Showing 201001 words to 204000 words out of 467220 words

Chapter 68 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12374

kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.*

*A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294*
*Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita*
https://wa.link/wwvjr3
*Location Kano, tana Nation wide delivery*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 14*


"Ban san shi ba ban kuma taSa ganinsa ba se ranar. Ni kaina Islam bansan ya akayi ba na kamu da sonsa har haka ba. Ta yuwu kodan yayi daidai da tsari da kuma mafarki na akan Abokin rayuwa shiyasa"

"Kiyi addu'a idan da Alkhairi a tsakaninku Allahya tabbatar amma ki cire son rai a yayin da zaki nemi zaSi a gurin Allah kuma ki dena wannan halin na zargin wata zata kwace miki abinda kike so sannan ki lallaSa Badar wlh Afeeyah samun mutum da ze soki tsakani da Allah kamar ita a yanzu yana da wahala"

"To ni yanzu taya zan bata ha?uri kinsan dai Badar sanda kake lallaSata sannan zata botsare ta fara rashin mutunchi ni kuma ba zan jure ba sena tanka mata"

"Tunda kece baki da gaskiya kuwa haka zaki yi shiru ko zaginki zatayi, yanzu ki kirata tazo nan ku sasanta tun wuri ma ba se kun koma Waki ku sake raba hali ba a ringa yawo daku a baki" Islam ta sake faWa ta kalleta da son jin ?arin bayani ta yamutsa fuska tace
"Eh mana, ce miki akayi duk wanda kake dariya dashi me sonka ne tsakani da Allah? A aji ranar ina jin Ummi na hirar kuna ce mata tana yawo bayan kuma abinda kukeyi kenan ko kuwa samarin da suke kashe muku kuWi ?annen babanki ne da zasu ringa muku bauta ba tareda suna benefiting komai a gurinku ba"

Take ta sake hasala tace
"Ita Ummin take cewa haka?"
"Bana faWa miki bane saboda kije kiyi tashin hankali, ke matsalarki kenan bakya cin ribar zance da an faWi abu kamar wuta fuu zaki tashi se daga baya kizo kina regretting action naki I'm only telling you so that kusan zaman da kukeyi da kowa kuma ba komai zakuci gaba da sakin baki duk sirrinku kuyi ta faWa a Waki ba, ai dai tun muna tare nake muku wannan faWan daga ke har Badar kun fiya saurin yarda da mutane baku da sirri".

Tilas ta kira Badar dan ta yarda da gaske bata kyauta ba ta ringa bata ha?uri bayan tazo, Badar bata da ru?o, sha yanzu magani yanzu ce dan haka take ta zazzage mata abinda yaje ranta maganar ta wuce. Ta dai gaya mata wlh koda wasa ta sake maimaita mata abinda tayi zata nuna mata bawai bata da zuciya bane ko kuma ita kaWaice me ba?in rai, zata fita a harkarta dan bazata cigaba da zama da ita Alhalin zuciyarta bata aminta da ita ba. Gurin Islam suka wuni, Badar bata iya boye abinda yake a ranta tayiwa Afeeyah murna akan Soyayyarta da Jay amma tace

"Afee karki sakashi a ranki sosai saboda gudun abinda zeje ya dawo. Muyita addu'a idan shine Alkhairinki Allah ya tabbatar amma magana ta Allah nafi sonki da Ahmad sedai idan kuma za'abi ta suna Jay Win nan fa ze Waga mana aji, ganinmu za'a ringayi muna cafkewa da world class Celebrities, Allah kenan sega Badar zata haWu da JAY a Sagas, kinga su MESSI duk zasu zama Abokanmu wayyo Allah na" suka ringa dariya, Afeeyah jinsu takeyi ta tabbatar gaskiya suke faWa mata amma kuma zuciyarta ta rigada ta afka ga koginda fitowarta se anyi da gaske.

******************
"Naziru kalleni dakyau nayi kama kama da wawiya da zaka zauna kana tsarawa wannan zancen na kama? Ni ba surutun banza da iska nake so naji ba, kuWina zaka bani maza ka zuba munsu anan" ta warware ?aramar Ghana Must Go dataje da ita kafin taci gaba da cewa
"Maza maza kana Satamun lokaci daga nan janguza zanje an yanka wasu filaye zanje na siye na ajiye abuna tunda lamarin ?annenku babu Allah yan iskan yaya sun zama Sarayi, yaron nan Faisal da Jafaru ya?i bashi kuWin shine yabi dare yayi mun sata, ni banma san nawa ya Wauka ba dan lissafi ya kwace mun tunda naga haka nace toh ba yanzu ya saba ba, daman na daWe ina ganin kuWin nayin ?asa se in Wauka ajiya ce ta saka sikayi laushi. Kuma fa kwana suke cikin sanyi yanda kace, kaji Wakin kuwa kamar dusar ?an?ara zata zubo....."

"Haba Hajiya, ki tsahirta mana karki ?ware" Naziru ya dakatar da hajiyar dake ta zuba kamar nunanniyar kanya kafin yaci gaba da cewa
"Na gaya miki Hajiya yawan shige da ficen da kuWi sukeyi a personal account Wina yana neman ya jawo mun matsala. Kinsan dai yanda EFCC yanzu suke saka idanu kan duk wani motsin manyan kuWi a ?asar nan, na gaya miki ba'a account Win company suke ba kuma ko a nan ne ke account Winki idan aka tura kuWaWen nan wlh suna iya rufeshi azo bincike ki saka kanki a matsala. Ha?uri zakiyi kamar yanda nace zan ringa ciresu a hankali ana juyawa se a ringa tura miki da kaWan ko Miliyan Waya ce duk wata".

"Ai shiyasa nazo da jaka tashi zakayi mu tafi bankin ka ciremun kuWina na gaji da wannan ?arairayin naka kullum bayan Alhaji Zakariyya ya gaya mun ya karSi nasa ni kake so ka cuta kenan ka cinye mun kuWi to baka isa ba" Hajiyar ta faWa cikin Waga murya. Naziru ya dafe kai, ya rasa bayanin da zeyiwa Hajiya ta fahimceshi, saboda Allah tayaya ze tura mata Miliyan Wari uku ko kuma ya cirosu ya zuba mata a Ghana Must Go a wannan halin da EFCC ta matsa ko da account Win kamfani cikin takatsan tsan suke abubuwa balle aga kuWi irin haka suka fita daga personal account Winsa ai tona masa asiri zatayi.

"Hajiya shima kayan kuWi ya karSa ba zallarsu ba kuma kiyi ha?uri ki dena Waga murya mutanen gidan sunajinki" ya faWa a tausashe. Ta zabga masa harara tace
"Ni kuWi na nake so, waima kayan uban wane kuWi kuke magana akai kamar wasu marasa gaskiya haka yace mun wai kaya ya karSa su kayan basu da suna ne bayan Mai akwai abinda ka fara siyarwa ban sani bane da ake samun kuWi saboda mugunta baka gaya mun ba balle na gwada nima?"

"Zinare ya karSa na gaya miki na fara ha?ar zinare a Zamfara ai"

"Dan ubanka da akace dutse yana ruftowa mutane so kake ka mutu saboda rashin godiyar Allah zaka zur?uma cikin rami wai ha?ar zinare Naziru?" Hajiya ta faWa tana zare ido kamar ance mata dutsen ya rufta dashi. Ya kalleta, da ace watace daban daya tambayeta a duniya waya kaita son zuciya amma uwarsa ce duk iskancinsa baze kwatanta haka ba se yayi murmushi yace

"Bafa da kaina nake shiga ba Hajiya kamfani ne suke ha?an da injina kuma jari kawai na saka ina karSan Wanyan gold se na fitar a sarrafashi"

"To nima ina so a saka kuWin, amma ni idan an ha?o gida za'a kawomun abuna in ajiye se yayi tsada sannan na fitar na siyar sar?o?ina ma zan kwashe su idan zan tafi Umarah Turai tace sunfi daraja yanzu acan zan siyar se in baka kuWin a ?ara jarin yanda za'a ringa samu da yawa. Wallahi fa ance kuWi akeyi sosai da harkar nan, kaga yaro bashi da ko taro amma dayaje ya shiga rami ya dawo kaga ya zama Miloniya wannan tubda da Inji nema za'a ha?o sedai muna zaune muyita karSar kaya toh haka za'ayi, amma bani ko Goma ce yanzu na tafi da ita dan na saka rai zan siyi filayen nan har nace a dubamun na bakin Titi zasu fi daraja idan an kwana biyu".

Naziru ya sauke ajiyar zuciya jin ya tsarata kuma ta hau kafin ta sake botsarewa ze san abinyi. Dole ya shirya suka fita Banki ya cire 10M aka saka mata a Ghanarta ko tsoro bataji ta haye Napep wai ta tafi Janguza, dayace ze kaita cewa tayi Aa, a dabararta karyaje yaga inda Filayen suke. Yakubu sau biyu yana sace mata Takardun Manyab Fikaye yaje ya siyar, dake bata mantawa da komai nata har gewaya take zuwa taga lafiyar kadarorinta Waya taje taga an yi gini har An saka Amarya Wayan kuma Plaza akayi tayi masifar tayi bala'in ?arshe tayi Allah ya isa dan Yakubun taurin kaine dashi kamar me kuma hauragiyarta ba tsorata shi take ba, sa'idar data samu yanzu matsayinsa daya ?aru a Kamfani, sedai shegen Yaron kamar yanda take faWa kansa kawai yake Azurtawa. Ko sun so ayi cuwa cuwar da aka saba ya kankane komai ya hana ta tabbatar idan suka matsa kuma kamar yanda yake cewa tsaf ze fasa ?wai, rabuwa dashi tayi yanzu amma tana nan zatayi maganinsa yanzu maganar auran Hajiya ?arama data taso ce a gabanta daia Abba Tee har iyayensa sunzo anyi tambaya shima Yakubun Aure zeyi.

AFEEYAH

Sannu a hankali soyayya da sha?uwa me ?arfi ta shiga tsakaninta da Jay, wani irin so take masa da bata san iyakarsa ba, kodan ya dace da duk wani mafarki nata akan Mijin da take so t aura ne oho?
Ahmad da kansa ya gane cewar akwai wani al'amari a gabanta wanda ya sake karkatar da hankalinta daga kansa saboda yar hirar da yake samun dama sunayi ma yanzu gagara takeyi, duk sanda ze kirata uzuri zata bashi na tana wani abun musamman da suka fara Second semester exam daga tace masa karatu takeyu se ta gaji zata huta alhalin lokacinta karankaf yanzun na Jay ne, karatun kansa ba wani mayar da hankali takeyi kamar da ba da idan akace zasu fara exam da sati Waya ma ta dena hawa Social media tattara hankalinta take tsaf har se sun gama sannan to wannan karon kuwa se a hankali, idan tana waya da Jay manta kowa da komai takeyi bata ma son abinda ze katseta se su raba dare suna magana har se da kansa yace ta kwanta tayi bacci dan bata faWa masa ma mun fara exam ba seda sukayi guda huWu ya rage uku su gama sannan ranar kuwa tasha fada ta kuma ?ara tabbatar da Jay baya Waukar nonsense dagaske kamar yanda yake cewa.

Har yajin kiranta yayi na wuni guda aikuwa taji a jikinta dan ya mata mugun sabo da soyayyarsa me tsayawa a rai. Jay ya iya soyayya, ya iya saka mace ta manta kanta duk taurin zuciyar Mace idan ta shiga hannun Jay tilas ta sallama dan yasan duk wani lago na mace da ze karya ta dashi, ita da kanta ta kance salon Jay da Ahmad yana kama. Tabbas da ta bawa Ahmad dama ta buWe masa zuciyarta ze mallaketa tsaf ta yanda wani baze samu matsuguni ba amma ta rasa abinda ya hanata yin hakan, ta yuwu dalilin zuwan Jay ne, wani lokacin se taji muryoyinsu har kamanceceniya yake mata kawai dai ta Jay tafi ta Ahmad tashi, haka idanunsu iri Wayane, seda tayiwa hoton Jay kallo na tsanaki ta fahimci haka idanunsu iri Wayane, shape Winsu, kalar kwayar idon da komai Badar tace mata wai Sexy Eyes kenan masu irin idanun sun iya soyayya kuma dasu suke cafke zukatan Yammata ta yarda da hakan dan bata iya haWa ido da Ahmad se taji gabanta na faWuwa duk sanda ta kalli idonsa ji take kamar ta sallama masa amma taurin kai irin nata ya sa har aka kawo i yanzu.

Saura kwana biyu su gama Exam ranar Ahmad ya kirata, kwana biyu ya bata space tunda tace masa Exam sukeyi idan ya kira bata Waga ba kota amsa ta bashi uzuri sosai ransa yake sosuwa shiyasa ya zaSi daya barta ta gama exam Win idan har da gaske itace uzurin daya saka baya samun lokacinta. Tana kwance duk batajin daWin dalilin yajin kiran wayar da Jay ta daka mata, tunda ya fahimci Exam suke kuma take wasa da karatunta tana biye masa shine yayi fushi. Ya gaya mata baya son mutumin da bashida focus, yana sonta amma baze taSa haWa lokacinta da Aikinsa ba me yasa ita zatayi wasa da Karatunta saboda shi?

Yace baze sake kiranta ba se sun gama kuma ta tura masa da Time table sannan idan ma ta kirashi baze amsa baz kullum da safe ze mata text haka da rana da dare amma babu phone call saboda magana dashi yasa takeji kamar wata mashashshara ce ta kamata duk ta rasa gane kanta. Tana ganin wayarta na ringing ganin Ahmad ne kamar ba zata amsa ba se kuma ta Waga dalilin tunanin da tayi a ranta, tabbas Alhakin Ahmad ne tun ba'a je ko ina ba Allah ya jarabceta da Jay.

A sanyaye suka gaisa daga ita harshi babu wani me karsashi,

"Yaya Exam Win? Saura guda nawa ku gama?" Ya kauda shirun da sukayi bayan gaisuwa ta bashi amsa a ta?aice da
"Lafiya lau, saura biyu"
"Masha Allah, Allah ya bada sa'a" daga nan suka sakeyin wani shirun. Ya sani idan zasu kwana a haka ba lallai ta sake cewa komai, wlh daze iya da ya rabu da yarinyar nan dan duk wata hanya da mace zata nuna bata ra'ayin mutum ta nuna masa amma zuciyarsa ta kasa ha?ura da ita. A kullum cikin Addu'a yake akan idan babu Alkhairi a tarayyarsu Allah ya cire masa ita daga zuciyarsa ya musanya masa da wadda ta fita amma abun kamar ana rura wuta ?aruwa yakeyi.

Idan Jafar yana bashi labarin sabuwar soyayyar daya gamu da ita se yace shi kam bashida sa'a ne a soyayya da Alama. Bega Yarinyar da Jay yake so ba, amma yanda har Jay yake labarinta ya sani ba ?aramin sonta yakeyi ba itama kuma tana riritashi, ze iya cewa be taSa ganin Jafar a yanayi na soyayyar gaskiya irin wannan ba, yace masa auran yarinyar zeyi, Bahaushiyace yar Nigeria a Zaria suka haWu. Ya?i ko gaya masa sunanta dayace ya tura masa hotonta ya nunawa Fatima ko ta santa nan ya fitittike ya ringa zuba masa Tijara yace kuma baze tura ba se ya dawo zasuje ya ganta face to face ko sunanta baze gaya masa ba balle ya faWawa Fatiman.
"Tana da Friends haWaWWu irinta zan samo maka guda Waya ka fita daga sabgar waccen Ajawon Fatiman da take wahalar da kai Yaya Ahmad" abinda Jay ya gaya masa.

Ahmad yaja numfashi, kusan minti bakwai daga shi har Fatima babu wanda yace wani abu. A sanyaye yace
"Fatima, idan wani laifi nayi miki kiyiwa girman Allah ki sanar mun na baki ha?uri, na gaji da azabatar da zuciyata da kikeyi kusan sati uku kenan kin hanani zaman lafiya nace zanzo kince Aa, idanna kiraki a waya koda yaushe cikin bani Excuse kike me nayi miki? Idan maganar kai gaisuwa da nayi ce kince Aa kuma na ha?ura bayan wannan wane laifi nayi miki da kike hukuntani ta hanyar azabtar da zuciyata haka?"

A maimakon ta sassauta se maganganunsa suka sake ?ukar da ita, ta tsani Namiji da bashida ra'ayin kansa se abinda mace tace yayi wannan yana daga abinda bata so da Ahmad yanda yake mata wani lako lako kamar ita ce Namijin shine macen, to tun yanzu baya iya taSuka komai daga abu ya haWa m
Su ya fara kamar zeyi kuka yana lallaSata idan sunyi auren kenan baze ringa tsawatar mata ba idan tayi masa laifi. HaWuwarta da Jay tasa ta ?ara fahimtar banbancin Namiji da muna Maza, duk yanda yake nuna So ta yake riritata idan tayi masa abinda be gamshe shi ba murWewa yakeyi ita ce zatayi ta lallashinsa da ban baki kafin ya sakko kamar dai yanzu daya yi fushi saboda bata maida hankali akan Exam Winta ba ta tabbata da Ahmad ne tsayawa zeyi yana lallashinta akan tayi kaza ko kartayi.

"Dan Allah Fatima ki tausaya mun. Na sani bakya sona Alfarma kike mun ina ro?on da ki daure kici gaba, ki dubi kalar jarabawar da nake ciki ta Sonki ki tausaya mun. Wlh Fatima da zan iya da tuni na cireki daga raina na rabu dake, koda baki taba buWe baki kin gaya mun ba nida kaina nasan bakya sona kina kulani ne kawai saboda wula?nta Wan Adam ba tarbiyyarki bace kuma na gode da hakan. Bazan gaji da ro?onki na akan ki bani dama, ki bude mun zuciyarki ko yaya ne in Allah ya yarda ba zakiyi nadamar tarayya dani ba" Ahmad ya sake faWa a sanyaye.

Zuciyarta tayi rauni da jin abinda ya ke cewa, wato shi da kansa yasan bata sonsa amma ya gaza ha?ura da ita tashi jarabawar Sonta ita kuma tata Son Jay Allah kenan.

Ajiyar zuciya ta sauke na shaking tace
"Nifa Ahmad ba haka bane ba, na gaya maka exam mukeyi ina bu?atar isashshen lokaci saboda nayi karatu shiyasa duk wani waya da wani chat na ajiye su amma mun kusa gamawa nan da Three days In sha Allah".
Yayi murmushi da jin abinda tace shima yace
"Ranar Thursday kenan zaku gama?" Ta yatsina fuska kamar yana kallonta tace eh, se ya sake cewa a sanyaye
"To yaushe zaki dawo Kano?"
"Paper safe ce, in har na gama komai kafin 12 ma zan taho a ranar in Allah ya yarda"
"To nazo na Wakko ki?" Ya faWa da sigar ro?o kamar wani me magana da ogarsa a gurin aiki, bata san sanda tsaki ya subuce mata ba tace
"Zan dawo da kaina, kasan Baffa ya hana ai ka ringa barin aikinka kana tahowa hidimata".
"Dan Allah Fatima karkice Aa kar kuma ki jingina maganar nan da Baffa sedai idan bakya sone kawai sena ha?ura" ya sake faWa gwanin ban haushi kuma ban tausayi kamar ze mata kuka, babu yanda ta iya haka ta yarda akan yazo ya Wauketa, ita kanta zata ji daWin hakan saboda hutun Session ne zata tafi da duka kayanta.

Ya ringa zabga mata godiya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login