Showing 354001 words to 357000 words out of 467220 words

Chapter 119 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12166

a sanyaye saboda yanayin da tayi masa magana duk se yaji ya tsargu. Da saurin gaske Fatima ta saki robar man da take shafawa, zuciyarta na bugawa ta yafa hijabin dake gefenta ta le?o, karaf idanunsu suka sar?e, ba?in ciki, takaici tareda kunya me tsanani suka dirar mata lokaci Waya. Dama yana zaune a falon ta wuce sa amma bata lura ba? Kenan ya gama ?are mata kallo babu riga ba wucewa Waya ba har fita ta sakeyi ta bashi baya harda dur?usawa ta Wauki kaskon wuta shikenan ya gama da ita, once again Jafar ya sake cutarta kawai seta fashe da kuka ta juya ciki duk shi da Umman suka bita da kallo.

"Nagode bari kawai na wuce ana jira na ne" ya sake faWa yana mi?awa Umma Ahmad, ta karSe shi tace
"To ko a juye maka ka tafi dashi?"
Shiru yayi hakan yasa ta kwantar da Ahmad ta fita, seya Wauke shi yabi bayanta bayan daya sake kallon kofar Wakin Fatiman yana jiyo shasshe?ar kukanta dan ?ofar a buWe take. A bango ya jingina yana sauke ajiyar zuciya, Umma ta fito daga kitchen da ?aramin flask din shayi se kular data saka alalan a ciki daidai nan Baffaya shigo da sallama hannunsa ri?e da ?aramar gorar zuma ya mi?awa Umma yana cewa

"Rukayyatu tace su da zuma suke shan kunu dadynsu ya hana su shan siga nasan kuma ta ?are Allah ba baki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? rigada zuba sukarin a kunun baki Waya ba"
"Ban zuba ba, tafiya zeyi dashi ai yace baze zauna yaci a nan ba" Umman ta faWa tana karSa se yace
"Ai shikenan se ya tafi da ita dukda dai ban sani ba ko se yar kamfani suke sha, Fatiman ta fito sun gaisa ne?"

"Eh mun gaisa" ya sharara ?aryar da seda Umma ta kalleshi yaji kamar ya nitse a gurin, a gurguje ya basu yaron ya Wauki kular da fulas Win ya fita. A bakin titi har yayi niyyar yayi sadaka dashi se kuma wata zuciyar tace ?ila Baffa ya fito yana kallonsa, kar yayi masa wata fassara ta daban dan haka ya sakasu a mota ya bar gurin. Jin Hajiya ta tafi yasa kai tsaye ya doshi gida, so yake yaje ya wonawa Fatiyyah, yanda ransa ya Saci seya tabbatar nata ya ninka nasa sannan zuciyarsa zatayi fari.

Joseph manager sa da tun yana cikin gidansu Fatima yake kiransa be amsa ba ya sake kira a karo na babu adadi, a speaker motar ya saka wayar bayan sun gaisa cikin harshen turanci Joseph din yake masa magana yace
"An turo da email baka duba ba"
"Na gaya maka ka rabu dani da duk wani abu daya shafi maganar club, suyi duk abinda suke ganin zasu iya ni na gama ba zan dawo ba" Ya bashi amsa.

Tamkar me lallaSa jariri haka Joseph Win ya kwantar da murya yana cewa
"Haba Jay, ta yaya kake so ka lalata mafarkinka a a gaSar kammalawa? Jay bafa akanka a ka farayin rashi ba, kuma na tabbatar da ace Ahmad ze dawo baze taSa jin daWin abinda kakeyi a yanzu ba. Break Win sati biyu aka baka, har head of managements seda suka tayaka alhinin rashin da kayi tun da kake wa ka taSa ganin ya samu dama irin taka amma ka ringa abu kamar wani ?aramin yaro kusan sati goma kenan ka kasa cigaba ka manta da baya sannan lokaci Waya kana so ka Sarar da abinda kayi shekaru kana ginawa kayi tunani akai mana".

Seda yaja iska kafin yace
"Ka rigada kasan dama ina shirin barin ?wallo gaba Waya, da zarar kwangilata dasu ta ?are shikenan bazan karSi wata ba zan bar ?wallo saboda yanzu ina da nauyi akaina dole na kasance a tare dasu"

"Na sani Jay to amma kayi ?o?ari ka fahimci abinda nima nake maka magana akai, ba yanda za'ayi ka ajiye aiki alhalin kwangilarka da ?ungiya bata ?are ba, zasu iya yin ?arar ka kamar yanda suke i?irari sannan zasu iya Sata maka suna ta yanda duk abinda kayi a baya ze tashi a banza. Watanni shida ne kawai, daga nan kana da damar zaSar bari ko cigaba amma yanzu dai ka duba karka bari ka lalata gobenka, Ahmad baze dawo ba, dole kuma kana bu?atar abinda zaka cigaba da kulawa da amanar daya bar maka dole se kayi tunani ka shirya abinda zaka kama idan ka bar sana'arka ta yanzu ba haka nan rana tsaka zaka ce ka saki komai saboda ka rasa Ahmad ba".

"Yanzu ya kake so nayi?" Ya faWa a sanyaye saboda hango gaskiya cikin maganganun Joseph Win, cikin Jin daWi yace masa
"Ka amsa mail Win ka kuma basu ha?uri sannan ka shirya ka dawo da saurin da zaka iya komai ze tafi daidai tunda coach da manager duk suna tare da kai badan haka bama kasan da yanzu ba wannan maganar akeyi ba".

Harya isa gida yana juya maganganun da sukayi da Joseph Win, seda yayi replaying mail Win ya kira coach Winsu sukayi magana kafin ya haWa musu conference harda manager club Win kusan minti ashirin kafin suka gama. Number Farouk ya laluba yana so ya masa booking flight a cikin satin dan ya yarda yana bu?atar yin nisa da Hajiya da kowa ma ko babu komai ze samu damar yin tunani sosai kan yanda ze Sullowa komai, bega number ba. Da safen ya tuna ya bawa Amal wayar ita kuma duk sanda ta dau?i wayarsa seta goge masa numbobi haka take, seya fita ya koma mota ya Wakko Wayar wayar sa ya haWo da kayan abincin da aka bashi dan ya manta dasu.

Kitchen ya shiga ya ajiye, ya buWe kunun ?amshi me dadi ya daki hancinsa, yanda yayi fari ?afal yasa yunwar dake cikinsa ta motsa, a cup ya tsiyaya ya zuba zuma ya zauna yana sha a hankali garWinsa na ratsa shi. Sak irin wanda yake sha idan yaje shago gurin Yah Ahmad, idonsa ya kawo ?walla amma be bari sun zubo ba, ya buWe alalan kafin ya ankara dai se gashi ya lashe komai tas. Shida kansa seda yayi dariya, daya bayar daya ?wari kansa kuwa. ?akin sa ya koma ya kwanta, dake yaci ya ?oshi nan kuma sabon al'amarin ya motsa masa. Ya lumshe idanunsa, hotunan Wazu suka fara gilma masa. Yanda ta ringa giftawa a gabansa, ganin daya mata idan aka bashi pensir ya tabbatar ze zana ta tsaf ba tareda kuskure ba.

Yayi juyi ya koma rubda ciki, so yake ya kori tunanin amma ya kasa. Ya zata idan mace ya haihu jikinta yana lalacewa ta canza kamanni, shekarun baya be taSa ganinta a yanayin daya ganta yau ba. Amma ze iya kwatanta komai da awon da hannunsa yayi waccen ranar daya fara rungumarta a gidan Anty Sauda sedai ta goge masa hadda yau Win, abinda ya gani ya zarce na baya burgewa da kuma Waukar hankali. Yah Ahmad ya taSa faWa masa duk sanda ta haihu ?ara kyau takeyi, jego yana karSar ta tabbas ya shaida hakan domin yana zaune lafiya ya kwashi ?afarsa yaje ya gano abinda yake neman hana masa zaman lafiya. Daya kasa ya?ar zuciyarsa ta saki tunanin seya tashi zaune a fili ya furta

"Matar Yah Ahmad ce, mallakinsa ce har abada bani da sauran gurbi a gurin". A hankali duk wani abu daya yun?uro masa ya fara sauka, Sacin rai ya fara ?o?arin maye gurbin farin ciki da nishaWin da tunanin baya ya fara saukar masa, da baccin ya?i yuwuwa se kawai ya shiga yayi wanka ya sake fita har sannan kuma beji motsin Fatiyyah ba.

FATIMA

Seda tayi kuka ta gode Allah kafin ta saka kaya ta zauna idanu sun kumbura ko abinci ta kasa ci. Umma bata ma bi ta kanta ba balle ta nuna tasan me takeyi ta cigaba da sabgoginta, seda Anty Sauda taso ta tarar da ita ta rafka tagumi ido sunyi luhu luhu take tambayar lafiya.

Anty Sauda ta gama sauraron meya faru tace
"Allah ya rufa Asiri, yanzu dai ina su Laylan? Ko sun ri?e su acan ne"

"To waya sani ne? Idan ma sun ri?e su ai babu komai se mu bisu da fatan Allah ya raya su shikenan dama Wa ai na gidan uba ne" Umma ta faWa se ta fashe da wani kukan tana cewa

"Wlh bazan yarda ba seya maido mun da yarana ai babu wanda yace ya ri?e su".

"Zuwa zakiyi ki sake cakumarsa da faWa kenan?" Umma ta faWa tana kallonta, ta Wauke kai tace
"Ni a ina na cakumeshi? Se kace wata yar tasha? Yarana kawai nace ya bani ai bani nace karya haifi nasa ba balle yazo yana yiwa mutane iko akan wanda bashida ha??i dasu"

"Izgili kike masa kenan? Ai ke Win da Allahn ya baki ba finsa kikayi ba kuma shima da be samu ba ba ?insa Allah yake ba. Tunda baki da hankali baki san me zaki faWa ba in sake jin kin tayar da maganar yaran nan wlh se ranki ya Saci wawiya kawai ki ringa abu se kace wadda bata yarda da ?addara ba" Umma ta faWa cikin hasala kamar ita akayiwa gorin haihuwar. Fita tayi daga Wakin, Anty Sauda ta kalleta tace

"Ba zaki canza ba, daga dawowar ki jiya har kin fara janyowa tana miki faWa. Me yasa ke ba zaki Wauki komai da sau?i ba a rayuwa Afeeyah? Wlh Jafar ya wuce wula?anci a gurinki yanzu domin kuwa ya cika Wan halak yayi muku abinda ko waWanda suka fito ciki Waya da Ahmad Win basuyi muku ba. Jafar be bar yayanki sunyi maraici ba, ya ajiye komai nasa ya tsaya akanku duk yanda mahaifiyarsa take hanashi amma be bari ba, tunda Ahmad ya rasu sau nawa Salim da suke uwa Waya yazo ya zauna yayi hira da yayanki sukayi wasa da dariya? Sau nawa sarki ya Wauke su ya fita yawo dasu? A cikinsu waye yake kaisu makaranta ya kashe lokacinsa da komai ya zauna dasu har se sunyi bacci sannan?"

Shiru tayi bata ce komai ba, Anty Saudan taci gaba da cewa
"Kar ma ki yaudari kanki ki Wauka saboda ke yazo gidan nan" se ta Waga kai da sauri ta kalli Anty saudan, ta haWe rai tace

"Eh, tuntuni nasan abinda ?aramar ?wa?walwarki take raya miki kenan akanki yake waWannan abubuwan to ki sake tunani. Ina da ya?inin ke baki kai wannan tasirin da Jafar ze lalace saboda ke har ya ringa ?etare unarnin mahaifiyasa ba, idan ma kina tsammanin tsohuwar ala?a ce ta saka yake hidima dake da yaranki to ba haka bane. Kin fi kowa kusanci da Ahmad na tabbatar da ke zaki bayar da labarin tarin ?auna da sha?uwar da take a tsakaninsu hakan ya isa ya baki amsar damuwar sa akanku, ba saboda ke yakeyi ba saboda amanar Wan uwansa yakeyi"
Tayi ?asa da murya tana kallon Fatiman tace

"Idan ma kina da muradin farfaWowar tsohuwar ala?a ke zakiyiwa kanki ya?i domin na tabbatar ya rigada ya wuce wannan wajen tuntuni" tana gama faWa mata haka tayi wani murmushi daya ?arasa tarwatsa zuciyar Fatima da maganganun Anty Saudan suka daskarar, ta ringa binta da kallo ba tareda ta iya cewa komai ba. Ita kuwa kamar ma bata ce wani abu ba, kwanukan abincin da bata taSa ba taja gabanta ta buWe ta fara ci tana kallonta har sannan kuma tana mata murmushi irin me ?ular da mutum Win nan. Yini guda sur maganganun Anty Sauda sukayi ta nu?ur?usarta.

Wane ma irin abu ne haka Anty Sauda har zatayi tunaninsa? Ta yaya zata ce wai tana tunanin farfaWo da tsohuwar ala?a? Ala?ar da ta daWe da mutuwa an binneta har labarinta ya shuWe a bayan ?asa dan daman batayi yaWon da zata bar baya me tsayi ba. Tunanin ya sake takurata, daga ?arshe cike da tabbatarwa ta sake jaddadawa zuciyarta ita ta Ahmad ce, yanda ya bar duniya ya tafi da duk wani muradi da shau?i na rayuwarta.

Bayan sallar isha'i tana kwance ta jiyo hayaniyar su Layla. Bata ko Waga daga inda take ba har seda Amal ta shiga da gudu ta faWa jikinta tana cewa
"Momy dama nan gidan kika dawo?"
"Waya kawo ku?" Ta tambayeta bayan data tashi zaune, Amal Win tace

"Uncle Salim ne, Dady ne ya Wauko mu daga Islamiyya da wuri yau shine ya kaimu gidan Momy yanzu kuma tace uncle Salim ya kawo mu gurinki, yana waje yace kije ku gaisa".

Hannunta ri?e dana Amal Win bayan data saka Hijabi suka fita, a falon tsakar gida ta tarar da Salim Win suna magana da Umma Ahmad na hannunsa suka gaisa Umma ta fita ta basu guri.

"Ya ?arin hakurin mu" ya faWa yana kallonta, ta kalleshi itama bata amsa ba ta Wauke kai gefe saboda yanda yake mata wani kallon ?urilla tamkar taci masa bashi. Yayi murmushi kafin ya mi?a mata wata nannauyar envelope dake gefen sa ta karSa tana juyata a hannunta jin da nauyi.

"Alhaji ne yace a kawo muku, kiyi amfani dasu ayi musu siyayyar makaranta. An rigada an biya school fees na manto tellers Win ne a gida amma gobe idan direban da ze ringa kaisu ze zo ze taho da su, ga sa?o nan babu yawa kuma" ya nuna kwalayen caprisone da fresh yo se festo biscuit.

Murya babu amo tace
"An gode, Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da "amin" kafin sukayi shiru na kusan minti biyu, jin be sake cewa komai ba yasa ta yun?ura zata mi?e ya dakatar da ita yana mi?a mata wayar sa yace

"Amm, Wan sakamun lambar wayarki mana. Na ringa kira ina jin yaya kuke".

Kallon tara saura kwata tayi masa, Salim Win da tsayin shekaru takwas na auranta zata iya irga sau nawa suka taSa gaisawa, tunda ta koma gidanta bayan Ahmad ya rasu sau uku ya taka ?afarsa shima duka da dalili ?awayen Momy ya kai sukayi mata gaisuwa shine saboda rashin ta ido irin ta mutum yanzu zece ta bashi lambar wayarta ya kirata yace mata me?

*ASSALAMU ALAIKUM*
*Matan kwarai matab albarka ina gaisuwa. To kunsan dai ba iya shafa mai fata yai kyalli shine cikar kyawun mace ba, a ganki dumur-mur, jiki duk tsoka jiki duk laushi ko ina oga ya kama yaji shi tibis shi ne magana.*

*Ina farin cikin gabatar muku da ingantacciyar SABAYA wadda zata cike miki gurbin wannan ramar ta kuma tabbatar miki da mafarkinki na zamtowa matar sakawa a gaban mota*

*Kiran waya kawai zakiyi ko chat, a tuntubi Maman khadijah mai garin kunun sabaya, tana Palladan anguwan Fulani Zaria Kaduna state tana kuma aika sa?o duk inda kuke a faWin tarayyar Nigeria, kar a manta siyan na gari mayar da kuWi gida*

*Phone no.-08033411249 OR 07037777442*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 30*

Wani iri ta ringaji bayan da suka kwanta, Amal na ma?ale jikinta dan Ahmad a gadonsa ta sakashi itada yaran suka kwanta a babban gadon. Lokutanbaya ta ringa tunawa yanda wataran Amal zata dasa rigimar ita tare dasu zata kwanta da sauran sunji haka suma suce ai nan zasu kwana, idan tayi masifa Ahmad yace ta rabu dasu, yana yawan nanata mata
"Komai na rayuwa lokaci ne Fatima, idan ma mun rayu dasu har girma akwai lokacin da ko an ce suzo su kwanta tare damu zasu ce Aa, idan kuma mutuwa ta Wauke mu da wuri kingaba zasuji babu daWi ba duk sanda sa'anninsu suka basu labarin sunyi bacci tare da mahaifansu".

Har wanka wani lokacin yi musu yake koya dur?usa su hau bayansa ya ringa musu doki idan tayi magana yace wata rana ba zeyi ba. Tunanin yasa sababbin hawaye suka Salle mata, ta ringa share su daga kwance, ta yaya ma zata bari a rabata da yaranta bayan a yanzu bata da kowa se su? Maganar da sukayi da Baffa kafin ta kwanta ta tsaya mata a rai sanda ta bashi kuWin da Salim ya kawo ya gaya mata sunyi magana da Al?ali, ya gaya masa sun bar mata ri?on yaran daga nan har zuwa lokacin da Allah ze sake fito mata da miji tayi aure zasu karSe su.

Ta sake rungume Amal a jikinta tana shafa kan Layla dake gefenta Nayla kuma ta Wora ?afafunta a kan jikinta can bakin gado ta saka kanta, zata ha?ura da komai saboda su koda hakan yana nufin ?are rayuwarta a gida ta zaSi hakan akan dai ace za'a rabata dasu. To daman me yayi saura a zuciyarta yanzu? Bata zaton akwai wani lungu da soyayyar Ahmad bata cike ba da har wani ze samu gurbin da ze zuba tasa.

Aure ko wani abu daya dangance shi baya cikin lissafin ta, Ahmad ya tafi da komi, shi kaWai take so shi kaWai zata iya rayuwa irin ta aure dashi zata kame kanta har zuwa lokacin da rayuwarta zata ?are ta tarar dashi su Wora daga inda suka tsaya, shine mijinta a duniya kuma shine mijinta har lahira da yardar Allah. Haka ta kwana tana sa?a da warwara, ta ina zata fara? Ya rayuwarta data yaranta zata kasance da hannu Waya babu miji su kuma babu mahaifi?

Idan zuciyarta tayi ?o?arin raunata se tayi saurin ?arfafa ta da cewar dole ta koyi yanda zata tsayawa kanta ta kuma tsayawa yaranta domin gobensu tayi kyau rayuwarsu ta inganta. Yaranta mata ne suna da bu?atar kulawar uwa, ba zata taSa yarda wani abu ya shiga tsakaninta dasu ba, raunin da zata nuna kuma shine abu na farko da ze bayar da damar da za'a cimmata har a iya yin galaba akanta a tarwatsa mata duk wani shirinta akansu, dole ta jajirce tana kuma da ya?inin ubangiji ze kama mata.

Washe gari tun Asuba suka tashi, kafin bakwai ta gama shirya yaran tsaf tayi musu abin kari Umma na tayi mata tsiyar yanda ta zage ko tunanin jikinta batayi sedai kawai tayi murmushi. Bakwai da yan mintuna suna tsaka da karyawa suka jiyo horn Win mota daga waje, Amal ta zabura ?iris ya rage ta zubar da shayin gabanta Fatiman ta janye shi tana mata tsawa.

"Motar Dady ce" Amal Win ta faWa kamar zata tashi sama. Fatima ta harareta tana goya mata jakarta tace
"Dado ba dadi ba, ki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login