Showing 336001 words to 339000 words out of 467220 words

Chapter 113 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12157

kafin suka shiga motar suka cigaba da tafiya. Seda ya shigar musu da komai cikin gida, ya fitar musu da wanda zasu ci a lokacin ragowan ya saka a fridge.

Suna zaune a falo Amal na kan cinyarsa yana bata Ice cream Win a baki duk ransa a dagule da kukan da yaga tanayi sannan tunda suka dawo ta shige Waki bata sake fitowa ba. Daman dai haka take masa, bata taSa yarda su zauna a guri guda daya shiga gidan ko tana zaune a falo zata tashi ta bar gurin.

Agogon hannunsa ya duba ?arfe tara harda minti ashirin kimanin minti Arba'in da shigarsu gidan kenan. Layin Baba Bilki ya shiga kira dan yaji ko ta taho tunda dare ya farayi tace masa gata nan sun fito yanzu za'a kawota.

"Je ki duba me Momyn ku yakeyi a Waki" ya aika Layla ta dubo Fatiman dan haka nan zuciyarsa taki tsayuwa da shigewarta Wakin, shigar yarinyar babu jimawa ta fito da gudu tana ?wala masa kira
"Dady bata da lafiya kazo" da saurin gaske ya mi?e har yana kayar da Amal dake cinyarsa ya tsallake ta ya shiga Wakin. Fatiman na dur?ushe a ?asa dafe da cikinta tana salati ga ruwa me hade da jini malale akan tiles da alama daga jikinta yake. Duk se ya diririce, haihuwar su Layla ta dawo ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sa, kusan haka yazo ya tarar da ita cikin wani yanayi amma wannan yafi wancan tashin hankali dan be manta ba duk sanda sukaje Asibiti likita na nanata karta bari na?uda ta kamata a gida saboda complications Win dake tattare da cikin amma saboda taurin kanta tunda suka taho me yasa tasan bata jin daWi bata faWa sun wuce asibiti ba?

Ganin tunanin baze kai shi ko ina ba yasa ya nufeta seda ya isa kanta kuma ya tsaya jikinsa na rawa salatinta na masa amsa kuwwa. Da sauri ya fice ya Wauki wayarsa, Fatiyyah ya shiga kira.

"Fatiyyah na zaune dirshen gaban Hajiya tana rera kuka, hajiyar dake jijjiga jiki tsabar yanda bala'i yake cinta tace
"Ki dena asarar hawayenki, na gaya miki lamSo nayi saboda na zata harkar da mutunchi muradina ze cika cikin sauri. Amma yanzu tunda har Audu ya iya kallon ido na ya gasa mun maganganu billahillazi se kowa ya gane bashi da wayo, ai ha uban wani ya haifa mun Jafarun ba da ze zama bawan Aisha da Yayanta. Biyar daya kashe se an biyani kuma ze zo ya tarar dani dan ubansa zanji idan ya sake wata uwar ne bayan ni ai na gayawa me gadin can da yaga shigowar sa yazo ya faWa mun"

"Ba gara ma ki gayawa wani daban ba, yan unguwan nan kaf munafukai ne indai sabgar gidan Ahmad ce babu me faWa miki komai wlh gara ma kije ki zauna a gurin da kanki" Fatiyyan ta sake faWa tana goge hawaye. Hajiya na shirin bata amsa wayar Fatiyyan tayi ?ara ganin Jafar ne yake kira yasa tace

"Saka a sifika".
"Kizo gidan Yah Ahmad yanzu kuma kiyi sauri" ya faWa cikin sigar bada umarni kafin tace wani abu kuma ya kashe. A fusace Hajiya ta cangala ?afarta ta mi?e tana cewa
"Sun dawo ashe, aiko sena ci abu ta kazan maigadin ku kuma ya gama aiki a gidan nan tunda bana uwarsa bane. Har ni in bashi sallahu ya mayar dani shashasha ze gane bashi da wayo" suka fice zuwa gidan Ahmad Win.

A dur?ushe suka tarar dashi kusada Fatima yana mata sannu, Hajiya ta shiga tafa hannaye tana rafka salati tace
"Yau naga abinda ya isheni ni Binta, Jafar abin har ya kai haka har uwar Waka take kawo ka ni Binta ina me aka mun wannan shammatar?"

Shida Fatiman suka kalleta, ya zabgawa Fatiyyah hararar data saka yan cikinta juyawa kafin ya mi?e yana cewa
"Kizo ki kamata mu tafi Asibiti"
"Ta kama wa? Lallai Jafar na yarda ka kwashe kayanka daga gaban ma'aiki. Kamar ma baka ganni ba kake cewa tazo ta kama wannan yar iskar mayyar yarinyar? Wato ta cinye Ahmad shine ta ta waiwayo kan taka kurwar to ?aryar uwarta tasha ?arya wlh, ni ba Aisha bace, ko da yake ai haWin baki ne su da Aishar to duk na ishe ku riga da zani harda fatala mu zuba mu gani shege ka fasa ka wuce ka fita daga gidan nan kafin kasa zuciya ta Webe ni nayi maka baki" ta faWa tana zazzaro masa ido.

Tsayawa yayi a inda yake be motsa ba idanunsa kan Fatima dake malelekuwa nishi kawai takeyi bakinta ya mutu ko salatin ta gagara yi, a yanda taken yana zaton har a gurin Allah a wannan gaSar da yake yana da uzurin ketare umarnin mahaifiyarsa, amma gudun kokonto ya saka cikin muryar tausayi yace mata

"Hajiya baki ga halin da take ciki ba? Ku taimaka nata dan Allah mu kaita Asibiti kina kallo zafa ta iya rasa ranta"

"Ka sake cewa tak anan sena maka baki Jafaru, kayi abinda nace salin alin ka fice daga Wakin nan kafin na nuna maka Sacin raina. Ai gara ta mutu a rage mugun iri jinin maita" Hajiyar ta sake faWa ko a jikinta. Ya kalli Fatima data fara nishi ilahirin jikinta yana rawa da alamun abinda yake cikin ta yana neman hanyar fitowa duniya, da saurin gaske ya isa gareta a abinda be wuci sakanni ba ya sureta ya fice daga Wakin ya bar Hajiya da Fatiyyah da baki a hangame. Baze iya zuba ido amanar Yah Ahmad ta salwanta akan idonsa ba, al?awari yayi na kare masa amanarsa da ransa da numfashinsa babu kuma abinda ze sakashi ya ?arya wannan al?awarin.

Abinda ya sake karya masa zuciya su Layla daya gani tsaye a ?ofar Wakin suna kuka ya tabbatar duk abinda aka faWa ya isa kunnensu, duka suka bishi su ukun suka shiga gaba ya shimfiWe Fatiman a baya ya fice daga gidan da mugun gudu bayan Liman daya Soyewa Hajiya ya wangale masa Get. Wani Asibiti daban ya kaita ba wanda sukame zuwa ba, Emergency CS aka shiga da ita, ita yake fata ta rayu dan ya rigada ya cire rai da abinda yake cikinta.

Ya kasa zaune ya kasa tsaye a bakin ?ofar dakin tiyatar, zargin kansa yakeyi akan koma menene ya faru, da ace tunda ya tarar da ita a halin na?udar ya kawota Asibiti be tsaya kiran wata Fatiyyah ba da duk haka bata faru ba amma ?addara ta rigada ta riga fata se dai yayi Addu'ar ta rayu dan idan ta mutu be san me ze gayawa iyayenta ba.

Har ya cire waya ze kira Momy se kuma ya mayar jiki a sanyaye ya zauna, kusan awa guda da mintina sannan suka kammala aikin, likitan yace ya bishi office wannan yasa jikinsa ya ?arasa mutuwa har seda wata Nurse ta sake zuwa kiransa kafin ya iya Waga ?afafunsa yaje. Zama yayi yana kallon likitan dake yan rubuce rubuce a takadda kafin ya gama ya kalle shi yace

"An samu nasarar yin aikin ta samu baby boy sedai bashi da wadatacciyar lafiya dan haka an kaishi NICU, ita Win ma tana da bu?atar hutu sosai saboda jininta ya hau dan haka bama bu?atar kowa ya shiga inda take har se an bada damar yin hakan" ya mi?a masa takardar da yayi rubutu yana sake cewa

"Se aje a buWe fayil a biya kuWin duk abinda ya kamata, Alfarmar fuskarka ce har ta saka ma aka karSeta ba tareda ka buWe fayil ba, Allah ya raya ya basu lafiya".

A fili ya ringa jera hamdala rabin damuwarsa ta washe tunda duka amanar Yah Ahmad suna raye,
"Amma zan iya ganin babyn dan Allah" ya faWa,
"Ba yanzu ba" likitan ya bashi amsa.

*****************
A can gida kuwa mamaki ne ya sumar da Hajiya a tsaye, bata farfaWo ba seda suka jiyo ?arar fitar mota aiko ta zabura tayi waje sedai ko haya?in motar bata tarar ba. Liman dake rufe get yana hangota ya ?arasa da sauri ya fice daga gidan. Ashar me mai?o ta lailayo ta antaya bakinta har kumfa yake ta shiga zazzaga tijara har waje ana jiyo muryarta. Ita dai Fatiyyah ta haWe hannaye kawai tana kallonta, tafi minti talatin a tsaye tana sakin maganganu tamkar farin shigan hauka kafin aka buWe kofar gidan Baba Bilki ta shigo Salim na bayanta ya ru?o mata jakarta.

"Ke kuwa Binta a ko ina se kin kwance hali kin nuna ke karya ce? Kinzo gidan mutane cikin dare kina gwada ?warewarki a tashanci ma?wafta duk suna jiyoki ki ko kunyar ace uwar Malam ce ke bakya ji unguwa kowa na ganinsa da mutunchi amma kinzo kina zubar masa dashi saboda shashanci kuma a gaban surukarki ni dai Allah ya nuna mun ranar da zaki san kin girma kiyi hankali" Baba Bilkin ta faWa tana kallonta seta zabura tayi kanta tana cewa

"Ni kike cewa karya Bilki?"
"Na faWa ko ba ita bace? Nace ko ba karyar bace ke? Idan ba karya ba wace dabbar arzi?i kika sani da take zama tayita ihu tana hauka balle azo cikin jerin mutane? To tun da sauran mutunchi ki fice daga gidan nan wlh kafin na kira masu gadin unguwa su fitar dake shashashar tsohuwa kawai" Baba Bilkin ya sake gasa mata magana.

"Billahillazi se kin san kinyi dani Bilki, kinci bashi ko dole ki biya zaki tabbatar da ni karya ce zan kuma nuna miki halin yan tasha" Hajiyar ta shiga kurarin banza tana zabura Fatiyyah na ri?e ta kamar gaske wai zata daki Baba Bilkin. Haka dai ta jata suka fita daga gidan tana cigaba da zagezage. Bayan fitar su Salim daman tunda suka shigo ciki ya wuce bema tsaya ba ya fito yana cewa Baba Bilki
"Babu kowa fa a gidan?"
"Babu kowa? Kodai suna sama ina zasu iya da hargowar wannan matar ?ila can suka haye suka kulle kofa"

"Aa basa nan Hajiyar ce babu lafiya sun tafi Asibiti da Alhaji Jafar" Liman ya bata amsa, nan da nan hankakinta ya tashi tace

"Badai wani abu wannan mahaukaciyar tayi mata ba ko? Na shiga uku kar dai illata musu ya tayi yi maza ka kira Malam Win kaji suna ina ni Bilki idan wani abu ya samu amanar Amadu ya zanyi" ya ta ?arasa tana matse ?walla. Salim ya kira Jafar ya gaya masa Asibitin da suke sannan ya shaida masa ai ta haihu.

"Hajiya na nan ko ta tafi?" Ya tambayi Salim Win ya gaya masa ta tafi sannan ya kashe wayar shi kuma ya gayawa Baba Bilki Fatima ta haihu.

"Allah kenan, kwana Arba'in da rasuwar Babana Allah ya mayar mana da magajinsa, bari na haWo mata kaya dan na san babu shiri suka tafi" Baba Bilki ta faWa tana shigewa cikin gidan. Abubuwan da ta san Fatiman zata bu?ata ta Wiba, babu kayan jarirai a Wakin ?asan tasan ma Jafaru ya siyo dan haka kawai suka tafi, seda sukaje kafin suka san CS akayi mata, dare yayi dan haka Baba Bilki tace Salim ya tafi da yaran da suka rigada sukayi bacci can gida shima Jafar ya tafi ya huta ita zata kwana.

Kafin wayewar gari labarin haihuwar ya karaWe dangi kowa yasan an samu Ahmad, tun sassafe suka fara tururuwar zuwa Asibitin amma babu wanda aka bari yaga Babyn dan har sannan ba'a fito dashu daga NICU Win ba, Fatiman dai ta farka tun cikin dare kuma jikinta da sau?i sosai. Guraren tara na safe Jafar ya koma Asibitin, a hotel ya kwana saboda ya kira Liman ya tabbatar masa Hajiya tana unguwar bata tafi ba sanin ba zasu kwashe ta dakyau idan yaje gidan ba yasa ya gwammace tafiya hotel Win, ya dai ?udurce a ransa seya saSawa Fatiyyah, sabon halin data samu na haWashi da Hajiya dole yayi maganinta.

Gurin likitan ya fara zuwa daya kafa naci seda suka barshi ya shiga gurin jariran aka Wakko masa dan ?aramin babyn me kama da Yah Ahmad kamar an tsaga kara, be ma taSa ganin jaririn da kamanninsa suka fita irin haka ba, ya rungumeshi hawaye na sakko masa yace
"Allah ya ji?anka Dan uwana ina kewarka na kasa sabawa da rashinka, na godewa Allah daya bani fuskar da zan ringa kallo tana ragemun raWaWin kewar rashin ka. Allah ya rayaka Ahmad yasa ka gaji kyawawan halayyar mahaifinka" ya faWa yana sumbatar goshin yaron daya buWe ido yana kallonsa hawayensa suna Wiga akan jikinsa da babu kaya.

Seda yayi masa huWuba ya Wauke su a hoto kafin ya mi?awa Nurse Win da tausayinsa ya cikata yaron ta mayar dashi cikin gadon da yake.
"Se yayi kwana nawa a nan za'a fito dashi?" Ya tambayeta bayan sun fito tace
"Ai Alhamdulillah jikin nasa ma yayi kyau dan kaga a jiyan bayan an ciroshi fatarsa tayi shuWi amma kaga yanzu ya washe ina ganin in har komai yayi daidai zuwa gobe ma za'a iya fito dashi tunda jikinsa da ?wari amma dai ka samu Dr ze ?ara maka bayani".

Sanda yaje Wakin da Fatima take ya tarar da su Anty Maimuna ?annen Momy se Anty Sauda Yayarta da Baba Bilki, a mutunce suka gaisa sukayi masa barka ya matsa gefen gadon da take, da a zaune take yana shiga ta sulale ta kwanta harda rufe ido kamar me bacci. A kanta ya tsaya a hankali yake tambayar ta ya jiki, ko motsi batayi ba balle ta amsa shi, ya zura hannayensa a aljihu yana ?are mata kallo kafin ya juya yayi musu sallama ya fita ya tafi gida dan Liman ya gaya masa Hajiyar ta tafi tare suka fita da Fatiyyah tun sassafe.

Yana fita Anty Sauda ta fara mata faWa akan me tana ji yana mata magana tayi banza dashi.

"Aa fa ki barta, Allah kaWai yasan me uwarsa ta mata jiya tunda ai a unguwar tasu ta kwana waya sani ma ko ita ta tadomata da na?udar ai wlh ko ni dan dai bazan iya share Jafar bane shi yasa na kulashi amma cin mutunchin da uwarsa ta mana da safen nan ai wlh da wani daban ne cikin yayanta har duniya ta tashi nida sake ko kallon inda yake balle magana ta haWa mu. Kinga tijarar da tayi a tsakar gida kuwa har Ahmad dake kwance a kabari yau seda Binta ta zaga babu irin abinda bata faWa ba se kace wani ya tilastawa dan nata yayi abinda yakeyi na rantse da Allah yau badan Momy ta hanani ba so nayi na hau iskar ?arya na yiwa matar nan jahilin duka na ?arya mata ?afafu ta tsugunna gaba Waya. Haba me za'ayi da mutum irin Binta banda ?addara" Anty Maimuna ta faWa cikin ?unar rai.

Baba Bilki ta karSe ta ci gaba da sharhi Anty Sauda dai "Hmmm" kawai tace domin ta tabbatar duk tijarar da tayi musu bata kai wadda taje har gida da farar safiya tayiwa Ummansu ba. Tana hanya zata taho Asibitin Umman ta kirata ta cikin wayar ta ringa jiyo muryar Hajiyar tana zazzaga cin mutunchin se abinda ta manta ne bata faWa ba su sakar mata kurwar yaro idan ba haka ba kuma zasu ga abinda zatayi yanda suka cinye Ahmad Jafar yafi karfinsu sedai kallo tayi tijararta son ranta ta tafi Umman dai daman bata kulata ha Waki ta shige ta kulle kofa har tayi ta gaji ta tafi kafin ta fito ta dai kira Saudan kuma taji komai sannan tace mata daga Asibiti idan an sallami Fatima ta taho gida ai ta gama takaba babu kuma sauran zaman da zatayi.

Da daddare ranar Alhaji Audu tareda Baba Al?ali sukaje suka duba Fatiman, acan suka tarar da Alhaji Babannan. Baba Al?ali yace
"Ikon Allah, Alhaji Yusufu ashe ana ganinka? Rabon da mu haWu tun ranar bakwai Win ?aninka se gashi har ka rigamu zuwa ganin Wan naku". Bece komai ba ya gaishe su kawai Alhaji Audu se kallonsa yakeyi, wato shida Babannan Win kamar kwabo da kwabo a halayya, babu me kafiya da ru?o a cikin yayansa kaf kamar Babannan Win amma kuma tamkar shi can ?asan zuciyarsa me laushi ce. An fito musu da yaron se lokacin itama Fatiman ta ganshi kowa faWi yake sak Ahmad, da zasu tafi Baba Bilki ta raka su nan ta labarta masa abinda Binta tayi dan baya gidan Asubancin zuwa Gumel yayi Jana'izar wani Abokinsa se yamma ya dawo dan haka be samu labarin abinda ya faru ba.

"Har gidansu yarinyar taje, Wazu da ?annen mahaifinta suka zo suke zancen daman Yayarta tace da an sallameta gida zasu wuce tunda dai ta kammala takabarta to nima na goyi da bayan hakan kaga idan ta tafi shikenan an kashe bakin tsanyar Malam baze cigaba da yi musu sunturi a gida ba balle har uwarsa ta samu na zagin mutane tana binsu da sharri" Baba Bilkin ta faWa. Alhaji Audu yayi shiru se Baba Al?ali ne yace

"Binta ba zata canza hali ba, babu inda zataje domin ai ko ta kammala takaba akwai sauran ha??o?in ta da ba'a rigada an sauke ba dole ta jira a raba musu gado daman jiran da akeyi Allah ya sauketa lafiya daga nan kuma muga abinda hali zeyi wata can Binta kuma bata isa ta canza mana duk abinda mukayi niyyar aiwatarwa ba".

Seda aka kwana bakwai kafin aka sallami Fatima suka koma gida, a tsayin kwanakin tun washe garin data haihu Jafar be sake shiga Wakin da take ba, kullum kuma zeje Asibitin a fito masa da babyn ya Sata lokaci dashi yana masa zance kamar wani taSaSSe idan ya gaji ya mayar dashi yayi tafiyarsa hidima dai daga kan magani har abubuwan amfani shi yakeyi musu. Ya bawa Baba Bilki kuWaWe masu nauyi akan ko wani abu ze taso, siyayyar jaririn ma yayi har abinda ba zasu amfani dashi nan kusa ba ya siya ya ajiye a gidan kafin su dawo.

Da fari yayi tunanin ya gargaWi Fatiyyah ya kuma ja mata kunne akan shiga huruminsa, ya gaya mata ze iya zaSar Amanar Yah Ahmad akan Auranta dan haka ita ma ta zaSarwa kanta mafita tsayawa huruminta ko kuma cigaba da shiga sabgarsa da haWashi da mahaifiyarsa amma kuma dayaje ya samu Hajiya ta kwasa mata nata jan kunnen seya canza shawara.

Ranar daya je gidan dukansa ne kawai batayi ba shidai ya kwantar da kai ya ringa bata ha?uri ta shata masa layi akan Momy da yayanta muddin yana so yaga haske kuma yaci gaba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login