Showing 216001 words to 219000 words out of 260999 words

Chapter 73 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

kawai kiyi abunda ya dace don ki ceci kanki, nabarki lafiya afusace ya juya zai bar dakin har ya kusa fita karaf idanuwanshi suka sauka akan parveen dake kwance saman carpet tana yin bacci, Arude ummi ta furta yanzu zan maida ta saman gado, bansan ya akai ta faWo ?asa ba wani Wan iskan kallo big guy ya watsa mata.

Kafin ya maida dubanshi ga batul ke ina yar uwarku take? ya akai naga ku huWune? Where s hannah !

Sai daya ambaci hakan batul ta tuna da babu hanna acikinsu, waige waige ta soma yi jikinta na rawa tace bansan a ina take ba, tare da ita muka nufo dakin aunty ummi, ni na ru?o hannunsu ita da Parveen bansan ta kufce min ba, dama aruWe take

GyaWa kanshi yai okey, wuce kije ki kwanta, zanje na nemota ya faWa tare da juyawa ya kalli ummi dake ta rawar jiki ina ?ara jaddada maki kada ki bari yaran nan su wayi gari babu lafiya, idan kunne yaji jiki ya tsira yana fadin hakan ya haura ?afa yabar Wakin.
Fitar shi keda wuya, Ummi ta Waure fuskarta tamau babu annuri, ranta ya 6aci matu?a, hankalin batul ba ?aramin tashi yai ba ganin tana tunkarota, girgiza kai tadinga yi tana nufar bango harta kure mashi,
 Dan Allah kada ki ta6ani, bani da lafiya... da?yar ta furta maganar,
 Ni ki ka kai ?arana a wurinsu? Yaushe kika fita daga dakin munafukar banza, harni zakija ma bala i ina zaman zaman lafiyana? Kinsan wacece ni? Don ubanki!

Girgiza kai batul tayi tuni hawaye sun wankan fuskarta aunty ummi kiyi hakuri bazan ?araba, dan Allah kada ki ta6ani
Tsawa ta daka mata kashe ki zanyi, kinyi kuskura batul da kika gaya mashi abunda ya faru tsakanina daku, wallahi sai kinyi danasanin sanina da kikayi, don kuwa daga rana irinta yau bazaki ?ara dariya ba zan ?untata maki har sai kinji kin tsani kanki

Fashewa batul tayi da kuka mai tsuma zuciya, saboda rashin imani ummi ta sanya hannu ta sha?i wuyanta tamkar zata kashe ta,
 Jibarki dallah, jahila dake, bakisan komai ba sai cin abinci da bacci, ni ban ta6a ganin da?i?iya ba irinki

 Batul ! Batul! Meyasa kike kuka ? Jin muryar Parveen yasa ummi yin saurin sakin wuyan batul, jiki ba ?wari ta sulale ?asa tana cigaba da yin kuka

 Kiyi min shiru idan kika bari wani yaji wallahi saina na?asa ki wawuya da sauri batul ta haWiye kukanta, baiwar Allah hada sanya hannu ta share hawayen fuskarta.
Shu umin murmushi tasaki kafin ta juya tana kallon parveen data farka tana faman mutsustsuke idanuwanta
 Ke tashi ki koma saman gado ki kwanta muryar ummi ce ta fargar da Parveen ta ware idanuwanta sosai akan fuskokinsu
Muryarta da kasalar bacci tace batul make faruwa? Meyasa kika zauna a ?asa ? Tai maganar tana kokarin mi?ewa da niyar taje wurin Batul, ummi ta dakatar da ita cewa nayi kije ki kwanta saman gado, babu abunda ya sameta, kaya zan bata ta sanya ajikinta jiki asanyaye parveen ta nufi gadon donta kwanta sai dai hankalinta bai kwanta ba da yanayin data riski batul
 Parveen ki kwanta kiyi bacci, lafiyata ?alau, yanzu aunty ummi zata bani kaya in canza na jikina sai inzo mu kwanta a gadon ajiyar zuciya parveen ta sauke jin batul tayi mata magana, hayewa tayi saman gadon ta kwanta batare data rufe idanuwantaba.
Ta6e baki ummi tayi tare da mayar da dubanta kan Batul, badan taso ba tace shashasha, Ki jirani in dauko miki kayan cikin sanyin murya batul tace toh
Wuce wa tayi cikin Wakin can inda katafaren closet dinta yake, ta bude ta dauko jibgegiyar sweater tare da dogon wando, ta haWo da duvet, ta nannaWosu ta dawo inda batul take a zaune ta wurga mata su saman jikinta
 Salon kuma kiyi min ?azanta, ni bana sharing kaya da wani don yazamarnin dolene ta faWa tare da juyawa ta nufi gaban mirror inda ta daura A.c remote ta kashe ta gaba daya, ta kunna masu room heater, duk don saboda gudun kada gobe aji basu lafiya, shiyasa tayi hakan.
Mi?ewa batul tayi hannunta ruke da sweater din, ta zame hannun doguwar rigar jikinta, da dabara ta zura sweater din, tayi mata girma, haka wandonma yayi mata faWi, ahaka ta sanya su, kafin ta cire rigar jikinta, anan ?asa tabarta, ta nufi saman gadon ta haye gefen parveen ta kwanta, ta lullu6e masu bargon su dukansu, kafin ta rungume parveen a jikinta, duk don ta samu sau?in raWaWin da take ji, ta tsorata da ummi kalaman da tayi mata sun tsaya mata arai, fargabanta kada ta kashe ta, tuni idanuwanta sun cicciko da ?walla
Cikin muryar raWa parveen take yi mata magaba batul tayi maki wani abu ko? Ni naji ajikina da?yar ta iya furta kiyi shiru parveen kada tajimu, ni batayi min komai ba, bana jin daWin jikinane
Sautin kuskus din da suke yi ne yaja hankalin ummi ga kallon bargon da suka lullu6a dashi atsawa tace kada in kuskura in ?arajin maganarki! Ko tari bana sonji tsit sukayi shiru suna faman ?an?ame junansu .........





*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'?*



Idan muka koma 6angaren Hajiya saratu data gar?ame kanta acikin toilet, tsoro da fargaba sun hana ta sukuni, ta haWa uban gumi zufa ta ko ina take tsastsafo mata, ga wani takurarran bacci daya addabi idanuwanta, ta rasa ya za ta yi, ta kasa tsaye takasa zaune, sai zarya take yi acikin toilet, jin shiru tsit babu sautin komai daga waje hakan yasa tayi tsammanin ko dai jami an sun kashe macijin ne, cikin sanWa take yin tafiya tana tunkarar toilet door, ta ru?o handle din ?ofar ta buWeta, shigowa Waki tayi ta nufi wayarta dake ajiye saman bedside drawer takai hannu ta Wauke ta tana ?a waige waige duk tabi ta ruWe.



Layin pravin ta danna ma kira, kusan sau uku bai Waga ba, hankalinta ashe take fadin pravin ka Waga kirana mana


Sake kiran layin tayi, a lokacin da kiran ya shigo mashi yana a kwance saman shimfiWeWWan gadon hajjaty, sleeping dress ne ajikinta, shi kuma shorts ne babu riga, ya rungumeta a kirjinshi, sun manne ma juna, duvet din daya lullu6a masu iya saitin kafaWunsu ya tsaya.

Bacci ya ?aura ce ma idanuwan hajjaty, tun da tayi tozali da narkekan macijin nan, lallashinta yake yi duk don ya samu ta kwantar da hankalinta.

 Pravin wayarka fa tana ringing yakamata ka duba me kiranka

 Nasan wa ke kira na, bai wuci hajiya saratu bace, ta gama ci min mutunci shine yanzu take kirana saboda ta tsorata da ganin maciji, wallahi ba zan je ba, nafi so taji a jikin ta

Muryar hajjaty ?asa ?asa tamkar me yi mashi raWa ta furta please, matarka ce, yakamata kana darajata

 Ni ma ai batasan darajata ba, saratu bata girmamani, tayi min gori ta gaya min maganganun da suka ?ona min rai, sau?in ma ba ita ka Wai bace Ina dake

Lumshe mashi ido hajjaty tayi,
Yaci gaba da cewa kina ?aunata tsakani da Allah, baki ta6a guduna ba, kin rabu da kowa naki kin biyoni Nigeria, a zaman da mukayi dake ni baki ta6a yi min laifi ba... ?ayataccen murmushi tasakar mashi.

 Ina fata kai ma ba zaka ta6a guduna ba, Kuma ba zaka ta6a yi min laifi ba, pravin bani da kowa a halin yanzu Allah ne gatana sai kuma kai, dan Allah ka ru?e min amana kada ka aikata abun da zaiyi silar rabuwar mu, ka ji tsoron Allah a dukkan lamuranka na rayuwa, idan kana tunawa da mutuwa zaka ?ara jin tsoron Allah, bana so wata rana muyi abun da zamu yi danasani arayuwarmu...

Bai bari ta ?are maganar ba yai hanzarin katse ta my woman, bansan yaushe kika fara yin wa azi ba, idan ban manta ba, Ni ne na koya maki alwala ko

Dariya ta saki jin abunda pravin yace, kafin ta ?ara cewa wani abu ya rigata fadin muyi bacci please dare yana ?ara nutsawa da shagwa6a hajjaty tace ni dai ka tafi Wakin matar ka, ita yakamata ace kana atare da ita bani ba

 Bana so in bar ki ne saboda na lura haryanzu jikin ki bai daina kerma ba

 Amma itama saratun ai tsoron take ji, tana bu?atarka agefenta, pls ka tafi wajenta, Ni nafiso kana kamanta adalci a tsakanin... bai bari ta ?are maganar ba, yai saurin haWe bakinsu, ya zura hannayenshi biyu cikin rigar baccin jikinta, sarrafata ya soma yi cikin ?an?anin lokaci ya fara caza mata kai, yayi mata hakanne don ya mantar da ita zancen tafiyar da take yi mashi, kuma yaci galaba akanta, bai rabu da ita ba har saida yaji ta fara yin bacci tukunna ya ?an?ameta.

Phone dinsa sai ringing take yi, tana daga can gefe daya saman mattress din, a hankali ya raba jikinsa daga nata.

Ya laluba hannu ya dam?o wayar, murmushin mugunta ya saki kafin ya Waga kiran.

Ko sallama babu hajiya saratu tace pravin ina ka shiga? Ina ta kira baka picking! Ba zaka dawo daki ka kwanta ba ne ?

Tun daga kan muryarta ya fahimci babu natsuwa atare da ita
 Me zan dawo nayi maki? Ni da bani da amfani awajenki ?
Muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace kaga ni ba wannan na tambayeka ba, ina son ganinka ka, pravin, hankalina ba akwance yake ba, nasan kaga abunda ya faru Wazu

Tuntsirewa yayi da dariyar mugunta, ran hajiya saratu ya 6aci matu?ar masifa ta soma zazzaga mashi sai da tayi mai isarta tukunna ya katse ta da cewa saratu kenan, kefa da kanki kikace nine Wan kwali ke ce hula, hakan na nufin kece namiji ko? To meyasa kike neman mace donta baki kariya? A tunanina ni yakamata inji tsoro bake ba, shi namiji da jarumta aka san shi bada ragwantaka ba !

Takaicin duniya ya ishi hajiya saratu, cikin lalama tace pravin dan Allah ka dawo Waki, idan saboda abun da na fada maka ne ya 6ata maka rai, zan baka ha?uri

 Bana bu?atar ha?urin ki saratu, lokacin daya dace ki lallasheni ki tarairayeni ki bani hakuri bakiyi ba till now da bu?atar kan ki ce ko? An gaya maki ni shashashane bansan ciwon kaina ba ?

Shiru bata tanka mashi ba, kuma tana sauraronshi.

 Ko gobe kada kiyi tunanin zan dawo gida, ni yanzu haka ma gani akwance tare da wadda tafi ki iya tarairayar miji..... tsawar da ta daka mashi ce ta sanya shi yin shiru, tamkar zata fasa mashi screen din wayarshi ya isa haka! Ya isa! Kada ka ?ara maimaita min maganar da kayi idan ba so kake ranka ya 6aci ba...... bata ?are maganar ba, yai rejecting kiran, Ya jefar da wayar saman mattress, Ya janyo hajjaty a jikinshi, ya daura hannunshi saman sumar kanta, har cikin ranshi yana ?ara jin ?aunarta, bai da tamkarta a duniyar nan, saboda kyautata mashin da take Yi, yana matu?ar ?aunarta, kiss ya manna mata saman forehead nata, kafin ya cusa kanshi gefen wuyanta, ?amshin turarenta ya daki hancinsa ahaka bacci yai awon gaba da shi.

Jefar da wayar hannunta tayi saman gado, ranta ya 6aci matu?a pravin ya ?ona mata rai, kishine da ita, gani take kamar dagaske ne abun da ya faWa mata yana can shida wata suna she?e ayarsu, kokwanton maganarshi take Yi, ta riga ta yarda da pravin tasan bazai Iya cin amanarta ba, wata kil ya faWa mata hakanne don ya huce raWaWin abunda tayi mashi.

Damuwace ?arara akan fuskar hajiya saratu, adaddafe ta nufi gado ta haye ta kwanta idanuwanta suna fuskantar ceilling, babu alamun zata runtsa adaren Yau.


*Hajiya Turai=ؔ?*


Safa da marwa take Yi acikin Wakinta, Hannunta ru?e da wayarta, night gown ce a jikinta.

Fuskarta tayi jawur tamkar wadda tasha kuka, musamman kumatuntu, green eyes dinta kuwa sun ciza launinsu, tarasa ina zata tsoma ranta taji daWi, since wuraren ?arfe goma take kiran layin dr.jazz babu alamun zai Waga, gashi har dare ya nutsa bai dawo gida ba, ta kira layin Sir mubarak kusan sau talatin shima Bai daga ba tamkar ta fasa ihu haka take ji.

 Mom kamar daga sama taji an ambaci sunanta, tsabar ruWi sai taji kamar muryar jazz ne.

A firgice ta juyo don ganin wanene, Yana daga tsaye bakin ?ofar Waki, cikin shiga ta kayan bacci ya zura hannayenshi cikin aljihun wandonshi, matashin saurayi ne kamanninshi sak dana Sir mubarak.

 Ibad kai ma baka yi bacci ba ? Muryarshi da kalasa ya furta How can I sleep, Mom? Jazz hasn t come home yet. na jaraba kiran layukan wayarsu duk akashe, bansani ba shi jazz ko aikin kwana yake yi a asibiti, nazo ne naji ko sun faWa maki meya hana su dawowa gida ?

Ta lura da yanayin shi tsantsar damuwace akan face dinsa, batayi mamaki ba saboda ?aunar da suke yi ma Jazz, sun dauke shi tamkar sha?i?insu

 Ibad, I don t know why they haven t come home yet, I ve been trying their phones since 10 o clock, and nobody is picking up. I m really worried, inajin fargabar ace wani abun ne ya faru da su tuni idanuwanta sun ciko tab da ?walla.

Ru?o hannunta Ibad yai haba mommy, kada ki zubda hawayenki please, ki kwantar da hankalin ki, Everything is going to be okay. They ll come home safely.

girgiza mashi kai tai basu ta6a yi min haka ba ibad, daga jazz din har daddyn naku, kullum ne idan zasu kai dare awaje, sai sun kira awaya sun faWa min, amma yau shiru babu wanda ya tuntu6eni muryarta na rawa ta furta maganar, tausayinta duk ya kama ibad, jinta yake yi tamkar mahaifiyarsu data rasu.

Gyaran muryar da akayi masu ne Ya janyo hankulansu ga duban shi, tafiya yake yi yana tunkarosu tamkar baisan da su ba, Hannun shi ru?e da apple laptop dinshi, daga shi sai short a jikinshi, ?irar jikinshi da komai kalar na daddynsu ne, sai dai shi yafi ibad da daddynsu hasken fata nashi chocolate colour ne mai kyan gaske, sumar kanshi tasha gyara luf ta kwanta saman bayanshi, Yana da kirar karfi kamar Wan wrestling, wani irin daddaWan kamshin turarene ke fita sako da lungu na jikinshi, komai nashi da aji yake yin shi, mutunne shi maiji da kanshi, baida wasa a aikinshi, yana ru?e da mu?amin CEO na babban Companynsu dake a ?asar canada.

Kafafuwanshi suna asanye da slippers, magana ya somayi tamkar baisan furtata

 Mom, yanzu major ya kira ni awaya, ya fadamin suna atare da jazz wani aiki ne mai muhimmanci ya tsayar da su, so they couldn t come home tonight. But they ll be back early tomorrow

Ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta taji dadin jin hakan, Murmushi Ibad ya saki yana fadin mun samu nutsuwa yanzu, Mom ki koma daki ki kwanta, ?arfe 3 fa ta buga, gobe nasan zakiyi ramuwar bacci, murmushi tasakar mashi bari na koma ciki, mu kwana lafiya My Sons, ta faWa tare da juyawa ta nufi Wakinta, saman gado ta haye idanuwanta suna fuskantar ceilling, bakomai take jimawa ba face kwanan da za ta yi ba tare da mijinta ba, sun saba faranta ma junansu kafin su runtsa yau kuma babu shi atare da ita, ga kuma Wanta da take jin kewarshi,
Pillow ta janyo ta rungume a ?irjinta.


 Babban yaya nan fa ba kasar canada bace, taya zaka dinga yi mana yawo da short a tsakar falo? Kai ala dole ga bature ko? Ko kunyar mommy baka ji, Ibad ne ya fada da zolaya.


Ko kallo bai ishe shi ba, saman Sofa mai mazaunin mutun uku ya kishingiWa kanshi saman sofa hand, Ya daura laptop dinsa saman flat stomach dinsa.

In a husky voice ya furta ibad! Ina bu?atar abun sha

Ru?e qugu Ibad yai sam baya gajiya da zolayar yayan nashi duk da tazarar shekarun dake atsakaninsu, domin kuwa Zaki ba ?aramin mutun bane

 nan fa ba canada bace, Nigeria ce daddy Ya hana ana aikena idan dare yayi yamutsa fuska Zaki Yai Ibad ya fara haya?a shi.

Calmly ya furta Don t make me repeat myself kama kunne ibad yai sorry big bro, na tuna kada ka hanani silallan kashewa ya fada tare da nufar frigde Ya bude ya dauko mashi coke mai sanyi, ya dawo Ya daura mashi saman sofa table din gabanshi.


 Babban yaya gashi na kawo, Ni zan cire maka murfin? banza yai mashi tamkar baiji me yace ba.

Bottle opener yaje ya dauko ya zu?unna agaban table din Ya soma kiciniyar bude murfin, sai nishi yake yi, sam bai saba da wahala ba, ibad mugun sangartacce ne yayanshi ya 6ata shi da hutu, dogon tsoki zaki Yaja, ya yunkura ya mi?e Ya ajiye laptop din gefe Waya, ya kai hannu ya kar6e coke din da bottle opener din, sau Waya ya murWa murfin ya cire.

Washe baki Ibad Yai babban yaya ba za ka yi bacci ba? kana bu?atar hutu fa, kai kullum aiki baka gajiya !

Banza yai dashi baice komai ba, a tsanake yake kur6ar coke din me sanyi, Ibad ya ?ura mashi ido yana kallon bakinsa har haWiyar yawu yake yi.

Janye coke din yai daga bakinshi, Ya galla mashi harara meyasa kake kallona kana haWiyar yawu kamar wani maye? Idan so kake kasha bakasan inda zaka dauko bane

Kwa6e mashi fuska ibad yai Ai ni nafi so kasha


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login