah. Wani irin abu yakeji a zuciyarsa da baze iya fasaltawa ba, ?ansa na cikinsa a gabansa ya faWi cewa mutuwarsa da rayuwarsa bata da banbanci a gurinsa shi kuwa wane irin bigire ya Wora rayuwarsa akai? Anya idan ya mutu ze ringa samun kyawawan Addu'oi daga zuri'ar daya tara kuwa?

"Alhaji da akwai wani abun ne?" Ahmad ya sake tambayarsa karo na uku, yana ta masa magana amma ya zubawa guri guda ido yayi shiru. Yayi firgigit irin na wanda ya farga daga wani tunani kafin ya gyara zama yace
"Babu komai, fita zakayi ne?"
"Eh Alhaji, yau Jafar ze taso da daddare zasu sauka Abuja, ina tunanin na tafi can na jirashi da safe se mu juyo tare"

"Toh Madallah hakan yayi Allah ya kawo shi lafiya, nima dai inaga Abujar zan bika muje can na zauna na lokaci ko na samu jikina ya daidaita dan a nan mutane ba zasu barni da hayaniya na warke yanda ya kamata ba" Alhaji ya faWa, Ahmad yayi murmushi, yasan da Hajjaju yake dan itace kamfanin hayaniya a gidan. Ba Alhaji ba hatta shi da yake yawan zama tare dashi idan tazo gajiya yake da sauraron maganarta kansa har ciwo yake Wauka inaga Alhajin da ba lafiya ce ta ishe shi ba?

"?arfe nawa zaka tafi?" Ya sake tambayarsa. Ahmad ya duba Agogo yace
"Da jirgin shida kona tara nake tunani dan yanzu zanje gidan Baba Al?ali yace yana son ganina".

"Akan maganar neman auranka ne, kayi ha?uri da abinda ya faru ban shawarce ka tarko aka kafamun na shiga da kyakykyawar niyya bansan cewar wanda yayi shi da wata manufarsa ta daban ba. Mun tattauna da shi yace ze kiraka ku sake yin magana daga nan ze yanke rana da lokaci da za'aje masa neman Auran. Dama ina so naji zancen Muhalli ka tanada ne ko kuwa baka fara shirin komai ba game da auran?"

Ahmad yayi kasa?e yana sauraron Alhaji, kalmar ha?uri da Alhaji ya fara da ita ta saka jikinsa sanyi la?was. Ya ringa tisa maganar Alhajin harya gama kafin ya fara tattaro amsar da ze bashi a zuciyarsa.

Shifa Fatiman nan sun kusa sati biyu rabon da suyi magana da ita tun ranar da Baffanta yace ya turo iyayensa be sake komawa ba haka be kirata ba itama bata neme shi ba ya kwanta jinya daga nan kuma wannan lamarin ya faru ya maida hankali ga jinyar Alhajinsu. Daman shi bashi ya tado da zancen aure yanzu ba Alhaji ne gashi yanzu har magana taja ana batun za'aje tambaya dukda cewar Mahaifinta ya bashi dama amma ai itama yana bu?atar amincewarta tunda dai da ita ze zauna idan bata sonsa baze samu farin cikin da yake fata a zamantakewarsu ba.

"Kayi shiru baka ce komai ba" Alhaji ya faWa yana kallonsa, ya shafa kai yace
"Dama Jafar nake jira yazo tunda shima da tasa maganar se mu shawarta inda zamuyi gidan"

"Toh yayi, da akwai filaye dana siya nan bayan Sufi Mart, kuje kuga gurin idan yayi muku se ku zaSi biyu a gina" Alhaji ya sake faWa.
"Mungode, Allah ya ?ara girma" Ahmad yayi godiya kafin ya tashi ya fita. Gidan Baba Al?ali yaje, har number Baffansu Fatima Al?alin ya karSa a hannunsa da zummar ze kirashi ya basu lokacin da zasuje haka ya bashi dan bakinsa ya kasa buWuwa ya fayyace wa kowa halin da suke ciki da Fatima. Idan yana da rabon auranta ya sani ze samu, idan ba rabonsa bace in sunje Mahaifinta ze musu bayanin komai, baya so ya faWi har yanzu basu samu daidaito da ita ba saboda kar daga baya Allah yayi faruwar auransu ya zama yan uwansa su ?i karSarta yanda ya kamata.

Ya faWawa Al?ali Yakubu filayen da Alhaji yace suje su gani in ya musu shida Jafar.
"Lallai kun gode, toh amma idan akace gini za'a tado zeja lokaci fa ta yuwu sama da s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hekara kafin ace anyi Auran nan dan nidai kunsan bana son wannan ginin burbur na zamani da akeyi wata shida ace ko ?asa da haka kaga anyi gini har an tare ruwa be daki bulo da ciko sun zauna da kyau ba, in dai ba kuna so a saka auran da nisa ba shekara zuwa da rabi ba kamata yayi ace an nemi ginannen gida ko kuma cikin waWanda aka fara ba'a kammala ba in ma tsarin ginin akwai abinda be muku ba kwaskwarima zatafi sau?i akan ace a tada sabon gini".

Ahmad ya jijjiga kai dan yayi na'am da maganar tasa Al?ali Yakubu ya sake cewa
"Zan same shi zamuyi maganar" daga nan suka sake tattaunawa har bayan la'asar sannan ya koma gida. Ya zata da wasa Alhaji yake da yace zashi Abuja seda ya koma ya tarar dashi da Hajiya Rabi a shirye wai tare zasu tafi. Jirgin ?arfe shida suka bi, A katafaren gidan sa na Abuja sukaji zango, gidane da bayyana tsaruwarsa ma Sata lokacine. Bayan shi yana da gidaje da bazasu irgu ba a Abuja Manya da ?anana banda Estate da Plazas da sauran Kadarori da iyalansa ma basu san da wanzuwar wasu daga ciki ba.

Manya Manyab Mansions Win da barin su da akeyi babu kowa ciki se masu aiki da suke kula da gidajen tasa yayi shawarar bayar dasu haya suka zama Masaukan Manyan ba?i tunda da komai na more rayuwa a ciki mutum sedai ya shiga yayi iyakar zamansa ya fita. Wannan gidan kaWai ya ajiye yake sauka a jiki idan yaje Abujan, duk zalama da son duniyar Hajiya Binta ya rasa yanda akayi bata taSa nuna sha'awar tana so ta koma Abujan da zama ba, a Shekarun baya dai Aisha ce ma ta ringa nacin daya raba musu gida, kodai ya maida Hajiyar wani guri daban ko su ya fitar dasu amma daya shawarta da Abokanansa akan hakan suka ce masa Aa, a girmansa da shekarunsa be kamata ace ya rarraba kan iyalansa ba, ai duniya ma se tace be isa da gidansa bane shi yasa ya kasa haWe su a inuwa guda wannan ne ya da?ile maganar.

Ahmad yafi gane sauka a Hotel idan yazo Abuja amma yanzu saboda Alhaji tilas ya shiga Waki ya kwanta yanajin duk babu daWi, Sha biyu da rabi na dare su Jafar zasu sauka amma Alhaji yace yayi kwanciyarsa in ya dawo ya kwana a Aiport da safe ya taho gida babu wanda ze fita Wauko shi a daren nan baze yi masa musu ba ya kwanta yana ta jiran kiran Jay aikuwa ?aya saura se gashi ya kirashi ta WhatsApp wai ya fito yana ina?

"Alhaji yace ka kwana a Aiport seda safe ka wuto gida" Ahmad ya bashi amsa yana dariya dan ya san abin seya zafafi Jafar aikuwa ya sha?a yayi tam yace
"Amma fa ce mun kayi zaka zo ka jirani a Abuja yanzu kuma kana cewa Alhaji yace menene Allah Yah Ahmad ko"

"Toh ai ina Abujan, tare muka zo da Alhajin shima ze tareka"

"Ya samu sau?i kenan? To nidai gaskiya ka saci hanya ka fito ina jiranka" cewar Jafar, Ahmad ya girgiza kai yace
"Kayi ha?uri ka zauna zuwa Asuba zan fito kasan yanayin gari yanzu yan one chance fa sun takura shiyasa naso na zauna nan na kama mana Waki amma da muka iso yace dole mu wuto gida tare". Saboda Haushi Jafar kashe waya yayi be cewa Ahmad komai ba ya ringa kiransa kuma ya?i ya Wauka duk ya damu ya kasa bacci.

Can jimawa seji yayi ana buWe Get, ta window ya le?a yaga Jafar na fitowa daga mota filin gidan tarwai yake da haske dan haka yana iya hango yanda ya cukule fuska. Masu gadi ne suka biyoshi da Back pack Winsa wadda daman ita kaWai yake ru?owa idan ze yau kuma ya ganshi da saitin Akwati me biyu da Kit, daga sama yake hangosu kuma dare ne amma a hakan yaga kyansu, bakinsa har kunne dan ya san wannan tsabar Masoyiyar da ake wa kowa rowarta ce, lallai Jafar da gaske yakeyi, a saninsa be taSa ru?owa wata Mace tsaraba.

Falon ?asa ya sakko tarbar sa nan ya tarar da Alhaji da alama motsin buWe ?ofa ne ya fito dashi shima. Jafar ya gaida Alhaji yana hararar Ahmad wanda ya gumtse dariyarsa jin Alhaji na cewa
"Ka karya mun dokar gida kana sane ko?" Shiru yayi Alhaji ya juya ya koma ciki se sannan Jafar ya farawa Ahmad mita suka wuce sama tare.

"Kai baka san dare bane wai ka bari da safe se kayi surutun naka mana" Ahmad ya faWa yana zama a gefen gado. Jafar ya shiga cire kayan jikinsa wayarsa daya ajiye kusada Ahmad ya shiga ringing.
"Toh fa, ruhi na kira" Ahmad ya faWa cikin sigar tsokana yana mi?a masa wayar ya karSa yana wani tura masa baki kamar yaro. A speaker ya saka wayar, muryar Afeeyah dake cakuWe da bacci ya ziyarci kunnuwansu a lokaci guda.

"Love, ka isa gida?" Ta faWa, Jay ya wani langwaSe kafin yace mata
"Yes Bae na iso gida, waifa Alhaji cewa yayi na kwana a Aiport ba za'azo a Wauke ba"

"Kai! haba dai" ta faWa" tana ware ido, yace
"Wlh fa, but na dawo, na gaji da yawa wanka nake so nayi yanzu, I'm sorry for keeping you late na hana kiyi bacci"

"Haba mana, kana zaton zan iya bacci Alhalin kana hanya ban san ka isa gida ko Aa ba?"

"Awwwnn I'm blushing" ya faWa yana shafa kai tareda satar kallon Ahmad dake kallon wayar babu kyaftawa yana auna kalaman me magana a cikin wayar Waya da Waya. Be sani ba ko kewar Fatima ce tasa yakejin muryar Budurwar Jafar tamkar tata ko kuma irin shau?i me nuna tsantsar soyayyar da take yiwa wanda take magana dashi wanda ya daWe yana fatan yaji daga Fatima ne yasa har yake hakaito ita take maganar ko yaya? Besan Jafar ya kashe wayar ba seda ya taSa shi yana cewa

"Da akwai abinci a gidan nan kuma? Yunwa nakeji wlh"
"This is past 1 fa Jafar kai kake neman abinci irin wannan lokacin?"

"Bazaka gane ba, zumuWin ganin Afeeyah yasa na kasacin komai, naji haushi sosai da ba zan ganta yau ba, Allah badan Alhaji ze hana ba yanzu zan tafi Kano irin 6 na isa na wuce gidansu kawai"

"Ka Wauka a Turai kake kenan ko Yaya? To a Naija ?wamushe mutane akeyi a Abuja-Kaduna Road yanzun da tsakiyan rana ma balle ka kai musu kanka da daren nan, Allah ya tsare hanya kaga Ransom Win da zasu saka akanka nasan sedai FIFA ta biya badai Alhaji ba".

Da Jafar yayi wanka ya haWo Tea nan ya hana Ahmad sakat da zancen Afeeyah, idan ya buWe wayarsa ze nuna masa hotonta se kuma yace
"Aa ma,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login