Showing 174001 words to 177000 words out of 467220 words

Chapter 59 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12120

gabanta yasa ta kauce ya sake tareta yana cewa

"Nayi sallama kin bini da tsaki ki amsa mana Ammata" ya faWa da wata cukurkudaddiyar hausa yanda kasan wani Yare yake.

Tsakin ta sake masa tayi baya a tsiwace tace
"Ka matsa Malam ni ina da abinyi"
"Zan masa amma se kin mun abu uku, firstly ki amsa sallamata dan wannan dolene a musulunci kinsani then you tell me your name, lastly you give me your digits" ya ?arasa yana irgawa da yatsunsa. Harara ta galla masa amma yanda ya bake hanyar tasan ko tureshi tace zatayi ko gezau bayi zeyi ba kuma duk inda tayi binta yake wannan yasa ta amsa masa sallamar a ?ufule tana cewa

"Se ka matsamun na wuce Malam tunda na amsa maka sallamar ai"
"Ai baki cika sauran sharuddan ba" ya sake faWa se tayi saurin tareshi da cewa
"Nayi wanda zan iya"
"Baki isa ba, na miki rangwame cikin biyu you choose one, either you tell me ur name or you give me your contact, barshima, bari sunan, bani number kawai" ya faWa yana mi?a mata wata tsadaddiyar waya da bata taSa ganin irinta ba. Ta harareshi taa harari wayar tana cewa

"Ashema kai zaka zabarmun abinda zanyi? To sunana Afeeya, dan girman Allah ka matsa ka bani hanya dan ka rigada ka makarar dani"

"Kince Allah wuce Afeeyah, suna me kyau kamar yanda kike da kyau" ya faWa fuskarsa Wauke da murmushi ya harWe hannaye a ?irji yana jifanta da wani kallo.
Tuni tayi masa nisa, a jikinta taji har sannan yana biye da ita bata waiga ba har ta shiga Department dinsu ta sauke numfashi ganin yan Ajinsu a waje suna hirarraki alamar Malamin bezo ba, ba tareda ta tsaya ba ta shige ciki abunta dan zuciyarta wani bugu take kamar wadda tayi tseren gudu.

Ta wutsiyar ido ta kalli window inda taji alamar idanun mutum akainta, yana nan tsaye kuwa ya harWe hannayensa a
?irji damatsansa sun ?ara fitowa kamar an aje duwatsu se tayi sauri maida kainta kan desk tana jin yanda zuciyarta take tsere, bata dade da zama ba Malamin ya ?araso, ya ringa zabga dictation suna rubutawa ajin awa biyu ne amma tsabar mugunta ya roqi next Lecturer da ze shigar musu ya ara masa lokacinsa tun takwas da wasu mintina bamu muka samu kanmu a hannun Dr Abolude be barsu ba se sha biyun rana zuwa sannan hannun kowa ya sage nata kam har sun kumbura gefen inda take ri?e da biro sunja ruwa daman haka yake mata duk sanda tayi dogon rubutu tofa se tayi jinyar hannu abinka da Jiki duk Madara inji Qawayenta.

Taimakon da Allah yayi musu da yace ba lokacin ze karbi note din ba Class rep ya hada ranar Wednesday ya kai masa kuma shine CA dinsu, tayi hamdala a fili dan rubutun nasu rabi da rabi tayi, idan tayi nata se ta kama na Badar duk a tsoron kar a tashi karSa ta rasa gara ko yayane dai ta rubuta mata wani abu.

A mugun gajiye ta wuce Geography mosque dan Azahar ta kawo kai gara ta tsaya tayi sallah kafin ta koma Hostel ta Wan kwanta zuwa La'asar suna da wani Ajin. Seda tayi alwala ta shiga cikin masallacin tayi Nafila raka'a biyu kafinta nemi guri saitin fanka ta kishingiWa tana jin kamar tayi bacci saboda gajiya ga bashin na daren jiya da batayi dakyau ba. Wayarta ta shiga Vibrating ta janyota daga cikin jaka, gaba Waya ta sha'afa da ita.

Tun gurin ?arfe Tara an kikkirata dukda bata duba ba tasan baze wuce Ahmad bane me kiran yanzun ma tana cirota kiran nasa na tsinkewa a nan taga missed calls Win daya mata guda biyar se Message da yake tambayar lafiya yana ta kiranta bata amsa ba idan tagani ta kirashi.
Tayi ?aramin tsaki da batasan dalilin yinsa ba kafin ta danna kiran layin nasa ringing biyu tayi ya katse se gashi ya biyo baya dukda uban katin wayar da yake loda mata duk satin duniya amma idan ta kirashi baya Wauka, ire iren halayensa na kyautatawa da suke son tursasa zuciyata sonsa kenan badan ta aminta dashi ba har ?asan rainta.

Cikin muryarsa me sanyi amma ba kamarta mata bafa Aa irin ta Mazajen da hayaniya bata dame su ba yayi mata sallama, ta amsa kafin ta gaishe shi wannan tarbiyyar Ummansu ce gaisuwa ga duk wanda ya girme su ta kuma rigada ta zame mata jiki.

"Fatima! Lafiya ina ta kiran wayarki tun da safe baki Wauka ba?" Ya faWa bayan daya amsa mata gaisuwar. Taja numfashi saboda Fatiman daya kirata, bata so amma ta rasa ta yanda zata gayawa Ahmad ya dena. Sunan Innar Baffansu ce kuma sunan Kakarsu data haifi Ummansu sannan Babbar Yayar Baffansu wadda ita ta ri?eshi itama sunanta Fatiman. A hannunta ya girma bayan rasuwar Iyayensu, su uku kacal suka haifa daga Ita se shi se ?aramar ?anwarsu Umma Halima ita Umma FaWima wadda ta ri?e Baffa ta girme musu sosai dan shekaru bakwai ta bawa Baffansu shi kuma ya bawa Umma Halima shekaru biyar, wannan tudu ukun da naci na sunana FATIMA yasa kowa yake jin nauyin faWarsa se AFEEYAH La?abin da Baffa ya bata ko a makaranta a rigister kaWai ake kiranta da Fatima amma kowa da AFEEYA ya santa banda Ahmad da bata tsammanin ma yasan ana Kiranta da Afeeyah.

"Kinyi shiru, kina jina kuwa?" Ya sake faWa abinda ya maidota daga tunanin data tafi ta sauke numfashi kafin tace
"Ina jinka, ina Class tun 8 bamu jima da fitowa ba na shigo masallaci kenan daman yanzu nake so na kiraka" tayi masa ?arya badan tana da niyyar kiran nasa ba. A tausashe ya sake ce mata

"Ayya sorry love, gaskiya Malaman nan suna wahalarmun dake da yawa amma kun gama gaba Waya yau koh?"
"Aa fa ina da wani Ajin 4-6 ma" tabashi amsa, cikin jimami ya sake cewa
"Toh Allah ya bada sa'a, in sha Allah kamar yau ne zaki ga kun gama ai sedai ki ringa tuna baya kina kewa. Nima daman Wazun na shigo Zaria na Wauki Jafar yanzu haka ma muna hanya zan kaishi Abuja ze koma London. Naso mu haWu amma babu komai in Allah ya kaimu se Wednesday zan juyo ko Thursday zan tsaya kafin na wuce Kano na ganki.

"Allah ya tsare hanya ya maido da kai Lafiya" ta faWa, cikin tsokana yace
"Shifa Jafar, baki yi masa Addu'a ba? Ko na bashi wayar ku gaisa harda ma fa saboda shi naso mu haWu yau dai Abokanan faWa suga juna"

Cikin sauri tace "Allah ya kiyaye ko Inuwarsa bana fatan Allah ya nunamun ballantana wai mu gaisa dashi, idan so kakeyi na sake faWa maka na tsaneshi fiye da yanda yake tunanin shi baya sona" cikin tsiwa take maganar tareda fushi tana tuna kalaman Jafar ?anin Ahmad, shekara guda kenan amma ta kasa manta abinda yayi mata.

Murmushi Ahmad yayi haka kuma ta jiyo wani dogon tsaki daga cikin wayar wanda ta tabbatar da Jafar Win ne yayi ai ko a fusace ta Waga murya tace
"Allah ya tsinewa tsaka ma ballan tana kai abin banza"
"Fatima" Ahmad ya kira sunanta se tayi shiru amma bata amsa masa ba yaci gaba da cewa
"Ni nake Driving, idan na isa zan kiraki Ok?"
"Allah ya tsare ka kula mun da kanka kaji" ta fada bawai har ranta ba sedan tabbatarwa da tayi wayar a speaker take kenan tunda yace shi yake tu?i Jafar yana jin duk maganar ta keyi shi take so ta bawa haushi".
"I will, you take care too I love you" Ahmad ya sake faWa tana jiyo Jafar Win cikin fushi yana cewa

"Wlh Yah Ahmad either you cut this call ko kayi dropping nawa a nan, da wata muryarta ta Villagers ko Turanci bata iya ba"

"Tunda ba karatun fatiha na kasayi ba ai da sau?i, kaida Turancin yake yaran Babarka ai se kayi tayi" ta faWa bata jira amsarsu ba ta kashe wayarta tana jan tsaki daidai nan kuma aka fara kiran sallah.
Fita tayi ta Waurayo bakinta ta dawo ranta na suya, Bata taba haWuwa da mutumin dayaci mutuncinta yaci na iyayenta irinsa ba ita kuwa bata da babban ma?iyi daya wuce wanda yace ze keta Alfarmar iyayenta a duniyar nan, za'a iya takata ta shanye amma fa kar a taSa mata Iyaye Jafar kuma ya keta wannan Alfarmar ya zagesu shiyasa bashi da sauran mutunchi a idonta balle ta raga masa.

Shi kansa Ahmad Win Alfarmar Baffanta yaci da har taci gaba da kulashi dan yace ba laifin Ahmad bane ba ba kuma shi ya saka Jafar yayi abinda yayi ba dan haka ko a gurin Allah laifin wani baya shafar wani ta ha?ura taci gaba da saurararsa amma wannan dalili yasa karSuwar daya fara samu a gurinta a baua ta wargaje kuma har zuwa yanzu tsayin shekara daya da faruwar abun ta kasa mantawa haka zuciyarta ta gagara yarda da Ahmad Wari bisa Wari har yanzu.

Tana tare dashi ne kawai saboda karamcinsa amma a kullum cikin addu'ar Allah ya fiddo mata da Miji daidai da ita takeyi ba zatayi Wage ba ta kai kanta inda bata isa ba domin daga abinda Jafar yayi mata ta saka a rant tana tareda babban ?alubale idan ta shiga zuri'ar su Ahmad domin ba ?arya Jafar yayi ba ya faWi gaskiya ita Win dasu akwai banbanci, tazarar dake tsakanin su tamkar ta sama da ?asa ce ta fito daga gidan Talakawa amma masu wadatar zuciya, Babanta Bakanike ne Ummata kuma Tela ce basu da wani gata sena ubangiji saSanin su Ahmad da suka fito daga babban Ahali tana nufin gidan da aka tara Arzi?i na KuWi dana Zuri'a, Mahaifinsu Babban Attajiri wanda duk mutumin daya kwana ya tashi a Nigeria baki Waya yasan sunansa.
*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*

*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*

*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*

*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*

*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*=?
?
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY =؅?=د?*

*Address =?G?=?G?:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 9*

Bayan ta idar da sallah tayi addu'a tana shirin tashi Maman Minal ta shigo masallacin, Roommate Winta ce dan haka ta dakata ta jirata tayi sallar itama kafin suka rankaya Hostel. Tana hango Senate Building Gayen Wazu daya tareta ya faWo mata a rai, taSe baki a fili tace
"Wani sangangan dashi kamar basamude, kai wannan duk yanda akayi ya hada jina ma dasu"
"Suwa?" Maman Minal ta tambayeta seta tsuke baki tana cewa

"Ai yau gamo nayi da safen nan in gaya miki" ta kwashe da dariya tace
"Gamo Afee, na Aljani kona soyayya?"
"Mutum Aljan dai, wani fa sangamemen mutum in gaya miki, wlh gani na nayi a gabansa kamar nida Ruth, kofa fuskarsa bana iya gani sosai saboda yanda yayi sama da yawa".

Tsabar dariya seda Maman Minal ta kware ta dage Ni?ab din fuskarta dan tasha iska sosai idonta cike da hawaye tace
"Kinga kin sakani irin dariyar da babu kyau meye kuma Mutum Aljan ana zaune lafiya? Inaga irin yan Basketball Win nan kika gani sune zabga zabga ni jiya da daddare da naga wani Yaro seda gabana ya faWi, kinga tsayi? gashi siriri kamar ze tsinke".

"Wannan ba siriri bane gaskiya yana da yar ?iba badai sosai ba amma fa dogone yanda kika san jinjirin samudawa" ta sake faWa tana hakaito Jay a zuciyarta.

"Allah ya shiryaki dai Afeeyah a ina ke kika taSa ganin jinjirin samudawan toh da har kike kiran wannan haka?"

"To dai yau na ganshi, Allah yasa mu sake haWuwa zan muku video sa ku gani" ta sake faWa tana ?o?arin zaro Id card suka shiga hostel.

Sururat na maida shinkafar data tace cikin tukunya sukayi sallama, ta amsa tareda watsawa Afeeyah hararar wasa setaa ajiye jakarta akan gadotna tana cewa
"Whats up my love?"
"My dear, if u like call me Shahrukan but you must wash this plates" muka kwashe da dariya harda ita da tayi maganar Maman Minal tace
"?arshen love kenan ba, amma dai a mata ha?uri ta huta yanzu, kinga duk ta rigamu fita da safe"
"Wlh Anty Zarah na you dey spoil dis girl, haba yarinya se gaye cinguli work she cannot do" Sururat ta cigaba da Mita, Afee ta rungumeta ta gefe tana dariya tace
"Haba sisi na kinsan fa zan wanke yanzun haka wlh kaina ciwo yakeyi, we had a boring class and i still have one more to go" mtsw tayi ?aramin tsaki danda gaske kan nata ciwo yake mata.
Fuskarta Sururat ta nuna tausayawa kafin tace
"Eyya, let me finish cooking then you eat and get some sleep you will fell better, sannu kinji".

Afee ta wuce gaban gadona ita kuma taci gaba da hada Salad Win da takeyi, kayan jikita ta cire ta daura Zani harta zauna kuma kawai ta Wauki Hijabi da Jakar kayan wankata da Bucket daya ta sauka ?asa. A bathroom Win down floor tayi wanka ta ciko bucket da ruwa ta koma lokacin har Sururat ta gama abincinta zuba musu a babban Try kamar yanda suke ci yawanci idan kowa yana Wakin yau su uku Badar na Kaduna tasan dai tana hanyar dawowa Ummi kuma se Five zata gama Lecture, Ruth tana kan gadonta duk yanda suke janta a jiki da nuna mata an zama Waya takan kama kanta musamman irin lokutan da suke cin abinci sedai ta Wibi nata a plate daban amma ba zataci dasu ba.

Tsaf suka cinye abincin data saka musu suna santi dan Sururat ba daga nan ba gurin iya girki, ta wuce wanka da sauri dan tana da aji ?arfe biyu ita kuma Afee ta tattare gurin ta haWe kwanukan dattin duka a bokiti ta sauka dasu ?asa. Wata Mama da take kai munu ruwa da wanke wanken wasu lokutan n
Ta bawa kwanukan na koma Waki. Maman Minal tace mata

"Afee bari naje dakinsu Nnenna mu ?arasa Assignment Win nan"
"Sannu Eng girls" ta faWa tana hayewa gado. Tana ganin ?o?arin Maman Minal wato Anty Zahra, Mechanical Engineering take aji biyar. Matar aur???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e ce harda yaranta uku kuma da auran nata ta fara karatun lokacin tana da cikin fari gashi a shekara hudu tayi yaya uku kuma cikin luWufin ubangiji bata taSa samun carry over ba Allah ya taimaketa ya bata Miji me fahimta da son tayi karatun duk dashi ba dan boko bane hasalima iyakarsa secondary school amma be tauyeta ba kuma iyayensa sun bata gudummawa Yaranta uku duk a hannun uwar Mijin suke yanzu da sun shekara zata ce ta yaye su taji da karatunta suna can Kaduna ita kuma ya kama mata daki a Off K tun Level one ba kuma ya gajiya da kawo mata ziyara A final year din nan ne ta dawo cikin makaranta gaba daya da zama kuma a nan suka haWu Waki Waya da ita sedai idan Mijin zezo ne zata buWe
Wakinta na Off K ko idan matsalar rashin ruwa ko wuta ta faru a cikin makaranta zasu tafi can duka. Ita ce ta zama Kamar Babbar Yayarsu duk abinda taga zasuyi mara kyau zata tsawatar musu tsakani da Allah take zaune dasu shiyasa suke bata girma sosai.

Bata san tayi bacci ba seda ?arar Alarm data saita ta manta wayar a saitin kanta ya tayar da ita, a firgice ?iris ya rage ta faWo daga gado. Ta ringa tsaki kamar wani ya aje mata wayar, ganin tsakin baze kai ta ba ta miqe. Duk sun fita se ita kaWai ashe, a gurguje ta sake watsa ruwa saboda yanayin garin da akwai zafi tayi Alwala, Riga mara nauyi me spagetti hannu ta saka ta zame ribbon Win kanta, tafi kwana uku bata taje kan ba sedai ta saka hannu ta warwareshi dan bata son jan gashin ta koda kanta ne balle wani yaja mata shiyasa bata kitso ta kwantar sa gaban da bruah kafin ta saka Chantilly cap ta zura Jilbab kalar Maroon me duhu tun wanda Ahmad ya bata haWuwarsu ta farko, Son Hijabin take kamar rai, dukda ya sake siya mata wasu har Number matar da takeyi wato *UMMU MAHEER 07061838488* Ta karSa a gurinsa saboda duk wanda ya gani se yace yadin masa kyau a ina ta siya shine kawai Ahmad ya bata shawarar ta fara siyarwaq sosai kuma take cinikin Hijaban a cikin Campus.

Ta kalli kanta a Mudubi, gani tayi tayi haske fau da yawa kamar wata Zabiya yau hakan yasa tayi saurin cire Hijabin ta lalubo wani Fari ta saka, Badar ta tsani Hijabin, na Anty Sauda ne da tayi Umarar Azumi dashi ta karbo duk sanda ta saka se Badar tayi tsaki tace "se kace fatalwa" ita kuma son Hijabin takeyi.

A gurguje ta fita, tana shirin kulle ?ofa Badar ta hawo saman da ubannin ledoji tana nishi, ta banka wa Afeeyah Harara ita kuma ta fashe da dariya saboda yanda ta rungumo kaya kamar irin haWamammun Yaro boys da ba zasu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login