Showing 264001 words to 267000 words out of 467220 words

Chapter 89 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12367

shikenan tunda wahala bata ?are miki ba kuma hakan kika zaSama kanki ba damuwa"

"Toh ni ya zanyi? Wlh na tsani Jafar kamar yanda na tsani mutuwata a yanzu amma kawai ji jakeyi idan na auri Ahmad ban masa Adalci ba. Dan Allah ki bani shawara ya zanyi?" Ta sake faWa cikin tsananin kuka. Da Anty sauda ta fahimci dagaske she is confused seta sassauto daga fushin da rashin wayon Afeeyahr ya tunzurata ta shiga mata maganganu da haska mata hanya har seda ta fahimtar da ita kuma ta dawo kan saiti kafin ta barta.
Ta sake kiran Badar sukayi magana itama dai irin kalaman Anty saudan tayi mata su biyun suka samar mata da nutsuwa ta zahiri amma a baWininta a hargitse take, ta kasa harhaWa abinda ya faru. Tunani takeyi ta yanda zata rayu da Ahmad alhalin zuciyarta tana cike da soyayyar Wan uwansa Jafar, kwarai kuwa daidai kukaji ta faWa. A zahiri ta tsani Jafar amma a baWini cikin zuciyarta kamar ana ingiza wuta ne ana watsa mata fetur, ko gezau bataji dan gane da tarin soyayyar da takeyi masa ba sema ?aruwa da tayi.

A gidan Alhaji Audu kuwa tun dare Hajiya Binta take zazzaga bala'i a tsakar gida wai anja mata ?a an kaiwa mayu, babu wanda ya tankata daga Momyn da takeyi da ita har Hajiya Rabi kowacce ta sakayo ?ofar part Winta sun barta tana ta haushi ita kaWai a tsakar gida ko sanyi bataji seda ta gaji ta tafi ta kwanta asubar fari kuwa ta sake dasawa sau?in da aka samu Alhaji Audu baya nan yana UK sunje wani taro shida Alhaji Zakariyya da Yakubu Bechi se ana saura kwana uku a fara biki ma sannan zasu dawo.

JAFAR
Tun cikin dare yake sa?a da warwara, maganar tayi masa nauyi a zuciya, yana da bu?atar wanda ze tattauna dashi amma ba abu bane kuma da ze iya furtawa wani saboda gudun abinda ze iya zuwa ya dawo maganar ta fita taje inda be kamata aji ta ba. Ba kalar lissafin da beyi ba na possibilities da zasu iya mallaka masa Afeeyah. Abu guda dai ya Ahmad shine katangar da take tsaye tsakaninsu, muddin yana raye baze mallaketa ba koda kuwa shida kansa ya yafe masa ita ya bar masa ita baze taSa karSa ba saboda ya sani itace Mace mafi soyuwa a zuciyar Yah Ahmad.

Tunda yayi sallar Asuba yake kwance har goma na safe shi be koma bacci ba kuma be iya tashi ya fita ko ina ba, Allah ya taimakeshi Hajiya tunda ta shiga da Asuba ta dubashi bata sake komawa ba, Fatiyyah ke neman damun rayuwarsa da kiran waya toh ya kashe wayar ya huta. Tun jiya da suka dawo be sake ganin Yah Ahmad ba bema san a inda ya kwana ba duk se yaji babu daWi kenan yayi fushi me tsanani dashi to amma bashi da wani zaSi daya wuce abinda yayi jiyan. Akwai so da sha?uwa me tsanani tsakaninsa da Afeeyah, bazeyi kaffara ba idan ya rantse akan itama tana jin makamancin abinda yakeji akanta yanzu domin So ba ?arya ba ya gasgata Son da take masa a baya, koda ace tayi abinda tayi ne saboda ta gwara kansu kodan wata manufa toh tabbas itama ta faWa cikin ramin muguntar data gina musu.

Gadar da sabuwar ?iyayya a tsakaninsu a yanzu ita kaWai ce mafita. Ze so ace duk sanda ta ganshi bayan ta auri yayansa ya zama babu abinda zata tuna se ba?a?en maganganu da Alwashin daya ci akanta ta yanda zata tsaneshi ba kuma zata taSa tuno wani abu na jin daWi daya faru a ruyuwarsu ta baya ba wannan ita kaWai ce mafitar da yake gani.

Abunda yayi masa saura yanzu be wuce yaje ya wanke kansa a gurin mahaifinta ba. Kamar yanda yaje ya sameshi sukayi magana yace ya bashi lokaci ya turo iyayensa baze so ya ringa masa kallon mayaudari wanda yaje bata lokaci gurin yarsa ba. Shi kaWai yake ganin ze iya fasawa wannan sirrin dukda ma wuyaci ne yarsu bata rigada ta faWa musu ba amma ya kamata yayi clearing air kar taje ta bayar da bayanin da ba shikenan ba taSatashi ta Sata Ahmad a gurinsu su ringa musu wani kallo na daban.

Ko karyawa beyi ba daga sallar Azahar ya fice daga gidan ya tafi gidansu Afeeyah, seda yaci rabin hanya kafin yayi tunanin rana ce, babu tabbacin ya sami Baffanta a gida yanzu toh amma a ina ze same shi toh? Ya nemi gefen hanya ya faka mota, ya ciro wayarsa ya kunnata sa?onnin Fatiyyah wasu na ture wasu suka fara shigowa. Be bi takansu ha ya shiga WhatsApp, tun waccen ranar yayi blocking Afeeyah yayi Achieving chat Win. Ya tuna sanda Baba Al?ali yace masa ya karSo masa numbs mahaifinta ta tura masa be kai ga bashi ba me afkuwa ta afku number itace sa?o na ?arshe data aiko masa se I LOVE YOU data rubuta a ?asa da Emoji heart me bugawa daga nan yayi blocking nata.

Number ya Wauka, ya kalli chat Winsu yana scrolling sama wani abu na masa yawo a zuciya take ya danna delete ya goge shi gaba Waya ya wuce inda ya adana number Baffan ya kira. A nutse suka gaisa yacewa Baffan yana son ganinsa ne, dukda Baffan be gane wanene ba amma ya kwatanta masa Garejin da yake yace yana can lokacin. Da tambaya ya kai kansa, Baffa na ganinsa ya ganeshi, fuska a sake ya tarbeshi, ya shimfiWa masa abin sallah kan babbar tabarmar da suke jam'in sallah akai sannan ya aika yaro ya siyo masa ruwa da Lemo dukda yace a ?oshe yake.

Kasa dena kallonsa Baffa yayi sanda ya kai ayar bayanin da yake yi masa se jinjina kai yake yana yiwa Allah tasbihi.
"Tabbas tun ganina dakai na farko nake maka kallon sani amma na gaza tantance a ina na san fuskarka, Allah kenan me tsara komai yanda yaso, Allah yasa hakan ya zamto Alkhairi a rayuwarmu baki Waya" Baffa ya faWa bayan daya gama jimami.

"Ina neman Alfama Baffa maganar nan ta zama iyakar nida kai, na zaSi na sanar da kai ne saboda karka ringa tunoni ko ka ringa bada misali dani a matsayin mara cika al?awari, Yah Ahmad yana son Afeeyah so me tsanani bana son abinda ze janyo damuwa cikin soyayyar da yakeyi mata, itama na ja mata kunne akan karta gaya masa ina sake neman Alfarma akan ka ri?e min wannan sirrin Baffa" Jay ya ro?eshi.

Bayan tafiyar Jay Baffa kasa cigaba da aiki yayi ya tattara ya tafi gida, baze iya Soyewa Ummansu Afeeyah ba dan ya gayawa Jay cewar ze sanar mata,
"Wlh nima Malam tunda na ganshi nace wannan fuskar kamar na santa ashe jinin Ahmad ne ikon Allah"

"Amma ni Ru?ayya gaskiya zuciyata ta kasa aminta da yin shiru akan maganar nan, ina tsoron zamani da halayyar yayan zamani. Gaskiya ni zan kira waliyyin Ahmad, tunda Yayan mahaifinsu kenan duka su biyun ko na faWa masa maganar nan saboda ba fata ba wani abu ya biyo baya kar azo a Worawa yarmu laifi ko a zargeta da wani abu da ba shikenan ba. Wannan rayuwa ta kafafen sada zumunta, idan ya zamana wani daya san tsakaninsu ya maido da abinda ya faru a baya bayan data rigada ta auri ?an uwansa bana tsammanin da akwai wanda zeyi mata uzuri ko ayi hasashen a baya abin ya faru dan haka maganin kar ayi kar a fara zanyiwa tufkar hanci in sanar da magabatansu koda hakan yana nufin fasuwar auran gaba Waya yafi akan ace ayi wani abu a Wu?un?une" Malam Hafizu ya sake faWa.

Umma tace amma Malam se nake ganin..."
"Bazan karSi uzurinki ba Ru?ayya, ki tuna yanda Mamana bataji kunyar idona ko naki ba a nan gurin ta zaSi Jafaru tace shi take so ba Ahmad ba. Ki tuna irin ?uncin da take ciki keda kanki kike faWar dalilin rabuwarsu da Jafarun ne ya saka ta shiga wannan halin. Ko kukan da take tayi daga shekaran jiya zuwa jiya na tabbatar ta gano cewar gidansu ?ayane abinda ya sakata a ruWani kenan, ina kyautatawa Yata zato amma kuma shaWan baya raina ?ofa, sanar da magabatansu maganar nan shine hukuncin da nake ganin ya dace idan yaso su acan su duba suga abinda ya kamata suyi komai ya wakana kuma daga baya da sanin Allah" Malam Hafizu ya sake katseta yana kuma latsa wayarsa ya nemo number Baba Al?ali ya watsa masa kira

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 3*

Seda yayi masa kira biyu a jere be amsa ba ya ajiye wayar yana ce mata
"Inaga baya kusa da wayar, idan ya gani ze kirani" be gama rufe bakinsa ba wayar tasa ta shiga ringing ya amsa yana sake ce mata

"Kin gani ma harya biyo".

A mutunce suka gaisa, bayan tambaue tambayen iyali da sabgogin rayuwa da kuma shirye shiryen biki Malam Hafizu yace
"Kayi ha?uri na kiraka a wannan lokacin" daga can gefen Al?ali Yakubu yace
"Haba dai babu komai, ban lura ba wani me ?iriniyar Aboki nane nan da suka taho biki tun yau saboda zumuWi shine ya latsa mun wayar ya sakata a silent, seda na zan duba lokaci naga kiran naka"

"Masha Allah, Allah ya rayasu yayi musu Albarka" cewar Malam Hafizu kafin nan ya shiga kora masa bayanin ainihin dalilin daya saka ya kirashi. Al?ali Yakubu yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi yana sauraronsa harya kai aya, sun tattauna sosai, Al?ali Yakubu yace ya saurareshi zuwa dare ze sake kiransa domin yana da bu?atar yayi magana da Jafar, ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????harda Ahmad Win idan ta kama daga nan sukayi sallama. Umma tayi zukuWi fuska kamar zatayi kuka tace

"Anya kuwa Malam maganar auran nan zata yuwu?"
"Duk abinda kika ga ya faru da sanin Allah Ru?ayyah, Alkhairi muke ro?o a koda yaushe dan haka muna ?addara duk abinda ya same mu cewar shine mafi Alkhairi a gare mu" Baffa ya bata amsa daga nan ya mata sallama ya koma gareji.

Al?ali Yakubu kuwa suna gama magana da Baffa ya shiga kiran Ahmad, har wayar ta fara ringing se kuma yayi saurin datseta ya kashe ya canza akalar kiran zuwa layin Jafar cikin Sa'a ringing biyu ya amsa. A ta?aice yace masa idan babu abinda yakeyi ya zo gida ya sameshi ya amsa masa da toh dan ba abinda yakeyi Win tunda ya bar gurin Malam Hafizu yake gararamba a kan titi ga yunwa ta fara addabarsa amma baze iya tsayawa ko ina yaci abinci da rana haka fatsar fatsar ba abinda yake damunsa ma ya ishe shi base ya ?ara da hayaniyar mutane ba. Gidan Al?alin ya tafi, ya tarar da Amina me bin Dada da yaranta har sunzo Biki wai da yake a Lagos take aure ita kuma ana cikin hutun makaranta ne daman, bayan musayar gaisuwa Hajiya Balaraba tayi masa tayin abinci ya amsa se tasa aka bishi dashi falon Al?alin danshi ya rigada yaci nasa.

Seda yaci ya ?oshi yayi hamdala kafin Al?ali ya zayyano masa dalilin kiran da yayi masa, kansa a ?asa ya gagara Wagowa balle yace masa wani abu, me yasa Baffan Afeeyah zeyi haka bayan yace masa karya gayawa kowa?

"Kayi shiru Jafar, dagaske Matar da ?an uwanka yake Shirin aure itace wadda kaima kaso ka aura?" Al?ali ya jefa masa tambayar. Seda yayi dagaske kafin ya iya Waga kai amma be bari sun haWa ido ba yace masa

"Hakane Baba, bansan ita bace Fatiman Yah Ahmad, a Zaria muka haWu sau Waya kuma na taSa zuwa gidansu se ranar dana raka Yah Ahmad na gane itace kuma a take a lokacin na ha?ura da ita na kuma gogeta daga zuciyata saboda ya rigani shi ya fara sonta kuma ko ba haka ba bazan taSa jayayya da Yah Ahmad akan komai ba balle har mu haWa neman matar aure kawai na sanarwa mahaifinta ne saboda karya ringa mun kallon mayaudari badan wani abu ba".

"Al?ali yayi shiru yana nazartarsa kafin yayi murmushi yace
"Shi Ahmad yasan da wannan maganar?"
"Be sani ba kuma ina ro?on ka Baba dan girman Allah karka sanar da kowa kayi mun wannan alfarmar maganar nan ta zama sirri a tsakanina dakai daga nan gurin kar a kuma tayar da ita, ba Yah Ahmad ba babu wani daya kamata ya sake sanin wannan maganar".

***********
Babu jimawa sosai da zuwan Jafar Ahmad ma ya shiga gidan. Jiya a falon Mamy ya kwana jiya saboda yanda ransa yake a Sace da abinda Jafar yayiwa Fatima ya shiga yana yiwa Momy mita Hajiya ta fara tijara bayason ta sake ?ara masa Sacin rai shiyasa yayi kwanciyarsa a can kawai da safe kuma da wuri ya fita saboda an kawo musu kaya suna restocking shago so yakeyi komai ya daidaita kafin ya fara hutun angwanci shiyasa ko wanka beyi ba ya fita se bayana Azahar ya dawo kuma be ga motar Jafar ba alamar ya fita kenan. Be huce da abinda ya farun ba shiyasa yanayin wanka yaci abinci ya shirya zeje gidan Baba Al?ali ya kai masa ?arar Jafar, IV da aka kawo ya tsayar dashi ya ware nasa ya cire na Jay sannan ya kwashi na Fatima ya kai mata gidan Anty Sauda da kuWaWe tunda ta?i faWa masa nawa take da bu?ata ya kintata ya bata abinda yake ganin ko zata nemi ?ari ba da yawa ba. Ya fito yaga missed call Win Baba Al?ali kafin daman can ya nufa.

Harara ya makawa Jafar sanda ya shiga kamar wasu yara shi kuma ya fashe da dariyar da be shirya ba, cikin fushi Ahmad ya gaida Baban kafin ya fara rattabo masa abinda Jafar yakeyiwa Matar da ze aura har da wanda ya mata jiya haWuwarsu ta farko, Baba Al?ali ya ringa masa faWa yana cewa

"Koda wasa karna sake ji, idan da kirki matar yayanka ai itama yayarka ce. Yaya ina yabonka ashe kaima kana kan turba irin ta uwarku? To ahir Winka, yanda kace ka barta har tashin duniya to kar koda wasa ka sake shiga sabgarta balle wani abu na Satanci ya biyo ba. Idan ba zakuyi mutunchi da zumunchi ba to babu ruwanka da ita ka kama kanka ka kama mutunchinka kuma ka bashi ha?uri kayi masa Al?awarin haka ba zata sake faruwa ba" yayi masa biji biji shikenan magana ta wuce da zasu tafi ma a gidan suka bar motar Jay suka tafi a ta Ahmad yana tambayarsa beji yana maganar ba?in da zasu zo masa biki ba abokanan sana'arsa.

"Nifa ban gayyaci kowa ba" ya bashi amsa yana kwantar da kai a jikin kujera dan Ahmad ne yake tu?i, Ahmad Win ya harareshi yace
"Kai ka isa ma, Adam ya gaya mun already ya shirya komai zasuyi chattering Plane akwai kusan 40+ Abokanan ka that are coming from uk, sannan a nan ma daga Sangarena na gama arranging classmates Winmu na FGC da zasu zo suma, Friends Winka na nan ne bansan ya zakayi dasu ba yanzu zamuje mu nemi reservations na rooms ya kamat mu gama komai fa kafin a shiga next week Ammar da Yasir suna Bristol suna jiranmu yanzu can zamuje ga IV kuma nan idan da waWanda zaka bama hardcopy"

"Duk yanda kaga ya kamata Yah Ahmad ayi, i told you I'm not feeling my self wlh, bari na fara daidaita tukunna koma menene yayi saura se nayi" Jay ya faWa. Ahmad ya taSe baki yaci gaba da tu?insa can kuma ya sake ce masa

"Fatima bata so muyi pre-wedding pictures"
"Ni kuma Fatiyyah wanted but i said no. Ya kamata ma naje gurinta fushi takeyi ta kasa gane halin da nake ciki ta bani iska jiya har Hajiya ta kira wai na dawo bata sani ba" Jay ya bashi amsa Ahmad yayi murmushi yace
"Ya kamata dai, ka duba yanzun ko zaka samu flight kaje ka rarrasheta ko gobene seka dawo idan ba haka ba zaka gane kurenka yaro idan kaima idan ka shiga hannunta".

*****************

Kwanaki nata tafiya lokacin biki kuma yana ?aratowa domin ana lissafin kwanaki bakwai kacal suka rage ranar Waura aure, a Sangaren Amaryar Jay ma a wannan rana zasu fara gaba tarda Waya daga cikin jerin gwanon events da suka shirya zasuyi, shagali sunfi kala goma dan wata rana ma events biyu zasuyi sedai abinda ya rage armashin sabgar Ango daya ce baze samu halartar ko mai daga ciki ba bayan Waurin aure da Dinner da yan gidansu suka shirya. Shida yaje da niyyar lallashinta se gashi ya sake tunzurata suka rabu dutse a hannun riga har tana i?irarin seta fasa auran tunda ta lura daman ba sonta yakeyi ba so kawai yake ya wula?antata ya nunawa duniya be damu da ita ba ko ya akayi kuma bayan ya dawo Kano har yana murna da jiran jin iyayenta sun aiko sunce sun fasa bashi yarsu se gata ta kirashi tana kuka ta bashi ha?uri se kuma yaji tausayinta daya kwatanta abinda yake ji a zuciyarsa game da wata kwatankwacin haka itama takeji dole ya rarrashi kansa ya kuma tattara hankalinsa guri guda ya fara shirin biki shima tareda tattalin Amaryarsa yana nuna mata zumuWinsa dukda bekai zuciya ba.

A Sangaren Amarya Fatima kuwa ta gagara Waukar dangana duk yanda taso data ya?i tunanin Jafar ko zaluncin da take tunanin yayi mata abin yaci tura. Zuciyarta ciwo takeyi mata, kullum dare se tayi kuka kukan da ita da kanta bata san na menene ba amma abinda tafi ?arfafawa kanta guiwa akai shine kukan tsana da jin haushin Jafar ne. Tun Anty Sauda na ta tata tana lallaminta harta gaji ta watsar da ita badai ta mata wasa da sabgar gyaran ciki da waje idan ta bata abu ta tsaya mata iskanci zageta takeyi tas ta kuma kasa ta tsare se tayi tace ita ta sani itace wahalalliya idan taga dama karta saki zuciyarta sudai babu abinda ze hana suyu rawa suyi juyi ranar biki.

Seda biki ya rage saura kwana biyar kafin sukaje yi mata jere dukda an rigada an kai kayan gado wanda za'a Waura an Waura

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login