Showing 288001 words to 291000 words out of 467220 words

Chapter 97 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12230

ya fita da ita. Me gadinsu da zuwan Jafar Win ne yanda ya buga ?ofa yana nan tsaye yana ta faman zare ido se gashi ya fito da Fatima wadda yake jiyo nishinta tun daga nisa cikin tashin hankali ya buWe masa mota ya sakata kafin ya buWe masa get Win ya fice cikin matsanancin har yana kusan ture megdin can babban Gate Win shigowa layin. Asibitin, besan Asibitin da take zuwa ba dan haka ya nemi wanda ya fara cin karo dashi bayan daya hau titi ya kaita, tare sukasha gumurzun kamar ma ya manta matsayin ta a gurinsa cikin ikon Allah a ?asa da awa guda da zuwansu ta sauka, ta samu tagwaye duka mata kukan jariran daya karaWe kunnuwansu ya maido dashi ainihin hayyacinsa harya fahimci shirmen daya tafka, suluf ya silale ya bar Labor room Win wani abu da baze iya fassarawa ba yana mamaye zuciyarsa. Seda Nurse ta biyoshi tana tambayarsa kayan da za'a sakawa babies kafin ya tuna irin fitowar da sukayi, ya tambayeta ko nan kusa akwai inda ze samu 24hrs Mall yaje ya siyo dan basu fito da shirin komi ba.

"Karka damu munada kaya a nan saboda irinku, duk abinda suke da bu?ata za'a basu se a shigar maka a bill ina dai jiran goron Albishir tabarakallah masha Allah kuma duka yaran kai sukayo hasken fatar ne inaga da gashinsu irin na uwar" Nurse ta faWi tana murmushi, murmushin ya mayar mata shima kafin yace
"Karki damu keda kanki zaki zaSi abinda kike so"
"Selfie kawai zamu Wauka tare ni ya isheni tukuici" ta sake faWa tana zaro wayarta, se a sannan tunanin yazo masa yayi saurin ce mata
"Kar wadda ta Wora mana yara a social media ki gaya musu"
"Ai kam bari nayi sauri naje Allah yasa qta batayi karambani ba" ta faWa tana juyawa ciki da sauri.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina bayannsa da bango fuskar sa bata Soye farincikin dayake ciki ba, Yah Ahmad ya haifi tagwaye burinsa ya cika,
"Allah yasa kamarsu Waya" ya faWi a fili, tunanin kiran Ahmad Win yayi se sannan ya tuna da ya bar wayarsa a motaseya tashi da sauri ya tafi ya Wakkota nan ya tarar da tarin missed calls na Ahmad, Fatiyyah harda Hajiya.

Ahmad Win ya kira dan Hajiya yasan kwanan zancen baze wuce Fatiyyah ta kirata bane shine ta kira tayi masifa.
"Kana ina? Me yasa ka kulle matarka a gida wacece takiraka?" Ahmad ya jefa masa tambayoyin a jere bayan daya amsa kiran
"Oh ta kiraka kenan? Amma yarinyar nan bata da hankali. Ta kira Hajiya ma fa dan naga missed calls Winta ita bata san dare ba zata fara kiran mutane tana musu shirme? ni bama maganar ta ya saka na kiraka ba, ka kunna Datan ka yanzu i have a surprise for you" Jay ya bashi amsa. Ahmad yaja tsaki yace
"Banason shirme, tsakanin kai da ita ai a nemi me hankali. Yanzu Jafar ?arfe Waya wata random mace ta kiraka ka tsallake matarka ta sunnah ka fita sannan ka kira kana mun wani shirme wane banzan surprise zaka bani? Afeeyan data kiraka kake so ka nunamun ko menene? To tun da wuri ka bar koma wacece kake tareda ita ka koma gida kafin ranka yayi mugun Saci dan matarka ta kira Hajiya ta gaya mata kuma kasan halinta."

"Dan Allah ya Ahmad ka rabu dasu ta daWe bata kira Hajiyar ba just come online please" ya katse Ahmad be kuma bashi damar cigaba da faWa ba ya kashe wayar. Ahmad da ransa duk a Sace yake ya jefar da tasa wayar ya kwanta ba tareda ya kunna data kamar yanda yace masa ba, dole ma ya binciko wacece wannan azababbiyar Afeeyar da Jafar ya haukace akanta take neman hargitsa masa gida. Shi har ya fara tunanin ma Aljana ce, idan ba haka ba matar da yace tayi aure meye zata kirashi cikin dare kuma?
Har ya fara bacci bayan sun gama magana da Fatima Fatiyyah ta kirashi tana kula wiwi akan Afeeyah ta kira Jafar ya fita kuma ya kulleta a cikin gida yace tayi ha?uri ze kirashi yanzu yayi ta kiran wayar kuma tana ringing ba'a Wagawa.

Jafar yayita gwada kiransa Online bata shiga, ya taSe baki yace
"Oho nadai rigaka ganinsu kuma ni zan fara Waukansu, se kuma gobe tayi kazo kana masifan me yasa ban gaya maka ba. Ya duba agogo, ?arfe uku saura lokacin be kamata ya taso kowa a sannan ba gara kawai da safe seya kira can gidan ya gaya musu su kuma su kira yan uwanta. Yana nan zaune seda suka gama shirya yaran tsaf tareda Mamansu kafin suka bashi izinin shiga ya gansu a Wakin hutun da suka kaita. Ya shiga da sallama ciki ciki, Fatiman na kwance ta zubawa yaran dake cikin gado daban ido tana kallonsu, duk scan Win da tayi babu wanda ya taSa nuna yan biyu ne a cikinta yarinya Waya suke shirin tarba se gashi ubangiji ya basu biyu a lokaci guda. Yaran nata wutsil wutsil a cikin gadon abinsu gwanin sha'awa, kamanninsu Waya kuma Ahmad suka biyo hasken fatarta kawai suka Wauka da kuma yanayin gaSSansu da alamu irin jikinta zasuyi. Ta saki murmushi a ranta tana ayyana ya Ahmad zeji wannan abin mamakin? Ta haihu baya nan kuma yaya biyu?

*ASSALAMU ALAIKUM JAMA'AR ANNABI*
*Kun sai dai bana kawo muku tallahn hajar banza, to ku marmatso yauma tafe nake da abin arzi'qi niqi niqi*

*Shin kina sha'awar fara sana'ar kayan makwalashe dangin cake musamman me farfesun madara?*

*Ko kuwa kina cikin sana'ar kina neman yanda zaki sake bunqasata kuma kina buqatar sabon signature recipe na Milk cake wanda kasuwarsa take ci a yanzu ta yanda duk inda aka dandanashi za'ace wannan cake din wancece?*

*Shin Matsakarki rashin customer ce ko kuwa kin kasa gane kan sana'arki ta cake kudi kawai kike narkawa amma babu riba??*

*To su Binta a marmatso domin damar da kuke jira ce tazo har qofar gida. Shahararriyar me harkar kwalam sa makwaleshu fannin Cake wato MCUBES BAKERY musamman me farfesun Madara (Milk cake) tazo muku da MILK CAKE MASTER CLASS. kar kiji ance master class ki dauka na wanda suka rigada suka iya ne suna neman qarin ilimi, Aa ajin nan na kow ada kowa ne domin zata faro komai ne daga Basic ta yanda zaku samu gamsashshiyar fahi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mtar*

*This is a money back guarantee class! We will not let you go till you are satisfied with the class. The milkcake that make a statement...99.9% positive review...no fails. Get into the milk game with the best milkcake in kano WE ARE READY TO TAKE YOU ON THE BEST EXPERIENCE <؉?=?O?*

*Ina masu son su koya perfect milk cake koh kuma suyi upgrading recipe dinsu toh kuzo kuyi joining class din mu yanzu! It s money return granteee! Improve your business now by joining us!*
*Ga promo kuma*
*15k early bird !*
*20k Reg Fee!*

*Limited spots available, DM to reserve yours.*
*http://Wa.me/2348134606093*

Group enter the link below +?

 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/BAY5WE5skLg0N9rf8x3gcW

*INA FATAN BAKU MANTA DA CAKE DIN NAN DA UMAIMAH TAKEYIWA KHALIL BARAZANA DASHI BA, TO A GURINTA TAKE YO ORDER, KU DAI KARKU BARI WANNAN GARA BASA TA WUCE KU*

Sallama tareda motsin shigowarsa yasa ta juya se a sannan ta tuna tare dashi sukaje Asibiti. Ta gyara kwanciyarta tana jan abin rufar dake kan gadon da take dan maternity gown ce a jikinta bata wuce ?wauri ba.
"Sannu" ya faWa kamar wanda aka cusawa tsumma a baki ba kuma tareda ya kalleta ba ya wuce inda yaran suke tanajinsa yayi bismillah a fili dan haWama duk su biyun ya Wauka ya rungume harda wani lumshe ido se kace nasa. Yafi minti biyar dasu a ?irjinsa kafin ya matsa inda doguwar kujera take ya zauna har sannan yana ri?e dasu, ta saci kallonsa, fuskarsa a washe har ha?oransa sun bayyana yayi pecking kumatun kowacce kafin taga yana motsa baki can kuma ya shiga tofesu da yawu, ko me ya karanta se Allah ta raya a ranta kafin ta lumshe idonta saboda bacci me cike da gajiya dake neman fizgarta. Muryar qata nurse ta saka ta buWe ido da taji tana cewa

"Aa baban twins ba zaka rage mana ka kwashe duka biyun, to bamu aron Waya ta fara shayar da ita da alamu yaran nan zasuyi ha?uri ba waddata nemi abinci kai sukayi ko Mamansu?"
Murmushi kawai yayi mata a ransa yana cewa
"Yan Ahmad sukayi" kafin ya mi?a mata Waya yana tambayar wacce ce Hassana
"Inaga ta hannunka ce, duba farcensu wadda aka sakawa marker ce Hussaina" ya duba Wan ?aramin hannun yarinyar yace
"Ok hassanan ce a hannunki" daga nan ya fice da Hussainan a hannunsa ya basu waje ira kuma ta shiga gwadawa Fatiman yanda zata shayar da ita.

"Madam wai zafin aikin daya haWa ki dashi ne be sakeki ba naga kinata faman haWewa Baban twins fuska?" Nurse Win ta sake faWa cikin wasa tana karantar yanayin Fatiman, se tayi murmushi tana kallon yarta tace
"Ba Mijina bane ?aninsa ne"
"Ikon Allah, daman sister Naja ta faWa muka ?aryatata ashe da gaske take" Nurse
Win ta sake faWa, seda yarinyar ta ?oshi kafin ta fita da ita ta karSo mata Wayar, Allah ya taimaketa tun kusan kwana uku kenan Nonon ya kawo ruwa, farko harta damu seda Anty Sauda tace mata ai yana haka daman sannan ta nutsu.

Nan Wakin ya sake komawa bayan ta shayar da duka yaran ya saka su a kafaWa yana rirrigasu har sukayi bacci kafin ya kwanta kan kujerar ya shimfiWesu a ?irjinsa ?aunarau me sanyi tana ratsashi. Fatima na kwace lamo kamar me bacci amma tana lurada duk motsinsa, haushinsa ya cikata ya kankanesu ya bata yayanta su kwanta tare taji Wuminsu ya hana. Tana so ta tambayeshi koya kira Ahmad amma miskilanci ya hanata a haka har bacci itama ya kwasheta. Da Asuba ma bata san sanda ya fita ba se kukan yaran ne ya farkar da ita, ta sake basu suka sha kafin ta shiga banWaki ta canza pad tayi tsarki ta dawo ta zauna akan gadon tana tunanin inda zata samu waya ta kira Ahmad.

Bakwai da yan mintina Baba Bilki, Hajiya Rabi, Hajiya ?arama tareda su Maimuna suka je Asibitin nan aka fara rige rigen Waukar yaran. Bayan yayi sallar Asuba ne ya kira Momy ya gaya mata dan ya sake kiran Ahmad be Wauka ba yasan fushi yakeyi kuma yaso ace shiya fara gayawa zancen haihuwar amma kuma baze yuwu yayi ta zama da ita a Asibiti ba dan haka ya turawa Ahmad Win selfie daya yi musu shida yaran babu bayani sannan ya kira Momy ya gaya mata nan ta sanarwada Hajiya Rabi da Baba Bilki suka fara shiri bakwai suka tafi Asibitin bayan sun biya can gidan Ahmad yacewa Hajiya ?arama ta Webo mata abinda take ganin zata bu?ata da sukaje ta tarar da akwatin da Fatiman ta haWa tuni se kawai ta Wakko Shi suka tafi.

Ahmad kuwa haushin Jafar da abinda yayiwa matarsa ya saka yana ganin kiransa da Asuba ya?i Wagawa daman ga Fatima ma yayita kiran wayarta bata amsa ba yasan ta yuwu bata farka ba dan yanzun da cikinta yayi nauyi seyayi da gaske take tashi daga bacci ita ana cewa in ciki ya tsufa ba'a iya bacci to nata da baccin yazo mata. Seda ya shiga jirgi kafin su tashi sannan ya kunna Data, yana kallon message Win Jafar ya?i buWewa musamman da yaga hotone, seda ya sauka Kano, yana cikin Taxi da zata kaishi gida ya sake duba whatsapp status Win yammatan gidansu ya fara ganin kyawawa yara akai, Annah ce tazo masa a rai dan itama cikine da ita haihuwa ko yaushe a fili yana kallon hoton yana murmushi yace
"Inama na samu irinsu nima".

A status Win Asharb Win Baba Al?ali yaga ya saka yaran da caption 'su Ahmad an zama Baban Yan biyu', jikinsa har rawa yake ya danna masa voice call akayi sa'a Yana online ya amsa cikin muryar tsokana yake cewa
"Aa kaga latest dady twins"
"Wai yaran waye wannan naga kowa yana ta sakasu?" Ya tambayi Ashrab Win, da fari ya zata raina masa hankali zeyi seda ya fahimci dagaske besan Fatima ta haihu ba kafin ya gaya masa harda sunan Asibitin da suke dan barinsa gurin kenan yakai Hajiya Balara dangi duk an hallara ganin yayan Ahmad banda Hajiya Binta dake gida ranta kamar kaskon da aka soya barko abu goma da ashirin ya haWe mata, ga takaicin Jafar daya hanata bacci jiya se Asuba baccin ya saceta ta farka kuma da safe ta ga gida babu kowa se Momy, seda ta shiga gurin Alhaji yake ce mata ya akayi batabi su Rabi Asibiti gurin Matar Ahmad ba

"Meya sameta, ko Sari tayi?" Ta tambayeshi ba ko tunanin komi abinta, Alhajin ya kalleta kaWan kafin yace
"Haihuwa tayi, sun samu tagwaye"
Irin makami me linzamin daya dirar mata a zuciya sanda taji labarin haihuwar Zubaida ne ya sake mata dirar mikiya, ta zabura tana kallonsa tace
"Maza?"
"Matane" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba, yanajin ajiyar randa tayi kafin tace
"Da sau?i, wato saboda zalama tazo ta gaje Wan abinda ya tara shine zata fara da yan biyu? Su dai yayan matsiyata halinsu Waya, daga Zubaida har Rabi ga wata nan an samu ?ari, gaskiya na tausayawa Ahmad, kowa na farawa da magaji Shi an fara masa da masu cinye masa Arzi?i".

"To Binta ai gara shi a ?alla ansan yana haihuwa kinga akwai fatan yanda ya haifi matan gaba ya haifu Namiji, ina wanda kuma har yanzu bamu san nasa kwayayen akwai na ?yan?yasa ko babu ba?" Alhaji Audun ya mayar mata da martani fes yana kallon fuskarta, se tayi kasa?e tana itama tana kallonsa kafin ta fice daga falon tashin hankali na rufto mata, tabbas ?alubale ne babba ace Ahmad ya riga Jafar haihuwa dukda mata ya haifa amma abinda be taSa faruwa ba yau Alhaji ya kalleta harya tarewa wani faWa a gaban ta kuma ya aibata nata lallai tsuguno bata ?are mata ba, wato Aisha shammatarta tayi bayan tasan yanda tayi ta cusawa Audun Ahmad da duk abinda ya shafeshi.


************
FaWar irin murnar da Ahmad yayi bayan daya kyalla ido yaga yara har biyu a matsayin nasa Sata lokaci ne, har hawaye seda yayi, ya rungume matarsa a gaban kowa yana jinjina mata, ma'aikatan Asibitin kuwa kaf seda ya bisu da abin arzi?i sukaci tudu biyu dan kafin Jay ya tafi bayan daya biya kuWaWen da aka rubuta musu seda ya sallame su sannan ya wuce gida ya kwanta abinsa ya shiga ramuwar bacci ba tareda yabi takan Fatiyyah ba duk irin tijarar data ringayi tana takalarsa be kulata ba a ransa yace taci Albarkacin Yayan da yayi shi yanzu ya girma, bata ma san Fatima ta haihu ba se washe gari bayan an sallamosu sun dawo gida.

Jay kam yasha mita a gurin Ahmad har seda yaji kamar ya bar garin ko ze huta ga uban nin tambayoyi, ya Fatima tayi? Me ta ringa cewa ya tayi kaza daya gaji yace
"Idan zata sake haihuwa zan maka video*
"Lallaima, wato kai ka zama Wan rakiyar matata labor kenan. Kai tsayama amma dai baka kallanmun abu ba?" Ya faWa yana Waure fuska irin he is serious, abin ya bawa Jafar dariya yace

"Ayi shiru kawai abinda ya faru ai ya rigada ya faru kona gani na manta kawai". Yanda yaga Ahmad Win yayi fuska yana muzurai alamar be karSi wasan ba ya sakashi fashewa da dariya kawai ya barshi, maganar gaskiya kuma bega jikinta ba, Shi baze ma iya cewa ga abinda ya faru a gurin ba koma ya gani Win dagaske ya manta balle ma be gani ba.

"Ranar da jarirai sukayi kwana biyar ranar aka kaisu Allurar BCG, daga Asibitin Ahmad yace zasu biya can gida akaiwa Alhaji su ya gansu.
"Dagaske dai ba zaka barni na tafi gida wanka ba?" Ta faWa tana kallonsa, kafin ta haihu rimi rimi sun shirya zataje wankan gida amma yanzun fafur yace babu inda zataje baze iya rabuwa da Yayansa ba. Ahmad ya kalleta shima kafin yace
"Kin fi so muyita maimaita magana ne, naga ita kanta Umma saboda ta yarda zan iya kulawa dake babu wanda ta turo miki"

"Saboda dai Baba Bilki tana nan ne ya saka kai wace kulawa kake bani bayan duk ka dena sona yanzu ta yaranka kawai kakeyi banda ni" ta mayar masa cikin shagwaSa, yana murmushi yace
"Ai abin cikin ?wan ne yafi ?wan daWi dan ma ba dake sukayi kama ba inaga da dasu zan ringa yawo suk inda zanje bazan iya rabuwa dasu ba, yawwa amma kin yarda wai Jafar ya fini son yaran nan?" Ya tambayeta. Tayi shiru, hoton ranar data haihu a Asibiti yana dawo mata yanda Jafar ya zubasu a ?irjinsa kamar su zama abu guda da yanda ya ringa yawo dasu a kafaWa ya rirrigawa tabbas taga tsantsar ?auna

"Kema kin yarda kenan?" Ya katse mata tunani tayi murmushi tace
"Haba dai, zedai so su iyakar nashi amma babu ma yanda ze haWa kanka dashi"

"Amma fa nima na kusa yadda, jiya na bawa Fadil Baby 1 kinga yanda ya zaburo ya karSeta kawai ya rufeni da faWa wai bansan wahalar da Mamanta tasha bane shiyasa zan bawa yaro ri?onta idan ya kada ita fa? Se naji wani iri, ban yi tunanin wai ze kayar da ita ba amma Shi bakiga yanda ya damu ba kuma tsawan da yayi ya sakata kuka duk ya rikice kamar shima yayi kukan" Ahmad ya faWa yana daidaita parking a gidan Audu Bechi.

"Uhm" kawai tace, to me zata ce masa? Ashe Jafar Win yana shiga gidan rabonta dashi tun a Asibiti Fatiyyan ma tun ranar da suka koma gida data shiga sun daiyi waya tace mata ta tafi Abuja so tunaninta ma tare suka tafi.

Falon Momy sukayi masauki dan sun tarar Alhaji na wanka se kawai suka fara shigewa ciki. Momy ta kashe jikokinta ta ri?e yan uwanta na mata tsiya.
"Ai tayi ?o?ari kwana biyar fa da haihuwar bataga wannan gwalagwalan jikoki da Allah ya bata ba da Su oo ne ai ita zatayi zaman daSaron" Anty Zainab ta faWa sukayi dariya gaba Waya. Bayan gaishe gaishe Salim yazo yace Alhajin ya sakko, Momy na ri?e da Yarinya Waya Hajiya Rabi na ri?e da Waya se Fatima da Ahmad

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login