Showing 189001 words to 192000 words out of 467220 words

Chapter 64 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12142

wai wancan satin ya kawo mata wasu Wirka Wirkan yayan ?abilu gida wai Yawon Campaign suka zo basu da masauki duk Hotel da suke Kano bega inda ze kama musu ba se gidansa yace ahine ta zo nan take gaya mun na kirashi nayi masa tatas ya sallamesu be daddaraba shekaran jiyan sega wata ya sake kaiwa wai sati ma zatayi a gidan shi zasu tafi Abuja dan haka zata zauna a gidan har ya dawo data kira waya ta gaya mun na sanarwa ubansa bece komai ba, se Al?ali na kira na gaya masa shi kuma ya kirashi sukaje can aka kashe maganar to Allah yasa dai yaji, Haba Yanda kika san su kaWai ne Yaya a gidan nan kullum cikin sakani magana da Wakko mun zance suke Salim da Babana na rasa yanda zanyi dasu".

"Hmmm, Anty Aisha kenan, ai bazangaji da gaya miki ba kin tafka kuskure a baya kuma sakamakon sa kike girba a yanzu. Sufa Yaya kiwo ne Allah ya bamu, ba kuma iyakar wanda ka haifa daga cikinka sune naka ba, Malamai fa suna cewa ranar Lahira hatta akan gidan auranmu da zamantakewar mu se anyi mana Hisabi kinga kenan dole mu yi iyakar iyawarmu gurin ganin mun sauke duk wasu nauyi daya rataya akanmu shine kuma ya haWa da kula da tarbiyyar yayanmu da duk wand suke zagaye damu. Kinga waWannan yaran da kika ringa zuba ido ana cutarwa? Rayuwarsu ta ringa gantafalfala alhalin kinada halin taimaka musu ki kwatar musu yancinsu ta yanda koda basu samu dukkan gata ba zasu samu rangwamen halin da suke ciki amma kika naWe hannu da sunan ba ruwanki baki shiga abinda ba'a sanyaki ba wlh ko kaffara bazanyi ba harda ha??insu cikin abinda ya saka kika gaza ganin daidai a cikin taki zuri'ar.

Kuma irin tarbiyyar da kika bari aka ginasu akanta ita naki yayan da suka tashi suka Wauka, abinda da yawa muke kasa ganewa kenan a duk sanda kaga ?an wani musamman na kishiya yana abinda be kamata ba kar kace babu ruwanka ko bazaka tsawatar masa ba domin ze cuWanya da naki Yayan, duk bakin tarbiyyar da kika ha?i?ance kina yi musu kuwa kina can ba zaki san lokacin da zasu Wauki halaye marasa kyau Win da kika bari suka ci gaba ba.

Kinzo gidan nan kin tarar da yara da yawa, da ace ke me dabara ce a sannan jan su zakiyi a jiki kiyi musu irin tarbiyyar da Kike fatan yayanki su tashi akanta, haka mata masu wayo sukeyi suja yayan kishiya a jiki su kula dasu da tarbiyyarsu karki taSa duba halin uwarsu ko abinda zata miki domin taki gaban kike gyarawa, yanzu wa gari ya waya? Banda Ahmad da Matan da kika samu Allah ya duba miki ya sassauta abin akansu dukda suma Win da nasu, gaba Waya yayan gidan nan babu wata sha?uwa ko soyayya a tsakaninsu, kowa kansa ya sani wlh ina jiye muku ranar da mutuwa zata fara Wauki Wai Wai tsakanin Iyaye ko yayayen, kar a wayi gari a ce cikin Rayayyun yan uwa a rasa masu duba bayan abinda ?an uwansu ya bari.

Wlh ki farka ki dage da Addu'a ki kuma sa a miki Allah ya haWa miki kan zuri'arki dan wlh cikin waWannan Yayan naki Ahmad kaWai nake da tabbacin yau idan wani cikin sauran ya faWi ya mutu baze bar zuri'arsa tayi kukan maraici ba, amma kinga wannan Uban namu da Salim? Allah ya rufa asiri kawai kawunansu kawai suka sani sedai Allah ya duba ya shiga cikin Lamarin".

Jikin Momy yayi la?was kamar an zubawa Salak gishiri, maganganin Maimuna sun shigeta kuma ta sani gaskiya ta faWa a yanzu ne take nadamar rayuwar baya data zama kamar hoto bata taSuka komai gurin gyaranmakauniyar tafiyar da akeyi a cikin gidan ba, a lissafinta idan taja nata yayan sun isa suyi rayuwarsu sedai kuma ta tafka kuskure gashi kuma yanzu tana girbar abinta saboda wannan hanyar da Yayayen nata suka Wauka ta kowa kansa ya sani ta samo Asali daga abinda suka tashi suka gani anayi a gidan nasu ne.

Maimuna na kurbar shayi tace
"Gara dai ki yi ta kanki kina kallo ita Harbutsatstsiyar gidan naku duk da rashin kan gadonta batayi saken da kan yayanta ya rabu ba kuma komai da ita suke shawara bakinsu Waya ke kuwa fa? Banda Ahmad wa yake zuwa ya dur?usa gabanki ya faWa miki halin da yake ciki ko ga wani abu da zeyi?"

"Allah ya rufa asiri dai Maimuna, gama cin abincin mu fita rana ta farayi kuma yai Juma'a ki samu ki gama da wuri" da haka suka bar zancen.

Ahmad kuwa bayan fitarsa Kusan karo sukaci da Hajiya dake fitowa daga Wakinta da tabarma a hannunta da alama shimfiWa zatayi ta zaunasana'ar tata ta sakawa masu shiga da fice idanu.

"Aa, Amadu har ka fito kenan" ta faWa fuska a washe ba kamar Wazu dayace .ata Zasuyi tafiya tareda Alhaji ba.
Cikeda gajiya da tambayoyinta yace
"Na fito Hajiya, na gaya miki Alhaji yana jirana tafiya zamuyi"
"Ayyo to, da ai da Yakubu zasuje,sedaga baya Yakubun yace yana da aiki nace ma suje da Faisal shi kuma wai tes zeyi a makaranta ashe kai ya kira banda Alhaji seya tattagoka tun daga Abuja base ya Wauki Direba yayi tafiyarsa ba? Shikenan dai, ya akayi yau naga ka shigo mana gida hannu na dukan cinya babu yar tsarabar daka saba ri?owa ne?"

Ahmad yai zuguWi yana kallonta se kuma ya zabura daya tuna abi da yake gabansa ya tafi yana cewa
"Idan mun dawo zan kawo muku" ya wuce da mamakin Hajiyar, tsarabar da kullum ya kawo haka zata amshe tana aibata shi tana masa shaguben Allah sa da kuWin Halal ya siyo shine yau tambayar bata gani ba?.

Hajiya ta bishi da kallon tsana ?arara tana jan ?wafa, ta tsani Yaron ya kuma zamar mata ciwon ido dan ta rasa ya zatayi dashi. Yanzu da Ala?a take ?ara ?arfi tsakaninsa da Alhajin ya sake dagula mata lissafi ba kuna zata lamunta ba duk yanda zatayi setabi gurin datseta tun kafin tayi ?arfi. Ko yanzu da gayya take ta jansa da magana saboda ya Sata lokaci har Alhajin ya fito yayi masa tijara burinta kenan ba wani abu ba.

A gurguje ya shirya, wata dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya ya saka ta haska Fatarsa dake da duhu bacan ba Winkin babbar riga ne, be sakata ba ya ri?e a hannu da hular da ze saka da Agogo, Takalmi da Azurfa, cikin sauri ya fesa turare ya fita da silifas a ?afarsa. Alhaji na tsaye bakin motar da zasu tafi a ciki an kawo masa ita daidai Barabder yana waya da alama Ahmad alamu sun nuna Ahmad kawai yake jira kenan.

Cikin tsantsar ladabi jikinsa har rawa yake ya dur?usa yana gaida Alhajin, wata Kafirar Shaddace data sha aiki na Alfarma a jikin Alhajin, yanayin ?irarsa ga shigar da yayi ta ?asaita yasa kwarjininsa nunkuwa tamkar wani Basarake. Ba yabi ba fallasa ya amsawa Ahmad gaisuwar kafin yace masa
"Ya haka zaka fito kamar wanda aka koro?"
"Babu komai Alhaji, daman so nake sena shiga mota sena ida shiryawa".

Harara Alhajin ya maka masa, yasan abinda yake nufi dan haka sum sum ya shige falon ya shiga ?arasa shirinsa. Tsaf ya fito bayan ya kafa hula Babbar rigar ce dai be saka ba saboda karta yamutse kuma takura masa ma zatayi, data son ransa ne ma Normal Kaftan ze saka na yadi ba shadda ba sedai sanin halin Alhajin tsaf idan yayi shigar da bata gamsheshi ba dizgashi zeyi gaban jama'a babu ruwansa. Shi Mamaki yayi ma da Alhajin ya nemi ya rakashi wata unguwa me muhimmanci irin wannan domin be taSa ba, Yanzu da sabgogi sukawa Su Zakariyya yawa Yakubu ne abokin rakiyarsa ko Faisal, wani Sa'ilin har Lawan Wauka yakeyi ya rakashi be san dalilin daya saka Alhajin nemansa ba.

A kunne motar take dan haka yayi bismillah ya shiga, Alhaji ya gama sallamar Balarabe me ban ruwan Fulawa kafin ya buWr gidan gaba kusada Ahmad ya zauna yana hailala, wannan kuma haline klda su Naziru ze fita a gaba yake zama. A Warare Ahmad daya gama karanto Addu'ar hawa abin hawa ya taka motar suka tafi, a tare suka ringa Wagawa masu aiki dake musu Allah ya tsare hannu, Alhajin me halin tsiya dana kirki kenan, a Sangaren mu'amala da mutanen waje bashida matsala. Duk qanqantar mutum in har musulmi ne yazo giftashi zeyi masa sallama har ya bashi hannu suyi musabiha barshi dai da halinsa idan ya motsa wannan kam kowa ma yi masa yakeyi.

Tafiya sukeyi babu me cewa komai in banda karatun Al?ur'ani da Ahmad ya kunna can ?asa yana bi a hankali. Jefi jefi Alhajin yake amsa waya, wata ta kasuwanci wata kuma Abokanansa ne masu tambayar ko ze samu halartar Waurin auran bikin Wan Abokinsa ne da sukayi makarantar sakandire tare. Sun mi?e hanya sosai kamar daga sama Ahmad yaji Alhajin yace




*Masu qorafi akan kun gaji da jin labarin Fatima, kuyi haquri kubi komai a sannu idan kuma baku iya jurewa ku tsallake >?y?>?y? duk wanda yake bibiyar rubuta kunsan yanda nake, nakan fitar da komai dallah dallah ta yanda me karatu ze ringa ji tamkar film yake kallo ko kuma a gabansa akeyi. Wanda salon yayi musu a hakan sunfi masu qorafin yawa amma dole nayi addressing issue din na haqurtar da wanda suke son ayi sharp sharp kuyi haquri ku bi a sannu in sha Allahu ba zakuyi nadamar bin tafiyar nan ba =?O?=?O?=?O?*
*Innar Mahiru*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH*
*MUNA GABATAR MUKU DA UMMU-MAHEER COLLECTION Ita din dai kuka sani taku ta gargajiya da take kawo muku kayayyaki irin na yangayu daga kan ATAMFA, BUYERS BATIK, COTONOU BATIK, SWISS LACES, LAGOS LACES, MAYAFAI, KAYAN KWALLIYAR YARA DA SAURANSU. TA SAKE SHIRYOWA TSAF DA COLLECTION NA HIJABAI IRIN NA AFEEN JAYY FA AMMA BANA HAJJAJU BINTA GUMAMA BA*

*YI MAZA KU GARZAYO DOMIN KUYI SIYAYYAR KAYAN SALLARKU A GURINTA CIKIN RANGWAMEN FARASHI GA BIYAN BUQATA*

*DA AKWAI NORMAL HIJAB ME HANNU, MARA HANNU, POCKET HAND SE WANDA KIKA ZABA KALA KAWAI ZAKI BADA AYI MIKI AIKIN, JILBAB DINMU TAMKAR SAUKAKKE DAGA EGYPT, WANDA SUKA SIYA ZASU BAKI TABBACIN INGANCIN YADINMU. DA AKWAI NORMAL YARD, AKWAI LONDON CREP IYAKAR KUDINKI IYA SHAGALINKI*

TWO PIECES GOWN DA V HIJAB NA YARA DA MANYA HARDA MA ABUBUWAN DA BAN FADO BA ZAKI SAMUSU GURIN UMMU-MAHIR DA YARDAR ALLAH.

*SANQAMA MATA KIRA KO CHATTING AKAN 08142548705/07061838488 KO KUMA KIYI JOINING GROUP DINTA KAI TSAYE DOMIN SAMUN LATEST DESIGN AND AVAILABLE KAYA DA SUKE A QASA*
*MADALLAH DA MASU SO FISABILILLAHI IRIN NA AHMAD BECHI*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 12*

"Rayuwa kenan, duk waWannan da kaji muna magana dasu a sanda mukayi makaranta ?yamatarmu sukeyi saboda su lokacin a gaban Iyayensu suke mu kuwa Almajiranci aka kawo mu Kano, naci da dagiya tasa muka Shiga Bokon amma yanzu dubi ka gani kowanne cikinsu so yakeyi yayi ala?a damu, bakaga ro?on da Alhaji Mustapha ya ringayiwa Babanku Al?ali akan ya Waga tafiyarsa Umarah yaje masa Waurin aurannan ba, Allah kenan wato shiyasa duk yanda mutum yake karka rainashi dan baka san me ze zama a gaba ba, a lokacin suna ganin su yan gatane se gashi a yanzu da Yan Bokon cikin su da Yan Kasuwar babu wanda ya zarce nida ?an uwana" Alhajin ya faWa cikin Alfaharin abun.

Murmushi Ahmad yayi, be tanka ba dan Alhajin yakanyi magana shi kaWai wani sa'ilin, ya tabbatar idan so yakeyi ya bashi amsa kai tsaye ze ambato sunansa a cikin maganar, to mema zece masa shi?
Yana wannan tunani kuwa yaji Alhajin ya sake cewa
"Ya aikin Super market Win kuwa? Jiya Asiwaju ya kirani yana ta zuzuta gurin yace har yafi na Kano girma da tsari ko?"

"Ina ga dai kallon tsoro yayiwa gurin gaskiya amma befi rabin na nan Kano ba, kawai dai yanda aka fitar da taswirar ginin ne yasa ya Wauki hankalinsa, an kusan kammala komai dan har an fara zuba kaya ma, yace so yakeyi a buWe ranar Bikin haihuwar Yarsa, daman na bari sena dawo ne se muyi maganar" Ahmad din ya bashi amsa yana shafa kai domin ko Legos Win baje baniyyarsa daga Zariya idan ya dawo Kano seya bi jirgi. Ginin sabon Shopping Mall sukeyi wanda wani Aminin Alhajin Asiwaju Bayerabe Attajirine a birnin Ikkoh ganin yanda Bechi Mall ya samu karSuwa a Kano yasa yace Ahmad yaje ze bada fili suyi haWin guiwa ya sake gina Bechi Mall a Lagos Win gashi har an kusa kammala komai se abinda baza'a rasa bane ya rahe a gurin.

"Ai tun daga plan daman da gani kasan ginin ze bada ma'ana, Allah ya sanya Albarka yasa a buWe a sa'a. Maganar kayayyakin mu kuma idan kuna ka samu Idi kuyi yanda kuka saba".

"In sha Allah" Ahmad ya faWa daga wannan seda suka sake shafe kusan minti talatin suna sharara gudu a titi kafin Alhajin ya sake cewa
"?an uwanka fa? ya tafi ne ko yana nan har yanzu?"
"Aa ya wuce tun ranar Litinin, be kira waya bane?" ya faWa yana satar kallon Alhajin. Shiru yayi harya fitar da ran ze amsa masa kafin yaji yace
"Kai kafi kowa kusanci dashi ka ringa masa faWa kana nuna masa rayuwa shi yaro ne har yanzu baze gane abinda ake son nuna masa ba. Saboda nayi masa faWa nasan uwarsa ce ta zugashi tace ya dena kirana ko? To ka jaddada masa wallahi, muddin na sake samun labari makamancin wanda ya faru sena a nan ze gane ni ba abokin wasansa bane, kuma daga ranar ya bar buga Ball".

"In sha Allah zan sanar masa, hakan ba zata sake faruwa ba" Ahmad ya amsa masa dan a yanda Alhajin yake magana ya hasala in kuma yace ze fahimtar da shi ya wanke Jafar daga laifin dayake zargin ya aikata yasan rufta kansa zeyi duk su hadu suyi laifi a gurinsa amma banda haka a bune a buWe kawai dan shi Alhaji besan me duniya take ciki ba shiyasa ya Wauki abin da zafi. Rape Allegation ai ya rigada ya zama ruwan dare akan Celebrities, Matan sun maida wannan harkar samun kuWi a shekara ?aiWaidaikun Manyan Celebrities ne suke tsallake sharrin Mata ba tareda kaji ance anyi ?ararsu akan sunyi Molesting wata ba abinda ya faru da Jafar kenan wata yarinya tayi ?o?arin Sata masa suna akan yayi Raping nata shi Alhaji har se bayan ma anyi case an gama yarinyar ta ?aryata kanta har kotu ta yanke mata hukunci kafin can ya gano tsohon labarin a Jarida.

Shine dalilin tattago Jafar yazo gida babu shiri, sunga Tijara daidai gwargwado wanda hakan yayiwa da yawa daga cikin Ahalin gidan daWi dan Alhaji kulle ido yayi ya wanke Hajiya tass ita da Wan gaban goshinta. Cewa tayi ita bataga laifi ba idan ma Jafar ya aikata abinda kace yayi, ubanwa ya kai yarinyar gurinsa?/ ko janta yayi ta ?arfi? Basu suke bibiyarsa kamar jela yana yakice su ba banda ma rainin hankali Maza nawa ta buWewa ?afa se shi data raina take bibiya da sharri zatace ya mata FyaWe shine fa Alhaji ya zazzage mata tijara a tsakar gida yace ba zata saka yaje ya zubar masa da mutunchi a duniya ba. Abu Waya yasaka ya sassauta masa be tsaurara mataki akansa ba saboda sunan Bechi da be jona a sabgar ?wallonsa ba, ba kowa nema ya san ?ansa bane banda Close Family and Friends da yawa Muhammad Yayanta sukewa kallon Babansa dan dashi ake ganinsa ko Biography Winsa kayi searching it only shows Abdullahi Tijjani As his Father's name Nationality kuma Nigerian from Kano shikenan. Da?yar Al?ali ya kashe maganar Jafar ya koma ashe Alhajin be ha?ura ba.


Sun isa HaWeja Lafiya kai tsaye fadar sarkin HaWeja sukayiwa tsinke inda a can za'a Waura auran. Alhaji Mustapha Babandede yayi matu?ar jin daWin ganin Alhaji Alhaji Audu Bechi, suka ri?e hannun juna ana gaisawa yanda Alhajin ya sake da tsofaffin Abokanansa ana gaisawa cikin barkwanci ya bawa Ahmad mamaki, koda yake daman hakane, duk girma da wani matsayi da mutum ya kai a rayuqa idan ya shiga cikin waWanda sukayi gwagwarmayar Karatu tare se kaga duk an koma yara ana tuna baya. To tare akaci daWi aka sha wuya, lokacin da kowa be gama fahimtar tanadin da ubangiji ya masa a rayuwa ba.

Yakubu ya taSasu labarin daya kai Alhajin taron Tsofaffin Walibai a ranar har rawa yayi, wai hana yin video akayi shiyasa be Wakko musu ba abun ya basu mamaki suka ringa hakaito Alhaji yana rawa wane irin farin ciki ne haka ze sakashi ya taka se gashi yau Ahmad yaga makamancinsa a fuskarsa dan Dariyar da Alhajin yakeyi harda ?ya?yatawa abin ya tashin kansa ya kuma sake tabbatar da Abotar makaranta tana da wani ?arfi da tasiri na daban sama da sauran Abota, an girma shekaru sun taru amma idan aka haWu se a ringa ji kamar an koma bayane.


Se bayan da aka Waura auren a gurin Reception ya haWu da yayayen Abokanan Alhajin waWanda suka kawo iyayensu. Wasu ya sansu suna hulWa wasu kuma ranar ya fara ganinsu, Basu bar HaWeja ba se ?arfe huWu bayan sunyi sallar La'asar kafin kowa ya kama gabansa. A hanyar dawowa Alhaji ya ware yana masa labari irinsu "kaga wane? Lokacin da muna makaranta fa kaza da kaza amma yanzu kalli kaza ya faru" Ahmad ya lura Alhajin na cike da shau?in ganin tsofaffin Abokanai shiyasa yau harya maidashi abokin hira.

"Ya kamata ku motsa ku fito da mata kuma tunda ?annenku mata sun tsaya shiririta. Kasan ban fiya mayar da hankali gurin gayyato tsofaffin Abokanai na na ?uruciya sabgar auren yayana ba amma ina ganin wannan karon har Gala Nigh zan shirya mana ta yanda zasu zo su kwana musha hira kafin ranar Waurin aure" Alhaji ya fada.

Ahmad ya shafa ?eya da hannu Waya yana murmushi me kama da dariya, wato su Alhaji har Gala Night za'ayi lallai abin nayi ne, shi kuwa Alhaji yanayin nasa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login