Showing 126001 words to 129000 words out of 467220 words

Chapter 43 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12384

nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* >?t?>?t?
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*

*Siyan Nagari Maida kudi gida*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 30*

Se gurin sha biyu na dare suka samu sauqin Jamar da suka cika gidan maqil kamar wani sabon yinin biki akeyi,Binta na daki ita da Lantana da yau ta samu guri ga qugunta gana Binta akan Kujera tana bata shawarwari ita dai Binta jinta kawai take badanta fahimta ba, yanayin da take ciki yau din baze misaltu ba, Tashin hankali Kishiya biyu a rana daya. Bata iya runtsawa ba har gidan yayi shiru alamar kowa ya watse, maganganun habaici tasha su a waqe sedai wai yau ita Binta ta gagara yin gaba da gaba da mutanen da sukazo har gidanta suka takaleta da bala'i, yanda yan uwan Hadizan suka zo, dukda basu shigar mata ba waqe waqensu kadai ya sanar mata a shirye suke jira suke ta tanka musu su qaddamar mata dan haka ta kama kanta tana lissafin abinda zatawa Amaruar da zarar an watse domin ta rantse ba'ayi Macen da zata sha gabanta a gurin Audu ba, dole ta fita ta bar mata gida tun gabanin dayar da yake iqirari ta shigo.

Tana zaune tana gyangyadi Audu ya shigo, tayi firgigit ta miqe, Lantana dai tuni ta kwanta tana janna Rago taji Laushin Katifa ita ko tuna tana da Miji da yaya batayi ba ta baje a dakin Bintan.

"Bakuyi bacci ba ashe? Daman wasu kaya nazo dauka se gobe idan Allah ya kaimu zan shigo gidan" ya fada daga inda yake tsaye kafin kuma tace wani abu ya juya abinsa ya fice.

Washe gari ma haka gidan ya tashi da hayaniyar ?awayen Hadiza da suka kwana a gidan kamar wanda suka rako budurwa, tana jinsu suna cigaba da Habaice habaicen da suka fara jiya, gidanbe zama nasu ba se bayan la'asar zuwa sannan Yan Bechi sun tafi ?awayen Hadizan ma duk sun tafi gida ya rage Binta da Amaryarta dake can sama abinta. Audu be shigo ba se bayan sallar Isha'i, Ni?i Ni?i da ledoji yana daga labulenta ?amshin gasassun Kaji dana Tsire suka ziyarci hancinta dan ita din ba daga nan ba gurin iya tantance ?amshi. A tsaitsaye suka gaisa yace mata seda safe ya fita, data rasa abinyi se kawai ta dora hannaye a kai ta rushe da kuka.

Washe gari bayan data gama lallashinkanta ta kuma tsara yanda zata ci uban Amarya domin ance ba'a bori da sanyin jiki, ?arfe tara tayi wanla tsaf ta she?a kwalliya irin wadda ta manta rabon da tayita, ta kashe Wauri ta fesa Turaren da Mama ta bata sanda zasu taho, fuskarta fes amma da za'a tona ?asan ranta yafi gawayi duhu. Ta fito saSe da Naziru, tana fitowa tayi kyakykyawan gani, Amarya Hadiza cikin nata salon gayun ta fito daga tsohon kitchen Winsu na tsakar gida hannunta dauke da Fulas na ruwan zafi da kuma na Abinci.

Cikin taku me kama da rausaya ta kama matakalar bene ta haye abinta kamar bata lura da tsayuwar Bintan ba. Binta ta bita da idanu tana jin tamkar ta sha?ota amma ta cije, seda ta daidaici Hadizan ta isa saman har yaci ace ta zauna kafin ta yun?ura zata bi bayanta sallamar Lantana ta sake dakatar da ita.
"Yawwa, riqemun shi" ta fada tana mi?a mata Naziru ya lafe amma haka ta yakiceshi ta bawa Lantana ya kuwa tsanyara kuka amma bata dakata ba ta haye saman tana fadin
"Shegen Yaro me dafar tsiya".

Seda ta saisaita kanta ta gwada takun da zata shiga dashi kafin ta tura ?ofar ta shiga kanta tsaye ta durfafi dakin baccin Audu. Hadiza na tsugunne tsakiyar falon tana gyara zaman abin karin data ajiye musu tana kuma dakon fitowar megidan dake ?arasa shiryawa a ciki tajo an buWe ?ofa ta daga kai taga Binta ce bata kalli sashen da take ba ta wuce kai tsaye abinta zata shigar mata Waki babu shiri ta daka tsalle kafin Binta ta kai ga ?ofar tuni ta cimmata ta tare mata gaba cikin yanayina babu yabo babu fallasa take faWin "baiwar Allah daga ina?"

Binta ta kalleta she?e?e kafin tayi tsaki tace
"Ban gane daga ina ba? Kanki daya kike mun wannan tambayar ko kuwa baki san ni wacece ba sannan baki san cewar nan Win dakin Mijina bane?"
"?akin Mijinki fa? da alamu kece kanki yake da motsi a ciki shiyasa har kika gaza tantance a inda kike, to idan ma ada nan din ?akin Mijinki ne a yanzu ba nashi bane mallakina ne, sannan ko ace har yanzu yana mazaunin ?akinnasa bakida damar ko shiga tunda ina ciki, kwana nane dole ki jira harse randa na gama uzurina na fita kafin ki shoga ki shimfida naki mulkin" Hadiza ta mayar mata da martani cikin lafazin dake nuna daidai nake dake. Binta ta lafta mata harara tareda da jan dogon tsaki ta kauce mata ta kama mabuWin ?ofar tana cewa

"Idan na shiga se ki fiddo ni waje isashshiya me Waki" bata ko gama rife bakinta ba kuwa Hadizan ya fizgota ta maidota bayaz Binta tayi taga taga zata fadi ta kama bango, data tabbatar ta daidaita a ?asa ta shammaci Hadizan ta wats amata mari.

"Bantan uba, kika mareni? Wlh kin jangwalowa kanki masifa da bala'i se kin san ni kika mara" Hadizan ta fada a haukace kafin tayi ?asa, Binta na jira taga ko ramawa zatayi se ji tayi ta wawashi ?afafunta kafin tayi wani yun?uri ta kaita ?asa. Dambe ne rikica ya sar?e tsakaninsu, Binta nada garin jiki haka kuma tana da ?arfi amma naci da dakiyar zuciyar Hadizan tasa take neman cin galaba akan Bintan dan tunda ta fahinci ?afafunta nan ne Rauninta su take ri?ewa ta watsar da ita a ?asa ta hayeta ta kila idan ta mirgine ita ma ta sakata a Osi ta daka haka suke ta birgima a falon sun yi watsa watsa dashi labulen ?ofar dakin kansa yayo ?asa sun rikito da ?arfen.

Audu na bandaki ya ringa jiyo kamar hayaniya kamar kuma ana dukan Bango, ya bude ?ofa ya le?o da kunnensa dan son tantance daga ina hayaniyar take tashi idan ba gizo ba se yaji kanar daga Falo ne, ?arar fashewar abu dayaji Tusss ta sakashi rarumar Kwangorinsa ya Waura din daya jikinsa duk kumfar da be gama Waurayewa ba ya fito yana goge ta fuskarsa, yana buWe ?ofa ya tarar da dambaruwar da ake kwasa a falon, ?arar dayaji kuma Talabijin dinsa suka rikito da ita ta fashe basu ma lura dashi ba, seda ya buga musu tsawar da ta saka dole suka shiga taitayinsu sannan kowa taja gefe tana sauke numfashi kamar Zakaru.

"Wane irin hauka da dabbanci kuke mun a gida? nan Win sansanin dambe ne ko yaya? ke Binta me ma ya kawoki nan ma da farko?" Audu ya faWa cikin tsananin fushi yana kallon Binta dataji jiki dan gar bakinta ya fashe yana zubarda jini. Cikin kuka tace

"Bakaga abinda wannn mahaukaciyar daka auro a matsayin mata tayi mun ba se tambayata kakeyi meya kawoni dakin Mijina?"

"Wane Wakin Mijin naki? Ai kinsan banida wani Waki a cikin gidan nan yanzu. Banda fitina da son tayar da zaune tsaye meya kawoki? ki maza ki bar nan gurin kuma wannan ya zama kado na ?arshe da zaki sake tako ?afarki zuwa saman nan muddin bame dakince ta baki dama ba, fice Malama" Audun ya sake mayar mata da bacin ran dayafi na farko, Binta ta kalleshi ta kalli Hadiza dake sakin murmushin cin nasara wani kuka me tafe da zallar ba?in ciki da takaici ya zo mata seta wuce tana yinsa wiwi dan tasan a yanda ransa yake a Sacen nan idan ta tsaya zubar da mutunchin seyafi haka Hadiza ta bita da kallo.

"Ke kuma akan me zaki kamata da dambe?" ya maida dubansa ga Hadiza se tayi ?asa da kanta kawai ba tareda tace komai ba, yayi tsaki ya juya yaba ce mata
"Ki Gyara gurin kuma ki samarmun wani abun da zanci tunda kun lalata wannan"
"Yanzun kuwa in sha Allahu" ta fada tana du?awa ta fara tattare barnar da sukayi ranta ?al da beyi mata faWa kamar yanda yayiwa Bintan ba.

Binta kuwa seda taji kanta na barazanar fashewa kafin ta ha?ura ta dena kuka. Fuska tayi luhu luhu ga kuka ga Kutufon data sha a hannun Hadiza. Har mamaki takeyi yanda Hadizan da take gani tafi ?arfi ta lallasata tilas ta canza salo tunda dai a doke ita zata ji jiki to ita ma ta ?ar?ashin ?asa zata bi mata kamar sauran ta hanyar tuggu da munafunci dan ta rantse ba zata zauna ba Wayar ba zata shigo ta tarar da ita ba. Ta tafasa ruwa ta gargasa jikinta ta kwanta tana cigaba da ?ulle ?ulle a ranta.

Audu kuwa fes suka karya da Amaryarsa suna raha da jin dadi ya mata sallama ya fice ba tareda yako le?a ya gano halin da Binta take ciki ba. A haka yayiwa Hadiza kwana uku ya koma dakin Binta, a ta?in kwanakin nan kan Binta ta raina kanta domin duk wani tuggu da take jin ta iya Hadizan ta doketa ta shanye a kwana uku seda ta maodata abar tausayi a cikin gidan ta kankane komai ba ga me gidan ba hatta su Mairo se yanda tace dasu dukda daman Mairo bata da Matsala Lantana ce yar kwal uban kuma tun washe garin tarewar Hadizan ta saita mata zama data sakko da kwanuka Lantana na wanke wanake ta ajiye mata seta matsar dasu gefe bata wanke ba, bata kulata ba se da maigidan ya dawo har sannan kuma Lantana bata tafi ba taba daka dan yanzu ta zama ta hannun damar Binta da ita ake shawarta komai tunda basa haWuwa da Turai suna zaune Audun ya shiga ya cewa Lantana ta fice masa daga gida an sallameta. Binta tayi tsugul zatayi magana ya yarfata yace idan ta sa baki se tabi Lantanar tunda gidansa ne akan me Matarsa zata sakata abu ta?iyi Lantana ta ringa tumami tana ro?on ayi ha?uri dakyar ya barta bayan yaja mata gargaWi shikenan ta shiga taitayinta.

Kamar yanda Audu ya faWi kwanan Juma'a na zagayowa Iyalan Gidan Sarkin ?araye wanda suka samu rakiyar Ahalin gidan sarkin Kano dan can aka ajiye Amarya masu yi mata danki ne sukayi gaba suka dirarwa gidan Audu. Unguwa tacika ma?il ana ta kallon su masu busa Algaitu natayi. A cikin gida kuwa yai din ba Binta dake neman haukacewa ba su Turai na danneta hatta da Hadiza tasha jinin jikinta ganin wadda ake shirin kawo musu a matsayin ta ukun ta tabbatar wannan duk abinda suke ta?ama dashi ta damesu ta shanye, abun da ta sakawa ranta kuma suka shawarta da Yayarta shine ta zauna lafiya da Amaryar, babu ruwanta da shirginta muddin ba ita ta sanyota ciki ba domin fada da saraki babu riba.

Se bayan Isha'i Amarya ta iso bisa da rakiyar Gimbiyoyin Kano da ?araye da suka kawota. Dattijai ne na ?warai, dukda kasancewarsu sarakai sun san mutunci da darajar Dan Adam, sda suka shiga dakinBinta da kuma na Hadizan suka kai musu Amarya kamar yanda Al'adar Bahaushe take, kafin su iso Kano seda suka kaita Bechi gurin Dangin Audu suka kwana sannan suka dakko hanya washe garin suka iso Kano dan haka babu wanda yazo daga can.

Amarya na lullube cikin Alkyabba yar ubansu ?warjinin matan da suka rakota yasa su Turai suka kasa iya daga ido dakyau su kalle su bare su gano ya Amaryar take, Binta dai tana kwance dan ta gagara zama abin dai ba'a cewa komai aka gama musayar gaisuwa da Mi?a Amana suka wuce dakin Hadiza.
"Dukda ban ga Amaryar dakyau ba gani nake yarinya ce ma babu wani abu da ze firgitaki akanta Binta" Turai ta faWa bayan fitarsu. Binta tace
"Hmmm" kawai dan baki ya mutu.

An bar Amarya da kuyanginta guda biyu ragowar suka musu sallama suka wuce. Turai taso su le?a Amarya tunda yan rakiyar sun tafi amma Zainab tace Aa, su bari sa dawo takanas su ganta kawai hakan sukawa Binta sallama suka tafi. Ranar Ango be kwana dakin Amarya ba, nan dakin tsakar gidan dai ya shige abinsa ya kwana. Washe gari kafin sha biyu Kuyangin Amarya suka ?arasa mata gyare gyare sukayi mata sallama kamar yanda ta basu umarni su koma gidan sarki saboda Ango yace ayi masa uzuri base sun zauna ba da akwai masu taimaka musu da ayyuka har biyu anan gidan ya gayawa Yayanta Najibu kuma ya sanar da iyayensu suncr babu komai itama jiyan ya gaya mata shiyasa bayan sun kammala komai tace su wuce kawai.

Tun la'asar sakaliya Ango ya shige dakin Amarya wadda bata le?o tsakar gida ba balle mutan gida su ganta. Hankalin Binta yayi ?ololuwar tashi da jin Al'amarin daya auku, kasa zama tayi ta tafi tagar dakin Amarya ta dasa kujera ason jin me zasu tattauna daya shiga daki tun yanzu tsabar zirgilli se gashi ta jiyo wa kanta abinda yafi ?arfinta ta ringa kuka a tsakar gida jin Audu yana yiwa Amarya kyaututtuka cikin fitar hayyaci yace har gidan da suke ciki ya bata. Hadiza dake girki ta ringa wa Binta dariya kamar zata kife, faWi take "Allah ya ?ara, a garin gulma da munafunci zaki jiyo abinda ze toshe miki dodon kunne ki dena ji gaba daya"

"Idan baki rufe mun baki ba senayi ?asa ?asa dake Hadiza" Bintan ta zaburo mata. Hadiza ta gyara tsayuwa ta dafe kwankwaso tace
"Idan baki fasa ba Binta, ai kin san karon mu dake wancan da nayi miki kadan ne wlh yau sace ki zanyi tas dan naga wannan luhu luhun jikin naki yasa kike neman masifar mutane"

"Zaki gane kurenki wlh dani kike magana" Binta ta maida mata tana shigewa daki dan ba hauka takeyi ba da zata sake gwabza dambe da Hadizan har yau bata gama jinyar ?asusuwanta data tasamma karya mata ba.

Haka Ango ya yiwa Amarya sati guda, rawar kan da ya ringayi ba Binta ba Hadiza kanta ranta ya sosu amma da yake ita tana da kissar zaman duniya seta shanye bata ko nuna a fuska ba wannan tasa Audun yake ta tata ya kuma hadata da Amarya a cewarsa ta zama ?anwarta ta ringa kula da ita Binta kuwa data tayar masa da hauka fita yayi a sabgarta ta nemi shiga sabgar yar Amaryarsa da banda gaisuwa da murmushi babu abinda ke hadata da mutanen gidan nan ya nuna mata ya fita hauka.
"Wlh ko bisa kuskure naji hannunki ya taba jikinta se kin gane baki da hankali" ya faWawa Binta sanda tayi niyyar marin Aisha lokacin daya hadasu su ukun.

Haka aka ci gaba dagurgura rayuwa, watanni uku Bi ta ta tayarwa da Audu zancen ya kamata a Webo yaran Bara'atu da Tagwayen Zubaida su dawo gida kodan saboda makaranta dan a yanzun ta dan rage abubuwa a ?o?arinta na son maido da darajarta data zube a idona Audun. Ya kuwa ji dadin maganar harya zanta da Hadiza da kuma Aisha. Hadiza tace zata ri?e su, zata karbe kayansu tunda daki daya ne da ita ba ze yuwu su ringa kwana can ba se su zauna nan dakin da Abdullahi yake amma Binta tayi tsallen Albarka tace ba'a isa ba. Ai ita ta tado da maganar a dakko su kuma ita ta zauna da uwarsu ita suka sani sannan itace babba a gidan dan haka ita zata ri?e Yaran. Daman ita Aisha yar kallo ce a tsakaninsu, idan ba an sako ta ba tafi ku mutu bata ce musu, seta wuni a daki in har ba ita take da girki ba shine zata fito Mairo tanayi tana kallo harta fara karban wasu abubuwan tana tayata dan a gida bata girki kusan yanzu ne ya kamata ace an fara sakata ire iren wadannan ayyukan se kuma Aure yayi mata sammako shi yasa koda suke rigimar waye ze ri?e yaran bata saka musu baki ba ?arshe da Audun da kansa yace Binta ce zata ri?e yara haka kuwa akayi ya debo su suka dawo gidan, an musu nisa a makaranta wannan tasa aka sake maidasu baya Zakariyya ya wucesu se aka hadasu su biyar harda Naziru aka saka su.

Zama yaci gaba matayen uku suka samu ciki kusan lokaci daya, Binta bata lura da cewar sauran biyun duk sun samu ?aruwa ba domin a duk sallar da zatayi se tayi addu'ar Allah yasa duk su kasance juya basa haihuwa ita kuma Allah yasa duk shekara tayita haihuwar Yara Maza ta cika gidan dasu tana ta kaWifiri da iyayi wai ita me ciki bata san su biyun ma sun rigata samu ba se randa zataje Asibiti ta fito ta gansu duk su biyun kowa da shirin fita, bata ta Aisha domin tunda ta ganta tace wannan me sau?i ce Hadiza ce a gabanta dan haka ita ta harara tana cewa

"Karma ki kuskura kice yau ma binmu zakiyi, ba zaki tashi fita ba se kinga zan fita da Mijina to se ki taka ?afarki ko ki fita ki hau Bus"

"To ai yau ba ranar girkin ki bace balle ki nuna mun isa da iko, Miji kuma namu zakice dan bake kadai kike dashi ba" Hadiza ta maida mata. Aisha na gefe tana kallonsu bata ce uffan ba sema lafewa datayi jikin katanga tana kallonsu sega Audu ya fito

"Uhm Bismillahi zaku fara ba kudai se kace kajin hausa wlh baku da aiki se faWa ce cacar baki Allah ya sawwa?a muku" ya faWa yana baza babbar riga. Binta ta tunzura dan ta tsani wannan wula?ancin da yake mata a gabansu ya ringa nuna ita ba komai bace daidai suke da ita dan haka tace

"Idan ma fita zatayi ka gaya mata ko ta taka ?afarta ko kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login