Showing 453001 words to 456000 words out of 467220 words

Chapter 152 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12190

dai ta haWa kaida ka kwasota can ku ?arata amma ni babu ruwana daku".

Har sallar isha'i suna gidan lokacin Alhaji ya dawo dan sanda sukaje baya nan seda suka shiga ta gaishe shi kafin ya mayar da ita gida be kuma tsaya ba yana sauketa yayi tafiyarsa. Duk seta tsargu, me yake shirya mata ko kuma me yake nufi da ita dan tasan shirunsa ba Alkhairi bane. Yanda tayi tunanin zata iya jurewa ta shareshi se ta nemi gazawa. Allah ya sani ya mata banzan sabo a Wan lokacin da suka kasance tare. Kwana biyun nan da tayi ba tareda shi ba ita kaWai tasan yanda taji danma yanzu tana bacci sosai data fara tunaninsa bacci yayi awon gaba da ita shikenan kuma se idan ta sake tashi. Harta kwanta tunani da kewarsa ta addabeta ta tashi bayan ta zame Ahmad daga jikinta dan tun jiya da sukazo ya ganta da zasu tafi be bisu ba, falo ta koma ta kwanta akan kujera ta kirashi, ringing biyu ya Waga yayi shiru a hankali ta saka masa kuka.

Jay dake zaune a falonsa yana shan tea bayan daya gama lallaSa Fathiyyah tayi bacci suna zaune lafiya suna yar soyayyar su daga taci grapes ta fara amai tana gamawa kuma jikinta ya saki tace bacci takeji ta kwanta shine ya dawo falo ya kunna Tv yana so ya kawar da kewar Afeeyah dake neman fin ?arfinsa. Ya fahimci tana da raini, idan kuma ya sake mata baze iya ?wan?wasa taba shiyasa yayi banza da ita yana so ya nuna mata ya rayu a baya babu ita yanzun ma babu abinda ze rage shi idan bata nan ya kuma san a yar banzar fitina irin tata ba zata iya masa fushi ba yanzu kamar yanda shina baze iya mata ba amma beyi zatonzata sakko da wurwuri haka ba har wani tsalle yayi da kiran ya shigo amma dan ya nuna irin be damu ba shine ya Waga yayi shiru.

Yana jinta tana kukan dake dukansa har cikin ransa amma ya dake. Baya son kukan mace ko kaWan amma dalilin ta ya koyi dakewa dan Yah Ahmad yasha gaya masa haka take masa se tayi abun laifi seta kama kuka yanda sedai shi ya Sige da rarrashinta sanin wannan halin nata yasa yake nuna be damu da kukan nata ba dan yasan muddin tasan yana affecting nasa shikenan ya shiga uku ta samu makamin ya?ar sa. Ta ringa rera kukan kusan minti biyar ?iris ya rage ya fara rarrashi yaji tana cewa
"Kayi ha?uri, na kasa danne kishin kana can tare da wata mace shiyasa kawai na taho. Idan na gidan zanfi samun nutsuwa akan ina can ni kaWai bayan na saba koda yaushe kana tareda ni". Gashin jikinsa suka zuba, muradin kasancewa taredaita ya motsa masa. A hankali yace
"Zaki iya fitowa yanzu?" Ta dakata da kukan ba shiri ta kalli agogo, ?arfe goma da rabi da minti biyar. Yau Win da wuri Umma ta kwanta mura takeyi tasha magani a Baffa kuma be jima da shigowa ba bata zaton yayi bacci sannan. A hankali kamar tana gabansa ta girgiza kai kafin tace
"Dare yayi fa"
"Toh shikenan, bari ni nazo" ya faWa a kasalance kafin ya kashe wayar. Ta rasa ya zatayi, tasan tunda yace gashi nan to zuwan zeyi. Ba'afi minti goma sha biyar na se gashi ya kirata yace yana waje. Tayi ?wal ?wal kamar zatayi kuka da harta tsara yanda zata sulale ta fita se kuna tajiyo Baffa ya fito tsakar gida ko me yakeyi se Allah. ?asa ?asa tace
"Baffa yana waje, ni wlh kunyarsa nakeji bazan iya fita ba" ya kashe wayar kawai se jiyo wayar Baffa tayi tana ?ara ta kasa kunne tana ji suka gaisa bata san me yace masa ba taji yana subhallahi bari na dubota toh tanajiyo takun Baffan tayi maza ta kwanta kamar me bacci a falon seda ya kira sunanta sau uku kafin ta tashi tana matse fuska Baffan yace
"Kinyi bacci ashe, ga Jafaru can a waje ya kawo miki maganin wai. Wannan ciwon kan naki dai ya kamata ki koma kiga likita tunda sunce duk sanda ya motsa kije".

Bata jima ba ta dawo cike da farin cikin albishir Win da yayi mata na tafiya second phase na honeymoon, koda yake dama basu gama ba aka katse su. In four day's time yace zasu tafi ta kwanta cike da murna amma data tuna ups and downs Win da suka sha a waccen tafiyar se murnarta tayi ?asa, a ranta ta ringa tunanin kamar itama akwai abubuwan daya kamata ta gyara ?ila su fahimci juna. Ta tuna maganganun da sukayi da Anty Sauda jiya da tace mata ta fiya kishi idan kuma har bata sakawa zuciyarta salama ba bazata taSa jin daWin zaman aurenta ba zata ?are rayuwar ta ne kullum cikin ?unci tun kuma yana ta tata wata rana seya gaji domin duk yanda mutum yake sonka idan baya samun farin ciki tareda kai dole ze bi inda kwanciyar hankalin sa take, wannan ta ri?e za kuma ta gwada ta gani.

One last chapter.

*ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA YAN BAIWA*
*Ya akaji da mining? To ku marmatso kusa domin nazo muku da sabon al'amari da ze wanke muku takaicin mining da mukeyi tayi bamu san inda muka sa gaba ba. Shin yar uwata kina da labarin META FORCE kuwa?*
*META FORCE sabon kasuwanci ne a duniyar crypto, tabbas Meta force decentralised chain ne nasan yan baiwa sun san abinda ake nufi ga wanda kuma be taSa jin kalmar ba yana nufin kasuwancin da idan aka fara shi ba'a taSa iya kullewa ko a gudu da kuWin mutane. Yanzu kun banbance tsakanin platforms na cuta da META FORCE ko?*
*META FORCE kasuwanci ne na duniya baki Waya bawai iya Nigeria ba, kamfani ne da suka zo da tsare tsare suna kuma da coin nasu na kansu wanda cikin jerin manyan coins da ake saka ran zasu tarar da darajar Bitcoin nan da wasu shekaru yar uwa karki bari ayi wannan tafiyar ba tare dake ba idan har kina da hali ki saka hannun jari a tafiyar META FORCE da yardar Allah se kin gode mana. Sirrin tafiyar META FORCE ita ce aiki a team me ?arfi. Da yawa zancen referal da ake ta faWa shi yake saryar muku da guiwa da shiga META FORCE, to bari kiji yar uwa idan har kinyi register cikin Team me karfi tamkar na MAMAN NASREEN zaki dara. Team ne dake Wauke da mutane da suka daWe da wayewa a digital marketing. Bakya bu?atar lallai se kin kawo referals kafin spill over ta tarar dake sedai idan kin so kiyi sharing abin alkhairi daya sameki tareda yan uwa da abokanan arzi?i. Ga yanda tsarin yake*

*META FORCE*

*A yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency, akwai Project dayawa acikin META FORCE wanda akayi lunching da wadanda ba ayiba amma za ayi nan bada jimawa ba. Guda uku da aka rigada akayi lunching sune*
*TACTILE*
*Uniteverse*
*Royalty Nft*
*1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zaki shiga meta force sai ka arayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din. Tactile yanada levels guda 12 kowane level da kudinshi*
*Level 1 5 dollars*
*Level 2 10 dollars*
*Level 3 20 dollars*
*Level 4 40 dollars*
*Level 5 80 dolllars*

*Spillover*da*over flow*
Sune kuWin da kamfani yake biya na aikin da team sukayi, hajiya kina zaune ko baki kawo kowa ba spill over zata tarar dake idan har TEAM Winki is active ma'ana suna aiki sosai kamar dai team Win MAMAN NASREEN, abun kuma yana ?ara armashi idan ya zama kema kin kawo wani yayi register a ?asan ki amma fa ba dole bane, kowa ya sani dai ko wanne kasuwanci yana ci gaba ne daga yawan traffic da yake akansa dan haka yawan jama'ar team Win ku yawan yanda kamfani zatayi appreciating naku ta ringa watsa muku ruwan spill over kamar a August.
*Uniteverse*
idan kashiga uniteverse munada tier 1 to 9
*Tier 1 50$*
*Tier 2 100$*
*Tier 3 200$*
*Tier 4 400$*
*Tier 5 800$*
*Tier 6 1600$*
*Tier 7 3200$*
*Tier 8 6400$*
*Tier 9 12800$*

*Royalty* NFT

*level 0-Zero NFT*
*level 1-Activator*
*level 2-Supervisor*
*level 3-Manager*
*level 4-Pro-manager*
*level 5-Pacesetter*
*level 6-Ambassador*
*level 7-Millionaire s club member*
*Masu NFT ana biyansu albashi duk wata wani lokacin ma sau 2 a wata kuma salary dinka yadanganta da level Win da kake*
*Nasan yan baiwa sun san me ake nufi da NFT kati me daraja kenan wanda shi kaWai idan kika siyar ze kawo miki kuWaWe da se kinyi kukan farin ciki ga wadda ta shirya bin jirgin tsira jirgin Alkhairi ta tuntuSe mu kai tsaye akan 09046470308*
*META FORCE tafiyar da babu nadama da yardar Allah*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 47*

Satinsu biyu a france Jay yayi resuming field domin ?arasa watanni tara da suka rage masa contract Winsa da club Win tayi expire wanda kuma daga shi yace zeyi retire, a sati biyun sosai taji daWin garin. Ya kaita yawo cikin Paris da makwafta, guraren sha?atawa shopping kusan babu wani babban kantida be kaita tayi siyayya ba dan wannan karon ma daga ita se kayan jikinta suka taho. Zata iya cewa wannan tafiyar harta fita farko daWi kodan yanzu ta sake karantar halayyarsa kuma tana ?o?arin koyon zama dashi ne. Dukda dai sukan haura, kusan rana bata fitowa ta koma ma ba tareda ya mata abinda take ganin be kamata ba dukda idan tayiwa Badar ko Anty Sauda ?orafi sukan ce mata wai ba wani abu bane, dama haka zamantakewar aure take se ta ringa tunanin to kenan ita da me tayi?.

Babban abinda yake haWasu faWa kusan kullum shine tashin sassafe. Se yace wai ba zata koma bacci ba idan har shima ba zeyi ba, ga wani mugun baccin daya sar?e ta ko a zaune gyangyaWi takeyi haka zata zauna idan yana morning workout by mistake bacci ya Wauke ta ya ringa sababi na babu gaira babu dalili kenan gashi bayada uzuri komai ?an?antar kuskure idan tayi ya ringa faWa kenan balle kuma ace tayi masa abunda tasan baya so ranar se tayi kuka ta ringa binbini kafin ta samu ya sakko su shirya kuma a haka kullum nanata mata yakeyi yana sonta, his life is now complete with her by his side da can kawai gararanba yake a duniya with no focus yanzun ne yake jinsa mutum na sosai. Halayyarsa da sabon yanayin data tabbatar da na shigar ciki ne da take experiencing dukda bata da tabbas yasa komai yake dagule mata. Se tayi da gaske take iya gujewa jidalinsa.

Satinsu huWu a can ya taho Nigeria dalilin Fatiyyah da bata da lafiya sosai har an kwantar da ita a asibiti. Tayi mamaki sanda zasu taho da ko kusa Fatiyyan batayi wani tashin hankali ba dan har gidan ya kaita suka gaisa ta mata sallama rana Waya kuma suka tafi ita ta wuce Abuja dan tace ba zata iya zama a gidan babu shi ba su kuma suka wuce Lagos in da sukayi catching flight Winsu to Paris tun zuwansu kuma ta lura akwai cigaba sosai cikin ala?ar Jay Win da Fatiyyah. Kusan kullum zece wai tana gaisheta ko da gaske yake ko ?arya ce ma duk shiya sani ita dai tace tana amsawa duk da ma baya kiranta a gabanta kuma ko ita ta kira baze taSa amsawa in her presence ba tunda lura dagaske kishi ne da ita kamar me, har tsiya yake mata yace wai ita wadda tayiwa ?wacen mijin ma ta ha?ura ta sauke makaman ya?in ta amma ita ko sunan Fathiyyah taji ranar wuni take tana kumburi kamar flour, sedai kawai tace hmmm dan tsakani da Allah ko sunan nata bata so taji a bakinsa. Kishinta takeyi kamar babu gobe, ita se yanzun ma ta fahimci tun asali soyayyar Jay tana daga cikin abinda yasa ta kasa gina zumunchi me kyau da Fathiyyah dukda ita taso hakan, in suna Nigeria a lokacin kusan kullum seta shigar mata musamman saboda abinci tunda ita ba girki takeyi ba ta kance kuma abincin Fatiman yafi na masu aikinta daWi amma ko ta shiga bata wani sakewa da ita balle yanzu kuma da suka haWa miji, son sa takeyiwa Jay bata zaton ze barta ta kwatanta ko irin zumunchin da sukayi sanda suna faccaloli balle har ace yafi haka.

JAY
Zuwansa Nigeria ya tarar da babban Albishir na cewar ciwon da Fathiyyah takeyi ba komai bane illah laulayin ciki. Har kuka seda yayi, irin murnar daya nuna tasa kaso casa'in na haushinsa da Maman Fathiyyan takeji ya ragu dan dama tunda aka sanar mata da zancen cikin take godewa daya kawowa yarta makamin da zata ya?i Fatima cikin ruwan sanyi yanda kuma Jay ya ringa Sarin jiki kamar ze haWiye Fathiyyah ya canzota ya sake fatanta mata zuciya harta ringajin ina ma tare da Fatiman suka zo taga wannan abun tasan ta shiga gidan yarta da burika tunda ita gata me cikin haihuwa zata zo ta cika gida da yaya ta mallake komai se gashi Allah ya nuna mata iyakarta, dama kuma Malamin ta ya gaya mata da zarar Fathiyyah tayi ciki burikansu da dama zasu cika zasu same shi yanda basu tsammata ba kullum cikin jiran cikin take da ake ta ce mata rabon nada nisa at long last dai bayan shekaru goma gashi ya iso, zata mayarwa da mutane da yawa martani ciki harda uwar Jafar Win dan sanda Fathiyyah tayi yaji bayan auran Fatima data kira Hajiyar cewa tayi karsu sake kiran ta akan wata Fathiyyah da ko haihuwa bata yi. Seda ya kwana biyu kafin ya tafi Kano sanarwada Hajiya Albishir dan bata ma san da zuwan nasa ba ya kuwa je ya tararda ita ba a yanda yaso ba

Gaba Waya Hajiyar ta sake zabgewa tsufa ya bayyanar mata lokaci Waya ga ?afarta data kama ciwo ka'in da n'in abun dai ba'a cewa komai kwata kwata beji daWin ganinta ba musamman data fasa masa kuka tana cewa ita ta gaji ma da ruyuwa tunda kowa baya sonta gara ta mutu kowa ya huta. Tunda ya tafi kaWaici ya ?arun mata babu me zama da ita suyi hira cikin yayanta. Naziru yana can a hannun hukuma, Alhaji Zakariyyah ya dena fita idan ba tareda wani ba saboda ciwonsa daya sake ta'azzara na mantuwa Yakubu yakan le?a ta a rana sau Waya da safe ko da dare yaga yanayin jikinta se Faisal matan ma sukan Wan je jefi jefi amma duk ba kamar Jay Win ba. Basa sauraron damuwarta musamman Yakubu tana fara magana ze hauta da faWa yace bata tausayin kanta, hawan jini yana neman ya kasheta amma kullum ba zata dena saka damuwar wasu mutanen a zuciyarta ba idan tayi ?o?arin ta nuna masa abun na ci mata rai ne faWar ita ce zata rage mata raWaWi baze fahimta ba, dama Jafar shi kaWai ne yake sauraron duk ?orafinta da maganganunta.

Tana ji tana ganin ana abubuwa a cikin gidan amma bata da ikon cewa ?ala, ga Wan iskan Hussanin nan se ya ringa shigar mata Waki ta yiwa uwarsa magana akan bata so ta hanashi amma ya?i ji da tayiwa Alhaji magana kuma shima cewa yayi gidan uban Usaini ne dan haka ita ko shi babu wanda ze masa shamaki da shiga tunda dai ba wani abu yake mata na rashin kyautawa ba balle tace ya mata kacaca haka randa za'a kai Lefen Salim maka yan uwan Momy suka ringa shiga har Waki suna ci mata mutunchi a faWar ta dan dai jaje suka shiga yi mata na abunda ya samu Naziru da ita kanta seta juya abin ya koma wai cin mutunchi data sake kaiwa Alhajin ?ara a maimakon ya bi kadin zance ya bi mata ha??inta se ya Sige da yi mata faWa har yana ce mata idan har zata ringa masa gutsiri tsoma a gida to se ta koma can wani gidan dan daman saboda kar kaWaici ya mata yawa a rabata da inda ta saba rayuwa yasa yace ta zauna a gidan amma tunda yaga alamar ba zata canza hali ba to shi baze iya surutu ba salin alin seta bar masa gida. Ranar tayi kuka kamar ranta ze fita a lokacin kuma ta sake tabbatar da dagaske fa ta rasa aurenta kuma ta rasa Audu. Nadamar da bata zaci zatayi ta ba ta fara saukar mata har ta zauna ta ringa tariyo baya tana auna abubuwan da suka faru a ?o?arinta na gano kuskuren da tayi da za'ace alhaki ne yake bibiyarta amma ta kasa gano komai.

Kowa yana cewa tana da son zuciya abinda ta kasa fahimta shin laifi ne idan mutum yaso kansa kuma yaso ace yayansa sune sama da kowa? Duk fa abinda tayi tayi shine saboda ta samu mijinta ta kuma inganta rayuwar yayanta wanda daga ?arshe duk sukayi masa butulci, idan har ba'a tausaya mata halin data tsinci kanta ba ai kuma be kamata ace kowa ya tsaneta ba. Wannan takarar da Alhajin ya mata tasa dole ta kama kanta dama bata ko fita tsakar gida saboda ?afarta komai a Sangaren ta takeyi su kansu matan gidan ba shiga shirginta sukeyi ba, da farko kusan kullum suna ?o?arin le?ata su duba ta da suka lura ma kuma zuwan nasu ba so takeyi ba musamman da Alhajin ya tarasu yace baya son duk wani abu da ze ringa kawo saSani tsakaninsu da Binta shikenan suka kama kansu tunda dai bata son abin arzi?in. Shidai Jay daya gaji da sauraron ?orafinta yace tayi ha?uri sannan ya kwaza mata Albishir Win daya taho mata dashi aikam take kukanta ya koma na murna. Ta ringa hamdala tana cewa

"Ashe dai ina da rabon ganin jininka Jafar? Ashe dai kaima zaka haihu? Ni dama nasan ubangiji baze bari ma?iya suyi nasara akaina ba. Duk masu fatan jinina ya gauraya dana tsiya sedai ta ?are musu akansu Allah nagode maka daka saka ba waccen yarinyar bace zata haifawa Jafar yaya. Allah ka toshe ta kasa ta gama haihuwa kenan har abada,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login