Showing 267001 words to 270000 words out of 467220 words

Chapter 90 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12252

jeren kitchen da sauran gyare gyare ya rage musu a ranar kuma Badar suka zo tareda Mamansu wanda dalilin zuwanta nema yasa suka jinkirta yin jeren. Momyn su Badar, Umma Halima, Abla Zainu ?anwar Ummansu data zo daga Yamai se Anty Sauda da Anty Hauwa sukaje yi mata jere. Basu tarar da kowa a gidan ba se megadi shi ya buWe musu gidan. Gadajenta guda biyu duka yan waje ne, Mijin Anty Sauda ne ya siya mata Gado Waya da Dining da Tv harda ?aton Fridge two doors a matsayin gudummawarsa. Kaya masu kyau da tsada, wannan gudummawa da suka samu tasa kuWaWen da Baffa ya bayar a siya mata gado da na gurin Umma da itama nata da take ajiyewa gurin Anty Sauda duk sanda Ahmad Win yayi mata kyauta, dasu suka ringa siyan kayan kitchen suna tarawa shiyasa da suka fito da kayan abinda yayi saura zasu ?ara bashida yawa.

Ganin kuWaWe da yawa yasa suka siya mata saitin wani gadon me haWe da kujeru, centre table, Tv stand da console. Mamansu Badar ce tace a cire dining saboda a bangaren da aka tanadawa matar gida babu space Win Dining acan Babban falon gidan na farko yake wanda tace a barwa Ahmad abinsa baza'a saka komai ba. Anty Sauda dai taso a mata kujeru biyu a gyara Babban Falon shima Momyn Badar tace Aa,

"Duk abinda za'a mata Sauda ba burge mutanen nan za'ayi ba dan sunfi ?arfinsa daga ?arshe ma ze iya zama abin magana ace komai shi yayi tunda an san ?arfin mahaifinta, ba za'ayi ?arya ba abinda yake dole shi za'ayi mata kawai" Momyn Badar ta faWa wannan yasa Anty Saudan ta ha?ura da zancen Kujerun aka gyara mata two bedroom da palour se kitchen da yake cikin part Winta. Guri yayi kyau, kayanta ba masu azabar tsada bane irin na Amaryar Jay amma duk hassadar mutum be isa ya kushe ba dan sunyi ?o?ari matu?a da gaske.

Suna shirin barin gidan bayan sun gama komai Bedsheets ne kawai basu shimfiWa ba, turaren wutar da suka saka suke jira garwashin ya cinye su kashe kafin su tafi sega Mata daga gidansu Ahmad masu tarbar yan jeren. Mazan da suka zo dasu ne suka fara shigowa da manyan kulolin abinci da kayan ji?a ma?oshi kafin matan suka biyo baya.

Hajiya Binta ce a gaba ita da Turai se Anty Zainab da Anty Zinnirah ?annen Momy se kuma Hajiya Balaraba da Hajiya Rabi tareda Baba Bilki sune ?arshen shigowa. A mutunche suka gaisa idan ka cire Hajiya Binta dake faman baza idanu tana kallin falon fuska kamar an watsa mata kashi se taSe baki takeyi seda Turai ta zungureta kafin ta amsa gaisuwar da Umma Halima ?anwar Baffan su Fatima take ta mata tsabar neman gurin zama.

Ba shakka guri yayi kyau, lallai Aljihun Amadu ya girgiza shi yasa ya kasa zaunawa ya huta to kar kuma ayi biki ya ras ana cefane duk an tatikeshi saboda jaraba" Hajiya Binta ta faWa, daga wanda sukazo tare har yan jeren akayi sa'a babu wanda yayi koda alamar da zata nuna cewar sunji me ta faWa. Bata ha?ura ba ta mi?e tayi gurin Wakunan kai kace gidanta ne ta shige, daga ciki ta ?walawa Turai kira ta bita jiki ba laka, da tasan tsiya Binta tazo yi da bata rakota ba dan yanzu cewa za'ayi tare suka shirya kuma ita wlh babu ruwanta.

"Dan Allah kuyi ha?uri, haka halinta yake idan bata takali masifa ba bata jin daWi a rayuwarta" Anty Zainab ?anwar Momy ta faWa cikin Sacin rai, sudai suka ce
"Hmm" se Momyn Badar ce ta ce mata
"Babu komai Hajiya ai da ganinta ma babu bu?atar ?arin bayani rikicin tsufa ne Allah ya rufa asiri, ku shiga kuga guri toh"
Duk suka mi?e, Wayan Wakin ba wanda su Binta suke ciki ba suka le?a kowa nata faWin masha Allah suka shiga kitchen daga nan se Wakin da su Bintan suke ciki Turai nata mata balbalin masifa suka le?a sudai suka wuce, abincin ma motar da sukazo da ita aka saka musu saci a gida sukayi sallama yan jeren ne suka fara ficewa bayan sun maidawa me gadi mu?ulli.

"Aa, naga duk kun shige mota ba zaku le?a kuga gidan Jafaru bane?" Binta ta faWa tana kallon abokanan tafiyarta da duk suka shige mota saura ita da Turai a tsaye, Hajiya Balaraba ta le?o tace mata
"Aa ai munga nan kamar mun shiga can ne tunda ginin duk iri Waya ne"

"Amma kayan ciki ba iri Waya bane ai, kuzo muje kuga inda arzi?i yake kaya na can kamar show room a gidan Jafaru" Hajiyar ta sake faWa, Baba Bilki tace
"Sanda suka zasuzo jera kayan a dangin ubansa wa kika gayawa?"
Zinnira dake cike da ita tace
"Barta Baba Bilki, ita ce ba?uwar ganin kaya se taje ta zaSi Waki ta zauna kafin surukar tatavta tare, kai muje dan Allah sa tari adaidaita su taho idan ta gama yawo zubar da mutunchin" Driver ze taka mota Turai tayi wuf ta shige tana cewa
"Muje se kin taho Binta"
"Wallahi sena gurza miki rashin mutunchi Turai, ni zaki wula?anta a gaban mahassada ki kwaremun baya?" Binta da itama ta turmutsa motar ta faWa cikin banbami, har sukaje gida batayi shiru ba babu kuma wanda ya kulata ita Turai ma a hanya ta sauka ta wuce gida tace ta tura a Wakko mata motarta.

"Wato Afeeyah da Allah yasa Jafar zaki aura da kin gane baki da wayo, uwarsa ta isheki tashin hankali nan duniya, keda farin ciki inaga daga randa kika saka ?afa a gidan Wanta kunyi sallama dan billahillazi wannan matar ruwa ba zata bari kisha cikin daWin rai ba" Anty Sauda take gayawa Afeeyah da dare bayan data koma gida. Badar tace

"Ashe da gaskene, ance daman bata da mutunchi wani abun tayi muku koh"

"Au ashe da kun sani ma shine kike kwance kina kuka saboda ba zaki auri Wanta ba? Ai se kinga matar nan Badar, idanunta kawai zaki kalla kisan ?wan?wararriyar mara mutunchi ce daga zuwa harta fara yada mana maganganu mudai muka taho muka barsu irin wannan matar ai koda kuWi ba zaka so ka auri Wansu ba dan wahala zaka sha. Wlh ki godewa, Ahmad Win nan da kike rashin mutunchi akansa shine Alkhairinki idan baki nutsu kin gane gaskiya yanzu ba akwai sanda zakiyi kukan da kin sanin abinda kika aikata masa a baya wlh" tana gama faWa ta shige Waki abinta.

**********

Bisa tursasawar Badar da sauran ?awayensu da sukazo biki suka shirya Henna party ranar Alhamis, a nan compound Win gidan Anty Sauda sukayi. Sun kira masu decoration an gyara musu gurin, small chops da drinks da akayi duk bata ma san sanda su Badar suka shiryashi ba tana can tana ba?in rai. Ta saka wata Atamfa Holland pusher pink da fari wadda daman ita Badar ta zaSa akan zata saka ranar dan haka akayi mata Winkin da baze sa lallenta ya Saci ba, sun rigada sunyi jan lalle jiya a Saloon Win da Ahmad yasa aka kaita gyaran gashi dan haka ba?i kawai sukayi, event Win was so fun, babu mutane da yawa just friends nasu yan Abu da few family se dabda za'a tashi Ahmad ya kawo su Maimuna da Sarah da twins Win Hajiya Rabi suma a nan aka musu lallen sukayi hotuna sosai da Amaryar Yah Ahmad suka kai gida ai kuwa Sarah tasha Ashar harda mangari a gurin Hajiya, abinda ya sake ba?anta mata rai ya kuma dugunzuma mata hankali yanda kowa yake zuzutun kyan Amaryar Ahmad dukda ba kwalliya tayi ba.

Yan gidan kusan duka seda sukayi posting hotunan da sukayi tareda ?annen Ahmad Win a status Hajiya ta ringa bala'i a tsakar gida tana kumfar baki, tun litinin hotunan Amaryar Jafar yake yawo a sohiyal midiya amma bataga wani a cikinsu yayi magana ba sema Baba Al?ali daya kira ya ringa faWa kan kayan da ta saka jiya da sukayi Ladies party yace Jafar yaja mata kunne karta sake irin wannan shigar yanzu hakan duk su Hajiya ?arama dasu Anna suna can Abujar da dangin Bintan dan yau Maman Fatiyyan tayi Kamu da Yini, washe gari Juma'a zasu tafi Mambila acan za'a Wauro aure se su wuto Kano su aje Amarya har magribar hoto Waya ta azazzali Munirah ta turo mata kuma bata ga sun saka a status ba amma shine dan munafunci zasu ringa saka hoton yar bakanike ba?auyar banza ta wani dankwama Atamfa riga da zani babu dai wanda ya tayata yan biki se zunWenta akeyi.

Su Afeeyah da dare bayan sun gama Henna partyn yan gidansu Ahmad wannan karon banda Hajiya sukazo Kamu dan daman an gaya musu kamun gargajiya irin nada zasuyi, suka fesa mata turare bayan sun sallami yammata da kuWaWe masu nauyi.
Washe gari Juma'a Umma tayi yininta a gida, Yan uwanta sunzo da yawa daga Niger ga dangin Baffa aka haWu akayi sabgar Arzi?i Amarya nata shige da fice cikin suturu na Alfarma da sukaji Winkuna dangi nata matsa tsiya wai bata fara'a, uhm basu san me take ciki ba sudai se kwasar rasu suke da kulera abinsu suna raha.

"Hauwa ciko kikayi ne?" Sadiya, Abokiyar wasan su Afeeyan ta tsokani Anty Hauwa. Cikin sigar sha?iyanci ta girgiza mata ?irji tayi fari da ido tace
"Ya ranki? Kinsan magani dace ne to Allah ya kawo lokaci nima na dace da maganin matsalata gadai abubuwan da Baban Mimi yake mun iskanci akai gasu nan sun fara tasowa"

"Yar uwa meye sirrin? Taki ce ta fito fili amma nan dukda kika ganmu packaging ne harda masu saka bra biyu danta ri?e musu shi da kyau" Aymana ta faWa, su Hauwa harda tura Wankwali gaba tace
"*TULA-TULA* ne sirrin, kin ganni sati na uku da fara sha bana tsallake gashi wlh abubuwa sunji sabis duk sun farfaWo sun fara komawa hayyacinsu ga ni'ima faca faca ai ni nayi hand over da duk wani maganin mata tunda na samu 3 in 1"

"Ashe dagaske yanayi, wlh wata ma?ociyata tayi amfani dashi haihuwarta shida amma idan kika ga Nononta zakice haihuwa Waya ko biyu tayi tace mana da sunfi nawan nan kwanciya amma data juri shan maganin yanzu gashi komai ya tashi kuma itama haka tace yana saukar da Ni'ima kuma ya mata maganin infection har muna ?aryata matar nan ashe da gaske takeyi" Sadiya ta sake faWa. Rumaisa matar babban ?an Umma faWima tace

"Maganin nan yana da kyau fa wlh, kwanaki can da mukayi bikin ?anwata Farida ai kun santa shi aka siyo mata da haWin sabayar matar tashasu bakiga yanda ta yi dumurmur ba kafin biki jiki duk ya cike tana she?i, nima naso na siya lokacin tace kayan sun ?are na manta kuma ban sake mata magana ba*

"Ai kuwa tayi restocking kaya, ba surutu ba maza ga number ta kowaccenku ta antaya mata kira ta karSi nata a kankaro mutunchi nidai na gwada tested and trusted *TULA-TULA duniya ne 08135613021*" har suna rige rugen amsar wayar.

?arfe shida suka bar Alfindiki suka koma gidan Anty Sauda. Ahmad ne ya kira Badar akan me kwalliya tana can tana jiransu, Afeeyah bata san wainar da aka toya ba kawai dai tace mata suzo su tafi daman kuma ta gaji dan haka bata musa ba suka ta fi inda motocin daya basu suke jigila dasu tun fara bikin suke jiransu Seda suka isa ta tarar da wata mata da uban akwatin make up ga kuma kayan hoto ko nata ne ko na photographer oho, Badar bata bata damar tambaya ko botsarewa ba ta nannaWe ta kalaman ro?o,

"Dan darajar Allah karkiyi abinda ze Sata masa rai, surprise party ya shirya muku a cikin gidan za'ayi ba a wani guri ba" Badar ta faWa. Afeeyah ta haWe fuska tace

"Amma ai na gaya miki bana sha'awar yin komai da bikin nan, kuma kinsan komai dake aka shirya me yasa baki gaya mun ba?"

"Saboda yace karna gaya miki, so yakeyi ya faranta miki we all know it is your dream to do cocktail party a bikinki"

"Ke kika gaya masa dan ni bamu taSayin wannan maganar da Ahmad ba" ta sake zaburo mata,

"Badan ni ba badan shi ba ba dan kowa ba dan sonki da Annabin Rahma Afeeyah karki Sata moment Win nan, pretend to be happy Even if you are not we will enjoy the moment on behalf of you just karkiyi disappoint Ahmad a gaban friends Winsa please" Badar ta sake pleading. Haka ta shiga wanka tana mita, cocktail a bikinta was on her must do list ita da Jay amma, har color setting sun zaSa yace all black party tace peach take so daga ?arshe suka tsaya akan Peach and black decor ashe duk lissafin dokin rano sukeyi.

Hawaye ya silmiyo mata ta saka ruwa ta Wauraye, daga gobe ta zama matar Ahmad, tana addu'ar Allah ya bata ha?uri da juriya ta kyautata masa ta bashi farin cikin daya dace dashi.blight make up akayi mata, matar nata zuzuta kyau da santsin skin Winta takeya. Wata ball gown peach color Badar ta kawo mata, ta kalli Badar Win data haWe cikin fitted gown black fuska ta sha shine shine tayi kyau kamar a saceta a gudu kafin ta kalli rigar data ajiye mata

"Bazan saka wannan ba" ta faWa tana haWe fuska, Badar ta Wage kafaWa irin ko a jikinta kafin tace
"Seki fita da towel Win jikin ki ai" ta juya abinta tana amsa waya.
"Amarya wai menene? Duk yanayinki is not lively, kowacce amarya ana bikinta tana farin ciki amma ke se haWe fuska kikeyi ko auran dole za'a miki ai se haka" Makeup artist Win me shegen magana ta faWa. Murmushi kawai Afeeyah tayi ta tashi ta saka rigar zuciyarta na tsinkewa, matar ta sake gyara mata gashinta tayi styling kafin tayi mata Wauri me kyau ta fesa mata spray Win fuska kafin tace ta gyara ta mata hotuna.

A falon Anty Saudan ta tarar da Ahmad ya haWe cikin suit black farar inner ya saka takalminsa ma ba?i se bow tie peach kalar rigarta, yayi kyau duk abinta bata isa tayi denying hakan ba, murmushin da yakeyi ya saka bayyana kamanninsa da Jay sosai.
Sosai akayi musu hotuna, decent hotuna wanda ko kusa be taSa jikinta ba ko wani abu amma sunyi kyau, presence Win Abokanansa da nata da suke ta Waukansu videos yasa ta saki fuskarta dole ta ke fara'a musamman da taga Bestienta fron no where yanda yake teasing nasu yasa har dariya ta ringayi a hoton.

A back yard Win gidan aka shirya partyn, babban fili ne ya siya ya shigo dashi zeyi swimming pool da gurin wasan yara, yanda aka gyara wurin ba zakace ma a cikin gida bane ga haske sosai gurin yayi kyau Deco Win peach and black ita kaWai ta saka peach gown duka braid's maid da groom's men black gown da suit suka saka
"You will be the only one wearing peach za'a dai taimaka miki a tsarma color a deco kar ki fita daban" conversation Winsu da Jafar take hawaye ya fara tarar mata a ido, shi yayi, wlh shawaransa ce wannan" ta raya a zuciyanta.

Yanda Abokanan Ahmad Win suka haWu har yasa yammatan suka raina kansu, but yanda yake da sau?in kai haka suke, very humble set of people party yayi daWi dukda babu wani kiWa me Waga hankali an ci an sha Champagne tayi kuka a gurin ga BBQ ga snacks wasu ma nan suka fara ganinsu sunyi playing games.

Bugun da ?irjinta yakeyi ya saka ta tabbatarwa yana kusa da gurin, ta runtse idonta da ?arfi daidai lokacin da sautin muryarsa ya gifta kunnenta
"I'm sorry Yah Ahmad, Fatiyyah ce ta ri?eni da rigima, wai kar nazo naga yammata" kalaman suka saukar mata kamar ana tsiyaya mata soyayyan mai a zuciya, tanaji Ahmad nace masa
"Babu komai, kaci darajar ?anwata" yayi wannan murmushin nasa dukda bata gani ba kafin yace

"Amaryarmu ina wuni? Wani abu ya shigan mata ido ne naga ta rufe?" Ya jefawa Ahmad maganar kafin ma yace komai ta buWe idonta fes akan Jafar, Ba?ar suit ce jikinsa head to toe babu ratsin komai kamar kamar wanda zeje Jana'izar kiristoci, idonsa sunyi Jaa kuma sun koWe kamar yayi kuka, indai ba gizo idonta ya maya ba se taga ya rame sosai yayi haske kuma hancin ya ?ara tsayi. A hankali ta sauke idonta ?asa, taga yanda rigarsa da be Sallewa ba take Wagawa alamar zuciyarsa na bugun daya wuce ?a'ida.

Yanda ta ?are masa kallo a yan sakanni haka shima ya kalleta, a hankali ya lashi busashshen pink lip Winsa na ?asa ya haWiyi wani abu me Waci dake masa yawo a ma?oshi kafin ya kalli Ahmad yace
"She is beautiful, tayi kyau sosai"
"I'm jealous" Ahmad ya faWa da sigar wasa kafin ya janyoshi kusada Afeeyah suka sakata tsakiya aka fara musu hotuna kamar ruwan sama, Faisal, Salim da sauran cousins Winsu dake gurin sukayi joining akayi Family picture,
"Ayi musu su biyu, abokanan faWa" Ahmad ya faWa da zuciya Waya yana matsawa daga kusa da ita, lokaci Waya suka kalli juna, kallo me cike da ma'anoni da yawa kafin a tare kowanne ya janye ya matsa daga gurin alamar baya so ayi hoton sedai ina aikin gama ya gama dan tuni me hoton ya samu perfect shoot sanda suka kalli juna lokacin camarar sa ta ?yasa musu.

"Muje ku gaisa da su Affan, tashi ma za'ayi" Ahmad ya faWa yana kama hannunsa suka tafi gurin friends Winsa, lokaci Waya ta faWa jikin Yah Malam daya zo suyi hoto, duk yanda take so ta daure, duk irin ?o?arin ri?e kanta da take so tayi ta gaza fashewa tayi da wani kuka irin me tafe da Waci da kuma ?uncin da zuciya take ciki, Malam ya ri?eta sosai jikinsa yana rawa, besan komai da yake faruwa ba, babu wanda ya gaya masa shiyasa hankalinsa ya tashi da irin kukan da ?anwarsa take yi a ranar daya kamata ace bakinta ya gaza rufuwa saboda dariya. Badar ta iske suz ita kanta zuciyarta ta raunana, vividly duk wanda yasan tsakanin Afeeyah da Jay kuma ya kalli yanayinsu a yanzu se sun bashi tausayi, idanunsu basu Soye abinda yake ransu ba, a tunanin kowannen su kallon tsana yake jefawa Wan uwansa basu san kallon ?auna bane dan ya zarce a kirashi dana so.

WASHE

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login