Showing 294001 words to 297000 words out of 467220 words

Chapter 99 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12238

kama da wuta saboda ba?in cikin shagalin sunan da akayi ga kuma dukiyar da Jafar ya hallakar yayiwa Yayan Ahmad bajinta, har kuka seda tayi dama cike yake dashi akan lamarin matarsa da tayi yaji tana can gidansu, tsabagen ita Hajiya Binta ta zama abinda ta zama wai Aisha Maman Fatiyyan ta kira tana tambayarta ba'asin abinda ya faru saboda bata yarda da maganganun da Fatiyyar taje tace ya faru ba, ita da take ta kaf kaf kar kowa yasan da Saraka a tsakanin Jafar da Matar tasa tana ta bin sa yaje ya taho da ita amma ya?i, wasan Suya ma sukeyi yanzu ya dena zuwa gidan se kuma ga sabon abu wai Aisha take ce mata Maman Fatiyyah ta kirata amma ta tura mata da number Bintan saboda ita bata ma san matar Jafar bata gida ba balle tasan abinda ya haWasu, ranar bata iya runtsawa ba. Sunje gidan Malamin da Turai ta kaita, bata tsammaci zata iya zare zunzurutun kuWaWen daya cajeta ba se gashi babu ko musu ta bayar koda yake hausawa suka ce ranar biyan bu?ata rai ba a bakin komai yake ba, toh yadai ce ta koma gida ta kwantaar da hankalinta tasha kallo, Ahmad dai daya shige mata hanci da ?udunduno zataga yanda Waukaka da shaharar daya Webo zata dishashe, gurin da Aisha ta samu har take iya goga kafaWa da ita seta rasa kwarin guiwarda ko ido ba zata sakw iya haWawa sa ita ba balle kuma wani Audu ?aramin Alhaji, Malam yace taje ta wasa wu?arta kawai dan seta zuba mulki irin wanda bata gwada ba ko a zamanin ?uruciyarta ba amma a maimakon biyan bu?ata tunda ta baro gurin sake rikicewa abubuwa sukeyi babu wani sau?i a ciki

Ranar da Maman Fatiyyah ta kira Aishar haka ta kwana da ba?in ciki kamar zuciyarta zata tarwatse ta fashe, washe gari da sassafe ta tafi Kaduna ko shi Alhajin a bakin megadi yaji cewar Alasan guda daga cikin direbobin gidan ya tafi kai Hajiya Kaduna, ashe dai dangi suna da rana sega Hajiya Binta gaban Hajiya Ummu tana kuka wiwi tana zayyano mata damuwoyin da suke neman hanata sha?ar numfashi da kyau.

Hajiya Ummu ta gama sauraronta tsaf kafin tace
"A duk abinda kika faWa Binta ni banga damuwa ba ke a karan kanki kece damuwar kanki, kece kike hana kanki sukuni tun zamanin ?uruciya Binta har girma yazo ace ba zaki kyale zuciyarki ta samu salama ba nan aka Waukeki aka kaiki inda za'a kula sa lafiyarki ki huta amma kika gudu kinfiso kizo ki yita tayarwa kanki hankali kina tayarwa da wasu yaushe zaki saduda ki bar zuciyarki ta huta ne Binta?

Kullum kukanki Yayan kishiyoyinki sunyi kaza sun samu kaza waya taSa Waga kai akanki da abinda naki yayan suka mallaka? Yanzu iya abinda ya faru a baya be isa ki gane babu meyi se Allah ba ?yashi da hassada basu isa komai ba akan bawa ba muddin ubangiji yana tare dashi?

Binta kiji tsoron Allah, ki ribaci lokacin daya ara miki ki gaggauta canza rayuwarki ki sauka daga kan wannan gurSatacciyar hanyar da kike kai domin babu inda zata kaiki se tashar dana sani a gaba idan kuma bakiji ba to ki tabbatar da cewar wata rana kina zaune zuciyarki zatayi bindiga tush ta fashe in har baki sahale mata nauyin abinda yafi ?arfinta ba, sama da shekara arba'in kina abu guda ki ha?ura mana Binta tunda keda kanki kin yarda ba riba kike ciba a kullum faWuwa kikeyi".

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 12*

Hajiya Ummu da Hajiya Salima be bisa dole badan ransu yaso ba suka raka Binta bikon surukarta, kuka ta dasa musu da sukace ba zasuje ba dan ita Hajiya Ummu tayi magana da Jay ya sanar mata da duk abinda ya faru yanda Fatiyyan ta ringa masa rashin mutunchi tana zaginsa kuma shi bashi yace ta tafi ba kawai ya mata gargaWi ne akan babu ruwanta da sabgarsa kuma yana da damar da koma wacece zata kirashi tunda Shi mijin mace huWune wannan tasa ta bar gidan ya kuma rantse baze bita ba duk sanda taga dama ta dawo. Dukda Ummun tayiwa Binta bayani amma ta?i ta fahimta, daga ?arshe ta fasa kukan kowa ya juya mata baya su da suke jininta ma sun kasa rufa mata asiri to waye zeyi mata? Ta gama black mailing nasu emotionally dole suka rakata anyi sa'a Maman Fatiyyar macen kirki ta nuna rashin jin daWinta akan zuwan da sukayi tace ai da sun barta kawai tunda ita ta taho duk sanda zaman gidan ya isheta zata nemi hanyar komawa Wakinta Hajiya dai tace Aa, ai tare zasu wuce haka ta kwasota suka dawo Kano a gabanta tayiwa Jafar Win tas ta kuma jaddada masa koma wacece ba Afeeyah ba ko bayan ranta bata yarda da zancenta ba, Fatiyyah ita tayi mata a matsayin ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?suruka karma ya kuskura ya sake tunanin cewar ze haWa ta da wata, sati Waya da haka suka tattara suka koma Uk aka cigaba da lallaSa rayuwa nan hankalin Hajiya ya kwanta ta maida ?aimi kuma gurin cikar burinta wato maido da martabarta kota halin ?a?a tayi al?awarin babu qata mace da ta isa tazo daga baya tasha gabanta a gurin Audu haka nan babu wani ?a da ze zarce nata a cikin gidan, dukkanin idonta na kan Ahmad, ya tsaya mata a ma?oshi.

Yanda ya taso da hasken da take gani a rayuwarsa alamu suna nuna Shi ze zama magajin Audu, dukiya da shaharar yayanta suka samu lokaci Waya yana neman shafeta koda yake daman Jafar dai shine komai nata duk wata tun?aho da firirita akanshi takeyi daga Zakariyyan, Naziru har Yakubun babu wani da zata Waga ta yaba duk ta cicciSasu ta kaisu ga tsira amma basa ta tata kowanne ?o?arin gina kansa kawai yakeyi to shina Jafarun yanzu abin nasa kamar wanda aka sakawa hannu lamuransa maimakon suyi gaba ja baya sukeyi

Gaba Waya ya zama wani abu daban, kwanaki Yakubu ce mata yayi yace ze bar ?wallo ya dawo gida kawai ko komawar nan tasa seda Maalamin Turai yayi aiki akai dan daman ya gaya mata Asiri akayi masa so akeyi zuciyarsa ta mutu yabar sana'arsa ya dawo kawai ya zauna ya zama abin tausayi ba kowa kuma yayi hakan ba se Aisha da Yayan Bara'atu suka haWa kai suke so su kassara mata ?a gashi daman Wan abinda ya tara ya kwaso yana kashe musu haihuwar yayan Ahmad hidimar da yayi ko shi ubansu be kashe kuWi haka ba to ba zata yarda ba dan har faWansu da Fatiyyah da tafiyarta gida ma ance bayin kanta bane Aljanu ne suka ingizata shiyasa ta mi?e dagaske take neman mafita kuma da WaiWaya se tayi maganinsu, me bara tayi ma balle bana?
yanzu aiki biyu ne manya akeyi mata bayan na karya Asirin da akayiwa Jafar se kuma na karkato da hankalin Alhaji Audu kanta wanda shima Aishar ce dai tayi ba?in tsafi ta janye Shi sannan kuma aikin da za'a disashe taurarin Ahmad da suke zamar mata tarna?i gurin cikar burinta hakan kuma baze tabbata ba se ya rabu da wannna ala?a?an daya auro, Malam yace ita ce zigar arzi?insa, taurarinta nada haske su suke sake haskaka nasa muddin yana tareda ita duk abinda ya niyyaci yi nasara zata kasance tare dashi kuma ta yarda da maganar, se sannan ta gano ainihin abinda yasa ma ta tsani yarinyar kamar mutuwarta ashe tanada ala?a da hanata samun cikar burikanta a rayuwa ne amma zatayi lokacinta ne seta gwammace ba'a halicci ranar da tayi sanadiyyar fitarta harta haWu da Ahmad Win ta shigo rayuwar su ba, bataji komai ba ta zare kuWaWen da ada ko za'a mutu ba zata iya ciresu ta bawa wani mahaliki ba amma a yanzu neman tsira takeyi, Hausawa suka ce ranar biyan bu?ata rai ba a bakin komai yake ba dan haka zata kashe ko nawane domin ta tsira da mutunchin ta.

(Yaushe Binta ta fara yarda da sabgar malaman tsubbu harta iya cire kuWi taububu ta bawa Malam =?2?=?2?=?2???
Kodai a garin neman taimako itama an taimaketa =?D?=?D?=?D?to maji ma gani dai).

BAYAN SHEKARA HU?U
Abubuwa da yawa sun faru na daWi da akasinsa, a gidan Alhaji Audu dai kusan za'ace anyi mi'ara ne koma baya domin kuwa a cikin shekarun burin Binta ya cika na ganin tauraruwarta ta dawo da haskenta full light domin har tana neman tafi da haskakawa, daidaiton daya fara samuwa a cikin gidan ya watse, ubangiji ya sake ara mata dama a karo na biyu, ta samu kansa fiye da da, iko take zubawa yanda taga dama abinda tace haka za'ayi duk kuma Wanda yayi yun?urin nuna mata yatsa Alhajin a shirye yake daya karyashi. Gaba Waya yanzun kusan ya saki komai nasa Zakariyya da Yakubu se Faisal daya gama makaranta tuntuni shima ta kuma cusashi ya samu kujera me tsoka a cikin sabgar gudanarwa ta rukunan kamfanin nasu, Naziru yayi nisa, sabgoginsa sunyi girman da yake ganin ya girmi cigaba cuwa cuwa cikin tsoron kar asirinsa ya tonu, yanzu shima ya tsaya da ?afafunsa dan ita kanta Hajiyar ganinsa wahalar gaske yakeyi mata se a shafe watanni be sanya ?afafunsa a gidan ba dan haka Alhaji Zakariyyan shine komai duk wani abu da za'a bu?aci Alhaji Audu yayi toh shine madadinsa se Yakubu da Faisal da aike take masa baya.

Wannan ta kawo tarna?i cikin ?udurin Ahmad na ganin cewar kan zuri'arsu ya haWu guri guda. Iya kar ?o?arinsa ya ringayi gurin cimma wannan burin kuma Alhamdulillah har an fara samun haske domin har WhatsApp group ya buWe musu yayi adding kowa harda Alhajin a ciki dukda babu wanda yake magana a ciki shikaWai yaje abunsa kullum cikin tura maganganu da wa'azozin malamai yake akan muhimmancin zumunchi da kuma yafiya akan abinda ya gabata, ya tura Azkar safe da yamma, duk wata Addu'a daya samo ya tura musu a hankali har aka fara samun masu amsawa da Amin ya zamana ana dan yin magana sama sama haske ya fara samuwa ciki al'amuransu kafin kuma kamai ya sake lalacewa harma yaso yafi da.

Babban abinda ya ?ara hargitsa komai shine yanda lokaci Waya aka wayi gari Alhajin ya bu?aci Alhaji Babangida, Alhaji Abdullahi da duk wani daya shafi Ahalinsa ta jini kuma yake cikin harkokin kasuwancinsa bayan Yayan Binta yace suyi retire a faWarsa sun kai shekarun daya kamata ace sun zauna sun huta sun kuma mori wahalarsu ta shekaru, sanda abin ya faru har cewa Babba Al?ali yayi babu Shi babu Audu ko mutuwa yayi ya yafe karya kuskura yaje kan gawarsa. Ba ?aramin gurmi aka sha ba kuma ko gezau Audun ya kafe akan maganarsa haka shima Yakubun a wannan karon ya nuna masa cewar jini Wayane yake gudana a jikinsu idan yana jin kansa kafaffe toh tare suka gado kafiyar seda suka kwashe shekaru biyu Al?ali be taka inda Audun yake ba haka kuma ko ya je inda ze sameshi yi yakeyi tamkar be sanshi ba, tun Audun na Waukar abin da sau?i harya fahimci na gaske ne to amma kuskure ya rigada yayishi babu kuma hanyar gyarawa domin duk waWanda Al?alin yake fushi akansu tuni suka kama wasu sabgogin a rayuwarsu tamkar daman zaune suke da shirin haka zata iya faruwa babu wanda koda wasa ya nuna damuwa ko ro?on ya bar masa aikinsa, da?yar da siWin goshi Ahmad ya daidaita tsakanin iyayen nasu, haka Yakubun ya sake tsayawa tsayin daka akan lamuran Audun da suke kama dana wanda baki yayiwa yawa, tun usulan yasan Audu ba jajirtacce bane akan neman tsari Allah ne kawai yake ri?e dashi ma badan haka ba da tuntuni ya daWe da rushewa shine fa ya tashi tsaye akan komai yake nema masa taimako, to abu dai akeyi yau sau?i idan kuma ya juya ya tafka wata hauma haumar se kowa yaji kamar ya yafeshi.

**********
?arfe uku da rabi ya shiga gidan, yanayin jikinsa da baya masa daWi ya saka ya baro Shago dukda lissafin shekara sukeyi, duk yanda yaso ya daure ya kasa dole se Salim da Mu'allim tareda sauran Manajojin ya bari su ?arasa idan yaso su aika masa ta Email ya duba. Salim tare suka gama karatu da Faisal yana kallo aka Wauki Faisal Win aka kaishi Kamfani shi yana gararamba a gari, da fari Ahmad ya nema masa aiki harya fara yace baze iya wahala akan salary da bekai ya kawo ba shine ya dawo yaci gaba da zama a Shagon kafin a hankali Ahmad Win ya fara nuna masa kasuwa da sauran harkokin da yakeyi har ta kai yana turashi ?asashe ya shigo musu da kaya dukda dai ba wata nutsuwa ya cika ba shine ma babban abinda yake haWa su da Ahmad dan duk sanda lissafi ze tashi ko kuWi su bi ta hannunsa se an ga ba daidai ba.

Salim Win nada muguwar halayyar da suka gada a gidansu ta kowa tasa ta fishsheshi kowanne ?o?arin gina kansa kawai yake babu ruwansa da damuwar wani. Yanda Sarki ya ware yake sabgoginsa na siyasa haka shima yake so ace yana cin gashin kansa ba ?aramar Sarna yakeyiwa Ahmad Win ba amma haka yake jure komai sedai in ya masa abu ya masa faWa da nasiha bama ya kai maganar gurin wani saboda Momy raWaWin ba?in cikin zaman gidansu kaWai ya isheta bare ya ringa ?ara mata da damuwar Salim.

Watanni byu kenan da shina Mu'allim Win Hajiya Rabi ya kammala Digirinsa kenan suna jiran a kirasu bautar ?asa dan haka yace masa da zaman banza ya ringa zuwa shima shagon ya zauna yaga yanda kasuwa take tafiya kafin yayi deciding abinda zeyi a gaba aiki ko kuma kasuwar ze kama kamarshi.

A hankali yake takawa saboda yanda yakejin jikinsa kamar a WaWWaure duk motsin da yayi kuma se yaji kamar seke Waureshi akeyi, ya ta'alla?a ciwon jikin da tafiyar da yayi, kwanansa uku da dawowa daga Chaina, tafiyar da yayi kuma gaba Waya ta sati guda ce zuwansa da dawowarsa haka tunda yaje be zauna ba ga gajiyar zaman jirgi gata yawo kuma ya dawo Winma be huta ba saboda so yakeyi su gama lissafi ayi clearing Mall Win kafin sababbin kayan da sukayi order su iso.

Bakinsa Wauke da sallama ya shiga falon dake gyare tsaf yayi sanyi yana tashin ?amshin turaren wuta da siwis likun iya fireshina, numfashi yaja taareda sauke ajiyar zuciya yana zama akan kujerar data fi kusa dashi wani sashi na gajiyar daya kwaso na barinsa. Daga kitchen yake jiyo motsi da kamar tashin muryar Amal, seya mi?e yana cije baki ya tafi kitchen Win, yana hawa steps Win gurin dining Amal Win ta fito da gudu da container me Wauke da Milk cake Win *Mcubes Bakery* a hannunta saura ?iris ta faWi ya zube Ahmad ya tareta.
*(Yake yar uwa me bu?atar kayan motsa baki dangin cake karki bari baki labarin Milk cake Win Mcubes Bakery, indai cake me farfesun madara kike nema a Kano karki tsallakewa domin ni kaina na cire mata hula =?M?, zatayi Master class duk me sha'awar koyon Milk cake ko fara sana'arsa karta Bari wannan damar ta wuceta. A tuntubeta kai tsayw akan 08134606093)*

"Easy Amali, me yasa kike gudu haka?"
"Idan na kamaki zaki sani yau a gidan nan" Fatima dake cikin kitchen ta faWa, hannun Amal Win ya kama ta zille ta sake kwasa da gudu tayi cikin falon seya shiga kai kawai yana murmushi da alama tsokana tayi, Fatima ta kalleshi tana murmushi bayan data ajiye ludayin datake juya miya tace

"Yaushe ka shigo?"
"Yanzun nan" ya bata amsa yana matsawa kusa da ita ya rungume tareda kissing goshinta.
"Yanzu fa nake so na kira Abdulaziz ya kawo maka abinci kuma gashi ka dawo" ta sake faWa tana jikinsa yana kallon cikin idonta yace

"Kewar matata nakeyi shiyasa na kasa zama nazo naga lafiyarta"
"Sannu da zuwa" ta sake faWa tana sakinsa, ruwa me madaidaicin Sanyi ta zuba a cup ta bashi yasha kafin ta kashe miyarta danta gama ta shiga zuba wadda zasuyi amfani da ita lokacin suna yar hira. Tare sukayi lunch yana tambayarta meya dawo da Amal gida.
"Wai amai tayi a school Win jikinta kuma yayi zafi sun kaita Asibiti daga can shine aka maidota gida tun gurin 11 fa gashi nan ni banga wani rashin lafiya tattare da ita ba tunda ta dawo take sakani magana" ta bashi amsa tana dungurewa Amal Win kai, kamar su Waya da yarinyar, itace gambon Layla da Nayla watanninsu goma ta samu cikin Amal Win babu kalar kuka da magiyar da batayiwa Ahmad akan a cire cikin ba amma ya?i, a lokacin taga asalin fushinsa, yace bata son sa Shi yasa bata son gudan jininsa, seda suka kwashi kusan wata uku kafin zamansu ya sake daidaita musamman da Jafar ya shiga yayi kinini yana sake ingiza wutar har yana cewa ze kwashe twins Win idan ta haihu shima wanda bata so Win ze Wauke, a maimakon ya sasanta su se iza wutar bala'i ya ringayi haka dai ta raini cikin ta haifeshi ya saka mata Ru?ayya sunan Ummansu kuma taso yar har kamar ma ta zarce yan biyun kodan ?iriniyarta ne se Allah, shekararta uku kenan ba ta kuma samun wani cikin ba kuma ba planing takeyi ba dan tun horon da yayi mata akan cikin Amal Win taji duk wani abu da ze saka su samu saSani akan Yaya ko haihuwa ma bata sha'awarsa.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 14*

"Ahmad" Alhajin ya kira sunansa cikin sauti me rauni kafin ya ciga da cewa
"Ina tsoron nayi mutuwar farat Waya irinta Ali na tafi na bar zuri'a a ta a yanda take yanzu"

Yanda Alhajin yayi magana ba ?aramin dugunzuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login