Showing 321001 words to 324000 words out of 467220 words

Chapter 108 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12101

bawai yayan AHMAD ABDULWAHAB BECHI kawai ba sannan Alhaji karku barshi shi kaWai, ina ro?on ku da ku kasance dashi a duk sanda bu?atar hakan ta taso koda kullum ba".

Hussaini ne ya fara mi?ewa ze bar falon Ashrab ya take masa baya hannunsa dafe da bakinsa a ?o?arin hana kuka me ?arfin dake kokarin kwace masa, suna fita kuwa kamar jiran umarni garada suka kware bakuna suna kuka kamar yan yara masu dauriya ne suke share hawaye kawai amma babu wanda ya tsawatarwa wani har seda sukayi me isarsu kafin cikin rawar murya Aliyu yace

"Yaya Jafar ze karSi Al'amarin nan? Duk nan mun sani bashida sha?i?i kamarsa me yasa aka zaSi Soye masa halin da Ahmad yake ciki?"

"Bana so na zama silar tauye kowa Yaya, idan Jafar ya sani ze baro duk abinda yakeyi ya dawo gida kuma suna tsaka da wasanni masu matu?ar muhimmanci a rayuwarsa ta ?wallo, yau zasu gama kafin mu isa na san bashi da sauran wani abu da zuwana ze hanshi ya cimmasa" Ahmad Win ya bashi amsa.

Kiran sallar Azahar ne yq tayar da sauran suka rankaya masallaci baki Waya se sannan kuma Alhaji ya fito daga falon daya Soye duk ya hargitse kamar Wanda ya kwana yana gudawa. Bayan an idar da sallah sun dade a masallacin har akayi sallar la'asar suka kammala saukar Alkur'anin da suka rarraba kafin su Ahmad suka koma cikin bayan sunyi sallama da yan uwansa kowanne ya wuce gida Dr Hassan, Salim, Yakubu se Ashrab da Hammad dan gurin Alhaji Abdullahi ne sukayi saura.

Cikin gidan suka wuce kai tsaye, yaya matan suna zaune jigum jigum kowacce dachijabi da carbi a hannu fuskoki sun kumbure saboda kuka, duk maganganun da aka tattauna a kunnuwansu ne dafifi sukayi a bakin kofa wasu ta gaba wasu ta baya suna sauraron komai da akace a falon.

?akin Hajiya yace Hammad ya shigar dashi, tana zaune jigum ta rafka tagumi. Babu wanda ya tsammaci Hajiyar zata ji wani rashin daWi dangane da ciwon Ahmad domin kowa yasan yanda ta washsheshi a gidan tun yana yaro har girmansa bata Soye ?iyayyar ta da adawar zumunchin dake tsakaninsa da Jafar amma se gashi ana gaya mata ciwon dake damunsa zama tayi a tsakar gida tana rusa kukan jaje, ta ringayi kamar me har ta gaji kafin tayi shiru har gida kuma tasa aka kaita ta dubashi dukda seda ta kwata halin taci zarafin Fatima har tana kiranta mayya waya sani ma ko ita ta lashe masa kurwa take neman binneshi za'a fake da daji?

Suna shiga Wakin tana kallonsa ta rushe da kuka tana cewa
"Amadu haka ka sake lalacewa? Ni Binta ma shiga uku ka ganka kuwa? Wannan ciwo masifa ne kuma bala'i ne, ina tsoron Allah ina tsoron wannan ciwo shi yayi ajalin ubana, har yau bana manta irin jinya me azabar da yayi. Haka ya rame yayi ba?i??irin kamar hakan nan ashe tsamurewar da kake tayi shine dalili kaima.

Amma wlh duk Aisha ce ta cuceka da ta mara maka baya ka auri mayya. Da zuciya Waya na tasarma hana auran nan amma saboda ni an camfani kowa kallon Azzaluma yake mun aka ce ba haka ba, ai gashi muna ji muna gani zata kashe mana kai wayyo na shiga uku idan y
Ka mutu Amadu wazan zaga ya kalleni yayi murmushi? Waye ze cigaba da kawo mun kayan alatu duk zagin da zan masa bazeyi zuciya ba wayyo Allah na" ta Wora hannaye akai tana rusa ihu.

Murmushin ?arfin hali kawai yakeyi kafin a hankali yace mata
"Ki yafe mun idan na Sata miki rai a tsayin rayuwata Hajiya"

"Haba Amadu, ai ko ma?iyin Allah baze ce yana da tabonka a zuciya ba sedai hassada irin ta mutum, kuma meye abin neman yafiya? Zakaje ka dawo lafiya lau ai ba gani ba na warke kaima ras zaka dawo" yiiiiii ta fasa wani kukan shidai Hammad da duk haushin Hajiyar ya cikashi ya turashi suka bar Wakin suka shiga na Hajiya Rabi.

A can uwar Wakanta suka sameta tasha kuka ta godewa Allah idanunta sunyi luhu luhu da?yar ta iya buWe baki sukayi magana daga nan suka wuce falon Momy inda dandazon yan uwanta da aminan arzi?i suke zaune har da Anty Sauda tareda wasu daga cikin dangin Fatima. Ya ringa wulga ido yana neman Momyn amma be ganta ba, Anty Maimuna na goge hawaye tace

"Tana cikin Wakin ta ku ?arasa" suka wuce cikin suka bar matan falon na share hawaye, waWanda basu ganshi ba tunda ya fara ciwon hankalinsu ya sake tashi matu?a domin da yawa basu tsammaci ciwon yaci ?arfinsa har haka ba.

Momy na zaune akan sallah tana jan carbi Fatima na kwace a bakin gado hannunta ri?e da carbin itama tana ja, a can ciki suka amsa musu sallama dan kowacce ta daWe da rasa muryarta. Hammad ya tsayar dashi inda Momy take kafin ya juya ya fita ya barsu su uku, Ahmad na kallon Momy data Wauke kanta gefe murya a raunane yace

"Har yanzu fushi kikeyi dani Momy?"
"Me yasa zanyi fushi dakai Ahmad? Ni bakayi mun komai ba" ta faWa ba taareda ta kalle shin ba, a hankali yace
"Kiyi ha?uri Momy, a duniya babu abinda nake gudu kuma bana son gani irin tashin hankalin ki shiyasa na Soye miki".

Hawaye masu Wumi na sakko mata tace
"Ya zamuyi da ?addara Ahmad? Tilas mu karSe ta mu kuma godewa ubangiji sannan mu ro?i taimakonsa ya hanemu da biyewa sa?e sa?en zuciya karta kaima ga aikata saSo amma kam ?unci da damuwa kan dole ne Ahmad mun kulla aure dasu"

"Ku lazumci karanta la'ilaha'illallahul azimul halim
La'ilaha'illallahu rabbul arshil azim
La'ilaha'illallahu rabbussamawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil karim in sha Allahu duk wani ?unci da damuwa ze barku, Addu'arku kaWai nake da bu?ata a yanzu da bayan bana nan karku zubar mun da hawaye" Ahmad ya faWa yana kama hannun Momyn dana Fatima, a tare suka sakar masa kukan daya karya duk wata jarumtarsa har seda ya bawa nasa hawayen da yake ta fafutukar hana su zuba sakkowa a lokacin.

Cikin muryar kuka yace
"Allah kasan ina sonsu, kai ka ?addara zan barsu yanzu ka kulamun dasu ka basu ha?uri da juriyar tunkarar duk wani al'amari bayan babu ni"

Kalaman sa suka ?arawa kukansu ?aimi, sun Wauki lokaci me tsayi suna kukan, Mama Balaraba ce ta le?a saboda Baba Al?ali da yayi maganar su fito su tafi, jirgin ?arfe shida zasu bi zuwa Lagos gashi har karfe biyar tayi, yanda suka haWa kai su ukun gwanin tausayi suna kuka yasa ta shiga rarrashinsu tana share nata hawayen daga ?arshe banWaki Momy ta shige ta barsu.

Har cikin falon da Alhaji ya shiga ya kulle kansa ya bishi yayi masa sallama suka kuma yi wasu maganganu tareda sauran wanda suka rage basu tafi ba kafin suka kama hanyar airport, duk yanda akayi da Momy akan tazo tayi masa rakiya kuwa tace ba zata iya ba se su Anty Maimuna ne suka bisu tareda tsirarun wayanda Baba Al?ali ya bari su bisu saboda koke koken da matan suke tayi.

Ahmad Win se Dr Hassan, Salim, Ashrab, Al?ali Yakubu da Yakubu ?arami se kuma Fatima suka tafi Lagos, acan suka tarar da Hussaini da Aliyu harda Aminu. Damuwa da Alhinin rabuwa da Ahalinsa ta mots masa jikin dan ma Dr Hassan yana tafe da yan ?ananun abubuwa daya san ze iya bu?ata na gaggawa dukda haka suna sauka Asibiti suka wuce dashi, wannan ya sake Waga musu hankali, ?arfe goma sha biyu da rabi na dare jirginsu ya Waga zuwa kasar ingila, sun tafi cike da taraddadin jikin Ahmad dan a yanayi na rai fakwai mutu fakai suka tafi dashi sun kuma bar mutanen gida cikin yanayi marar misaltuwa, dukda cewar sun rigda sun karaya, amma basu cire rai da ikon Allah ba domin dai shine me kashewa ya kuma raya a sanda yaso.

A can gida bayan fitar su Ahmad a hankali Alhaji ya saki numfashin daya tokare masa ma?oshi har yakejin tamkar wa'adin iskarsa ya ?are, direwar numfashin ta taho tareda kuka, akan hannu kujera ya kwantar da kansa ya bawa hawayensa damar zuba sosai har suka fara ji?e takardun dake ajiye a gurin, seda ya samu rangwamen kaso me gwaSi na daga abinda yakeji a ransa kafin ya tashi yana layi tamkar wanda ya shawu ya haye sama yasha magungunansa sannan ya kwanta yana kallon sili a ransa yana tunanin rayuwa tun daga ?uruciya har zuwa yanzu.

*************
Shida saura agogon landan bakwai saura a Nigeria jirginsu ya sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na Heathrow, tamkar kuma jikin Ahmad Win yana jiran lokaci suna sauka shima ya farka daga baccin dolen da aka sanyayi cikin wani yanayi daya gama kiWimar Fatima, Dr Hassan da Salim da sukazo tare dashi har suka fara kukan rasa shi domin basu hangi alamar sauran lokaci tattare dashi ba sedai kuma cikin hukuncin ubangiji bayan da suka isa Asibitin cikin motar Waukar marasa lafiya ta Asibitin da suka tarar tana jiransu babu Sata lokaci likitoci sama da goma suka rufu akansa kowanne yana gwada kalar nasa ilimin da baiwar da Allah yayi masa har kuma suka samu nasarar lafar da ciwon daya taso masa sedai yanayin fuskokinsu bayan sun fito ya sake jefa su Fatiman cikin ruWanin abinda ya kamata suyi.

Farin cikin yana raye ko kuwa damuwar rashin gamsuwa da fuskokin likitocin da basu ce musu komai ba bayan shaida musu yana raye?
Se daga baya ne ma suka kira Dr Hassan, bata san me suka ce masa ba shima daya fito fargaba da damuwar kan fuskar sa ta ninka farkon zuwansu.

Tana zaune kan kujera ta jingina kanta a bango gaba Waya ta fice daga hayyacinta, bakinta a bushe ?amas, rabonta da abinci tun kunun da Momy ta tilasta mata tasha kafin su taho a jirgin kuwa ko ruwa bata iya sanyawa cikinta, ga damuwa, ga gajiya ga tata lalurar da take Wauke da ita a jikinta.

Cikin tsananin tausayawa Dr Hassan yace
"Sannu Fatima, sunce jikin nasa da sau?i har na ro?i ko zamu iya ganinsa yanzu amma sunce Aa, ki daure mu tafi masauki yanzu ki samu ki huta zuwa yamma idan Allah ya kaimu nasan zasu bari mu ganshi in Allah ya yarda".

Haka ta ringa binsu zalo zalo ba tareda tace komai ba har suka fita daga Asibitin ya tare musu taxi, babu nisa tsakanin Asibitin da Hotel Win daya kama musu Waki. Bayan tayi wanka tayi sallar Asuba data riskesu a jirgi tana zaune tana kurSar ruwan shayi da take jinsa tamkar maWaci hannu guda tana danna wayarta. Tunani takeyi ta yanda zata kira gida ta sanar dasu sun sauka da kuma halin da akw ciki kuma bata da layin ?asar sannan bata san ma ina ne Wakin da Dr Hassan ko Salim suke ba balle ta ari wayarsu dan tasan su ba zasu rasa ba.

Dabarar kunna WiFi ce tazo mata yana connecting kuwa ta shiga WhatsApp ta kira Momy voice call, a ta?aice sukayi magana daga nan ta kira Ummanta suka gaisa harda Baffa yana ta ?arfafa mata guiwa tareda addu'oin Allah ya tashi kafaWun Ahmad kafin ta ajiye wayar ta kwanta badan tana jin bacci ba se dan kawai komai ma ta gaji dashi.

*************
PARIS, FRANCE
Jafar na tsaye gaban dressing mirror yana taje sumar kansa da tayi yawa, yakai kusan sati shida rabonsa da aski shida duk satin duniya yakeyi aski. Fatiyyah na kwance akan gado tana danna waya ta kalleshi tace

"Wai me yake damun Ahmad ne naga kowa yan gidanku suna ta status da hotonsa sunata wasu maganganu".

Kallonta yayi kamar be gane abinda take faWa ba ko kuma yaya ne oho, ta taSe baki bayan data saci kallonsa dan tasan baze wuce yayi mitar daya saba yace batada kunya tana kiran sunan Yayanaa gatsal ba, Jafar kuwa can wani lissafi ya tafi a ?wa?walwarsa. Kusan sati uku kenan da ya san Yah Ahmad bashida lafiya appendix ya fito masa har ma an saka rana za'a cire kuma se aka Waga aka bashi magani suna jira suga ko ze narke a yanda ya sanar masa kenan amma be yarda ba yana jin kamar akwai abinda Ahmad Win yake Soye masa, abinda yasa be tsananta ba saboda beji wani abu daban a gurin wani ba, ya bari akan koma menene zeje gida saboda sauran lokaci kaWan zasu buga wasan samun gurbi a gasar buga kofin duniya da za'ayi shekara me zuwa wanda kuma shine wasa na ?arshe da yake zaton ze buga, gaba Waya ma yana shirin yin ritaya ne daga buga ?wallon gaba Waya saboda abinda shima be san komenene ba.

Hannu ya mi?a mata yana cewa
"Kira AFEYAH a wayarki ki bani" kafin ma ya dire ta zaburo masa tana cewa
"Wai me kake nufi Jafar? Fatima ne baka iya faWa ba ko kuwa wani sabon salon munafunci ne yasa kake kiranta da Afeeyah? Wato tana tuna maka da tsohuwar budurwarka ko? Naga ko shi mijinta ban taSa ji ya kirata da wani suna idan ba Fatima ba se kai uban kilibibi ko kunya baka ji wlh shiyasa tunda nasan Afeeyah ake kiran matar nan a gida na tsaneta wlh idan bakayi wasa ba sena kunna maka bala'i, karan Ahmad zanyi mace kana son matarsa saboda tana sa sunan tsohuwar budurwarka aikin banza kawai".

Yana jinta tana hargagin ya wuce cikin wardrobe Winsa ya sako kaya kafin ya fito yana Waura agogo, tarata kawai yakeyi kuma kwana biyu ba wani daWin jikinsa yakeji ba dan da?yar ya iya buga wasan da sukayi jiya. Fita yayi ya bar mata gidan yana ji tana ta maganganu, yana tafiya a mota ya kira Faisal yana so yaji ko ya siyawa Hajiya wata wayar da yace masa dan tun sanda sukayi hatsari ba'aga wayarta ba idan zasuyi magana sedai ta wayar Faisal ko Sarah wasu lokutan kuma basa gida. A kashe yaji wayar Faisal Win, seya mayar da akalar kiran zuwa Sarah.

Murya a dashe ta amsa wayar ta gaisheshi kafin ma ya tambayeta meya sameta ta fashe masa da kukan daya sakashi yin fakin a gefen titi babu shiri san tu?i yakeyi a jona wayar yayi da sifikar motar

"Waya mutu?" Ya tambayeta dan yanayin kukan nata yafi kama da na Wanda akayiwa mutuwa, kafin ta tsaida kukan ta bashi amsa sega kiran Dr Hassan dan yana da number sa ta Uk, sukan haWu jefi jefi idan ya shiga be san me yasa yayi saurin katse kiran Saran ba ya amsa na Hassan, yanda yaji muryarsa yasa zuciyarsa ta tsananta bugu, kodai Hajiya ko Alhaji cikin biyu Waya ya mutu tunanin da ya ringayi kenan.

"Mun shiga Landan tareda Ahmad, munso mu kiraka tun kafin muzo to kuma se yace Aa kana da hidimomi yasanka idan kaji zezo zaka iya ajiye komai saboda shi kazo, kuma baya son haka, yanzu dai idan kana da lokaci a ?alla zamu iyayin sati guda, zaka zo ko mun samu s
dama muzo?" Dr Hassan Win ya faWa masa abinda ko kusa hankalinsa be Wauka ba, ta yaya ma za'ayi Ahmad ya tashi zuwa Landan be gaya masa ba ballantana ya tambayeshi abubuwan da yake da bu?ata ya taho masa dasu?

Kai tsaye yace masa
"Babu wani dalili da ze saka kai da Ahmad kuje Landan tare se na rashin lafiya ka gayamun me yake damun sa?"

Daga can gefen Dr Hassan yayi shiru kamar baya kan layin kafin a sanyaye yace masa
"Wata yar rashin lafiya ce ?arama, muna The Royal Marsden idan dai kanasa dama kayi ?o?ari kazo kawai".

Tamkar wanda ya jefawa dutse akai haka yaji wani duumm a kunnuwansa kafin daga bisani suka washe harya fahimci ya katse wayar, ya ringa maimaita sunan 'The Royal Marsden' a fili kamar me tilawar karatu so yakeyi ya tuna inane? Me ma akeyi a gurin amma ?wa?walwarsa ta gagara bashi haWin kai seda ya nanata sunan sau babu adadi kafin ya samu haWin kan tunaninsa ta hanyar tuna gurin. "Badai Yah Ahmad ba sedai ko shi Dr Hassan Win ko kuma Alhaji suka kai" ya faWa a fili cikin tabbatar wa kafin ya tayar da motarsa ya hau titi ya juya gida kafin ya isa ya kira Manager sa akan yayi masa ?o?ari duk yanda za'ayi ya samu jirgi zuwa London, idan babu ya shirya masa shatar ?aramin jirgi na musamman yana da babban uzurin daya taso masa.

Yanda ya bar Fatiyyah haka ya koma ya sameta akwance tana ta aikin chatting da ?awayenta, kaya ya shiga haWawa, bata ko kalle shi ba ala dole fushi takeyi ya kira Fatima da Afeeyah. Seda taga ya fito da akwati yana sauri kafin ta tashi zaune tana tambayarsa ina zeje be kulata ba ya fice daga gidan ta taSe baki ta koma taci gaba da abinda takeyi irin shi ya sani.
Kafin ya isa Airport manager ya kirashi ya sanar dashi an samu jirgi kuma nan da awa Waya ze tashi.

Jian da yayi na awa dayar jin sa yayi tamkar shekara guda kafin Allah yasa suka tashi. Tafiyar awa Waya da rabi ya sauka a Landan, ?arfe biyar da yan mintina na yamma ya Wauki shatar tasi daga filin jirgi zuwa Asibitin.

Wani irin bugu zuciyarsa ta ringayi, tsoron da besan dalilinsa ba ya dirar masa jikinsa ya ringa rawa, yanda yayi nisa a tunani har besan sun isa ba seda baturen direban ya taSa shi kafin yayi firgigit ya tashi yana sakw gyara zaman hular sanyin kansa da takunkumi ya sallameshi ya sauka rungume da yar akwatinsa kamar sabon Wan ciranin daya shiga birni. Kasa shiga Asibitin yayi kawai ya samu can gefe can ya tsaya yana ?arewa masu shige da fice kallo, kusan minti goma yana tsayen kafin doshi ?ofar shiga duk taku Waya tsoro da firgici na sake dirar masa.

******************
?arfe huWu suka sake komawa Asibitin bayan sunyi gajeran lunch wanda kusan ita Dr Hassan yafi tilastawa da taci abinci saboda ma safe da aka kai mata haka aka fito dashi tea kawai tasha yanayinta kuma ya nuna dauriya kawai takeyi amma ita kanta abar a baqa gado a dubata ce. Suna hanya yake ce mata

"Na kira Jafar na san kuma duk inda yake yanzu zuwa dare ko gobe da safe zezo, hargagi kam zamu shashi sedai kawai mu toshe kunnenmu dan anyi masa ba dadai ba".

"Allah sarki Yah Jafar, ai wlh dai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login