Showing 351001 words to 354000 words out of 467220 words

Chapter 118 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12176

ba taji saukar mari ta ?eya, a fusace ta fizgi yaron daga hannun Jafar ta dungurar dashi akan gado tana cewa

"Iskancin banza, da baki danu da Wan ba shine kika zo kina mana fuffukar banza? Ya mareki Win ni banji daWi bama da ba dukan tsiya ya miki ba tunda daman ke ai zuma ce se da wuta ake shan ki, da Allah ku muje idan ta ga dama ta barshi yayi kukan har numfashinsa ya ?are"

"Aa Umma, Afeeya dan Allah kiyi ha?uri wlh kuskure ne kuma ke kika ja me yasa zaki fincike shi daga hannuna yanzu kiyi ha?uri ki bashi daga baya idan ma zaki rama marinki na yarda" Jafar daya dur?usa gabanta ya faWa yana Wora mata yaron a cinya. Da idanunta dake cike da ?walla ta kalle shi, kusan sakanni biyar kafin ta janye bayan data ri?e yaron yana jin Wumin jikinta kuwa ya rage kukan ta rungumeshi abin tausayi se ya fara buWe baki alamar abinci yake nema.

Umma tayi tsaki ta fice tana cewa
"Mutuniyar banza, sa kika samu wanda yake ta taki ke da yayan naki ma shiyasa har kike iskanci". Umma Halima ta rufa mata baya, Baba Bilki dai seda taga ta saka yaron a hijabi kafin ta juya tana ce masa
"Seka taso mu tafi tunda hankalin ka ya kwanta ka haWa ta da Ummanta".

Be tashin ba se ido daya tsura mata, seda Baban ta buga masa tsawa ganin kamar ma baya hayyacinsa kafin ya tashi yana sauke ajiyar zuciya sannan ya galla mata harara ya fita daga Wakin, se lokacin ya gaida su Umman cikin tsananin kunya Baba Bilki ta tambayeshi sauran yaran yace suna gidan Maimuna ze kawo su daga baya sannan ya tashi ya fita.

Jikin motarsa ya jingina ya rufe idanunsa yana jin nutsuwarsa tana dawowa a hankali, kusan minti goma kafin Baba Bilki ta fito, ya karSi jakarta ya saka a bayan motar har ta shiga ta zauna yace mata
"Bari na duba na gani ko ta bashi ya ?oshi sosai"
"Amma dai shaye shaye ka fara ko Jafar? Kai iya abin kunyar da kayi yanzu be isheka ba se ka sake yin wani? To wuce muje mutumin kawai".

Kamar baze tafi ba ya tsaya yana Sata fuska seda ta balbaleshi da masifa kafin ya tayar da motar yana cewa
"Amma dai ko sallama se nayi dashi"
"Sallamo, nace sallamo Jafar, ka kiyaye ni wlh idan ba haka ba zan gwada maka tawa kalar tijarar fitinannen banza da wofi kawai. Ka mari yar mutane kuma ka biyota gidansu ka sake tunzurata ka haWa ta da uwar ta kaidai bakaji daWin halin ka ba duk zaman da kayi da Amadu ace baka kwashi komai a kyawawan halayen sa ba aiko bakaji daWin halin ka ba" ta ringa faWa har suka isa gidan Alhaji Audu a waje ma ya sauketa ya juya. Gidan Maimuna ya tafi, ya tarar da yaran har sunyi shirin bacci zasu kwanta acan ya shashance har gurin sha Waya da Mijin ta ya dawo kafin ya tafi lokacin sunyi bacci duk ta kwantar dasu ya ce mata ze zo da safe ya kaisu Tahfiz daga can idan an tashi ze wuce dasu gida dan befa ha?ura ba, Ahmad dai ya bar mata na Wan lokaci amma banda sauran.

Daga gidan Maimuna wani eatery ya samu ya zauna yaci abinci dan rabon daya saka wani abu a cikinsa tun da safe daya gama ya hau mota ya cigaba da zaga tituna ya shiga can ya Sulla can be kama hanyar gida ba seda agogo ya buga ?arfe Waya na dare a lokacin ya tabbatar Fatiyyah tayi bacci dan tana baccin wuri duk inda goma take ta kwanta sannan idan ma gidansa Hajiya ta tafi itama zuwa lokacin yasan ta gaji da jiransa ta kwanta dan ba ?aramin aikinta bane ta kwana a gidan tana jirabsa.

Tunda ya shiga cikin gidansu yaga ?ofarta a kulle yasan duk yanda akayi yar rahoton tata ta gaya mata ya shiga da Ahmad gidan shine ta tafi ta gani da idon ta, a yanda ya gaji kuma yau iya kukan Ahmad daya caza masa kai ya isa baya bu?atar sababin Hajiyar.

A waje ya ajiye motarsa dan kar ma a buWe get ?arar ta tashe su, fitilun falon ?asan duk a kashe ya ringa sanWa harya samu ya haye matakalar benen seda yaje ta kusan ?arshe kawai yaga haske ya gauraye falon, a tsorace ya juya sukayi ido hudu da Hajiya kamar wata sabuwar Aljana tana ma?ale jikin bango gurin switch Win fitilu.

"Munafuki algungumi, wato ka saWaWo kamar sabon Sarawo to ina kallonka daman zaman jiranka nakeyi sakko kazo nan" Hajiyar ta faWa tana zare masa idanu.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 29*


A hankali ya zame ya kwanta akan gadonsa wani sanyi yana ratsa ?ofofin jikinsa, kalaman Hajiyar sunyi matu?ar tsauri da yawa. Ta yaya za'ayi ace uwar data haifeshi ce take yi masa irin waWannan kausasan kalamai?

Sau tari ya kanyi tunanin inama ace ba Hajiya ce ta haifeshi ba? Ina ma ya kasance Waya daga cikin yayan tsakar gidan da suke ganin an fifitasu akan su?. Yah Ahmad yana yawan gaya masa wannan tunanin nasa bashida kyau a duk sanda kuma shaiWan ya raya masa hakan yayi saurin yin a'uziyya tare da neman gafarar ubangiji. Uwa uwa ce duk yanda take, a maimakon yayi kaicon kasancewar ita ta haifeshi yayi ?o?arin nema mata shiriya gurin ubangiji babu abinda yafi ?arfin sa kuma ya fi kowa sanin dalilin daya sa komai ya kasance a yanda yake.

Ya juya ya kwanta rigingine ?wallar da suka tarar masa suka samu damar zirara ta gefen idanunsa, ya mi?a hannu kan bedside drawer sa ya Wakko ?aramin frame me Wauke da hotonsu shida Ahmad, tsohon hoto ne a lokacin suna aji huWu na sakandire dan uniform ne a jikinsu sun rungume juna suna dariya duk inda yake yana tare da hoton a gidan sa na Nigeria ko a turai kai ko tafiya zeyi yana cikin jakarsa dan hoton yana tuna masa da abubuwa da yawa na rayuwar baya a yanzu da ya rasa Ahmad Win hoton seya sake zama abu mafi muhimmanci a tare dashi bayan yayan da Ahmad ya bar masa

"Tana so ta hanani kula da amanarka, ban san ya zanyi ba Yah Ahmad Hajiya ta kasa fahimta kuma bani da wanda zan kaiwa matsalata ya warwaremun bayan kai ya zanyi?" Ya ringa sambatu shi kaWai yana kallon hoton ba tareda hawaye kuma sun tsaya masa ba.

Ya fi minti ashirin cikin yanayin kafin ya mi?e ya share hawayensa ya shiga banWaki ya Wauro alwala. Tamkar a lokacin yake jin muryar Ahmad yana nanata masa
"Kada ka manta da kiran Allah a lokacin tsanani da kuma lokutan farin ciki domin kowanne Al'amari daga gare shi yake, idan ya kyautata maka ka gode masa seya ?ara maka haka idan ya jarabceka ka dangana ka nemi taimakonsa seya saka maka da mafificin alkhairin daya fi wanda kake tsammani. Ka tashi kayi sallah ka nemi taimakon Allah dukkan tsanani yana tare da sau?i Jafar" duk sanda ya kai masa ?arar Hajiya ko wata damuwa ta rayuwa abinda yake gaya masa kenan.

Zaune ya tarar sa Fatiyyah a gefen gadonsa bayan daya fito, ta saka wata fitsararriyar rigar bacci, irin zaman da tayi kaWai da ace cikin walwala yake babu abinda ze hanashi amsa gayyatarta amma ganinta a lokacin babu abinda ya ?ara masa se zallar takaici da ba?in cikinta. Beyi sa'ar matar aure ba. Fatiyyah bata da wani buri a duniya baya ga ta haWashi da mahaifiyarsa tayi ta zugata tana furta kalaman da zasu lalata rayuwarsa ya tabbata badan Allah da zuciya yake amfani ba da irin kalaman da Hajiya take jifansa dasu tabbas da rayuwarsa ta daWe da balbalcewa. Tana ganinsa ta nufeshi cikin karairaya tana yau?i kafin ta kai ga Wora hannunta jikinsa ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawar data saka ta bar masa Wakin babu shiri. Seda ya murWa key kafin ya tayar da sallar.

Idanunsa sun ?e?ashe sam bayajin bacci, yayi amfani da damar gurin kai kukansa gurin Allah ya kuma nemi Wauki tareda zaSi cikin al'amuransa, baya keSancewa, duk sanda ya tashi Addu'a ya kan ro?i Allah daya zaSa masa abinda yafi alkhairi a rayuwarsa baki Waya. Har aka kira sallar Asuba yana zaune, seda ya sake watsa ruwa yayi raka'atanul fajr kafin ya fita masallaci bayan ya kulle Wakin sa da mu?ulli ya saka a aljihu.

A falo ya tarar da Hajiya duk munsharinta ya cika ko ina da alama nan ta kwana tana gadin kar ya fita daga gidan. Seda gari yayi haske kafin ya fita daga masallacin ya Wauki motarsa ya shiga gari dan baze iya komawa gidan ba.

A Sangaren Hajiya kuwa hasken ranar daya galle mata ido dalilin labulen window data yaye tana le?en jiran dawowar Jafar ne ya farkar da ita, ta goge yawun daya ji?e mata gefen fuska da Hijabin data lulluSa dashi tana zare ido da alama tantance a inda take takeyi kusan minti uku kafin ta tashi ta shiga Wakin dake nan ?asa tayi alwala tayi sallah, babu wata cikakkiyar addu'a ta tashu, can bakin matakalar benen taje ta tsaya tana ?walawa Jafar Win kira.

Tayi yafi kai goma jin shiru ba'a amsa ba a fusace ta kama ?arfen ta fara hawa tanayi tana hutawa dan tunda ta rasa ?afa Waya duk ?aunarta da zuwa Wakin Alhaji Audu haka ta ha?ura dan ba ?aramar wahala take sha gurin hawa bene ba. Bayan kusan minti goma ta isa ?ofar Wakin Jafar Win ta shiga bugawa babu ?a??autawa, bugun ne ya tayar da Fatiyyah ta fito ba tareda ta ko sakaya jikinta ba dan rigar daren ce a jikinta har sannan.

Kallo Waya Hajiya tayi mata ta Wauke kai taci gaba da abinda takeyi zuciyarta na tafarfasa, Fatiyyah tayi mi?a tana gantsarewa ba ruwanta da a gaban wa take cikin takun isa isa ta matsa jikin ?ofar tana cewa
"Shifa baya son damuwa, gara ma ki buga a hankali idan ba haka ba baze buWe ba" ta fara ?wan?wasa kofar tana kiran
"Baby Hajiya ce fa kazo ka buWe".

A fusace Hajiya da mamaki da takaici suka daskarar da ita a gefe ta finciketa ta wancakalar ?iris ya rage ta faWi tayi saurin dafe ?ofa kai tsaye ta zabgawa Hajiyar kallon daya fi kama da harara muraran jin tana cewa

"Saboda ke ga tantariyar mara mutunchi har ni zaki tsaya kina cewa baya son damuwa, to naci abu ta kazanki ke da damuwar shegiya ko kunyar Allah bakyaji zaki fito gaba a haka ina uwar mijinki"

Mi?ewa Fatiyyah tayi ta shige Wakin ta bayan datayi ?wafa, badan Jafar yana gidan ba seta gungura matar nan ?asa idan yaso tace bata san ya akayi ba, tana shiga taji Hajiyar ta biyota tana huci tace

"Wuce ki haWa mun abun kari naci na tafi, dan abu ta kazan ubansa ze buWe Wakin ya fito ai tunda ba mutuwa yayi a ciki ba".

"Sallah zanyi" Fatiyyah ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba, Hajiyar tace
"Wato da ko sallah bakiyi ba tun asuba kina kwance, tir dake" tayi tsaki ta fita se kace ba lokacin itama tayi tata sallar ba. Bayanta Fatiyyah tabi ta sakawa Wakin mu?ulli a fili tace

"Wlh banga uban daya isa ya sakani girki, jarababbiyar tsohuwa kawai zanyi maganinki wlh ba banza kika ture ba" ta haye gado taja wayarta taci gaba da abinda takeyi kafin bugun Hajiyar ya addabeta.

Hajiya kuwa tun tana sauraron sakkowar Fatiyyah har ta gaji da zama, waje ta fita ta zagaya Wakunan da Jafar ya ?ara guda biyu saboda masu aikin da Fatiyyah ta ajiye yace baya bu?atar mai aiki ta zauna masa a cikin gida shi yasa aka musu Wakin daga waje, bugun jidalin suma ta musu, duk su biyu suka taso a gigice ?edarai dasu kana ganinsu kasan basu san Allah ba.

Seda tayi musu kallon sama da ?asa kafin tace
"Au kune sababbin masu aikin data canza lallai, to ke fito kije ki kirawo mun ita dan bazan iya sake hawa saman nan ba".

Wadda hajiyar ta nuna tace
"Sorry ma, a ?a'idar aikinmu bama shiga main hau se ?arfen tara na safe, sannan bama hawa saman Hajiya se ?arfe goma bayan ta sakko yin breakfast". Hajiya tayi sakare tana kallon ta cikin rashin fahimtar abinda take so ta gaya mata, ta gyara tsayuwa tace

"A ta?aice kina gayamun ba zakije ba kenan?"
"Na gaya miki ?a'idar aikinmu ne kawai Ma" matar ta sake faWa kafin ta maido ?ofa ta rufe dan dama Wayar tunda Hajiya ta fara magana ta koma ciki abinta. Da mamaki ya cika Hajiya tafiya ma kasayi tayi, yau ita Binta a cikin gidan Jafar matarsa ta gama yi mata tata kalar Wibar albarka yanzu kuma yan aikinta sun mata har ace ita tayi wannan lalacewar?

Da?yar ta tafi bakin get fuskar nan kirtif kamar zata yi aman wuta mai gadi da direba suna zaune tace musu
"Kai zoka kaini gida"
"Toh Hajiya bismillah" direban ya faWa da sauri yana mi?ewa dan zaman jiranta yakeyi. Tun asuba Jafar yace ya zauna kar yaje ko ina dan ze mayar da Hajiya gida. Bata ko Wakko takalminta ba haka ta shiga motar seda ta zauna direban ya tuna mata tace suje kawai. Cikin flat shoe sa Fatiyyah ta kan bari cikin motar idan ze kaita unguwa ya ciro mata Waya a booth bayan daya kaita gidan ta saka, yana sauke ta ya kira Jafar dake tsaye bakin layin su Fatima ya gaya masa.

Numfashi me nauyi Jafar Win ya ajiye, daya fita gidan Maimuna ya tafi, can ya jira ta shirya su Amal ya kaisu Tahfiz bayan da suka gama biye musu suka sha surutun daya rage masa raWaWin daya addabeshi. Bayan ya saukesu harya kama hanya zeje ya kama Waki a hotel se kuma kewar Ahmad ta kamashi hakan tasa ya karkata motar zuwa can gidan bayan ya isa ne kuma ya kasa fita daga motar, tara ma batayi ba ya za'ayi yaje musu gida? Sannan idan ya je ma me ze musu dan tsaf zata raina masa wayau. Yafi minti goma sha biyar cikin motar a bakin titin kafin direban ya kirashi. Kashe motar yayi ya tsallaka titin a ransa yana raya ba zeyi zuwan banza ba. Da ?afa ya ?arasa gidan dukda yanzu mota tana zuwa har ?ofar gida tun bayan da Ahmad yayi musu gyara ya siyi gidan dake bayan nasu aka haWe se aka fitar da ?ofar gidan ta cikin wancan layin dan shi mota tana shiga.

A ?ofar gidan ya tarar da Baffansu Fatiman, rabon da su haWu fuska da fuska kamar haka tun ranar daya je ya same shi akan dalilin daya sa be turo iyayensa nema masa aure ba kamar yanda yayi al?awari, ko lokacin rasuwar Ahmad daga nesa suka gaisa shiyasa da suka haWun duk se ya diririce kamar wanda yazo sata aka kama haka yaji badan sun haWa ido ba da niyyar juyawa yayi amma ba dama dan Baffan harya buWe ?ofa ze koma ciki ya hango shi ya tsaya.

Kai a ?asa ya gayar da Baffan bayan sunyi musabaha, ya tambayeshi mutanen gida kafin yace
"Nasan dai zancen gizo baya wuce na ?o?i Wanka ka biyo" Baffaya faWa se yayi murmushi yana shafa kai, Baffan ya wuce ciki yana cewa
"Bismillah shigo".
Kamar ra?umi da akala yabi bayan Baffan, Umma na cikin kitchen Win da aka bar mata shi a tsakar gida dukda an zamanantar dashi tace ita tafi son hakan Ahmad Win na goye a bayanta, yi masa wanka kenan ta goyashi ta bar Fatiman tana nata wankan shine ta fito tana ?arasa hada abin kari.

"Shiga falon bari ta kwanto shi" Baffa ya faWa Umma ta bi Jafar daya tsaya da kallon mamaki kafin ta kalli Baffa dake cewa
"Kwanto mutumin kirkin mana". Kwance shi tayi ta mi?a masa tana amsa gaisuwar da Jafar Win yake mata, a tsakar gidan ya tsaya yana kallon Ahmad kamar ze lashe shi don so, dare Waya kawai amma se yaji kamar ya shekara be ga yaron ba Umma da Baffa dai kallonsa kawai suke Baffan ya sake maimaita masa kan ya shiga falo ya wuce bayan daya kalli ?ofar Wakin dake tsakar gidan inda ya tarar da Fatima jiya.

Motsin da akayi ya saka Umma le?owa daga kitchen ta kalli Fatima data fito daga banWakin tsakar gidan, zani ne Waure a jikinta iya ?wauri se madaidaicin towel data yafa akanta data wanke ya sauka ?adan ya rufe mata ?irji, kiran sunanta tayi kafin kuma tayi yun?urin dakatar da ita harta shige falon tana cewa
"Ina zuwa Umma jinin ne ya dawo" ta shige da sauri gaba gaWi ta wuce Waki abinta.

Seda ta saka pad a jikinta ta goge ruwan dake Wiga daga gashinta kafin ta canza zanin jikinta da towel da be kaishi sauka ba. A hankali ?ofofin hancinta suka fara jiye mata ba?on ?amshin daya mamaye falon har zuwa cikin Wakin, ?amshine da ko a filin arfa ta sha?eshi tana da ya?inin zata gane hakan yasa ta juya da sauri ta kalli ?ofa, da acan Wakin Baffa data zauna jiya taji ba zatayi mamaki ba shawul Win da aka naWe Ahmad dashi jiyan kuwa tun dare ta wankeshi saboda ?amshin daya kama jikinsa shi kansa seda ta goge masa jiki tas suka kwanta dan ma Umma ta hana a masa wanka saboda dare to me kuma ya sake maido da ?amshin yanzu?

Tsaki tayi a fili taja manta zata shafa se kuma ta tashi ta fita falon, kaskon da Umma da gasawa Ahmad cibi dashi ta Wauka ta koma duk yanda yaso ya hana idanunsa kallon ta kasawa yayi haka yayi mata rakiya harta shige Wakin ji?a??en gashinta daya manne jikin farar fatar bayanta dake Waukar ido shiya fizgi hankalinsa, yayi saurin Wauke kai jin an sake shigowa Wakin ya wayance da mi?ewa tsaye yana jijjiga Ahmad daya motsa. Fuska ba yabo ba fallasa Umma tacr

"Kawo yaron ga abin kari can a falon tsakar gida"
"Ai wucewa ma zanyi Umma nagode" ya faWa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login