Showing 63001 words to 66000 words out of 467220 words

Chapter 22 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12141

mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*

"To ai babu damuwa samari ina jinka ka fadi abinda yake tafe da kai wadannan ba baqi bane Aminaina ne koma menene yake tafe da kai ka fada suji" Malam Hassan ya fada. Audu ya kalli mutanen da ya kira da Aminansa kafin ya sunkuyar da kai, bashida tabbacin basa cikin wadanda suka zugashi harta kori yarsa tunda yace Aminansa ne su dan haka baze fadi maganar a gabansu ba balle su hanashi karbarta. Qara qasa da kai yayi yace
"Kayi haquri Baba amma daka daure munje gefe dan maganar da take tafe dani dakai kadai zan iya tattaunata"

"Ka je mana Malam kaji abinda yake tafe dashi" daya daga cikinsu ya fada, Malam Hassan yayi shiru yana kallon Audu kafin ya yunqura ya janyo sandarsa dake gefe ya tashi, Audu ma ya miqe yabi bayansa yana kallon yanda yake tafiya a gicciye tamkar wanda ya taba samun ciwon mutuwar barin jiki". A soron gidan suka tsaya, Malam din ya kwalawa wata yarinya me suna Surayya kira ta fito da sauri, kamarsu daya da Zubaida dan seda gaban Audu ya fadi daya ganta.
"Kawo mun kujerata" ya fada mata ta amsa da "toh Baba" kafin ta juya babu dadewa ta dawo da kujera me qafafu hudu irin ta qarfen nan doguwa Malam din ya dogara ya zauna akai yana nunaqa Audu wani tudu me kama da Dakali dake cikin zauren amma da Qaton dutse akayi shi. Audu ya zauna yana fuskantar Malam din.

"Ina jinka samari, meke tafe da kai?"
"Kayi haquri da abinda nazo maka dashi Baba sannan ina fata ka fahimce ni"
"Ka tafi kanka tsaye bana son wannan alayen me yasa kake son magana dani?"

"Akan Zubaida ne" Audu ya fada yana kallon Malam din dan ganin yanda zeyi reacting aikuwa ya zabura tamkar ze fado daga kan kujerar Audu ya tare shi. Jikin Malam Hassan ya dauki rawa ya qanqame Audu yana cewa
"Zubaida naji kace? Ina ka ganta? Kasan Zubaidata? Dan Allah tana ina daman tana tana raye?" Malam din ya fada cikin rawar baki tareda daga sauti abinda ya fito da yarinyar dazun da gudu kenan tana tambayar
"Baba lafiya?"
"Sunan Yayarku ya ambata, dan girman Allah ka gaya mun a ina kasan Zubaida tana ina?" Malam din ya sake fada babu tsammani se ganin hawaye yayi a fuskar Malam tamkar yanda Surayya ta fashe da kuka itama tana ce masa
"Ina Yayarmu? Dan Allah ka gaya mana a ina ka santa?"

"Kayi haquri Baba zan gaya muku amma se ka nutsu ka dena daga murya karka janyo hankalin mutanen waje" Audu ya fada yana zaunar da Malam din a kan Kujerar daya tashi.
"Muje ciki Samari wannan maganar bata zau bace muje ka sanar mun inda kaga Zubaida" Malam ya fada yana miqewa, Surayya ta dauki kujerar jikinta na rawa suka shige ciki Audu ya mara musu baya.

"Tausayin Malam da Surayya ya rufeshi ganin yanda suke kuka tamkar ransu ze fita bayan daya gama basu labarin inda ya hadu da Zubaida.
"Allah ka yafe mun, wlh sharrin shaidan ne da zuciya ya ingizani na kori yarinyar nan. A sanadiyyar haka abubuwa da yawa sun faru. Baqin cikin rashinta ya saka mahaifiyarsu kwanciya jinyar da har tayi Ajalinta nima kuma na gamu da hawan jini har mutuwar Barin jiki na samu seda na shekara biyu ina jinya bayan rasuwar Habiba kafin Allah ya bani lafiya, wallahi nayi nadamar abinda na aikata babu inda kuma ban shiga ba a garin nan ina cigiyar Zubaida, har gidajen Mata masu zaman kansun na ringa zuwa ko Allah ze saka na samu wanda ya ganta amma ba'a dace ba se daga baya wani bawan Allah ya sanar mana wata Mata ce ta tafi da ita amma besan motar garin da suka hau ba. Tu daga nan na fawwalawa Allah na ke kuma Addu'ar idan har Zubaida tana raye Allah ya gama fuskokinmu kafin na koma gareshi kona nemi yafiyarta, dan Allah Samari tana ina? Ka kaini naga yata karna mutu da haqqinta a wuyana" Malam ya fada yana sake rushewa da kuka.

"Kayi haquri ka kuma kwantar da hankalinka Baba, naso ace mun taho tare da ita amma taqi tace ba zata dawo Kano ba se idan har kai da kanka kace ta dawo dan bata so ta sake shiga wani fushin naka amma yanzu tunda anyi haka zan koma Zariya gobe idan Allah ya yarda a gidan nan Zubaida zata kwana" da wannan Audu yayi musu sallama tamkar Malam Hassan ze bishi haka ya ringaji, bayan ya fito daga gidan su Zubaida harya dauki hanyar gida ya fasa kaitsaye ya wuce gidan Mai. Full tank yayi, a nan ya tsaya yayi magriba ya dan ci abinci dan rabonsa da abincin kirki tun safiyar jiya kafin su tafi Zariya.

Musbahu ya dauka, Dan Yaya Baba ne daya dakko ya sakashi a gidan Mai yace yazo ya rakashi a daren ya dauki hanyar Zariya. Musbahu ya ringa zare ido ganin inda sukaje, to me ya kawo su nan kuma. Zubaida na bacci taji bugun qofa ta tashi ta bude mamaki ya cikata ganin Audu.
"Dama baka tafi ba?" Ta tambayeshi, ya kalli Musbahu kafin ya kalleta yace
"Ki hada kayanki Asubanci zamuyi na je na samu Baba kuma ya yarda ki dawo gida"

"Qaryane, yaushe kaje Kano har ka dawo nan?" Ta fada tana kama qugu, yayi gaba yana ce mata
"Qanwarki Surayya ta girma kamanninku daya tamkar Tagwaye"
"Innalillahi dagaske kaje gidanmu, kaha Innata me tace maka?" Ta fada tana fashewa da kuka tareda bin bayansa da sauri seya dakata yace
"Kije ki hada kayanki, mahaifinki na cike da zumudin ganinki na tabbatar yau baze iya bacci ba".

Washe garin kuwa Asubanci sukayi, shidai Musbahu bakinsa fal da tambayoyi amma babu me bashi amsa. Har qofar gidan Malam Hassan ya isa da mota, tun daga nesa ya hangoshi zaune kan kujerarsa ya rafka tagumi gefe Aminan sa na jiya na tsaitsaye.
"Ina ga shine wancan" daya ya fada yana nuna motar dake tun karo su, Malam Hassan ya miqe jiki na karkarwa, Zubaida ta fashe da kuka ganin da gaske Mahaifinta ne tsaye qofar gida yanayinsa kuma ya nuna ita yake jira.

Audu kasa jure wannan yanayi na haduwar Uba da Ya yayi bayan wasu shekaru, be ko yi mata sallama ba yaja mota suka tafi.
"Wlh idan naji zancen nan a bakin wani nida kai ne" ya fadawa Musbahu sanda ya sauke shi a Gidan Mai.
Gida ya wuce, yayi tsammanin tarar da yaqi saboda fita daya sakeyi ya kwana amma se yaga akasin haka. Bintan bata nuna damuwa kamar jiya ba daya shiga wanka ya fito ya tarar ta shirya masa abinci ya zauna kuwa ya nadi abinsa dan a yunwace yake yana ci amma zuciyarsa da kwakwalwarsa suna kan Zubaida ko me takeyi oho.

Binta kuwa abinda ya faru jiya bayan ya shiga wanka fita tayi ta tafu gidan Baturiya.
"Bari kiji, duk matar da kikaga ta isa to wayo, dabara, kissa da kisisinarta ya kaita. Karki bata wayonki a gurinsa bayan kin rigada kin fara kafa gwamnatinki. Wannan ihu da hayagagar baze saka ya fasa abinda yayi niyya ba amma cikin salo da dabara se kiga kin rabashi da koma wacece dan haka ki koma gida ki bashi haquri da sannu ki gano bakin zaren sannan muyi qoqarin daukar mataki, sannan banda abinki ai da kishiyar gida gara ta waje. Kinsan duk Namijin daya saba zama da Mace biyu ma wuyaci ne ya iya haquri da daya dan haka in har ba so kikeyi ya aurota ya kawo miki ku zauna tare ba ki rabu dashi yayi sabgar gabansa" abinda Baturiya ta gaya mata kenan shiyasa ta dawo gida amma fa a zuciyarta bata jin zata iya jurewa kamar yanda tace mata amma zata gwada dauke kai dan kamar yanda Baturiyar ta fada tabbas da Kishiyar gida gara ta wajen.

Kusan sati daya da dawowar Zubaida gidansu kafin Audu ya sake zuwa, har cikin gida Malam Hassan ya saka ya shiga.
"Nayi ta neman inda zan zameka ashe itama ko sunanka bata sani ba, Yaro na gode, yanda kayi mun wannan Alfarmar ina fatan ubangiji ya jibanci lamarinka ya rabaka da iyayenka lafiya, nagode kwarai daka maidomun da Zubaida gabana, nagode daka zama silar barinta rayuwar barna" Malam Hassan ya fada daga nan ya basu guri shida Zubaidan dayaga tayi wani sanyi qalau tamkar ba ita ba.

"Nagode da abinda kayi mun Allah ya biya maka buqatunka na Alkhairi" tace daga nan sukayi shiru kamar kowannensu ya rasa abin fadi shi ya gaji da shirun yace mata
"Ina fatan abinda ya faru a baya ze wuce, ki cire komai daga ranki ki faro sabuwar rayuwa. Abinda ya faru qaddararki ce kuma Imanin mumini baya cika har se ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau sannan, ina fatan hakan ya zame miki kaffara. Sannan kuma ina nan akan bakana na neman yardarki, ina so da zarar kin kammala Istibra'i za'a daura mana Aure"

"Kayi haquri bana zaton na dace da nagartaccen Namiji kamarka, nagode da abinda kayi mun kuma in Allah ya yarda zan yita yi maka Addu'a Allah ya baka mace daidai da kai" ta fada cikin sanyin jiki. Babanta na cikin daki yana jiyosu yayi gyaran murya yana cewa
"Wannan wace irin maganace Zubaida, kana jina ko Yaro kaje in Allah ya yarda bata da wani Miji idan ba kai ba. Banda rashin wayo ki samu miji kamarsa har ki tsaya kinibibi ai yafiki sanin abinda ya dace dashi din kuma yace ke yake so"

"Shikenan Baba nagode, in sha Allahu kuma zan turo da magabata na e a tsaida magana".

Watanni uku bayan dawowar Zubaida gida, a hankali tun tana sharewa harta yarda ta sakarwa Audu fuska soyayya me sanyi ta qullu tsakaninsu, d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ukda tana matuqar jin kunyarsa kasancewar yasan komai na rayuwarta ta baya, ta kanga kamar wata rana ze goranta mata bama shi ba babban damuwarta yan uwansa take zaton ya zasu dauketa idan har sukaji ita din wacece a baya gashi yace mata yana da mata ire iren wadannan tunanin yake sare mata guiwa taji kamar ma Auranta da Audun baze yuwu ba. Watanninsu hudu tare Malam Hassan yace ya turo magabatansa saboda yana so ya hada da Auran Surayya ayi gaba daya, su uku suka rage cikin yaya shiga da mahaifiyarsu ta haifa ukun sun rasu suma bayan rasuwar Mahaifiyar tasu se Surayya da Ibrahim Wanda yake bin Zubaida ne suka rage masa be kuma sake Aure ba tun rasuwar Habiba shekara bakwai kenan.

Babu damuwar komai Kai tsaye Audu ya tafi Bechi ya samu Yaya Baba ya gaya masa cewar zasuje nema masa Aure nan da sati daya, mamaki ya kama Yaya Baba saboda Yakubu yaje Bechi ba'afi sati daya da tafiyarsa ba kuma beyi musu zancen Auran Audu ba dukda yaga alamar kamar Audun ma be san yaje din ba, tun rabuwar Auransa da Bara'atu abubuwa sukayi zafi tsakaninsa da Yakubu.

Yakubun Yayi fushi me tsanani shi kuma Izza da ganin yanzu ya isa ya hanashi ya neme shi su sulhunta. Yaya Baba bashida ta cewa dan haka ya amsa masa da Toh, ya kuma sanarwa da sauran yan uwansu abinda ake ciki take Hashimu yace ba zashi ba. Aminu ya samu Audu ya tambayeshi Yakubu yasan da magabar kuwa yace masa Aa.
"Wannan abinda kukeyi sam be kamata ba, kaine qarami dan haka ka nemeshi ku sasanta. Me yasa kakeyin tufka kana warwara? Kayi nasarar hade kanmu sannan kuma ka koma ka bata da Yayanka da kuke ciki daya akan Mace wannan wane irin abu ne?"

"To ni Aminu menene laifina a ciki, Shi ya fiya damuwa ne kawai idan ba haka ba menene nayin fushi akan na rabu da Bara'atu nifa nake zaune da ita ni nasan matsalarta amma shi ne da fushi dan na saketa?"

"Saboda yafika hango abinda yake daidai ne shi yasa kai kanka kuma da zakayi duba na tsanaki zaka gane abinda ake qoqarin fahimtar da kai. Da ace zaka ji shawara da ka haqura da sabon Auran nan ka maida Bara'atu dakinta" Aminu ya sake fada. Audu yayi shiru kafin ya kalle shi yace
"To kai ka aureta mana ko kuma shi din ya aureta tunda kun fini sanin darajarta".

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE17*


Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi.

"Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa
"Amma zaka zo ko? Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin"
"Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace

"Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma"

"Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko"

"To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace

"Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa"

"Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a? Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada. Yakubu yayi dariyar takaici yace

"Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su. Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi.

Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi. Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan?
Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi. Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta.

Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji. Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa
"Meye? Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan? Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?"

"Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi.

Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina? Ni yau babu wanda babu wanda nayi da ita zatazo"
"Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi"

Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu. Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba. Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace

"Kayi baqi"
Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login