Showing 420001 words to 423000 words out of 467220 words

Chapter 141 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12395

?o?ari yayi ba gurin danne Sacin ransa yake acting calm. Ya saci kallonsa dashi da Dr Ashir Win duk ita suke kallo, kamar wata munafuka ta juya a hankali ta nufeshi, nesa da inda yake ta tsaya kanta a ?asa tana sake ri?e jakar hannunta. Jay ya kalli Dr Ashir dayayi fakare yana jiran yaji ala?arsu da Fatima, yayi taku biyu ya cike sararin dake tsakaninsa da ita, ta zabura zatayi baya ?afarta ta gurWe hakan yasa ta tafi kamar zata faWi cikin azama ya tarota jikinsa ba tareda wani tunani ko shakkar komai ba kuma ya haWe bakinsa da nata.

Yanda kasan wanda aka tsura haka Dr Ashir ya shiga wulga ido yana duba cikin layin da yake shiru tamkar anyi ruwan sama iya kacinsu ukun ne a tsaye, ya kalli Jay daya saki Afeeyah amma nauyi da girman al'amarin dayayi mata ya saka ta gwammace ma?alewa a jikinsa akan ta buWe idonta. Tana jinsa cikin dasashshiyar murya yacewa Dr Ashir
"Kana bu?atar wani bayanin ne kuma?"
Ashir ya girgiza masa kai alamar Aa dan ya shiga ruWani baze ma iya magana ba.
"Ware" Jafar Win ya sake faWa yana nuna masa hanya da hannu Waya, Wayan kuma ya tallafe Afeeyah dashi. Ashir ya fara tafiya yana waiwayensu, harya buWe motarsa Jay ya sake tsayar dashi ta hanyar ce masa
"Nayi maka uzuri saboda nasan baka san ita Win tawa ce ba, idan har ka sake kuskuren koda yi mata kallo biyu ne a rayuwar ka, i will surely make you regret that".

Kai kawai Dr Ashir ya ringa gyaWawa kamar ?adangare ya shige motarsa yayi reverse zuciyarsa cike da tunani kala kala. Kenan Fatima matar aure ce all this time yake bibiyarta? Ko kuma daga baya tayi aure be sani ba? Shidai iyakar binciken sa akanta ance mijinta ya rasu yanzu shi kuma Jay wanene a gurinta haka? Bashi da me bashi amsa dan haka ya bar maganar a ransa har se yaje makaranta gobe ze tambayi ?awarta guda daya Fa'iza kenan.
*************************************
Seda ya dena hango motar Dr Ashir kafin ya tunkuWe ta daga jikinsa har ta kusan faWuwa Allah yasa ta tsaya da ?afafunta. A fusace ya shige gidan Sauda mr gadi dake laSe yana kallon komai yayi saurin buWe masa ?ofar. Motarsa ya shiga a tsiyace ya fito da reverse tana tsaye har sannan ya tsaya daidai itavya sauke glass Win Sangaren da take murya kamar an masa dole yace mata
"Get in side"
Ta kalle shi ta Wauke kai, se lokacin ta samu ?arfin guiwar barin gurin tayi taku Waya biyu kafin ta aje na ukun ya fafara mata tsawar data saka bata san sanda ta buWe motar ta shiga ba. Ya saka kanta tsakanin cinyoyinta yanda yake fella gudu akan titi ya tabbatar mata da ransa a Sace yake matu?a. ?arar watarsa ta katse shirun da motar tayi, ya Waga ya sakata a speaker, muryar Sarah ta ratsa kunnensu tana cewa
"Yaya baka dawo har yanzu"
"Na Wan yi nisa ne Sarah amma ina hanya, ya jiki nata?" Ya bata amsa yana sassauta muryarsa daga can tace

"Ai an sallameta ma yanzun muka dawo gida da Baba Al?ali yaje shine suka dawo damu da direbansa"
"Oh, toh bari zanzo gidan yanzu" ya sake faWa daga nan ya katse wayar sega wani kiran harya kai hannu ze katse shi yaga Baba Al?ali ne hakan yasa ya daga murya ba amo ya gaishe shi, daga can Sangaren cikin raha Al?alin yace
"Angon kasha ?amshi. Wato muradi ya cika babu wanda ka nema kayi masa bangajiya balle aje ga godiya ko? Toh in ma baka zo dan Allah ka gaishe ni ba kaz?????#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#$o ka kawo mun kuWi na dana ranta na biya maka sadaki dan Babanka cewa yayi a Waura bashi ka biyata idan tazo se ku warware, to ina bu?atar yan canji na a kawo mun su yanzu".

Murmushi Jay yayi ya saci kallon Afeeyah kafin yace
"Ina hanya zanzo yanzu"
"Allah ya kawo ka lafiya" cewar Al?ali daga nan ya katsewar shi kuma Jay ya kashe tasa gaba Waya dan kar wani ya sake kiransa har suka isa gidan Al?ali kuma ko tari babu wanda ya sakeyi a motar. Seda ya gama daidaita mota a gurin ajiyarta ya kashe kafin ya kalleta yace
"Muje" ta Waga kai ta kalleshi idanuwansu suka sar?e cikin na juna, tsayin minti biyu kafin ta janye nata da?yar saboda yanda ta ringajin kamar wani mayen ?arfe ne ya ri?e idanuwan nasu. A hankali ya saka yatsunsa biyu ya Wago haSarta, ya gyara zamansa ta hanyar matsawa sosai kusa da ita har suna musayar numfashi, murya ?asa ?asa kamar me raWa yace mata
"Ina da kishi kuma kin sani, koda wasa karki sake maimaita abinda ze motsamun shi, be it intentional or not ok?"

A hankali ta Waga masa kai saboda kusancinsu yayi yawa so kawai take ya matsa ko ya barta ita ta matsa. Ta rintse ido da sauri sakamakon saukar ji?a??un lips Win sa da taji a goshinta ya sakar mata peck daya bada sauti me ?ara sosai, ba zato kawai yaga hawaye na bin kuncinta. Ya saki fuskarta ya buWe ido da mamaki yana kallonta kafin yace
"Cizonki nayi kome?" Ta?i cewa komai sema kukan data ?arawa ?aimi harda shashshe?a mamaki da takaici suka kamashi lokaci Waya be san sanda ya balbaleta da masifa ba yana cewa
"Saboda na miki magana ta laluma shine har kika samu bakin yi mun kuka ko? Shi Wan iskan da kika hau motarsa yana wani kallonki kamar ze cinye idan nayi muku Allah ya isa dake dashi ai kin san zata biku ko? Amma banyi ba na yafe miki kawai dan na tuna miki bana son haka shine zaki mun kuka kada ki bari, ki jawo nayi miki abinda zakiyi kuka sosai Aafeeyah keep trying me" yayi ?wafa ya fita daga motar ba tareda ya sake kulata ba.

Yana fita ta haWe kanta da guiwa taci gaba da rera kuka kamar wadda ya doka kewar Ahmad me tsanani ta taso mata. Batavirga sau nawa a rana yake sumbatar goshin ta sannan ya kalli idonta yace
"Ina sonki Fatima". Yanzun da Jafar yayi mata hakan jiki da zuciyarta Ahmad suka hakaito mata jira kawai takeyi kalaman daya saba furta mata su biyo baya amma taji akasin haka tunawa da waye a gabamta ba wanda take tunani bane ya sakata kukan ta ringayi babu ji babu gani.

Al?ali ya kalli Jafar bayan ya gama sauraron tsarin da yakeyi masa yace
"Duk yanda kayi daidai ne amma dai ka dubi maslahar da ba zata Sata ran mahaifiyarka ba kodan halin da take ciki a yanzu. Sannan itama be kamata ace baka kira ba tun a jiyan, ko babu komai matarka ce kuma an mata abinda ya cancanci tayi fushin ne se a lallaSa ta a bata ha?uri har ta dangana. Ka kirata sannan ka shirya kaje tunda har mahaifinta ya kira waya, ita ma kuma kayi azamar sama mata guri ta tare kar kace zaka ja wani lokacin hakan ne ze kashe bakin tsanya kowa yaji shiru. Me wuyar ta rigada ta afku an Waura aure se muyi fatan Allah yasa hakan shi ya fi Alkhairi ga rayuwarku baki Waya. Ina ganin abu mafi sau?i ta dawo nan gidan ta idan yaso ayiwa gurin kuWi ka ringa biyansu haya kaga an raya gurin ba'a barshi ya mutu babu kowa a ciki ba".

"Ina cikin wannan shirin ai Baba dama akwai ginin da nakeyi da su biyun zasu iya zama a ciki, aikin dai da saura dan dama lissafin da nayi idan an bi komai a hankali har zeyi daidai na kammala ginin lokacin to kuma ga yanda komai ya kasance, kamar dai yanda nace kawai se mun dawo, zan saka ayi speeding aikin ta yanda zuwa sanda zamu dawo komai ya kammala. Bazan iya zama a gidan Yah Ahmad ba itama kuma nasan ba zata iya ba" Jafar ya faWa kansa a ?asa. Al?ali yayi dariya yace
"Oh Jafar Wan gatan Alhaji, banda kai waye Audu zeyiwa wannan ya?in?"
Yayi murmushi ya mi?e yana cewa
"Bari nace ta shigo ku gaisa". Al?ali ya buWe baki da mamaki yace
"Dole ko Malam Hafizu yace yin shine alkhairi"
"Bafa abinda kake tunani bane wlh Baba" Jafar yayi saurin faWa yana Waga hannu sama. Al?ali ya tuntsure da dariya kawai shi kuma ya fita. Tunanin baya yayi lokacin da Ahmad ya ringa zaryar zuwa gurinsa akan zancen aurenta har zuwa bayan auren irin zazzafar soyayyar daya ringa nuna mata. Abinda yake gani yanzu akan Jafar bayan ishara da ubangiji ya nunawa Hajiya Binta akan abinda ta raina yana gani harda ?a??arfar soyayyar jini dake tsakanin Ahmad da Jafar tasa zuciyoyinsu sukayi tarayya gurin son abu Waya.

Jikinta ya Wauki rawa ganin sun shiga layin gidansu, tunda suka baro gidan Al?ali ta juya masa ?eya tana kallon window dukda shima be kulata ba seda ta gansu cikin BECHI STREET kafin ta juya da sauri bakinta yana rawa ta fara masa magiya amma funfurus kamar tanayi da stirring motar be kulata ba. Hawaye suka shiga mata tsere, da?yar ta iya shiga ta gayar da Baba Al?ali shida ta san tsakaninsu babu komai se girmamawa tayaya yake tsammanin zata iya taka ?afar ta cikin gidansu a yanzu a matsayin matarsa?
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 42*

A ?ofar gidan yayi parking bayan ya dakatar da security daya tashi ze buWe masa ?ofa. Ya cire babbar riga da hular jikinsa ya ajiye a kujerar baya kafin ya fita daga motar ba tareda yace mata komai ba tana hangoshi har ya shiga gidan bayan daya gama gaisawa da waWanda suke zaune a wajen ta sauke ajiyar zuciya a fili sannan ta kwantar da kujera yanda zataji daWin kishingiWa, gajiya da baccin bata da bata samuyi ba jiya suka mata rubdugu, ga sanyin Ac daya cakuWa da ?amshinsa me daWi da sanya zuciya nishaWi, kafin kace me bacci ya kwasheta a gurin ba tareda ta sani ba.

Hajiya na kwance akan gadonta bayan Sarah ta kai mata abinci taci tasha magugunanta. Tunda suka koma gidan bata cewa kowa komai ba, da Momy da Hajiya Rabi harda Baba Bilki da ta dawo jiya suka shiga yi mata ya jiki ma ko kallonsu batayi ba. Seda Baba Bilkin ta takaleta tace
"Se kuma mukaji abin murna, ai da nasan da wannan sha'ani ina zan tafi in shantake a Bechi? Da bari nayi se randa uwarsu Usaini zata tare sannan mu taho duka da yan karSar amarya amma su Balarabe na komawa da suka bamu labarin auren Jafaru ba shiri na haWo Jaka. Ai abu yayi daWi Alhamdulillah dama sun dace sedai muyi fatan Allah ya tsare ya tsole idon ma?iya".
A fusace Hajiya tace mata
"Sedai ya tsole idonki Bilki. Banda gulma sa munafunci akwai wadda na kira a cikinku ne? Wato da ba'a shigo da gawata yanda kukayi fata ba shine zaku haWo kai kuzo, to aniyar kowa ta bishi" ta juya musu baya tana kumbura kamar balloon. Momy da Hajiya Rabi suka mata sallama suka fice, Baba Bilki kuwa gyara zama tayi ta cigaba da takalarta da magana wai ya akayi bata ga kowa a danginta ba kodai bata sanar musu da abinda ya faru ba? Ita dai hajiya bata kuma tanka mata ba daga ?arshe ta cicciSa ta shige Waki se lokacin Baba Bilkin ta fita tana dariya abinta.

Jay ya tarar da Sarah a falo tana waya yarinyarta Farha ma bacci a gefenta ganinsa yasa ta yanke wayar da sauri tana goge ?wallar data zubo mata sedai ya rigda ya gani. A sanyaye ya ?arasa kusa da ita ya zauna yana tambayarta ina hajiyar tace masa tana ciki.
"Me kuma ya faru kike hawaye?" Ya tambayeta kamar tana jiran haka ta fashe masa da kuka, jikinsa yayi sanyi ya jata jikinsa yana bubbuga bayanta ba tareda yace mata komai ba har tayi me isarta murya na rawa tace masa
"Auwal ne, munyi dashi akan zan kwana saboda jikin hajiya kawai kuma yanzun ya kirani yana zagina kuma wai idan na ?ara minti ashirin banje gida ba kar in dawo ya sake ni". Ya buWe ido da mamaki ya kalleta yace
"Ban gane ba, wani abun kikayi masa da zece haka ko yaya?"
Ta share hawayen fuskarta tace
"Banyi masa komai ba wlh, ai ka gani shiya kaini asibin ma da safe da kansa kawai dai ?ila yaje gurin hajiyarsu shine zata zugashi tunda dama duk yawancin rigimar da mukeyi ita ce take haWawa. Bata ?aunata kullum bata da wani buri illah ta kunna fitina a tsakaninmu yayi ta zagina yana cimun mutunchi kuma idan nace zan gaya muku ko na kai ?arar sa gurin Baba Al?ali hajiya ta hanani. Ni wlh na gaji Yaya, bazan iya irin rayuwar da Hajiya ?arama takeyi ba. Ita dama zaSin ta ne kuma taga zata jure duk wahala ta zauna dashi gaskiya ni bazan kassara rayuwata ba dan dama dole aka mun bada son raina na aure shi ba. Ina da me sona tsakani da Allah dana san ko yanzu na rabu da wannan ?addararren auren yana jirana. Na gaji da zama da Auwal da mahaifiyarsa ka taimakamun in dai ba so kuke ba?in cikinsu ya kashe ni ba".

Kafin ya ce mata wani abu suka jito muryar hajiya a fusace tana cewa
"Sedai kuwa ki mutu wlh akan dai ki kaso aurenki ki dawo cikin gidan nan. Wato duk abinda zan muku a duniya a maimakon ku gode mun sedai kuce na cuceku? Da nayi miki gata na samo miki miji irin na sauran yan uwanki shine har zaki ce tilasta miki nayi se kace kina raba daula da arzi?in da kike ci tare dani".

Sarah ta fashe da kuka tace
"Me nake ci a gidansa wanda ban samu a gidan ubana ba? Dame Alhaji ya rage mu? Na rasa wane arzi?i ne ya tsole miki ido da har kika zaSi jefa rayukanmu cikin ?unci dukda hakan kuma bamu kama ?afar su waWanda kike so mu kamo Win ba. In da kin bari mun auri nagartattun mutanen da suka zo suna son mu duk ba haka ba, kin biyewa rayuwar ?aryar da kika gani wadda babu kwanciyar hankali a ciki duk mu uku ace babu wadda za'a Waga ace gara matsalarta data wata? Wlh ni dai an cuceni bazan dena faWa ba da wannan auren gara ace na ?are rayuwata a gida kuma yanzun ma bazan kom ba na yarda ya sakenin ya fiye mun alkhairi" ta saSi yarta ta wuce Wakin ta na yammatanci tana sharSar kuka.
Zama hajiyar itama tayi ta fashe da kuka tana kallon Jay daya dafe kai tace
"Da wanne zanji? Ubanku yayi aure, kai ka auri wacce bana ?auna sannan yanzu tace zata kashe aurenta ta dawo ta zauna mun ni zata sake janyowa abin kunya wa taga ta taSa zuwa gidan nan da sunan yaji cikin yayansu Aisha balle zawarci?" Ta shiga tari har tana dafe ?irji ba kuma ta bar kukan ba. Cikin tsananin damuwa Jay ya koma kusada ita ya ri?e ta yana cewa

"Dan girman Allah hajiya ko dan lafiyarki ki dena saka dakuwa a ranki. ?azu fa kika fito daga asibiti kuma na tabbatar kawai sallamarki sukayi badan kin samu ishashishiyar lafiyar da zaki dawo gida ba dan Allah kiyi shiru". Kamar yar yarinya ta Wora kai a kafaWarsa taci gaba da kukan yana mata magiyar tayi shiru da?yar ta tsagaita saboda ?irjinta da yayi mata nauyi dalilin tarin da take tayi. Ya tashi ya Webo mata ruwa ta karSa tasha kaWan kafin ta zame ta kwanta tana numfashi sama sama tana jan hanci. Ya dur?usa a gaban kujerar da take yana cewa
"Dan Allah hajiya ki bar komai ya wuce a zuciyarki. Abinda be faru ba shi ake inkari akai amma ?addarar data rigada ta afku ha?uri akeyi da ita a rungume ta.
Bana jin daWin yanda komai aka tashi za'a ce ke a gidan nan, duk wani abun rashin jin daWi akanmu yake daga Wakin nan yake fita dan Allah hajiya kiyi koyi da sauran matan gidan nan. Ba damuwa kika fisu ba, yanzu ita Momy Wa fa ta rasa kuma wanda tafi so amma tayi ha?uri ta fawwalawa Allah komai"

"Ai duk mutuwar Ahmad ita janyo wannan bala'in da nake gani. Idan da yana raye ai da baka auri wannan shaiWaniyar yarinyar irin mayu ba, da be mutu ba ai ubanku baze takalo dawo da Zubaida saboda ya ba?anta mun zuciya ba kuma kaima da baka dawo ka zauna ana ganinka har a asirce ka a juya maka tunani akaina ba. Ban taSa zaton ko duk yaran nan zasu juya mun baya kaima zaka mun haka ba Jafar, amma se gashi a sanadinka naga ba?in cikin da zan mutu dashi. Gudan jinina ya auri yar matsiyata yar bakanike ba?in haure da ba'asan asalinsu ba. A da bani da wani buri irin naga jininka Jafar, ina burin naga yayan da zaka haifa amma a yanzu ina addu'ar idan har rabon haihuwa ne tsakaninka da yarinyar can yanda ake cewa Allah ya kaWar dashi. Gara ka dawwama a juya karka haihu da dai ka gurSa mun zuri'a da mugun iri" hajiya ta faWa. Jafar ya zabura daga tsugunnen da yake yana kallonta yace
"Haba hajiya, ashe bakya sona dama? Hajiya kin manta ke mahaifiyata tace? Kin manta kalamanki suna da kaifi akaina yanzu idan yan Amin suka amsa fa? Shikenan se in rayu in koma ga Allah ba tare da na bar wanda ze ringayi addu'a ba? Bakya so na mutu na bar abin za'a ringa gani ana tunawa dani kenan?"

"In dai da wannan yarinyar ne gara ka mutu baka haihu ba Jafar, ai kana kyauta kama sadaka. WaWanda ka kyautatawa a rayuwarka zasuyita yi maka addu'a kuma zata sameka har kabarinka ba lallai se ka haihu ba. A ta?aice bari ma na gaya maka, abinda zakayi mun kenan na huce ko da zaka rayu da Fatima to ban yarda ka haihu da ita ba" Hajiyar ta sake faWa with straight face bayan ta tashi zaune. Fuskar sa bata Soye firgicin da kalamanta suka sakashi ba, ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login