Showing 192001 words to 195000 words out of 467220 words

Chapter 65 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12140

se yasa yayi zaton kunya yaji da yace su fito da Mata tunda yau a giya tara yake yan mutunchin na kusa se yace masa

"Toakwai ta a ?asa kenan irin wannan murmushi da kake bugawa, Yar gidan wacece?"

"?uuu" cikin Ahmad ya kaWa, maganar tazo masa a bazata, ba tanan ya shirya tasota ba. Ya rigada ya gama tsara takan Baba Al?ali zebi shi ze kaiwa maganar auransa kai tsaye tunda dai shima Alhajin idan maganar ta tashi shi ze wakilta amma yanayin nasa neman auran yasa gara ya fara samunsa dan ya tayashi gyarota idanma matsala ta shirya afkuwa yanzu kuma Alhaji na nema ya titsiyeshi, be kuma san ya ze Wauki maganar ba idan ya sanar masa da wadda yake nema musamman da yaji ya tambayeshi Yar wacece kenan yana tsammanin ze samo yar wani Attajiri ko ?usar gomnati wanda yana faWar sunansa ze gano wanenene?

"Kayi shiru, ko babu ne?" Alhaji ya sake faWa yana kallonsa. Harda rage gudu Ahmad yayi kafin ya saci kallon Alhajin yaga shi yake kallo shima sannan ya haWiye yawu yace

"Wata yarinya ce Fatima, a Marmara gidansu yake amma cikin lungune se anyi tafiya kamar za'a shiga Alfindiki, Mahaifinta Bakanikene yana gyaran mota da babur Amma kafin ma na fara zuwa gurinta seda nayi bincike wlh mutumin kirki ne kwarai da gaske haka ma ita yarinyar tana...."

"Ban tambayeka halinta kona mahaifinta ba ko kuwa kai ne zaka mun binciken halin waWanda zan haWa surukuta dasu?" Alhajin ya dakatar dashi muryarsa dai kadaran kada han babu farin cikin da yake ciki dazu haka babu zafin da kai tsaye Ahmad ze zarce cewa be aminta da abinda yazo dashi ba.

Tamkar Ahnad yace
"Ai naga kamar su Yaya Naziru su sukayi binciken Matan da zasu aura shiyasa baka hanasu ba" se kuma yayi azamar kwabar zuciyar dake neman kwanto masa ruwa ya shiga taitayinsa, Ya sauke ajiyar zuciya tareda yin shiru Alhajin ya sake jefa masa wata tambayar yace
"A ina kuka hadu da ita?"
"A Shago, sunzo siyayya tare da Yayarta" ya bashi amsa a sanyaye Alhaji ya sakeyin shiru kafin ya kuma cewa

"Ita yayar tata budurwa ce ko matar aure?" Se Ahmad yayi saurin cewa
"Matar aurece, Dan gidan Balarabe Faranshi take aure ma yaranta uku yanzu" ya shaidawa Alhajin harda sunan uban Mijin Anty Sauda domin ya sanshi, dukda ya rasu amma har yanzu akwai manyan Yayansa da suke huldar kasuwanci dasu, dabararsa hakan zesa Alhaji ya fahimci ba a gidan banza ya nemo mata ba.

Alhaji ya muskuta yace
"Marmara? Ina ganin Musbahu ne kamar naje ?aurin auransa a nan masallacin sarki idan ban manta ba shekaru bakwai kenan yanzu dan tsiran auran da shekara Waya Alhaji Balaraben ya rasu. Amma yarinyar daya aura shi ai kamar Ba?ar buzuwa ce dan ban manta ba na halaci Dinner da Alhaji Balaraben ya haWa musu"
Rai fes Ahmad yace
"Itace, mahaifiyarsu ce Buzuwa amma mahaifinsu haifaffen nan Marmaran ne duk yan uwansa anan tsukun suke yaran ne dai sukayi kama da Mahaifiyar tasu shi yasa idan aka gansu se a dauka Buzaye ne"

"Wato farar fatar ce da dogon gashi suka ruWeka ko?" Alhajin ya faWa fuska babu wasa yana tsare Ahmad da ido nan ya diririce murnar da yake ta koma ciki, cikin in ina yace
"Aa wlh Alhaji kawai dai.."
"Kawai dai me? Da ba Suhaima yar gurin Alhaji Lamin kake nema ba?" Alhajin ya dakatar dashi. Tamkar ze fasa masa kuka yace
"Ni daman ita ta ke sona, kuma daga baya tace ita ba zata zauna a Nigeria ba tunda yan gidansu sun koma US sedai na bita can nima abinda ya rabamu kenan"

"Eh anyi haka, naji yayyenta biyu ma duk auransu ya mutu da sukace zasu bi uban su koma can da zama, Lamin,Lamin ban san kalar kwayar da yake sha ba. Haka kawai ya tattara wai shi ya bar Nigeria banda shirme waWanda suke a wajenma idan girma ya riskesu dawowa gida suke su mutu cikin Ahalinsu se shi ze tattara ya koma can, to ita kuma Safiyyah yar wajen Goggonka Salaha fa?" Alhajin yayi kiWansa ya taka rawarsa lokaci Waya.

Ahmad da gaba Waya ya gama shigewa ruWani, da fari abu kamar ze zo a sau?a?e amma kuma yana neman yayi wahala Alhajin se wani kale kalen magana yakeyi, ta maza yayi dan duk ji yake kamar ya fashe da kuka ko Alhajin ze barshi da zaSinsa yace

"Ai ita Abbanta yace yayi mata Miji, Momy bata gaya maka ba auran ma saura wata biyu yanzun ma Anty Maimuna tazo siyan kayan Lefe ?an Mijinta ne wanda Safiyyan zata aura"
"Wato sun hanaka zasu bawa ?an Mijin Maimuna, kai dashi waya fi kusanci dasu?" Alhaji yayi maganar cikin faWa Ahmad besan sanda ya Wage kai da hannu biyu ya saki sitiyari ba yana cewa
"Wallahi tallahi ba hanani sukayi ba, gajiya Abban yayi da jiran kuje ayi magana kuma daman ya rigani fara nemanta seda ma Anty Salahan tace a fasa dashi Mony ce tace Aa ba za'ayi haka ba tunda dai ya riga a bashi"

"Baka da hankali zaka saki mota?" Alhajin ya buga masa tsawa se ya nemi gefw ya faka, Allah yasa babu mota dake biye dasu gab kuma ba gudu yake sosai ba shiyasa daya sakwta bata watsasu wani gurin ba. To fisabilillahi kamar wanda aka ritsa a Kotu Alhaji se zabga masa tambayoyi yakeyi yana muzurai ba dole ya manta abinda yakeyi ba?

Shiru ne ya biyo baya, babu kalar addu'ar da Ahmad beyi a ransa ba akan Allah ya sassauto zuciyar Alhaji ya amince da bu?atarsa babu ja in ja.
"Tada motar muje gida, zamu ?arasa maganar a can" Alhajin ya faWa bayan daya mula. Jiki ba laka Ahmad yaci gaba da tu?i, har wani zazzaSi yake ji yana shirin saukar masa domin yanayin Alhajin ya nuna koda ace ze yarda da batunsa tofa se an kai ruwa rana.

Sun shiga Kano anyi magriba, a kusada wata Majalisa yace ya tsaya ganin suna hada jam'i da alama makararru ne nan suka yi alwala suka bisu. Bayan sun idar ganin Alhaji na lazumi Ahmad ya tsallaka inda yaga wani me gasa Nama yayi sa'a akwai wanda sukayi nan da nan yasa aka shiga yanka masa kashi kashi aka gama tsaf ya basu kuWinsu yara suka kai masa mota ya sake jido fruits ya ?ara daidai nan Alhaji ya shafa Addu'arsa ya taso suka cigaba da tafiya.

Har bakin falonsa inda ya Wauke shi ya tsaya da motar Alhajin ya sauka yana Hamdala, filin gidan tarwai da haske tamkar idan allurarka ta fadi zaka ganta. Sarah ce ta fito da Dogon Hijabi da alama aikenta akayi tana ganin Ahmad ta fasa ihun murna ta Waleshi, Alhaji ya zabga mata harara kafin ta sauka da gudu ta koma cikin gida se ga gayyar Maimuna da Yan biyun Anty da Mariya tareda Zayyad ta kirasu suka dabaibayeshi suna sowa da murna ga Yah Ahmad ga Yah Ahmad bakinsa ya gaza rufuwa ya ringa Waga wadanda ze iya yana saukewa kafin ya buWe Boot ya shiga fito da ledojin ciki tun a gurin yasa aka ware dan haka ya dan?awa kowa ta Wakinsu Hatta su Issa dake nan tsaye yayo musu kashinsu suka karba suna murna dayi masa Addu'a, ya gama rabon tsaf ya rage ledoji biyu a hannunsa, Alhaji na tsaye har sannan be shiga ciki ba yana kallon Ahmad.

A cikin Yaransa Ashirin da takwas ya fita daban kyautatawarsa ba kadan bace baga su iyayensa ba ga kowa daya rabeshi se yayi sambarka da halinsa, se yake ganinsa kamar shi a zamanin ?uruciyarsa.
"Ina nawa Naman toh? Tun Wazu nake haWiyar yawu a mota" Alhajin ya tambaya fuska a tamke kuma, Ahmad ya ?arasa gabansa ya rusuna yana mi?a masa Leda yace
"Fruits Win idan an gyara se a kawo tunda kafi so a matse"
"Allah yayi Albarka" Alhajin ya faWa bayan daya karSi ledar, cikeda farinciki Ahmad ya amsa da "Amin" domin yasan alfanun Addu'ar iyaye, ita take dabaibaye dashi yake ganin haske a rayuwarsa. Tasowarda yayi kamar hadari yayiwa jama'a da yawa rumfa a matsayinsa na matashin ?an kasuwa, buWe shopping mall Winsa ya saka kasuwar wasu da yawa tayi ?asa badan tasirin addu'ar iyayen ba ai da yanzu ma?iya sun kaishi ?asa.

Da kansa ya kaiwa Momy tata ledar kafin ya wuce Waki yayi wanka yayi sallar Isha'a dan an rigada anyi a masallaci. Ya Wan jima a zaune yana azkar da be samu yayi ba a hanya kafin ya sake shiga cikin gidan yana tafe yana kiran layin Fatima wadda tun suna HaWeja ya kirata basu wani yi magana me tsayi ba se yanzun yake sake so yaji ya take ya kuma ce ta tura masa da Kwalliyar Juma'ar da duk sati seya ro?a kafin ta bashi.

Busy yaji layin nata a ransa yayi tunani ?ila da yan gidansu take waya shi kansa badan tafiyar da yayi ba yau ya kamata ya le?a ya gaida Baffa dan kusan duk sati indai yana Kano ko Fatima bata nan se yaje ya gaishe su, yanzun babban abinda yake a ransa jiran jin amincewar Alhaji game da maganar auransu wanda kuma a jikinsa yana ji in Allah ya yarda ba za'a samu matsala ba fatansa daya Allah yasa kar Alhajin yayi zancen da Hajiya har ya gaya mata yar wa yake nema ita kaWaice a cikin gidan yake da tabbacin zatayi Adawa da auransa da Fatima domin ta tsani TALAUCI da TALAKA, ya tabbatar kuwa muddin ta sani se inda ?arfinta ya ?are gurin ganin ha?ansa be cimma ruwa ba na auran Fatima, ko ba dan komai ba ta samu hanyar rama tsaya mata a ma?wogwaro da yayi ya hanata rawar gaban hantsi, ya tabbatar zata shiga ta fita gurin ganin be samu abin da yake so ba amma Allah ya fita.

A haka ya shiga cikin gidan Hajiya Rabi na tsakar gidan tana bawa Baba Mairo sallahun abinda zata taho mata dashi wani satin idan zata zo, Baba Mairo dai me girkin gidan tun zamanin Hajiya na Amarya duk haifarsu akayi suka ganta a gidan bayan sun dawo nan Hotoro GRA kusan shekaru Ashirin kenan, wannan tazarar tasa bata biyo su ba saboda har yanzun Mijinta yana raye yana kwance yana Jinya se ya zama se sati sati take zuwa tana girkin Sadaka ana biyanta dukda girma ya kamata yanzun amma macece me lafiya da kazar kazar sannan aikin na rufa mata asiri shiyasa bata saki duka ta daina ba.

"Yaya Ahmad, an dawo" Antyn ta faWa kamar yanda yaran gidan suke kiransa tana murmushi, ya sunkuyar da kansa shima yana murmushin yace
"Tun dazu Anty, har nayi wanka naje sallah ina wuni" ya gaisheta bayan daya idasa kaiwa tsugunne ya sake kallon Baba Mairo da bakinta ya?i rufuwa da ganinsa yace
"Iya, ina wuni? Ya jikin Baba?"
"Lafiya lau Alhaji, Malam jiki da sau?i Alhamdulillahi ko da zan fito seda yace na gaishe ka na kuma ?arayi maka godiya. Na dai barwa Hajiyar tsakiya sallahu da aka ce baka nan amma naji daWisosai dana ganka mun gode Alhaji Allah ya saka da Alkhairi yaci gaba da yalwata arzi?i ya kuma rabaka da Alhaji Babba da Hajiya lafiya".

Anty ce ta amsa da Amin fuskarta a washe ta tabbata halin nasa yayi musu na Alkhairi, kyautar Ahmad irin wadda Annabi yace ayi ce, ka bayar da hannun dama ba tareda Hagunka ma ta gani ba, ya mi?e yana sake cewa Anty
"Ina Aboki? Dana dawo da safe banshi ba ina sauri shiyasa ban shigi na dubashi ba"
"Ai bama nan ma da wuri na fita ma kaishi Allura seda muka dawo Momy tace ka shigo amma kun fita da Alhaji, yana ciki rigima yake tayi tunda akayi allurar bari Hasna ta kawo maka shi ko zaka shiga?"
"Bari na le?ashi to ance idan anyi allurar ba'aso ana jagwalgwalasu ko ?ila zafi take masa" ya faWa yana nufar Wakinta. Tun daga wajen falon kuwa yake jiyo kukan Abdallah Autan gidan a yanzu me watanni uku kuma shine ?a na shida da Antyn ta haifa. Babban ?anta Musa da suke kira Mu'allim nada shekara goma sha takwas yanzu, se yan biyu mata Husna da Hasna masu shekaru sha biyar sannan Mariya me goma Zayyad me shekaru takwas sai kuma Abdallah data haifa watanni uku baya.

Fadar tashin hankalin da akasha da Hajiya akan cikin nan bata baki ne dan tabbas Allah ya hakunta zuwan sa badan haka ba iyakar ba?in cikin da takaicin da Anty ta ringa sha na Hajiya da gori da cin mutunci akan tazo tana ta zuba yaya saboda taci gado yar matsiyata yaci ace cikin ya bare kota haifi yaron da lalura se gashi Allah ya bata lafiyayyan ?a kuma Namiji abinda ya sake gigita Hajiyar ta ringa abu kamar wadda ta zauce, Allah kaWai yasan da yanda tasha kan Alhaji haka ya saka Antyn a gaba taje Asibiti aka juyar mata da mahaifa wai da shekarunsa rututu ga manyan yaya abin kunya ne ace har yanzu ana haihuwa a gidansa yana haifar ?annen Jikokinsa badan Manyan Yayan Alhaji Babannan da Babangida duk Mazane ba da yanzu ma ya fara aurar da jikoki itama Antyn tace daman ko bece ba ta gama haihuwar.

KarSan Abdallan yayi daga hannun Mariya dake jijjigashi yana cewa
"Ya haka, me yasa yake kuka kuma?"
"Wlh Yaya Hasna ce ta ja masa ?afar da akayi masa allura wai zata fi saurin saki shine fa yake ta kukan nan". Ahmad ya harari wadda aka kira da Hasna ta sunkuyar dakai kafin yace
"Banda cin zali ya za'ayi kija masa ?afa? idan ke kikaji ciwo aka taSa miki ya kikeji hum?"
"Kayi ha?uri Yaya" ta faWa tana sadda kai ?asa, yayi tsaki kafin ya juya da yaron?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya fita Husna Usainarta tace
"Wlh Naso Yah Faisal ne ko Yah Salim da kinji a jikinki banza muguwa kawai.

A falon Momy da Ahmad ya shiga ta karSi Abdallah tana cewa
"Meya samu babana tun Wazu nake jiyo kukansa kuma dai shi baya kukan banza?"
"Wai Allura akayi masa" ya bata amsa bayan daya sake gaiaheta.
"Wayyo, Babana yau ansha ?arfe, yi shiru kaji kar suyi mana dariya ace tsohona rago ne, Allah ya taimaka bata saukar masa da zazzabi bama zuwa safiya in sha Allahu ze ware" ta faWa tana zare masa dogon wandon dake jikinsa ta cire masa Diaper da aka matse masa cinya tana sake cewa
"Da gani wannan aikin Hasna ne uwar raino yau kam ai a Waga masa ?afa da wata Diaper a barshi yaji da sagaggiyar cinya" tana cirewa kuwa ya dena kukan ya shiga wulla ?afa, Ahmad yayi murmushi yace
"Babu baki, ?ila ma duk abinda ya takurashi kenan yake ta kukan haka su kuma basu sani ba, ina Anty Muna badai ta wuce ba?"

"Ka ganni Amadi sallah nayi kai nake jira ka shigo musha hirar yaushe gamo" Anty Maimunan ta faWa tana fitowa saga Bedroom Win Momy. A nan yaci abincin dare tareda Salim da tunda garin Allah ya waye se sannan ya shiga falon ya zauna da Momyn suka gaisa kuma yana gidan wuni sur sallar Juma'a kawai ya fita ya dawo wai bashida lecture a makaranta shine ya wuni bacci. Har gurin sha daya kafin Ahmad yayi musu sallama ya tafi makwanci ransa cike da mamakin abinda ya samu wayar Fatima yana zaunen ya kira yafi sau goma amma still busy ake gaya masa, abin ya bashi mamaki dan layinta akan tsarin call waiting yake in dai wayace da zasu gaya masa sedai idan a DND ta saka wayar ko kuma a kashe take sharrin Network yake ce masa busy, haka ya kwanta duk yanajin babu daWi ga kewar muryarta duk ta cikashi danya saba koda ba wata hirar soyayya suke ba amma yana jin daWin magana da ita a haka bacci yayi awon gaba dashi.

FATIMA
?arfe Waya harda mintuna suka gama Ajin ranar dan Lecturan nacewa yayi akan se yayi covering abinda ya rage mana sannan yayi fixing musu test ranar Monday saboda Next week ake saka ran fara First Semester exam. Sanda suka fita har an fara tafiya Masallaci, tayi murmushi tana kallon yanda Mazan Makarantar suke tafiya a sahu cikin shiga me kyau a fili tace
"Allah mun gode maka da kayi mu musulmai, dan Allah Badar kalle su, ina son Juma'a a school Win nan ranar ne wanda ma baka taba zaton musulmi bane zaki ganshi da Kaftan ya tafi masallaci".

Haka suka ringa hira suna ratsa mutane har suka isa Hostel. A gurguje suka yi Alwala, cikim postgraduate Hostel suka fita zuwa masallacin yau basu samu ciki ba saboda sun makara dan haka a waje sukayi sallar kafin suka koma Waki.

Ta kira yan gidansu suka gaisa a wayar Baffa dan har sannan ba'a gyara wayar Ummansu ba, yaran Anty Sauda na gidan ta Sata lokaci sosai suna magana dasu harda Autar Goggonsu FaWima da taje gidan hutun makaranta. Tana gama wayar kiran JAY ya shiga, tayi ?aramin tsaki kafin ta sauka daga kan gado saboda hayaniyar mutanen Wakin sunyi ba?i Jama'ar Sururat kunsan mutanen Yarabawa badai Waga murya ba idan suna magana.

Guri ta samu me kyau ta zauna kafin ta duba wayar yayi mata two missed calls, kusan Minti goma tana jira ya sake kira dan tace ita ba Asararriya bace da zata kira layin waje da Katin Ahmad, harta fidda ran ze kira se ga wayar ta shiga Ringing bata ko tsaya dubawa ba saboda yanda zuciyarta take azalzalarta da son jin wannan muryar tasa ta kai wayar kunnenta sedai Muryar Ahmad tayi mata sallama ba wadda tayi tsammanin ji ba.

A ta?aice sukayi magana dan rabta babu daWi dalilin ta tsammaci JAY ne, ya gaya mata yana HaWeja ya kai Alhajinsu Biki dalilin tafiyarsa da sassafe kenan maganar batayi tsaho ba sukayi sallama yana kashewa kiran da take ta zaman jira ya sake shigowa.

Ajiyar zuciya ta sauke me ?arfi har ranta taji daWin da ta kasa tantance na menene amma dukda haka seda taja aji wayar na dabda katsewa kafin ta daga
"Hello Baby" ya faWa da muryarsa me tsinka daskararren jini kota daskarar da tsinkakken to itama dai daskarar da nata jinin yayi dan hatta bakinta ji tayi ya mata nauyi ta gaza furta komai seda ya sake cewa
"I'm sorry, Assalamu alaikum".

A hankali taja numfashi kafin ta amsa masa daga nan ta sakeyin shiru.
Jay dake tsaye gaban Mirror

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login