Showing 162001 words to 165000 words out of 467220 words

Chapter 55 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12239

sau?inta ma is because Alhaji yana sonta I'm sure shiyasa takai yanzu a gidan nan.

Look at Anty Mardiyya ko cikin Co Inlaws ba kowanne taro take iya zuwa ba because of the humiliation she faced, haka kake so itama matarka ta tashi ana wareta kullum ana zaginta?"

"I'm different from Alhaji And Yaya Naziru, babu wanda ya isa ya wula?anta matar Aure na na Waga masa ?afa suma su suka bada damar da ake raina matansu kuma ni ba zan zama irin su ba"

"Zakayita faWa da yan uwanka kenan saboda matarka?"
"Bazanyi faWa da kowa ba kuma bazan bayar da hanyar da kowa ze taka matata ba, look Jafar duk ba wannan ta saka na kiraka ba, I have already made my mind so no going back. Nayi magana da Momy ta saka mun Albarka akan maganar i wanted her to talk to Alhaji about it amma tace ba zatayi ba nina sameshi na masa magana kuma ni bansan ta inda zan fara ba, idan yace Aa bansan ta yaya zan ro?eshi ba shiyasa nake so kai kayi masa maganar Dan Allah" Ahmad ya faWa cikin sigar ro?o.

Yanzu fa kake cewa ka shirya facing kowanne challenge amma kace ba zaka iya yiwa Alhaji Maganarta ba kaga kenan kaida kanka kasan maganar bame yuwuwa bace Alhaji baze karSeta ba, kuma ni yanzu da kake so nayi masa magana idan nayi and it turns out Negative response nasan ni zaka Worawa laifi saboda na nuna maganar batayi mun ba, kayi ha?uri for the fist time bazan iya maka abinda kake so ba, kamar yanda Momy tace ka sameshi da kanka, Yah Ahmad is high time you stand for your self. Alhaji fa ba Dodo bane bare ka ce tsoronsa kake ji, go meet him ka gaya masa bu?atarka but it should be you and him alone, karka bari maganar nan ta fita asan wa kake nema,
Allah ya bada sa'a but i will pray you change your mind kafin ka sameshi because magana ta Allah banji yarinyar tayi mun ba" matsayar Jafar akan zancen Fatima kenan.

A karon farko Ahmad yayiwa wani mutum ?arya, ya kasa samun Alhajinsu da maganar se kawai ya yanke komawa gidansu Fatima ya kuma tabbatarwa da Mahaifinta yayi magana da nasa Iyayen kuma sun yarje masa daya nemi auranta. A zuciyarsa ya tabbatar Allah baze bashi kunya ba tunda Aure yake so yayi ba wani mugun abu ba, kafin sanda zasu bu?aci ya turo ze san yanda zeyi da Alhaji, idan ma bashi ba Baba Al?ali ze kaiwa maganar Auransa kawai.

"Amma da akwai magana guda, Mamana Karatu takeyi, ta ?are shekarar farko zasu shiga ta biyu yanzu suna hutu ne saura yan kwanaki su koma A can Jami'ar Zaria take Karatun" Malam Hafizu ya faWa masa. Ahmad dake dur?ushe yana faman sunne kai yace
"Babu komai Baffa, gidanmu gidan Karatu ne. Idan Allah ya nufa zamuyi aure Fatima tana cikin makaranta bbau damuwa zanyi duk abinda ya kamata gurin ganin bata takura ba ko Karatunta be samu matsala ba, sannan idan ta zaSi har seta kammala kafin muyi Aure zan iya ha?uri na jira lokacin, fatana kawai na samu Amincewarta da taku"

"Allah ya shige mana gaba ya sa a ?ulla Alkhairi, bari na shiga ciki na turo maka ita" cewar Malam Hafizu daga nan ya shige gida.

Tun zuwan Ahmad na farko Malam Win ya sanarda ita daya wassafa mata kamaninsa ta ganeshi tunda ba sanin sunansa tayi ba. A lokacin ji tayi kamar tacewa Baffan nata ya sallameshi kawai yace ya mata Miji, tsakani da Allah be mata ba, kuma ita da wanne ido ma zata sake kallonsa bayan wancan abinda ya faru shi ma ya zeyi mata haka ya dawo? Dataji shiru be kirata a waya ba ta zata ya janza shawarane ashe shi me gaba Waya ya shirya mata biyowa ta hannun Baffa.

Tana jin yanda Baffan yake ta yabon Kamalarsa da hankalinsa sannan ya gayawa Umma yanda sukayi da abinda yace masa, Jiki a sanyaye ta fita, Dogon Hijabin datayi sallah dashi ne a jikinta, bata tsaya gyara fuska ba balle akai ga fesa turare ko sauran Al'adu da yammata sukeyi idan zasu fita hira haka zi?au Winta ta fita abinka kuma da jiki kalar Madara a hakan ma tayi kyau abinta.

A cikin gida kuwa bayan fitar Fatima Umma tayi jugum kafin ta kalli Malam tace
"Ban tsammaci yaron nan ze dawo ba, Anya kuwa Malam ba'a yi Wage da yawa ba? ?an gidan Alhaji Audu Bechi yazo neman Auran Afeeya, wannan fa ba irin Mijin Yayarsu bane idan ma ana maganar masu Arzi?i irinsu Alhaji Audu a ?asar nan Sirikin Saudatu inaga ai ko gurin baze le?a ba, gaskiya ni koda da sahalewar Iyayensa ba zanso wannan Auran ba, Malam kafa san irin zamanin da muke ciki yanda Aure ya zama ?warya tabi ?warya duk kuma wadda tayi kuskuren faWawa gurbin da ba nata ba zata fusakanci ?alubale"

Ki kyautata zato ki kumayi Addu'a Allah ya zaSa mata binda yafi zama Alkhairi, sannan ki tuna shi yaga Afeeya yace yana sonta bawai tura masa ita akayi ba, Nutsuwa da Kamalar yaron ta burgeni idan har Allah ya zaSa matashi a matsayin miji zanyi mata murna kwarai dan daga ganinsa mutumin kirki ne" inji Baffa. Umma ta nisa tace

"Toh, Allah ya zaSa mafi Alkhairi amma dai Alhaji Audu Bechi fa.."
"Ai kingama magana tunda kika mi?awa Allah zaSi sedai mu zuba ido muci gaba da Addu'a kawai" Baffan ya sake tareta.

Seda Fatima tafi minti biyar tsaye a soro kafin ta hada courage ta fita, wata irin kunya da nauyin sake haWa ido dashi takeji tasan yana ganinta wancan abun ne zero faWo masa a rai, da dai taga babu sarki se Allah yasa ta fitan, Ahmad na jingine jikin katanga ta raSe gefensa tana yar siririyar sallama kai a ?asa tamkar wadda ya kama tana gulmarsa.

Murmushinsa me kyau yayi ya amsa mata sallamar kafin ya tsaya dakyau yana fuskantarta, har sannan kanta a ?asa murya a sanyaye ta gaidashi
"Hajiya Fatima, se yanzu sarautar ta sakeki kenan har ina shirin na ?araso soron na taroki ai" ya faWa cikin raha. Bata tanka ba haka nan bata Wago kanta ba, ya waiwaya ya kalli Dakalin gurin kafin ya kalli mutanen da suke wucewa kamar an basu gadi duk wanda yazo seya zura musu ido sannan ya wuce se ya kalleta yace

"Mu zauna a nan ko mu tsaya cikin soron?"
"Bari na kawo maka abin zama" ta faWa kafin ta juya cikin gidan ranta babu daWi, shi gurin zama ma yake nema, ita data fita da niyyar su ?ar?are kuma yana neman yaja maganar da tsayi.

Kujerun roba ta kawo guda biyu ta saka a Soron ta koma ta dauko pure water da Zobon da Ummansu take siyarwa ta haWo masa da ?aramin kofi dukda bata da tabbacin zesha. Seda ta aje komai kafin tace ya shigo, yana ta doka murmushi kamar sabon Ango ya zauna, kallonta kaWai nishaWi yake bashi musamman yanda take sunne kai yasan meye dalilinta na?in haWa ido dashi amma a ganinsa wannan ai ua wuce, banda abinta idan Allah yayi wata rana na jikinta ma ai wanke mata zeyi balle gurin da ta Sata. A ta?aice yayi mata bayanin kansa da dalilinsa na zuwa gurinta.
"Kema se ki bani ta?aitaccen bayani akanki" ya faWa yana ?arewa fuskarta kallo.

Kyakykyawace Masha Allah komai na fuskarta Wan daidai hasken fatarta kuma ya ?ara ?awata kyan nata, tana da tsayi dan ko ze fita da kaWan ne sannan ba ramammiya bace kuma bata da ?iba, baze iya ?iyasta shekarunta ba saboda suffarta irin wadda bata nuna shekaru ce, se kayi wa mutum kallon yaron idan kaji ainihin shekarunsa kuma kayi mamaki. Yanayin zubin jiki da fuskarta yafi kama dana Jajayen Buzayen Niger ko kuma Fulanin Mambila, sannan daga yanayin goshinta ya fahimci tana da kufar gashi, kuma irin me Laushin nan dan gashin goshin nata a kwance yake luf kamar na Jariri sabuwar haihuwa gashi ba?i siWik.

"To ai kasan sunana Fatima kuma nan ne gidanmu" maganarta ta maido shi daga tunanin daya tafi. Ya saki murmushi, jan Ajin nata ya fara yawa, ya zata kuma tunda har yaga mahaifinta kuma zata Wan sake masa tasan dai bada wasa yake yi ba. Ya gyara zama yace

"Nasan sunanki Fatima kuma naga gidanku amma ai ni ba iyakar abinda na faWa miki a kaina ba kenan, na gaya miki mena karanta, aikina har adadin yan gidanmu da wanda nafi so seda na gaya miki fa"

Tayi shiru tana jinsa, idanun daya zuba mata su sukafi damunta da alamu kuma idan ba magana tayi ba baze dena kallonta kamar ze hango yan cikinta ba dan haka tace

"To ai ni banida wani abu da zan gaya maka ne, amma dai kamar yanda nace maka nan ne gidanmu, mu uku ne ai kaga Anty Sauda itace babbarmu se Yah Malam.."

"Jafar? wanda yayi mun sallama da Baffa?" Ya katseta, kai ta Waga masa kafin taci gaba da cewa
"Shi nake bimawa, ni kuma banida ?ani ko ?anwa, ina makaranta a Zaria Level two zan shiga ina karantar English Literature, bayan Baffa da Umma dasu Anty Sauda Ina da Best Friend Badar i think iyakar abinda kake bu?atar sani akaina kenan" ta ?arasa tana yamutsa baki.

"Masha Allah ku uku kacal a gidanku kenan, ashe ke Win Autace shiyasa shagwaSarki tayi yawa, shekarar ki nawa toh"

"20" ta bashi amsa a gajarce tana ci gaba da murza zoben hannunta. Sukayi jugum shi yana kallonta ita kuma tana faman juya Zobe, wayarsa dake Aljihuce ta katse musu shirun ya cirota ya duba, Jafar ne yake kiransa, ya nuna mata screen Win wayar yana cewa
"Jafar ne yake kirana".
Tankar wadda take zaune akan ?aya ta mi?e da sauri tace

"Ka amsa toh, bari naje ciki kafin ka gama". Kallonta yayi kaWan ya kasa fassara yanayinta amma dai kamar she is not comfortable with him, ya mata uzurin haWuwar farko ne dan haka ya mi?e shima yana laluba Aljihubsa yace
"Ai inaga zan wuce kawai idan naje gida se na kirashi wayarmu bata yankewa da wuri ga dare ma ya farayi karna zaunar dake a waje" KuWi ya zaro masu yawa daga Aljihun nasa ya mi?a mata yana cewa

"Kinsan farin shigan zuwa hira ne ni, bansan me akw tafiya dashi zance ba kiyi ha?uri ga wanan kisha Sweet kafin na sake zuwa"

"Nagode" ta faWa ba tareda ta karbi kuWin ba se wani kallo da ta musu ta Wauke kai kamar taga wani abunda bata so. Wayarsa ya sake mi?a mata uace ta saka masa Number ta wancan ta goge, nan ma seda taji jum sannan ta karba, ta saka number ta mayar masa. Akan kujerar data tashi ya ajiye mata kuWin ya juya yana cewa

"Zan kiraki idan na isa gida se kiyi saving number ta. Ki gaida Umma, se na sake dawowa" Ganin ta tsaya kamar wata sokuwa kawai tana kallonsa yasa yayi murmushi ya fice daga soron yanajin wayarsa nata ?ara yasan Jafar ne bala'in wutar ciki ne dashi yanzu idan ba Wauka yayi ba ya ringa kira kenan ga Mita kamar Mace.

Jiki babu ?wari ta haWe kujerun ta Wauke farantin ruwan da be ko taSa ba daman tasan ba sha zeyi ba Umma ce tace ta kai masa. Iyayen nata na yar hirarsu ta shiga. Seda ta ajiye kujerun a mazauninsu kafin ta isa gaban Baffa ta Zube kuWin da Ahmad ya bata.
"Wannan fa?" Baffan ya tambayeta yana kallon kuWin, a sanyaye tace

"Shi ya bani wai bezo da komai ba dana?i karSa shine ya ajiye akan Kujera ya tafi"

"Toh madallah amma idan ya sake dawowa ki gaya masa na hana karki ?ara karSan kuWinsa" Baffan ya faWa ta amsa da
"Toh Baffa" kafin ta mi?e tsaye zata wuvmce yace mata
"Kwashe kije dasu ai ke aka bawa"
"Ni babu abinda zanyi dasu Baffa" ta bashi amsa tana juyawa.

"Zo nan Mamana, me yake damunki? Ko wani abu yayi miki?" Baffan ya sake dakatar da ita saboda lura da yanayinta sam ba daidai take ba, murmushi ta ?a?alo tace
"Babu komai Baffa kaina ne yake sarawa zanje na ?arasa shirya kayana sena kwanta"

"Toh Allah ya sawwa?a ki samu magani kisha kafin ki kwanta Win idan be dena ba da safe se kije Asibiti, sannu ko" Baffa ya faWa cikin tausayawa. Seda ta shige sannan Umma ta gaya masa abinda take zaton shine sikar tsumewar Fatima. Yayi murmushi yace

"Ina ruwan Mamana, wato kunya ce duk ta dabaibayeta, to ya za'ayi abu ya rigada ya faru ta yuwu ma ya manta idan kuma ya ganota ya samu abin tsokanarta ai" tana jiyo Baffan daga Wakiz harta hasaso Ahmad ya dawo da zancen ai lumewa zatayi a ?asa kawai ta huta.

Harta bacci ya fara fizgarta wayarta ta tayar da ita, Data ta a buWe yake dan haka taga sunan Ahmad Bechi a truecaller, kamar ba zata Wauka ba se kuma zuciyarta ta kwabeta kan wula?anci babu kyau.
"Allah yasa ban tasheki a barci ba" ya faWa bayan data amsa wayar, cikin muryar da bacci ya fara tasiri a cikinta tace masa
"Aa".

Ahmad ya gyara kwanciya akan Gadonsa, tunda ya shiga gida suke waya da Jafar daya kai masa ?arar Hajiya wai ta kirashi akan seya Rantawa Faisal KuWi ze fara harkar Crypto kuWaWe kuma ba ?anana ba take cewa ya bashi ita lissafin Ribar da Faisal Win yace mata kawai za'a samu takeyi bata hango Risk da yake tattare da sabgar ba kuma wai rance bama kyauta take nufi harda bashi zuwa lokacin da ze turo kuWin shine ya kawowa Ahmad ?ararta ita da Faisal Win se kace ze iya masa wani abu akai be samu sun gama maganar ba se yanzun yana ta Allah Allah kar tayi bacci ba suyi magana ba.

"Kara zakiyi mun amma muryarki ta fallasaki, kiyi baccinki toh in Allah ya kaimu da safe sena kiraki ?arfe nawa kike tashi daga bacci?"

"Ko yaushe ma" ta bashi amsa cikin ?aguwa, ya fiya tambaya take ayyanawa a ranta. Ahmad naso suyi hira dan so yake ta sake dashi da sauri amma kuma bayaso ya shiga ha??inta dan haka ya mata sallama akan ze kira da safe dukda bata gaya masa sanda take tashi ba ya kuma jaddada mata kan tayi saving number sa.

Tsaki tayi bayan ta kashe wayar baccin data fara ya gudu se ta shige WhatsApp tana duba sa?onni kafin baccin ya dawo. Dm na samari gasu nan babu Adadi unread messages Winta sunfi dari duk ta tsallake ta wuce kan number Badar dataga ta mata magana da ita suke hira daman baccin ya kwasheta.

"Al'amin yace inya kiraki wayar bata shiga, a WhatsApp kuma baki buWe chat Winsa me yasa?"

"Blocking Winsa nayi" ta bawa Badar Win amsa ganin tana online. Tana turawa kuwa ta buWe ta shiga yi mata voice.

"Kina kuwa yanda ya gigice Afee zuwansa fa gidan nan biyu yau wlh se in kira masa ke a wayata na kira kuma bata shigo ba lokacin wai me ya haWaku ne? Dan Allah ki tausayawa guy Win nan wlh Al'amin yana sonki sosai fa" cewar Badar.

"Uhm duk ya gama haukansa can ya nemi daidai shi a gaba, wai ni Badar shikenan Namiji baze so ni saboda Allah ba se dan wata bu?ata ta daban? Ki faWamun tsakaninki da Allah ko da akwai wani abu da nakeyi mara kyau da yake Attracting yan iskan Maza zuwa gareni? Ni kenan duk wanda zece yana sona seya nemeni da lakata me nakeyi daya sa suke mun kallon Mara kamun kai Badar?" Fatiman ta mayar mata da Voice note muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka saboda zafin abinda take ji a ranta.

Allah ya mata farin jini bana wasa ba, bata taSa fita ta dawo gida Namiji be tsaidata ko an biyota gida ba amma duk wanda ta kula take ganin kamar zasu samu daidaito da tafiya ta fara nisa se ya kauce layi ya shigo mata da wani zancen na daban. Tun abin baya damunta har yazo ya fara bata tsoro ta yaya za'ayi ace duk wanda yazo yana sonta seya nemi ya taSa jikinta se kace ita kaWaice Mace a duniya ko kuwa duk suma sauran Matan haka ake musu??

"Na gaya miki Afee wannan matsalar fa bake kaWai ta shafa ba, abinda yasa kuke mun kallon Masifaffiya kenan na kasa tsaida saurayi ko Waya saboda ni bana iya shiru, mutum na zuwar mun da shirme a take nake tsigaleshi gara nayita zama single dina har Allah ya kawomun Mijin Aure na na gaske, ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ke kuma duk wanda yazo miki da suffar Salihai seki saki jiki se mutum ya nuna miki true color kizo kina ciwon rai kenan shima Al'amin Win shegene da gemunsa kamar Na Allah ai da kin gayamun da wuri wlh da daya zo Wazun sena wula?antashi dan iska shege me ci da buguzun da fuskar Salihai" Badar ta hau spark daga nan suka cigaba da tattauna abinda yake damunsu ya kuma zama ruwan dare a zamanin nan. Samari sun zama abinda suka zama kawai, sun maida mata tamkar wasu Takalma da zasu ce se sun gwada sun samu wanda yayi musu daidai kafin su siya a irin haka waWansu da ?adda take hawa da wanda suke kasa jure jarabawar ubangiji yayi musu suga kamar idan Saurayin ya gudu ba zasu samu wani ba se su bayar da kai bori ua hau wanda daman samarin yan latsine da sun samu abinda ya kawosu su fece shikenan se a shiga lahaula da Innalillahi Allah ya rufa asiri.

Soyayya ta ?ullu tsakanin Fatima da Ahmad ko ace farashin soyayya nata hauhawa a zuciyar Ahmad domin abinda yakeyi yafi kama da One sided Love sedai ya kasa fahimtar hakan. Kwana uku tsakanin zuwansa na farko ya sake komawa daga nan kuma ya mayar da zuwan nasa sau biyu a sati bayan nan kuma kullum a ?alla ze kirata waya sau uku yaji ya take, kulawa da tattali duk irin wadda yasan zata farauto masa da zuciyarta yana mata amma ko a jikinta shan ?amshin nan ma ?aruwa yake ko a waya idan suna magana yanayin da take amsawa tamkar bata so amsarta bata wuce Eh ko Aa shi zeyita zuba surutu inya gaji yace tana jinsa tace Wh bata da abin cewa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login