Showing 153001 words to 156000 words out of 467220 words

Chapter 52 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12233

ido ta juya bayan data masa wani kallo me kama da harara wanda yaji dirarsa har tsakiyar zuciyar sa.

"I will call u back, Jafar" ya faWa be jira amsarsa ba ya kashe wayar ya jefata a Aljihu daidai nan kuma Majid ya iso gurin yana bawa wata Mace me ciki ha?uri akan daWewarsa, Kwalin Gadon Jarirai ne a hannunsa da alama a store ya Wakko, daga nan yaci gaba da haWa mata kayayyaki tana nuna wanda take so yana Waukowa.
"Kalli wannan Sunyi kyau?" Matar ta nunawa Budurwar dake tsaye ba zaka taSa cewa tafiyarsu Waya ba saboda yanda ta kame gefe tana ta muzurai kamar wadda akayiwa wani abun,
"Sunyi kyau Anty, dan Allah ki barsu haka mu tafi ma sake dawowa wani lokacin duk na gaji" ta bata amsa.

"Aiko babu inda zanje sena gama siyan komao dan ba lallai na sake samundamar fitowa ba shiyasa ma nace kai tsaye mu taho nan dan nasan komai da nake so zamu samu in kuma ban ?arasa ba waye ze zo ya siya mun?" Matar ta faWa tana cigaba da duba kayayyakinta, Budurwar ta narke fuska kamar zatayi kuka tace

"Wlh zanzo na siya Miki amma ki barsu haka yanzu mu tafi dan Allah"
"Ai se kiyi, in kinga na bar nan to na gama abinda ya kawoni ne ahto" Me cikin ta sake faWa tana yin gaba abinta da alama wasu kayan ma zata tafi nema, ta kusada Ahmad ta gifta, fuskarta a sake ganin yana ta kallonta yasa tace masa
"Sannu" se ya shiga sosa kai, besan sanda ta iso inda yake ba kuma bawai da niyya yake kallonta ba, wani abu yake so ya tantance, idan ba idanunsa ne suke gizo ba gani yayi kamar mutum Waya da kaloli biyu a gabansa. Ita da budurwar kamar an tsaga kara, hatta da muryoyinsu, banbancinsu Budurwar fara ce tas ita kuma tana da duhu dan bama za'a kirata wankan TarwaWa ba, Ba?ace amma kyakykyawa ce tagaske Tabarakalla dan hartafi farar kyau sanda tazo kusa dashi sosai kuma ya fahimci ta girmewa waccan sosai, ba ita ba shikansa da alama zata iya girmarsa dukda da tana da kyan jiki.

"Kamar ku Waya" ya faWa mata kamar wani yaro yana nuna ?anwar tata data zabga tsaki har inda suke tsaye sun jiyota. Matar ta sake faWaWa murmushinta tace
"Haka ake faWa, amma na fita kyau ai" ta matsa gaban kayan da yake ta juyawa duk Unisex ne, suna waya da Jay yana jagwalgwala kayan. Nazira ce ta haihu yake so yaje yaga baby shine yake so ya zaSi kayan da ze kai mata ya kira Aslamiyya tace masa Anything pink is for girls blue na maza shine fa duk ya rikice ya rasa me ze Wauka kusan minti sha biyar yana abu Waya.
Ganin ta ciro wasu tana dubawa ya saka yace mata

"Yawwa dan Allah Anty wanne ne na mata wanne na Maza?". Tayi murmushi har ha?oranta suka fito kafin tace
"Wannan duk unisex ne, ana iya sakawa kowa kawai dai kasan Pink da blue color an fi sakawa Mace ko Namiji amma bayan su kana iya Waukan ko wacce kala zeyi, haihuwa akayi maka?"

Kai ya girgiza mata yana murmushi yace
"Aa, ai banida Mata. Yayata ce ta haihu baby girl nake so naje na ganta shine zan kai mata gift, ko zaki tayani zaSa toh idan ban takuraki ba?"

"Allah ya raya, ya kawo mata ta gari babu damuwa guda nawa kake so kuma kamar na wane kuWi?"

"Haba Anty Sauda jiranki fa nakeyi shine zaki shiga wata sabgar kuma da bakizo ba waye ze zaSar masa kayan? Duk ma'aikatan gurin nan ke kaWai ya gani da zece ki tayashi Waukar kaya ko kuwai neman gurin zama?" ?anwar tata ta faWa cikin bacin rai. A fili Ahmad yace
"Ikon Allah" yana kallonta yayarta me suna Sauda ta lafta mata harara kafin tace
"Wai ni dole na miki da ki biyoni ne ko yaya? Idan ba zaki iya jira nagama abinda nake ba FATIMA ga hanya yi tafiyarki mana"

Majid da se lokacin ya lura da Ahmad ne a gurin ya saki abinda yakeyi da sauri ya isa cikin ladabi yana cewa
"Ranka ya daWe wani abun kake bu?ata?"
"No, cigaba da aikinka kawai babu matsala ga Anty zata tayani zaSa"
ya sallameshi.

Bata tafin ba se ?ara lafewa bango da tafi tana cika tana batsewa kamar fulawar dataji yeast. Anty Sauda kuwa ta cigaba da Waga kaya tana zaSar nata dana Ahmad da yace kala biyar yake so.
"Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" yayi mata godiya, Majid ya karSi kayan yayi masa gaba dasu shi kuma ya kalli Fatima dake dabda fashewa yace
"Ki zauna kar ?afarki ta gaji bari a kawo miki ruwa me sanyi kisha".

Sanin idan ta buWe baki ba zata bashi amsa me daWi ba tasa tayi ?wafa kawai ta sake tsumewa. Seda Antynta ta gama jan ranta iyaka kafin aka tattara mata kayan da ta siya aka kai gurin biyan kuWi lokacin tuni Ahmad ya biya nasa an kai masa mota yana ?arasa wani abu kafin ya fita, ko tsinke ya Wauka a gurin seya saka kuWin balle ma wani yayi tunanin zuwa yace ze Wibi bati kamar yanda Salim yaso ya fara masa sanda yake zuwa seya kwaso Abokanansa su Webi abu ayita rigima dasu a gun biyan kuWi yace shiya basu ba zasu biya ba securities su hanasu fita, seda Ahmad Win yayi masa kaca kaca a gurin sannan ya samu salama dalilin kuma daya saka Salim Win ya bar aiki a gun wanda daman Momy tayi masa dole.

Suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa, Fatima nata zabga Mita Anty Sauda kuwa ta mata shiru kamar bada ita take ba, iyakar zafin ranar dake ratsasu ya isa sunfi Awa guda cikin sanyin RaSa kuma sanda suka shiga rana bata take kamar haka ba seda suka fito suka ganta ?wal da alamun hadari ze iya haWuwa zuwa jimawa. Wani abin takaici kamar an hana masu Adaidaitan hanyarsu zuwa duk wanda suka tare da sunce MARMARA zece ba nan yayi ba, wanda zasuje kuma da mutum a ciki su kuma ga kaya drop ma ya?i samuwa kamar wanda akawa baki.

Suna nan tsaye kamar Fatima zata fashe ga rana ga babban abinda ya dameta ita, yanayin da take ji a jikinta ta tabbatar period ze iya zuwar mata a kowanne lokaci dukda gobe take saka ran zuwansa shiyasa ma bata fito a shirye ba amma suna shiga gurin nan taji jikinta ya fara sauyawa irin yanayin da takeji idan jinin ze zuba dan bata wani laulayi ko ciwon Mara sedai taji jikinta na mata wani Yamm kamar tana jin sanyi dataji haka tasan any moment ze iya zubowa to wannan yanayin takeji shiyasa duk ta takura tun shigarsu gurin Miskilanci kuma ya hana tayiwa Anty Saudan bayani se ba?in rai takeyi tana tsaki.

Wata dalleliyar mota Ford fara tas ta giftasu se gata ta dawo da baya a hankali ta tsaya a gabansu, Ahmad ya sauke glass, fuskarsa me Wauke da murmushin yan Aljanna ta bayyana ya kalli Fatima suka haWa ido yanda tayi seda ya kusa bushewa da dariya amma ya kanne ya maida dubansa ga Anty Sauda.

"Bari na rage muku hanya to nima cikin garin na nufa" Ya faWa bayan da Anty Sauda ta masa bayanin sun rasa abin hawan hanyarsu ne, Fatima ta zabura tace
"Yi tafiyarka zamu samu" Anty Sauda ta galla mata harara ?asa ?asa tace
"Duk saboda ke yake wannan abun kiyi dagaske harya fusata ya tafi"

"Allah ya kiyaye ni beyi mun ba" abinda Fatiman ta faWa ya isa kuma har kunnen Ahmad dake ?o?arin saka musu kaya a booth securities biyu da suka hangoshi suka taho da sauri suna tayashi. Murmushi yayi da jin furucin Fatiman, sam kuma ransa be Saci ba illa ma burgeshi data ?arayi domin ta nuna ita Win Macece me ra'ayi wani abu da ta gani tattare dashi be ruWeta ba dukda yasan basu da masaniyar shine mamallakin gurin da sukayi siyayyar.

Akan shiga motar ma seda akayi daga da ita Anty Sauda ta balbaleta da masifa Ahmad ya shiga tsakani yana bata ha?uri tareda lallashin Fatiman kan ta shiga su tafi, shikam Ajinta burgeshi yakeyi saSanin sauran Matan da suke zuwa gurin kaga Mace har Mace amma babu Aji, wasu takanas suke zuwa ganin CEO saboda an san kusan koyaushe yana zaune a office Winsa indai yana Kano, wasu ma zuwa suke da ?aryar kaya zasu kawo, ba kuma zasuyi magana da Sales Manager ba seda CEO kai tsaye da Ma'aikatan suka gane me yake kawo su se suka fara hanasu suce basa karban kaya a hakan wasu zasu zauna a waje jiransa muddin anga motarsa a Parking lot kiran waya kuwa seda ya maida layinsa private idan beyi saving Number ba kira baze shiga ba sannan ya samu Sa'ida, kuskurensa saka Main Line Winsa akan Banner su.

Suna tafe suna yar hira da Anty Sauda har suka isa bakin titi inda ze ajiyesu dan Mota bata shiga har cikin layinsu, Anty Sauda ta fita ta kira yara suka fara kwashe mata kayanta, seda suka gama tas ta kalli Ahmad tace
"Mungode sosai, Allah ya saka da Alkhairi"
"Amin Anty, Allah kuma ya raba lafiya, gashi banga gidan ba balle nazo cin naman suna"

"Seka karbi number waccen, idan na haihu seta sanar maka ko?" Cewar Anty Saudan. Ya juya ya kalli Fatima yana cewa
"Kodai ki bani da kanki, kalli fa yanda ta haWa fuska Allah sa ba tunanin yanda zata sha?eni takeyi ba , daman idan kin haihu karki bari ta fara Waukan Babyn kar yayo gadon rashin fara'arta
".
Fatiman na zaune tana kuma jinsu kamar an dasata a gaban motar, tasan me afkuwa ta afku shiyasa ta kasa motsawa daga inda take. Abinda ta guda da hawa lift Win kenan, idan da Napep suka hawo bakinta alaikum se samu hanyar kurWawa ya kaisu har ?ofar gida data sauka ta afka kuma ba lallai kujerarsa ta nuna ba sabanin ta Ahmad da take fara tas ita kam yau ina zata kai wannan abin kunyar staining a motar jama'a daga Rage hanya?

Ya mi?awa Anty Sauda wayarsa ta sanya masa number Fatima wadda tare suka siyi layin banbancin lambobin ?arshene kawai da tata shiyasa ta ri?e kafin ta sake masa godiya ta shige layi ba tareda tabi takan Fatima ba.

"Ko ba tare kuke ba?" Ahmad ya faWa yana karantar fuskarta, dukda be santa ba amma wannan fuskar tata da akwai abinda yake damunta ba iyakar Miskilanci bane".

Fatima ta yun?ura domin babu amfanin zaman da takeyi a cikin motar. Ta kalli kan layinsu dukda tsakiyar ranace ?wal amma munafukai yan saka'ido na nan suna bin inuwar gefen Titi a haka zata ratsasu ta wuce?
Jakarta ta buWe da dabarar kiran Anty Sauda ta bada Hijabi A Mi?o mata tazo mata, da zasu fita harta saka Hijabinta haka nan ta canza kaya ta saka Abaya Light blue ashe rabon abin kunya ya jata da Hijabi ne Asirinta a rufe kota bata masa kujera shami?ewa zatayi ta tafi dan ba sake haWuwa zasuyi ba balle taji kunya. Takaicinta ya ?aru sanda ta zaro wayar taganta a mace, ita dai yau bata fito da sa'a ba.

Ta kalli Ahmad fuska a marairaice, so take tace ya bata aron wayarsa amma ina hali irin nata na shegen Miskilanci ya hanata se kawai ta rungume jakarta jin ya yiwa motar key da alamun ya gaji da jiranta ne ze tafi da ita ko yaya ta kama murfin motar ta buWe, tana zura ?afafunta waje Ahmad dake lura da duk motsinta yaga abinda take boyewa, da saurin gaske ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta da ?arfi. Ta dakata Win tareda kallonsa yace mata

"Me yasa tun a Mall bakiyi magana an baki pad kin gyara jikinki ba? Da a haka zaki keta titi ki wuce waWannan Mutanen?" Mutanen daya faWa ta kalla. Suna nan tun tsayuwarsu a motar suka baza idanuwa suna naWar rahoton gulma da munafunci wanda sukafi ?warewa akai. Fita yayi daga motar ya buWw booth, tana tunanin Pad Win ze Wauko mata ko me? Koda yake a yanzu ai pad bata da amfani a gurinta ta samu abinda zata rufa ta isa gida kawai take da bu?ata kuma wayar tasa dai itace mafitarta. Tana sa?a abinda zatayi ya dawo da leda a hannunsa ya mi?a matata karSa ganin kamar yadin Hijabi ko Abaya.

Hijabi ta gani data warwarshi har bata sanda ajiyar zuciya me Nauyi ta kwace mata ba, ta zura a jikinta kafin ta saci kallonsa kamar mara gaskiya tace
"Nagode"
"Babu damuwa, but next time idan kina cikin yanayin bu?atar taimako kiyi magana bakiyi Sacin rai kina kumburi ba"
"Toh" kawai tace masa kafin ta fita tana waiwayen inda ta zauna ya baci sosai kuwa kamar ma da gayya Jinin yazo da yawa dan ya kunyatata.

Murmushi Ahmad ya rakata dashi harta ?ulewa ganinsa, harya tada motar se kuma wani tunani ya saka ya gyara parking ya sauka yabi cikin Layin da sukayi. Beyi nisa da yawa ba ya tambayi wasu yara gidansu Fatima sukace basu santa. Ya ri?e ?ugu yana kallon Lokon da ya tabbatar idan ya ?ureshi ze tsinci kansa ne a wata unguwar daban ba wadda yake ciki ba, hagu da dama kuma layukan duk basa Sulla ya tabbatar gidansu na daga cikinsu, harya ha?ura ze juya tunda ya samu number wayarta sega wani saurayi ya fito daga wani gida da bokitin MarkaWe ya tareshi yana tambayarsa gidansu Fatima.

"Farace sosai?" Yaron ya tambayeshi ya gyaWa masa kai alamar itace, yaron ya ?walawa Waya daga cikin yaran dake wasa kira yace
"Ka rakashi gidan Malam bakanike"
"Bansan gidan ba" yaron ya faWa yana zabura ze koma gun wasansa wanda ya kirashin ya talle masa ?eya yace
"Gidan su Jafarun ne zakace baka sani ba banza gidansu yar Fara fa"

"To ai haka zaka ce mun ba yanzu Anty yar Faran ta wuce ba da Antynsu me Mota sun taho da kaya da yawa mu muka kai mata gidan ma ta bamu Cakulat" yaron ya sake faWa kafin yayi gaba yana tsalle, Ahmad ya zaro dari biyar a aljihunsa ya bawa babban yaron kafin yabi bayan wancan. Da yar tafiya daga Titi zuwa gidansu a can cikin Lokon suke har sun kusa shiga Alfindiki ma daWin da sukaji lokon gaba Waya lailaye yake da Interlock ga Fitulun Solar da alamu basu da matsalar haske har tsakar gida sun huta da kunna fiti. A ?ofar wani gida yaron ya tsaya.

Daga yanayin ginin zaka fahimci gidan masu ?aramin ?arfi ne, ya sallami Yaron da alawoyin dake cikin Aljihunsa sannan ya juya ya tafi daman gurin kawai yake so ya gani. Babu ?yama ya saka Ruwa daya zubawa Omo da freshner ya goge kujerar tsaf, ya maimaita gogewar har sau uku kafin ya saka clean ruwa ya goge sannan ya sake fesa Freshner akai sa'annan ya ya tayar da mota ya bar gurin.

Yana tu?i yana tunanota, yanda take haWa fuska tana motsa ?aramin bakinta ba ?aramin kyau tayi masa ba. Ya tuna idanuwanta sanda ta rasa mafita ya bata Hijabi, muryarta a karaye da tace masa ta gode har zuwa tafiyarta a sanyaye kamar wadda batada laka. Zuciyarsa ta ringa ayyano masa gidan data fito, yanayi na suffa da tsarin halitta daga ita har Yayarta be taSa hango daga irin wannan unguwar suka fito bama balle wannan gidan, seya tuna da wani abokinsa Munir da ya taSa ce musu Mata da suka amsa sunan Mata na cikin Lungu.

"Kunga unguwannin nan da muke gani as no go, wlh mata nacan, kaga yarinya kamar ita tayi kanta gashi sun ?oshi da tarbiyya kawai dai basu kai wayewar da muke kwaWayi ba amma ni dai idan na tashi aure Lungu zanje na samo mata wadda zan ringa FaWawa magana taji da Wan kuWina ?alilan Alaji a hankali na wayar da ita yanda nake so" inji Munir Win to yau ya gasgata zancensa domin Fatima dai kodaga Villa ta fito ta isa Mace kuma za'a nunata a ko ina ba tare da anji kunya ba, shikam yaga Mata dukda tace be mata ba, ze tabbatar da se yayi matan dan baze bari ta wuceshi ba, ita Win tayi daidai da tsari da ra'ayinsa.

Yama manta da zeje gidan Nazira seda ya ganshi a ?ofar gidansu tukunna ya tuna, kwakwalwa duk tunanin Fatima har ya fara loosing focus. Gidan ya shige akan se da dare idan ya fita seya kai mata kawai. Haka ya ?arasa yinin ranar har gizo take masa muryarta na masa amsa kuwwa. Ahmad be taSayin budurwa da yaji ta shiga zuciyarsa farat Waya a ganin farko ya sakawa ransa ya samu mata ba se akan Fatiman. Mutum ne shi da idan abu ya shiga ransa tofa se Allah, Fatiman kuma abin nata yazo masa da gaske, daga haWuwa yini Waya harya fara tsara rayuwar da zasuyi tare, har tunani yakeyi idan da gaske tace beyi mata ba wani kalar garari rayuwarsa zata shiga dan ya rigada ya kwallafa rai a kanta, shi kuma duk abinda ya saka rai da samu baya taSa saduda har seya mallaki wannan abun. Yaya zeyi idan ya gaza cin galabar zuciyar Fatima ta Aminta dashi.

Seda yayi sallar Isha'i ya tafi gidan Nazira, ya tarar da Matan Naziru Uwargidan Anty Mardiyya da Amaryar da yayi kwanannan Yusra wato Yuseebaby Shahararriyar yar rawar Nanayece a Sabuwar Manhajar Tiktok, su suka fara yankewa bin wa?a ana rawa a tiktok Win cibi. Allah kaWai yasan inda Nazirun ya yayibota kuma da yake me uwa a bakin murhune duk sukar da abokanan Alhaji suka ringa kawo masa akan Yarinyar wadda kowa ya bada shaidar bata jin magana cewa yayi tunda me Auranta yaji ya gani ai shikenan, Karuwa ma idan ta tuba ana auranta balle ita da babu wanda ze kawo shaidar cewa tana Alfasha, Yarinyar da har video take iyayi da undies ta Wora a Tiktok amma Alhajin ya murje ido yace babu komai ya aureta, koda yake umarnin Hajiya domin ita yarinyar tayi mata, yanda tayi suna tayi shura tana da followers bila Adadin a duniya baki Waya ba iyakar Nigeria ba ga uwarta tana da kuWi suna da ?aton gida wanda akace ire iren Alhazan da take hulWa dasu ne wani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login