Showing 417001 words to 420000 words out of 467220 words

Chapter 140 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12153

bakin gadonta kafin kuka ya ?wace mata yanda take kukan zaka san tun daga ?asan ranta yake tahowa. Tana ji suna buga mata ?ofa amma bata buWe ba, seda taji ?irjinta ya ri?e numfashi ma da dabara take jansa kafin ta ha?ura da kukan ta danno lambar wayar Jafar dishi dishi ma take ganin wayar ta shiga kiransa a ?alla ta amsa kira ya kai goma sha biyar be amsa ba wannan ya sake ba?anta zuciyarta, wato yaudararta yayi dashi aka shirya komai shiyasa ya mata ?arya yace ya tafi Abuja. Ta kwanta akan gadon saboda yanda nauyin da ?irjinta yai mata yake ?aruwa, tun tana iya jan numfashi har ya soma gagararta daga ?arshe bata san meya faru da ita ba ta farka kawai ta ganta kwance akan gadon Asibiti, Jafar na tsaye akanta fuskarsa Wauke da damuwa ?arara, motsin da hajiyar tayi ya ankarar da shi ta farka ya kamata ganin tana ?o?arin tashi zaune seda ya gyara mata pillow ta zauna dakyau kafin ya fita ya kira likita suna shiga Wakin kuwa murya tamkar zatayi aman Sacin rai tace

"Fita bana ?aunar ganinka a kusa dani"
"Relax hajiya yanzun kika farfaWo jikinki baya bu?atar wata sabuwar damuwar ko dan baki san a condition da aka kawo ki gurin nan ba?" Likitan ya faWa fuska babu walwala. Jay ya tsaya daga bakin ?ofa, sanda ya isa gidan ya tarar dasu Sarah tsaye bakin ?ofar Wakin ta cikin damuwa suka gaya amsa ta shiga ta kulle sunfi minti talatin suna bugu kuma ta?i ta buWe a saninsu kuka suk fushin da hajiya take bata shiga Waki tayi shiru balle har a ringa buga mata ?ofa ta?i buWewa hakan yasa ya kira securities aka sauke ?ofar nan suka tarar da ita a kwance tamkar matacciya hankali tashe aka kawo ta asibiti, tun shidan yammacin jiyan se yanzun ta farka ?arfe Waya na rana.

Kuka ta saka tana cewa likitan
"Dama ai abinda suke fata kenan shi da ubansa zuciyata ta buga na mutu se su samu sararin cin amarci da matayensu, ka fitar mun dashi daga nan in ba haka ba in janyo maka bala'i kaima".
Kafin ma likitan yace ya fita ya juya da kansa ciki matsananciyar damuwa ya koma reception ya zauna ya dafe kansa da hannu biyu. Ya rasa ya zeyi da al'amarin hajiya, a sama zancen ya tarar dashi wai an Waura masa aure da Aafeeyah sema bayan ya kawota Asibiti da yake tambayar su Sarah me akayi mata sukace basu sani ba sedai idan zancen aurensa dana Alhaji ne ya sakata a wannan halin, a bakinsu yaji wai an haWa auransa dana Alhaji an Waura a safiyar jiyan. Ya rasa me ya kamata yaji, farin ciki ko akasin haka?

Fatansa ne, burinsa ne kuma muradin sa ne auran Aafeeyah gashi Allah ya kawo masa shi a sanda be zata ba be kumayi tsammani ba sedai kuma ciwon da hajiya ya zame masa cikas be samu damar bayyanar da farin cikinsa ba yana asibiti har safiya shi ya kwana da hajiyar be ko samu kansa ba seda su Nazira suka zo da safiyar sannan ya tafi gida yayi wanka ya Wan yi bacci kafin ya sake dawowa asibitin gashi daga farkawarta maimakon sau?i abubuwan zasu sake rincaSewa.

Yana zaune Yakubu ya iso inda yake, seda ya taSa shi kafin ya san da tsayuwarsa akansa suka gaisa ya tambayeshi ko hajiyar ta farka yace masa eh likita na ciki yana dubata.
"Se ka samu kaje gida ka huta ai, kaga yanda ka firgice kuwa lokaci Waya? Allah yasa ma ka iya ko kiran amaryar taka kun gaisa dan nasan baka je ka ganta ba" Yakubu ya faWa yana zama kisa dashi. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ba tareda yace masa komai ba, hango likitan da yayi yasa ya mi?e tsaye, da hannu likitan ya masa alamar yaje suka tafi tareda yakubu zuwa office Win sa.

"A gaskiya Mr Jay muddin mahaifiyarku tana so lafiyarta ta daidaita se fa tayi ha?uri ta cire duk wani damuwa daga zuciyanta. Jinin ta ya dai sauka amma har yanzun she is at risk sannan zuciyarta kamar yanda muka gaya maka tun jiya tayi kumburi wanda aje damuwa a rai yake janyowa. Duk wani kulawa na magani da za'a bata muddin ba'a dakatar da source of ciwon ba ba za'a samu nasara ba. So sit and talk with her ku nuna mata illar dake tattare da ita da abinda zata iya janyo ma kanta muddin bata dena saka damuwa a ranta irin haka ba, ko yanzun fa da?yar seda aka sake mata alluran bacci tayi shiru tana ta maganganu marasa daWi gaskiya in har bata sawwa?ewa kanta ba to kamar yanda nace babu abinda zamu iya yi mata".

Jafar be iya cewa komai ba se Yakubu ne yayiwa likitan godiya suka fito waje.
"Kana ji ko? Koma menene me afkuwa ta rigada ta afku, hajiya ba zata canza ba dan da ace zata ha?ura duk da abubuwa ba su kasance haka ba. Kayi abinda zaka iya ka rabu da ita kawai Allah yaga zuciyoyinmu muna mata biyayya akan abinda zamu iya kuma be kauce shari'a ba, idan kace zaka biyewa halin hajiya da sunan biyayya wlh seta kaika wuta in bakayi wasa ba kayi abinda zaka iya kawai ka barwa Allah sauran, ni bari na wuce an jima idan ta tashi na dawo kaima da ka samu ka tafi gida ka huta haka" Yakubu ya faWa yana dafa kafaWar sa. Yayi murmushi yace
"Zan tafi, so nakeyi Sarah ko Nazirah su dawo be kamata a bar gurin babu kowa ba"
"Haka ne, to se an jima" Yakubu ya faWa daga nan yayi tafiyarsa.

Minti goma tsakani Faisal yazo tareda Momy da Hajiya Rabi harda Hajiya Balaraba, su ya bari a gurin ya tafi gida se sannan ya fahimci Fatiyyah bata gidan zuwan da yayi da safe yana sauri be tsaya nemanta ba, ya tambayi masu aikinta suke ce basu san inda ta tafi ba amma dai sunga ta haWa kaya a akwati ta tafi dashi. Ya wuce Wakin sa ya kwanta ransa duk a jagule, kenan yaji tayi? Tana da hujjar yin hakan ta ya ze Waura aure be gaya mata ba amma ai seta bari yazo suyi magana tunda shima ai ba sani yayi ba.

Se lokacin yaji za?uwar kiran amaryar daya san nada darun daban ne, dama sun rabu tana fushi jiya gashi kuma ta tarar da babban dalilin yin fushi shi kam yaga ta kansa ta ko ina bashida inda ze tsoma ransa yaji sanyi. Kiran wayarta yayi akasi aka ce a kashe take ya tabbatar kuma kashewa tayi da gayya saboda shi, lallai akwai rigima seya mayar da kiran layin Fatiyyah itama kamar na Fatiman a kashe. Yayi murmushi a fili yace
"Ni fa na shiga one chance Allah ya fitar dani lafiya kawai". Kwanciya yayi babu jimawa bacci yayi awon gaba dashi be kuma farka ba se shida saura na yamma, a gurguje yayi wanka yayi sallar la'asar yanajinsa kamar wanda akayiwa wankin ciki tsabar yunwa. Ya shirya tsaf cikin manyan kaya da suka matu?ar karSar sa. Ash Win shadda ce data ciza Winkin babbar riga da yar ciki, be saka babbar rigar ba ya ri?e ta a hannu ya kafa hula takalmi da agogo duk sababbi ya saka kamar yanda kayan suke sababbi. Shida kansa ya yaba da kyan da yayi, ya fesa turaruka na musamman ya kwashi wayoyinsa ya fita.

Seda ya tsaya a favourite eatery Win sa yaci abinci sannan yayi sallar magriba kafin ya kama hanyar gidansu Aafeeyah. Yana tafiya ya kira Sarah ya tambayeta ko hajiya ta tashi tace masa eh jikin ma da sau?i ai yace mata ya je unguwa idan ya dawo ze biya Asibitin sukayi sallama.
Seda yaje ?ofar gidan kuma ya tsaya ya kasa fita daga mota nauyi da kunya daya rasa na menene yaji suna neman rufeshi. Ya sake kiran layinta still dai a kashe, se kawai yayi shahada ya fita daga motar daidai nan Baffa ya fito daga gida da shirin zuwa masallaci Jay yaji kamar ya juya ya koma motar amma ba dama dole ya matsa gaban Baffan kai a ?asa ya gaishe shi shi kuwa fuska a sake ya amsa yana tambayar sa mutanen gida.

"Tana gidan Sauda ai, bakuyi waya kafin ka taho bane?" Baffa ya faWa ganin ya tsugunna yana sunne kai bece komai ba. Ya shafa ?eya yace
"Eh ta gaya mun na zata bata rigada ta tafi bane shine nazo na kaita", murmushi kawai Baffa yayi yasan ya faWa ne kamar yanda itama tayi masa ?aryar ta sanarwa Jafar Win zataje gidan Saudah sanda yace ba zata fita ba se ta sanarwa mijinta. ?ibar albarka taso yi musu a gida jiya bayan data dawo ta tarar da abinda ya faru haka ta tsallake yan uwa na kusa da makwafta da suka shiga yiwa Umma Allah sanya alkhairi ta zauna tsakiyar falo ta fasa kuka akan ita bata yarda ba ta yaya za'a Waura mata aure ba tareda an nemi amincewarta ba seda Umma FaWima tayi mata kaca kaca kafin ta shiga Waki ta ringa kuka babu wanda dai yabi ta kanta shine da sassafe ta shirya wai zata je gidan Saudah, Umma dama bata kulata ba tun jiyan ma data shiga tana iskancin shima kuma Baffan me biye mata wannan karon banza yayi da ita seda taje gurinsa akan Umma ta hanata fita yace ta kira Jafar ta tambayeshi idan ya amince shi ba ruwansa ai yanzu ba a ?asan ikon su take ba.

"To bari na shiga mu gaisa da Umma" Jafar Win ya faWa yana mi?ewa, Baffa ya juya ya koma cikin gida shi kuma ya koma mota, seda ya saka babbar rigarsa kafin ya shiga. Kamar ko yaushe dai kadaran kadahan suka gaisa da Umman, bega su Layla ba daya tambayeta tace Wazun Salim ya zo ya Wauke su ze kasu gidan Sarki yarinyarsa Humaira tana birthday.

Cike da nishaWi ya kama hanyar gidan Saudah bayan sunyi sallar isha'i tareda su Baffa, kunya duk ta dabaibayeshi da Baffa ya ringa nunawa mutane shine angon da aka Waura aure dashi Wazun dan ana ta tambaya ba'a ga ango ba. Me gadin gidan ya buWe masa ?ofa da sauri bayan dayaga fuskarsa ya bishi har inda yayi parking baki kamar ze yage yana masa banbaWanci ya sallame shi da kuWi masu kauri kamar yanda yake masa duk sanda yazo. Yana ?o?arin sake kiran layinta ko Allah yasa ta buWe Baban Hibban ya fito dan yaji an buWe get a saninsa kuma babu wani ba?o da zasuyi da ze shigo da mota har cikin gida. Ya saki fuska ganin Jafar, a mutunce suka gaisa yana tsokanarsa ango shidai se murmushi yakeyi suka shiga tare ya sauke shi a falonsa kafin ya wuce cikin gida ya gayawa Saudan zuwan Jafar.

Anty Sauda na Wakin ta tana masifa a waya, tun la'asar Aafeeyah tace mata an kirata daga makaranta wai an musu fixing test ?arfe biyar, dama ba wani kulata tayi ba tunda taje gidan dan haka bata hanata fita ba dai tunda makaranta zataje. Ita da taga har anyi magriba ma bata dawo ba ta Wauka gida ta wuce se da Umma ta kita babu daWewa ta gaya mata ga Jafar nan ze zo gidan sannan ta fara cigiyar inda Afeeyar ta tsaya, bata dai cewa Umman bata gidan ba ta kira wayarta a kashe dabarar kiran wata ?awarta Fa'iza da sukr masters tare yazo mata tana kira kuwa Fa'izan ta shaida mata suna tare daga makaranta gidanta suka wuce shine fa ta bata wayar take ta surfa mata bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ta kashe wayarta tana huci.

Jiran kusan minti sha biyar har Jafar ya ?osa ransa ya fara Saci, ya kalli Hibban da ?anin sa Musa da suke zaune dashi tunda suka kai masa ruwa yace
"Wai me takeyi da har yanzu bata gama ba?" Hibban yayi shiru se Musa yace
"Ai bata nan, amma Momy ta kirata a waya tana hanya ta kusa dawowa". Yayi shiru yana kallonsa fuskarsa ta canza zuwa Sacin rai, daga Waura musu aure jiya shine har zata fara yawonta a gari ba tareda neman izininsa ba? Lallai kuwa ze saita mata zama dan yana daga abinda yake haWashi da Fatiyyah idan kuma wannan salon zata Wauka itama ba zata ji daWin sa ba. Tashi yayi ya fita can bakin get ya tsaya me gadi kamar ze kwanta masa yana tambayar me yake da bu?ata yace babu komai se ya fitar masa da kujera ganin ya jingina da katanga ya tsaya. Be fi minti goma a wajen ba wata mota ta shigo layin kai tsaye kuma ta durfafo gidan.

AFEEYAH
Ta kasa yarda da abinda ta tarar bayan ya sauketa, gidansu cike da mata tana shiga sukayo kanya caaa masu guWa nayi masu jera mata kirarin amarya nayi. Da fari Wauka tayi tsokana ce amma kuma fuskokin da ta gani da yawansu ta san hidima ce kawai take kawo su gidansu kuma dai a saninta babu labarin auran kowa kafin ta tafi seda ta dangana da falon Umma inda Umma Halima ?anwar Baffa ta tareta bayan data rangaWa mata guWa a kunne ta cike da kiranta Amaryar Jafar. Abinda ya fara faWo mata Badar, daren jiya suna zaune aka kirata a waya bata gaya mata ko waye ba tunda ta gama kuma ta kafa mata tsokanar ta Jafar har tana cewa ya zataji ace tana komawa gida taga an Waura musu aure? Dama kuma tunda taje gidan zancen kenan take mata na babu wanda ta cancanta dashi a yanzu sama da Jafar Win ashe abinda aka ?ulla mata kenan shi yasa yaci kwalliya kamar ango yaje Wakko har hotunan da Badar ta musu kenan duk dalili kenan shikenan fa ta fasa musu kukan da takamaimai idan an ritsata da tambayar na menene bata da abinda zata faWa.

Tasan dai Ahmad ya faWo mata a rai amma kuma wannan be isa dalilin irin kukan da ringayi har cikin dare ba seda kanta ya Waure da ciwo kafin ta ha?ura tayi shiru amma bata iya ta runtsa ba. Duk idan ta tuna wai a Waura mata aure da Jafar wani abu takeji yana mata yawo akai,ta tuna yanda ya tsaya a gabanta yana gaya mata baya sonta ta gayawa Baffa a fasa maganar aurensu yanzu taka maimai bata sani ba, Baffa be karSi kokenta bane ko kuwa Alhajin su ne ya tilasta faruwar auren? Menene matsayin ala?arsu tunda da bakinsa ya furta baya sonta bata gabansa bashi da wani sauran mafarki tareda ita? Duk idan ta tuna wannan shi yake sake dawo mata da sababbin hawaye. Yanzu ze Wauka da gaske yanda ya faWa tana ?ulafucin sa ?ila ma yace Baffa ne ya ro?a aka Waura musu auren shi kenan ya samu dalilin gaya mata magana son ransa. Abinda ya ?ara ta'azzara damuwarta yanda har garin Allah ya waye be kirata ba tabbacin abinda ya faWa mata gaskiya ne baya sonta tunda da yana sonta dai ace an Waura masa aure da ita ai ya kira idan ma be sani ba su jajantawa juna dukda ma dai ta kashe wayar ta idan ya damu ya kamata ace yaje gidan ya ganta amma beyi haka ba.

Yanda Umma harma da Baffa suka fita a sabgarta yasa ta shirya zuwa gidan Dauda dukda itan ma tasan bagarar da ita zatayi amma ba kamar Umma ba idan ta gama fushi dole zata sakko ta kulata hakan yasa ta shirya ta tafi daga can kuma ta shiga makaranta yin test da suka tashi Fa'iza tace su biya gidanta akwai kayan da tayi order na yara sun iso ko zata dubawa su Amal abinda ya kaita gidan kenan harta shantake bata san lokaci yaja ba seda aka fara kiraye kirayen sallah se kuma ga kiran Anty Saudan tana masifa dan ta kashe wayarta aka samu arashi ta fita bakin titi tana jiran abin hawa sega Dr Ashir yazo wucewa dan unguwar su Waya da Fa'izar yace ta shiga ya kaita gida ganin ta daWe a tsaye yasa kawai ta shiga motar. A hanya ya fara yi mata tunin maganar su dan da gaske yake sonta tuntuni yake nacin ta bashi dama koda ba maganar aure ba yaje ya gaida Babanta amma ta?i, tana jinsa yana ta nanata mata yanda yake jinta a ransa da magiyar ta amince ta bashi dama ita dai bata ce komai ba har suka isa gidan dan jikinta yayi sanyi duk a takure takejinta data tuna wai fa yanzu matar aure ce ita, suna dab da shan kwanar layin a ranta ta raya ace kawai au tarar da Jafar a ?ofar gidan Sauda? Tayi saurin girgiza kai tana kore tunanin hakan daga ranta bata ma san sun isa ba seda taji motar ta tsaya, ta Waga kai ta kalli ?ofar gidan karaf suka haWa ido da Jay dake zaune ya Wora ?afa Waya kan Waya yana girgizawa.

Gabanta ya faWi, irin kallon da yake mata dukda fuskarsa bata nuna wata damuwa ko wani abu ba amma ta hango hakan a cikin idonsa. Dr Ashir kuwa gyara tsayuwar motar yayi da alama hira yake so suyi kafin ta wuce ciki, ya wani karkace yana kallonta ganin hankalin na waje yasa yabi inda take kallo da ido. Fuskar sa ta faWaWa da fara'a a fili yace
"AAJAAY ne" kafin tayi magana har ya buWe motar ya fita domin shi Win die hard fan Win Jay ne. Tana kallo ya nufeshi kamar wanda yaga wani sahabi ta buWe motar kai a ?asa itama ta fita.

JAY
Ba ?aramar dauriya yayi gurin hana Sacin ransa bayyana akan fuskarsa ba, tsayin kusan mintuna talatin yana jiranta kawai ta Sullo from nowhere tareda wani ?ato, da aurensa ta shiga gaban motar wani, se da yayi da gaske kafin ya iya karSar hannun da Dr Ashir ya bashi amma ya kaucewa rungumarsa da yaso yayi. Baya ko sauraren abinda yake cewa ya bita da kallo ganin tana shirin shigewa cikin gidan ba tareda ta kalli inda yake ba. A ta?aice ya kira sunanta, tayi tsam a inda take bata juya ba ba kuma taci gaba da tafiya ba saboda yanda taji muryarsa ta tabbatar ba ?aramin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login