Showing 204001 words to 207000 words out of 467220 words

Chapter 69 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12174

kamar wanda tayiwa kyauta daga ?arshe sukayi sallama bayan ya sake ro?arta akan dan Allah ko sau Waya ne a rana idan ya kirani ta ringa amsawa gaisawa kaiwai zasuyi baze ja mata lokaci ba tace Toh.

"Allah sarki Ahmad, wlh yana bani tausayi na daWe banga soyayya me zafi irin wadda yakeyi miki ba Afeeyah,dan Allah ki tausayawa mutumin nan yaci Albarkacin so wlh na tabbatar ba zaki yi nadamar auransa ba saboda yana sonki" Badar ta faWa, Afeeyah ta hararaeta tace

"Kyaji da fuska biyunki anjima idan Jay ya kira waya jikinki na rawa zakiyita karaWi kina bashi assurance na ze sameni ke ga campaign coordinator kuma se na gaya masa abinda kike cewa yanzu"
"Amma Thruth to be told Afeeya wlh Ahmad yafi sonki, ki gani fa shekara biyu yana binki kina jansa a ?asa na tabbata Jay baze Wauki haka ba Mace ta ringa wasa dashi kamar wani Toy, da yanzu ya daWe da sallama ki" Badar ta sake faWa. Afeeyah ta tashi zaune daga kwanciyar da take tace

"To ai banbancinsu kenan shi yasan mutunchin kansa baze zauna a ringa wula?antashi akan abinda yafi ?arfi ba shi kuwa Ahmad kamar mara zuciya ke nifa ba zan auri Mijin da zan ringa juyawa ba ga yan uwansa basa sona naje ana wula?antani baze iya tsayawa ya kwatar mun yanci ba".

Badar tayi kasa?e tana kallonta amma ta haWiye abinda tayi niyyar cewa ta canza maganar da wata tace
"Yawwa, nikam kinsan Familyn Jay ne?" kai ta girgiza mata tana cewa
"Aa, me yasa kika tambayeni?"
Tayi ajiyar zuciya zata yi magana kenan Ummi tayi sallama ta shigo, ciki ciki ta amsa fuska a Waure Badar ce ta tambayeta ya Exam ita kuwa ta zari Bucket ta fita dan tun daga ranar da Islam tace mata tana faWar maganganu akansu ta washsheta, bata son munafukin mutum, idan ta yarda dakai kayi breaking trust Winta shikenan kuma.

A gurguje tayi wanka ta shirya dan har Badar ta shirya zata fita Library tace ta jirata suje tare. Maganar da suka fara Wazu na rantaso take taji dalilin daya saka Badar ta tambayeta ko tasan Familyn Jay dan yanayin da tayi maganar ya nuna akwai wata a ?asa. A Frizlers sukayi Lunch, tana kallon Badar dake ?arasa cin abinta tace
"?azu kina tambayata akan Familyn Jay?" tasha ruwa ta goge bakinta kafin tace
"Oh yah nace kin san wani abu akansu kuwa?"
"Nace miki ai ban sani ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ta tambayeta tana yatsina fuska, Badar ta gyara zama tace
Ranar Monday da naje office din Yah Sani (Abokin Yayantane ta ne da yake Lecturing anan) kinsan na gaya miki na taSa ganinsa sunyi hoto da Jay sanda yaje Masters Uk hoton na office Winsa shine ina zuwa da na gani maganarku ta faWo mun a rai nave masa two weeks ago Jay yazo school Win nan, he was suprised yace mun wai ya akayi na sani, then i told him about your encounter kinga mamakin da yayi kuwa? Ashe Mamansa da Maman Jay cousins ne shima suna bala'in shiri sosai gurinsa ma yazo nan Zaria kwanan sa Waya ya wuce babu wanda ya san yazo dan da daddare ya shigo kuma a gidansa ya sauka da safen daya fito ma be san inda yaje ba kuma harya tafi babu wanda yace masa ya ganshi then he asked me wai waye Dad dinki a Nigeria da har Jay yace yana sonki?"

"Ban gane ba?" Afeeyah ta katseta fuskar ta na nuna alamar confusion, Badar taci gaba da cewa
"Nima abinda nace masa kenan, to cut the story short Afeeyah abinda na fahimta Mamarsa yar Jari hujja ce, Yah Sani ya gaya mun Jay personally bashi da matsala, and tunda yace yana sonki dagaske yake yi amma inda matslar take mawuyacin abune Mahaifiyarsa ta yarda ya aureki saboda a duniya idan da akwai abinda ta tsana be wuce Talaka ba. Yaranta auran Jari take musu kuma babu wanda ta Wora buri akansa Irin Jay saboda tafi sonsa duk cikinsu matsayin da yakai yasa ta tattara duk wani burinta na duniya akan matar da ze auro, ita a sonta cikin turawa ko larabawa zeyi aure ai kinsan Shahida Anchau ko?" Ta jefo mata tambaya, ruWu da tashin hankalin da ta shiga yasa dakyar ta Waga mata kanta da yayi nauyi Badar taci gaba da cewa

"To Mamansu babu yanda batayi akan a haWa auransu da Shahida ba kinga dai Abbansu kafin ya rasu yayi kuWi kamar me kuma har yanzu Mamansu kanta tana da kuWi amma wai Maman Jay ta?i, ba Shahida kaWai ba yace a Familynsu babu daga gidan da ba'ayi masa tayin aure ba amma ta?i bari ya karSa. Ki ga dai Familyn ANCHAU duk Kaduna babu wanda be sansu ba saboda tsofaffin kuWine, arzi?insu tun duniya na kwance har jikokinsu ba lallai suyi talauchi ba amma Mahaifiyar Jay ta raina su tace bataga yar da ta dace da shi a ciki ba. Ni wlh mantawa nayi ma tunranar ban gaya miki ba se yau abin ya faWo mun a rai nace masa ma zamuje tare ya faWa miki da kansa kafin ki ce hassada nake miki ko ?arya na shirya saboda na rabaki dashi".

?asa Afeeyah tayi da kanta tanajin wani abu nayi mata yawo tsakanin ?irjinta da ma?oshi ya?i wucewa yayi ?asa kuma ya?i haurowa ya fito. Wato kallon yar masu ?umbar susa Jay yayi mata saboda ya ganta fara ?al kalar madara ya sha?i ?amshin designer turare a jikinta ga Hijabin Crep yard da Ummu-Maheer tayi mata ze tsammaci irin yan Turkey Winnan ne ko Egyptian shiyasa yake sonta?
Kenan wannan ne dalilin da ya saka yake yawan kawo mata labaran ?asashen duniya idan ta nuna bata sani ba yace wasa takeyi masa? Bata manta ba ranar nan suna maganar kallon Ball da tace masa Badar na kalla a waya yace me yasa ita bazata kalla ba tace masa kawai, se yace ta ro?i Dadynta wannan Holiday Win suje Muje London ta kalli wasan sa Live har take ce masa ita Baffa ne da ita ba Dady ba kuma wace London ita da ko Aiport bata taSa zuwa ba ya ringa dariya yana cewa ta raina masa hankali kenan kallon yar Masu kuWi yake mata irin wadda Mahaifiyarsa take da burin ya aura lallai kuwa an yanka ta tashi.

"Afeeya your body is shaking, ki nutsu dan Allah ba fa na faWa miki maganar nan saboda ki saka kanki a damuwa bane ba...."
"Na fahimta Badar na gane wlh dama kuma nima ina yawan wannan tunanin a raina, Ahmad da be kaishi matsayi da suna a duniya ba Yan uwansa suna ganin ban dace dashi ba ina ga JAY wanda ba yan uwa ba na tabbata mutanen duniya kansu se sunyi mocking Winsa idan suka san yar wa ya aura, damuwata kawai Badar me yasa yasan da wannan tsarin na mahaifiyarsa ze zo gurina? Tun haWuwata dashi ban boye masa komai a kaina ba, na gaya masa Mahaifina ba kowa bane me neman na kansa ne amma se yayi dariya kawai yaga kamar wasa nakeyi, kuma banyi wani abu na ?arya da ze saka yayi tunanin na fito daga wani babban Ahali ba ko kawai kenan Surata ce ta rudeshi yayi mun kallon daidai da matsayinsa? Kenan a gidan Masu kudi kadai ake samun Yara masu Kyau da sura irina ba'a haifarsu a gidajen Talakawa?" se tayi shiru tana jin kuka yana taso mata, bata iya ri?e shi ba kuwa ta fara Badar ta mi?e hankali a tashe ta dawo kusada ita ta ri?e hannuna tana cewa
"Dan Allah ki dena kuka kinga ana kallonmu"
"Badar ina son Jay, idan na rasa shi bansan ya rayuwata zata kaya ba. Na sani ban kai koda matsayin me aikinsa ba amma zuciyata ta yi Wage ta kai kanta inda be kamata taje ba kuma shine sila, shi ya kwaWaitamun soyayyarsa irin wadda na daWe ina nema me yasa be dubi matsayi da tazarar dake tsakani mu ba ya shiga rayuwata da al?awarurrukan ?arya da ya san baze cikamun su ba ya san mahaifiyarsa nada zaSi kullum yake cemun duk abinda yake so shi take so ba zata taSa hanashi auran wata mace ba muddin yace ita yake da muradi?"

"To ai Afeeyah kinga shima Yah Sani ya faWi abinda ya sani ne kawai akan Mamanshi, zata yuwu ta canza ko kuma kamar yanda ya gaya miki ba zata hanashi auran duk macen da yace yana so ba tunda ta fi sonshi cikin yayanta doke taso farin cikinsa. Ni dalilina na faWa miki maganar nan saboda karki sake jiki kuma daga ?arshe ba fata ba ki zama disappointed, amma kamar yanda kika ce shi yasan wacece ke kuma a hakan yace yaji ya gani yana sonki ki kwantar da hankali all shall be well in sha Allah" Badar ta faWa cikin lallashi.

Afeeyah ta kife kai kan Table taci gaba da rera kuka tamkar har ranar rabuwarsu da Jay tazo, she can't imagine loosing Jay, is like loosing her whole life dan bata tsammanin zata sake moruwa, soyayyar sati uku jinta takeyi tamkar ta shekara Wari uku, da?yar ta ha?urtar da kanta ta kuma Wauki shawarar Badar da tace tayi confronting Jay domin tasan makomar relationship Winsu tunda wuri tunda dai shi zuciyarta tayi amannan da. Tabbas tana da bu?atar hakan, zata so ya furta mata da bakinsa tunanin da yakeyi akan Ahalin da ta fito sannan zata kawo maaa maganar Mahaifiyarsa taji view Winsa akai.

*Assalamu alaikum*
*Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?*

*SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu*

*Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.*

*Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.*

*A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294*
*Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita*
https://wa.link/wwvjr3
*Location Kano, tana Nation wide delivery*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 15*

A daddafe suka ?arasa exams idan kaga Afeeyah se ka Wauka jinya takeyi saboda yanda ta fita a hayyacin ta. Tun daga ranar da Badar ta bata ta?aitaccen labarin Mahaifiyar Jay ta shiga wani yanayi na tunani da lissafin yanda makomarta zata kasance. ?arin tashin hankalinta kwanki huWu kenan basuyi waya da Jay ba, zeyi mata text safe rana dare ya tambayeta ya take amma a ?arshe ze sake jaddada mata karta kuskura tace zata kirashi har se ta kammala Exam ta san koda ta kira kuma baze amsa ba ita kuma taso suyi magana, ya warware mata abinda ya addabeta a zuciyarta ko ta samu nutsuwa.

Ranar Thursday suka kammala, ?arfe bakwai da rabi suna shirin fita Ahmad ya kirata wai ya shigo Zaria yana Dogarawa lokacin, tayi kasa?e da waya tana mamaki dan gaba Waya ma ta manta da batun ze zo Waukarta yau, ita bata ma shirya kayanta ba dan lissafinta kawai se gobe Juma'a zata wuce gidan amma tunda yazo babu damar tace ya koma hakan dai dole zata shirya ta bishi su tafi dan haka suna fitowa daga Exam basu tsaya komai ba suka wuce Hostel. Ahmad ya sake kiranta akan idan babu damuwa zeje Kd yanzu ya amso wani sa?o kafin ta gama shiryawa ya dawo

"Idan ba sauri kakeyi ba ka jira kawai mu tafi tare se mu kai Badar gida" ta faWa masa, Badar ta ?walalo ido tana kallonta tace
"Ni nace miki yau zan tafi?"
"Nima ai ba yau nayi niyyar tafiyar ba saboda ya rigada yazo?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yasa dole zan tafi, ki tashi dan Allah karmu tsayar dashi" Afeeyah ta gaya mata. Dole Suka kashi kaya dan shirin da basu ?arasa ba kaWan ne, Badar nata mitar batayi sallama da Sweetynta Nurain ba kuma sunyi yau ze kaita yawo yanzu tasakata tafiya gida ita dai ta toshe kunne har suka kama hanya.

Badar da Ahmad keta hirar su ba tareda sun damu da Afeeyah ba dan daman sun saba muddin tafiya ztacehaWa irin haka shiru takeyi tabarsu idan ma daga shi se itane sedai ya gaji da magana ya kunna Radio. A gidan Hajiya Ummu Yayar Hajiya Binta ya karSi sa?on Laces ne ya siyawa Momy, a mota ya barsu ya shiga shi kaWai da ze fito Hajiya Ummu da itama zata fita daman shi take jira ta biyo shi suka fito tare.

"Au daman tare kake sa ba?i shine ka barsu a Mota Ahmad? Rowar yar tawa kakeyi mun ko kuma baka ri?eni uwa ba shiyasa ka hanasu shigowa?" Hajiya Ummu ta faWa. Ahmad ya duburburce, sam be kawo zata fito ba kuma shi be ?iyi musu tayin shiga ba sedan baya so su Sata lokaci dan yasan Antyn Ummun cewa zatayi se sun zauna sunci abinci dan shi kansa da?yar ta barshi ya fito shaf shaf Win gashi kuma yanzu yayi complicating abun.

"Wlh Mama ba haka bane, ita wannan gida zamu sauketa Fatima kuma mu wuce Kano tare. Naga rana tayine bana so mu Sata lokaci amma kiyi ha?uri bari su shigo". Yanda duk ya rikice yana mata bayani yasa tayi murmushi tace
"Karkayi kuka na yarda ba da niyya kayi ba". Ahmad yayi dariya, Badar da Fatima suka fito suka gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa wacece Surukar tata a cikinsu.

"Ki zaSa Mama" ya faWa yana shafa kai, tace
"Kowaccece a ciki Allah ya tabbatar da Alkhairi, saura Wan uwanka ya kamata shima ya bar ruwan ido haka ya fitarda mata" ta koma cikin gida bayan tace su jira tana zuwa. Hijabai ta Webo ta basu sukayita godiya. Badar data karSi ledar bayan sun shiga mota kafin Ahmad ya shiga tacewa Fatima
"Ke Hijaban Ummu-Maheer (07061838488) ne, kinga ledarta".
"Ai sun zaga duk inda bakya zato Kyau iya kyau, kasha gayunka da kuWi ?alilan a ringa zaton tafiyayye kika saka dole ki ganshi a gurin manyan mata irinsu Hajiyar nan".

Suna yan hirarrakin Ahmad ya dawo suka kama hanya. Tilas seda sukaci abinci sukayi Azahar kafin Momynsu Badar ta barsu suka tafi. A hanya Ahmad nata mata santin kirkin Maman Badar. "Ai Momy badaga nan ba gurin kirki, ita Badar ta gado" amsar data bashi kenan ta kame baki ya gaji da jan maganar shima ya kunna musu karatun Al?ur'ani ?asa ?asa suka cigaba da tafiya.

Lokaci lokaci yake kallonta yana ganin yanda ta mayar da hankali kan wayarta kome takeyi se Allah idan ta nisa kuma taja tsaki ita kaWai tayi tagumi ta kalli window. Yana so ya tambayeta me yake damunta amma ya kanne, so yake ya fara jurewa yana danne sonta ko ze samu ta fara dubansa da kimar da yake so. Bukar ya gaya masa ya bata iska, bawai barta ba tunda yana sonta amma ya koyi kamewa shima ya dena nuna mata cewar idan babu ita baze iya rayuwa ba.

Wayarta tayi ?ara, yana ganin yanda ta zabura ta duba in beyi ?arya ba har sautin ajiyar zuciyar da tayi ya jiyo. Suka haWa ido sanda ta saci kallonsa kafin ta Waga wayar. Zuciyarsa ta harba, daga yanayinta da yanda take magana a wayar dukda bajin me take cewa yakeyi ba tsabar yanda tayi ?asa da murya ya gane da Namiji take maganar. Kansa ya Wauki zafi, har wani sara masa yakeyi idanuwansa sukayi jajir lokaci Waya saboda wutar kishin data tashi ta fara ci balbal a zuciyarsa. Be san ta gama wayar ba seda yaga tana ?o?arin saka cajin wayar ta ajikin cajar motar. Murya a kausashe da irin sautin da bata taSa jinsa dashi ba ya kira sunanta kafinyace

"Ni ba shashashan Namiji bane da kina zaune tareda ni wani ze kiraki a waya ki Wauka, this should be the last time da zaki kwatanta wani abu kamar haka. Wlh kika sake sena fasa wayar idan yaso naga da abinda zaki cimun fuska kiyi magana da wani Namiji".

Tsabar yanda maganarsa ta shigeta har karkarwa jikinta ya Wauka, tunani takeyi daman Ahmad ya iya faWa irin haka? Yanda ya juye mata lokaci Waya ya firgitata ga speed daya ?arawa motar yanda kasan zasu tashi sama.

"Kayi ha?uri" ta faWa bakinta na rawa. Har suka isa Kano kuma be sake ce mata komai ba, a bakin layinsu da suka isa ya faka be kulata ba ya fita ya samu yara ya buWe booth suka kwashe mata kayanta. Be bata fuskar da zata sake masa wata magana ba, a wajen motar ma ya tsaya har seda ta sauka kafin yaja yayi tafiyarsa ya barta da bin bayansa da kallo.
A sanyaye ta isa gida kafin ta shiga dai tayi ?o?arin daidaita nutsuwarta saboda gudun tambayar meya sameta. Ta tarar da Anty Sauda da yaranta, ganinsu yasa ta sake sakin ranta musamman kuma da sahibul ?albinta ya kirata ya mata fatan sa'a akan Jarabawar da suka gama yace zasuyi magana idan ta isa gida. Wannan birkicewar ta Ahmad ce ta jirkitata amma tana shiga gida ta manta da babinsa ta shiga sabogogi sedai lokaci lokaci yakan faWo mata, yanda ya fututtuke se taji kamar Jay yana sababi, daman ance

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login