Showing 402001 words to 405000 words out of 467220 words

Chapter 135 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12098

ya ganta farar fata ya zata yar masu kuWi ce yake kira a zo a tafi da ita.

Fiye da awa guda da wasu mintuna tun tana saka ran samun mota harta sare ta nemi gefen hanya ta zauna kawai tana jiran hukuncin ubangiji sega wata galleliyar mota ta tsaya a gabanta, yanda taga me kajin ya taso da sauri ya nufo inda take yasa bata san sanda ta wancakalar da akwatinta da Jafarta ba ta bawa ?afafunta iska, Jafar ya fito daga motar haka nan ya ringa dariya haka me kajin yace
"Ranka ya daWe ta bani tausayi wlh tun tana tsayar da mota harta gaji ta zauna gashi kamar kallon Wan kininafin ma take mun dataji wayata tayi ?ara zakaga ta sake matsawa". Jay ya masa godiya ya bashi kuWi masu yawa sannan ya Wauke mata jakar ya saka a mota yana hango yanda tayi nisa tana cin gudu danma kan titi take bi bata nausa daji ba. Daidai inda ta tsaya tana haki yayi parking ya sauke glass, suna haWa ido bema san sanda ta shiga motar jikinta na karkarwa ta zauna ta haWe kai da guiwa ta fashe da kuka, se kuma yaji babu daWi.

Haushi ta bashi Wazun yanda ta ringa masa rashin kunya shiyasa ya ajiyeta ya juya warsa Kano tunda dama saboda ita zeje Kadunan ya karSi number me kajin ne dan yaji halin da take ciki har ya tsaya yayi sallar juma'a ya kusa ?arfi ma daya sake kirashi yace bata samu mota ba shine kawai zuciyar musulunci tasa yayi niyyar juyowa se kuma motar ta tsaya seda yayi waya aka kawo masa wata aka Wauki waccen Win sannan ya juyowa. Zuwan da yayi jiya gurinta ne ya zame masa jidali, haka kawai ya tadowa da kansa tsohon tsumi, soyayyar ta me zafi ta ringa dafa zuciyarsa daren da?yar ya iya runtsawa in ya tuno yanda ya barota tana kuka duk se yaji ya tsani kansa tunda shine sanadin kukan nata. Kukan kuma shi ya tabbatar masa da har yanzu akwai soyayyar sa a ranta kamar yanda yake dakon tata soyayyar ?arya kawai suke shararawa da suke cewa basa son junansu shiyasa ya kira driver yaran yace base ya Wakko su ba zeje dakansa duk don yaje gidan ya ganta seya fake da Wakko yara daga school.

Shiru suna tafiya har tayi kukanta ta gaji bece mata komai ba seda yaga ta Wago ta mayar da kanta jikin window tana kallon waje kafin ya nemi guri ya gangara gefen hanya ya tsaya. A baya ya Wakko ruwa ya mi?a mata, ta kalleshi ta kalli ruwan sannaan ta karSa nurya kamar an masa dole yace
"Ki wanke fuskar ki". Ta Salle murfin motar, haushin kanta me tsanani ya kamata data fahimci motar da tayi zaton ta kidnappers ce ta ringa gudun ceton rai ce. To ya akayi ta rikice? A saninta ba'a wannan motar suka fito ba waccen farace glass Winta me haske ne wannan kuwa ba?a ce siWik haka????""""""" "
" " "
""""""""""""""""""" "!"""#"$"%"&"'"(")"*"+","-"."/"0"1"2"3"4"5"6"7"8"9":";"<"=">"?"@"A"B"C"D"E"F"G"H"I"J"K"L"M"N"O"P"Q"R"S"T"U"V"W"X"Y"Z"["\"]"^"_"`"a"b"c"d"e"f"g"h"i"j"k"l"m"n"o"p"q"r"s"t"u"v"w"x"y"z"{"|"}"~""?" gilasanta har na gaba rabinsa an masa tint ita ce ta rikice tun farko ko kuwa mugunta tasa ya canzo mota danya wula?anta ta?
Ta wanke fuskar ta koma cikin motar dan tasan idan ma ta sake cewa ya ajeta ?arshe sedai ta isa Kaduna da ?afa tunda yau da ?afar hagu ta fito bata da sa'a.

Ledar abinci ya sake Wakkowa ya bata ta haWe rai ta?i karSa ya Wage kafaWa ya mayar ya tada motar suka cigaba da tafiya kafin yace
"Kunyi maganar da Baffa kuwa?" Tayi masa shiru. Ya kalleta cikin hasala yace
"Ok I'm sorry for dropping you on the road, Sata mun rai kikayi kin san abubuwan da bana so amma kina jin daWin yi mun su. Bana so ina kai miki hannu amma ke kika tunzurani duk yanda mutum zeyi miki abin kirki ba zaki yaba ba sedai wula?anci ya biyo baya saboda kinga nayi sanyi ko? Ai kinsan ba haka nake ba da amma kici gaba, you will regret it soon" yayi ?wafa har suka isa gidan Badar da tayi mamakin yanda akayi ya sani be sake ce mata komi ba. Da?yar Nurain yasha kansa ya shiga ciki, yana zama wayarsa tayi ?ara ya Waga Afeeyah ta tsaya tana kallonsa ganin yanda fuskar sa ta canza da alama abinda ake gaya masa a waya bame daWi bane.

Sarah ce ta kirashi take ce masa "baka zo asibiti ba tun jiya Yaya gashi har an sallameta mun dawo gida yanzu". A ta?aice ya ce mata
"Meya faru?" Dan ya gane zancen hajiya ne ta gaya masa komai a gajarce ya mi?e yana cewa
"Ina Kaduna amma yanzun zan kamo hanya. Ya jikin nata da sau?i amma?" Cikin damuwa yayi maganar daga nan ya kashe bayan data tabbatar masa Hajiyar tana lafiya se abinda ba za'a rasa ba. Fuuuu kama iska Afeeyah taja akwatin ta ta shige Wakin Badar duk suka bita da kallo shidai yayi musu sallama bayan ya gaya musu uzurin daya taso masa. Afeeyah kuwa kasa zama tayi data shiga Wakin. Gaba Waya abinda zuciyarta ta raya masa matarsa ce tayi kiransa shine ya tashi kamar mazari ya tafi da Badar ta shiga tace mata ya juya Kano bata kuma ce mata komai ba akan abinda ya mayar dashi seta sake tabbatar da hakan ne, ranta ya sosu, sabon fushi ya tashi.

"Na aiketa ne ko yaya balle nabi sawunta asibiti? Ai bata nemi izinina ba kafin ta tafi neman jidalin, haka wacan karon da sukaje sukayi hatsari babu wanda yasan inda sukaje, indai juninta haka wata rana zataje ta mutu a banza ba'a sani ba" Alhaji Audu ya faWawa Jafar daya shiga gurinsa bayan ya fito daga falon Hajiyar data gama masa kuka tace daga zuwa gidan Dr Hassan Zubaida ta kamata da kokawa ta kada ita kuma Alhaji ko bi takai beyi ba harta kwana a asibiti shida matansa babu wadda yaje dubata. Yasan dai zancen wai Hajiya Zubaida ta kamata da kokawa ba gaskiya bane koda kuma hakan ne to ita ta jangwali faWan aka fi ?arfin ta domin dai yasan halin ta sarai kawai dai yaji rashin jin daWi da Alhajin beje ko ya aika an dubota ba, duk da halinta ai matarsa ce ko babu komai taci arzi?in su.

Yayi shiru kafin a hankali yace
"Amma Alhaji harda rashin kulawar da kake nunawa Hajiya yake ?ara ta'azzara lamarinta. A baya sanda kake ta tata ai ba haka take ba abubuwan da sau?i amma yanzun damuwa tayi mata yawa, kuma auran nan ma daka Wakko zakayi da dai ace kawai" seya kasa ?arasa saboda yanda Alhajin yake kallonsa sannan shi kansa maganganunsa basu wani yi masa ma'ana a kunne ba. Alhaji ya gama ?are masa kallo kafin yace
"Oh, ta yi nasarar ya?ar naka auran ta wargatsa shine ta turo ka ka ya?i nawa? To kai kayi kaWan ka koma kayo gayya tukunna may be idan kuka dakeni naji a jiki na se na janye na fasa auran, kulawa kuma na?i na batan, ko kai ne me rubuta lada da zunubi akan lamarin Binta nuddin kace ban kyauta ba ka zalunce ni. Tashi ka bani guri in Allah ya yarda ranar lahadi i yanzu ina tare da amaryata idan yaso da kai da uwarka ku haWiyi zuciya ku mutu".

Jiki babu ?wari Jafar ya mi?e, har ya kusa ?aramar kofar komawa cikin gida Alhaji ya dakatar dashi yana cewa.
"That reminds me. Malam Hafizu ya kirani, duk yanda yaso ya canza zance ya Worawa yarinyar laifin da bata aikata ba na gane uwarka tayi tasiri ta yuwu barazanar data saba taje tayi musu ko kuma kaita aika ko? To duk Waya. Nan Ummu tazo jiya ta ro?e ni arzi?i akan in baku lokaci. Wlh kai baka isa kasa nayi kaffara ba, tunda farin cikin uwarka ka zaSa sama nawa da wasiyyar Wan uwanka daya rayu yana baka kariya, abu Waya ya ro?i alfarmar kayi masa ka?i dukda cewar ya ?are tasa rayuwar gurin ganin ka samu farin ciki. A cikin falon nan cikin kalamansa na ?arshe seda ya ambaci mu kula da kai karmu barka kai kaWai kar a bari kayi kewarsa amma ka kasa yi masa abinda kai da kanka ka faWi ya bar maka wasiyyar yinsa. Matarsa kaWai yace ka aura ka ri?e masa yaya amma ka kasa. Na taya ka jin kunya Jafar, idan na rantse bazanyi kaffara ba ko mace huWu ka bari a yanda Ahmad yake jin ka ze iya sakin matarsa ya aure naka duka amma kai ka kasa yi masa wannan alfarmar, ai shikenan Allah ka ji?an Ahmad ka sa yana masauki maWaukaki wanda ka keSancewa salihan bayinka" yayi shiru saboda muryarsa da tayi rauni.

Kuka Jafar ya saka daga inda yake tsaye kamar ?aramin yaro yake cewa
"Wallahi ina ji ina ma ni Win ne na mutu ba shi ba nasan Momy ba zata masa abinda Hajiya takeyi mun ba, da yanzu ran kowa be Saci ba saboda shi, albarka ce zata cigaba da dabaibayeshi shi ba tsinuwa da tashin hankula ba, idan da anso na zama kamar shi ai se a haifeni a Wakin da aka haifeshi"

"Fitar mun daga nan, kuma ka gaya mata na saketa saki biyu, idan taga dama tayi zamanku bani da matsala da ita" Alhajin ya sake faWa take kukan Jafar ya tsaya cak.

*Kina neman abin cire kwaWayi? Ke ma'abociyar kayan ?walama ce irin su cake da dangoginsa? Kina neman cake me farfesun madara (milk cake) me tayar da kai da cire duk wata ?walama? Ina gabatar muku da MCUBES BAKERY (08134606094). Kunsan dai bana tallata abin banza domin ba kasuwanci kaWai nake dan na samu kuWi ba, daWi nake ji na zama silar da mutum ze samu ingantaccen abinda ze gamsar da bu?atar sa. Ku gwada cakes Winta issa money back guarantee. Har yanzu da nake rubutun nan baki na cike yake da garWin Milk cake tareda cocunut heaven Win ta dana kora nake ji. Kunga coconut heaven Win nan, bari nayi shiru kar in saki layi, Location Sharada Kano tana aikawa ko ina*.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 39*

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

Cikin razana yace haba Alhaji, haba dan Allah ya zaka yanke wannan Wanyen hukuncin?"
"Nine na yanke Wanyen hukunci? To fitar mun daga Waki kafin ka zageni ko ka rufeni da duka, ka kuma tabbatar da ka gaya mata sa?ona" Alhaji ya tare shi, yanda kuma Alhajin ya tsare gida yasa tilas ya haWiye sauran maganganun sa ya juya kamar me ciwon wuya yana waiwayen Alhajin. Ya tsaya a bakin ?ofa yana saita kansa amma nutsuwar ta?i zuwarasa. Zargin kansa yakeyi da lalata komai, shine silar mutuwar auran Hajiyarsa a ?o?arin sa na kuSutar da ita yaje ya ?arasa lalata komai. Yanzu shi ta yaya za'ayi ya sanar mata da wannan sa?on? Ta ina ze fara?
Gaskiya baze iya ba, baze taSa iya furtawa Hajiya waWannan muggan kalaman ba kuma ta silarsa.

Tafiya yayi har ya kai gurin motarsa ya tuna a can falon Hajiyar ya baro mu?ullin da wayarsa. Yayi jimm dan so yayi ya gudu ba kuma ze sake waiwayar gidan ba har se wutar taci ta cinye da ace iyakar mu?ullin motar ne ma tafiya zeyi amma wayarsa na gurin kuma wadda tafi muhimmanci a gurinsa. A hankali ya juya ya koma ciki yana ?issima yanda ze kaucewa Hajiya ya fito ba tareda ta tsayar dashi jin ba'asin zuwan sa gurin Alhajin ba, daga ?arshe duk yanda ya lissafa zeyi se yaga babu fita tsareshi zatayi ?ila tasa ya furta sa?on da aka bashi. Fasa shiga Sangaren Hajiyar yayi ya wuce na Momy.

Tana zaune hannunta ri?e ?wayoyin magungunan data Sallo zata sha, kwana biyun bata jin daWi sosai, kewar Ahmad ke damunta, yawan tunanin da takeyi kuma yasa ?irjinta ya matsanta mata da ciwo seda ta koma asibiti rubuta mata magani. Yana shiga falon kamar wani ?aramin yaro ya zauna a ?asa ya fashe da kuka. Momyn tayi hanzarin haWiye maganin hannunta ta shiga tambayar sa meya faru amma kamar tana tumzurashi yaci gaba da kukan harda shashshe?a gaba Waya ya Wagawa Momy hankali se tambayar sa takeyi meya faru amma ya?i cewa komai seda ya mula yayi me isarsa kafin murya na karyewa ya gaya mata Alhaji ne ya aikeshi wai ya gayawa Hajiya ya saketa.

Momy ta ringa salati ta zauna jiki a sanyaye tana kallonsa tace
"Kuma ka gaya mata?"
Ya girgiza mata kai alamar Aa, ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace
"Amma dai shima Alhaji be kyauta ba, wane irin abu kenan haka? Gara da baka gaya mata ba. Yanzu dai ka dena wannan kukan dan Allah kana Waga mun hankali kayi shiru bari na kira Al?ali ai bama ze yuwu ba" ta janyo wayarta ta shiga kiran Al?alin sedai rashin sa'a aka ce wayar a kashe. Ta Wauki hijabin da tayi sallah dashi ta saka tana ce masa
"Tashi kawai muje gidan mu same sa"
"Aa Momy, da dai kawai a kira Momy ko Ashrab se su haWaki dashi" Jafar ya faWa seta girgiza kai tace
"Babu wannan maganar gara muje mu iske shi a daren nan a kashe maganar nan tun ba'a janyowa yarinya da iyayenta kata'i ba. Ya za'ayi ya saki Binta akan auren Fatima? Haka kawai ma ta washshi yarinyar balle yanzu ace tayi silar mutuwar auranta ai baze yuwu ba gara Al?alin yazo su san ma duk yanda zasuyi a kashe maganar bazan iya da jidalin Binta ba dan nasan har ni se abin ya shafa" ta fice daga falon bashi da zaSi dole yabi bayanta bayan daya share hawayen fuskarsa idanunsa sunyi jajir.

A fili yayi hamdala sanda ya le?a falon Hajiya yaga babu kowa alamar ta shiga ciki, ya kwashi wayarsa da mu?ullin motarsa da sauri ya fice. A hanya Momy nata mitar me yasa Alhajin zeyi haka. Yayi ?asa da murya yana gaya mata abinda ya faru har ya janyo wannan hukuncin na Alhaji, Momy ta ringa salati tana kallonsa tace
"Amma dai kai mutumin banza ne Jafar. Yanzu ashe kai ka kitsa komi a rashin hankalinka gyara zakayi gashi nan ka lalata komai a maimakon ka gyara yanzu wa gari ya waya? Ina amfanin katoSarar da kaje kayi?" Shi dai be iya ce mata komi ba har suka isa gidan Al?ali tana masa faWa bayan sun isa kuma suka haWu ita da Mama Balaraba suka sashi gaba kafin Al?ali ya Wora da nasa.
Al?ali yace
"Banda rashin tunani taya zakaje ka samu yarinya ka yi mata waWannan maganganun? Ai yanzu kaji daWi ko? Ka janyo mata saki. Ni babu ruwana babu kuma inda zanje, salon tace da haWin baki na bayan kai kaje ka shirya komai a sokwanci irin naka. Se kaje ka isar mata da sa?on tun wuri tasan matsayinta".

Gaba Waya suka sake caza masa kai. Shida yayi tunanin samun mafita se gashi suna sake jagalgala komai kowa shi yake bawa laifi. Meye aibu cikin abinda yayi? Shifa maslaha ya nema saboda tunanin da ?wa?walwar sa ta bashi ta hanyar tunzura Afeeyah tace bata sonsa da kanta ne ze kuSutar da auran Hajiyarsa, idan yaso daga baya idan komi ya lafa seya koma ya lallaSa Hajiyar ya auri Afeeyar cikin daWin rai amma kowa ya kasa fahimtar sa kusan ma marinsa Al?alin yayi da yake ?o?arin fahimtar dasu kyakykyawar niyyar daya aikata abin da ita. Haka ya mayar da Momy gida bayan da?yar ta shawo kan Al?ali tace yaje ya samu Audu, tunda da gyara a sasanta bama se wani yaji ba maganar ta tsaya iyakarsu shikenan.

Ya isa gida ya tarar da Fatiyyah, irin tsayuwar da tayi a falo tana kallonsa ya tabbatar masa cike take da nata bala'in se kawai ya Wauke kai kamar be ganta ba ya wuce sama tabi bayansa har Waki tana sakar masa maganganun daya fahimci tana da masaniya akan tafiyarsu da Afeeyah Kaduna kowa ya gaya mata oho.
"Nan ka fita ka barni ina murkususun ciwo ban ko isheka kallo ba ashe ka tafi gurin yar iska karuwa munafuka, babu ko kunya ka Wauke ta a mota ku tafi Kaduna wlh kaji kunya Jafar. Duk matan duniya farare da ba?a?e ka rasa wa zaka so se Fatima, ?as?antacciya, ina faWin rai da jiji da kan nata suka tafi? Ka gama tisa mun rashin mutunchi kullum gaya mun kakeyi ni ba tsarar ka bace ba type Win ka bace ni ashe a lungun alfindiki taste Win naka ya ?are yar bakanike ita ce kalar ajin naka da kake faWi ai dai ka faWi babu nauyi wlh".
Yanda take maganganun cikin fusata babu ko War na tsoronsa a fuskar ta yasa ya shanye kawai ya shige Waki ba tareda ya tanka mata ba. Bata ha?ura ba ta bishi ciki, harya cire kaya ya Waura towel tamkar meyi da gunki bece mata komai ba seda tasha gabansa yana shirin shiga banWakin tace
"Wlh baka isa ka haWani kishi da ita ba. Ko kishiya zaka mun ka auro isashshiya da zan goga kafaWa da ita ba Fatima ba kuma sena gayawa Hajiya inda ka tafi tana can kwance a asibiti an raunatata a garin ?wato muku yanci kai kana can kana yawon barbaWa a titi da da guzuma me yaya huWu, duk ma abinda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login